-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Sababbin Sakonnin Kalaman Soyayya

Sababbin Sakonnin Kalaman Soyayya

Sababbin Sakonnin Kalaman Soyayya 

Samun ki a rayuwata ya bani k’warin guiwar tunkarar matsalata da samun nasara a kan dukkan abun da na sa a gaba.

 Kulawarki a kaina na k’ara min jarumta, soyayyarki a gare ni na sanyawa na ji ni a matsayin cikakken mutum. Nagode mosoyiyata, ina alfahari da samun ki a rayuwata.

A gare ki nake samun bargo, a dukkan lokacin da sanyi ya rufe ni.

 Ina samun tsaro, a dukkan lokacin da hatsari ya tinkaro ni. Ina samun farin-ciki, a dukkan lokacin da damuwa ta lilliɓe ni.

 Fatana da burina mu mutu tare mu tashi tare mu rayu tare a gidan Aljanna. Ina Son Ki Mai sona Fiye Da Yadda Nake Son Kaina.


Ina son ki kuma zan cigaba da son ki na tsawon rayuwata mai sona. Ni da ke tamkar k’ashi ne mai k’warin da bana fatan ganin ranar da zai yi targaɗe balle har ya kai ga ya karye. 

Ina Son Ki Daga cikin biliyoyi da Miliyoyin yammata na zaɓo ɗaya tamkar da dubu. Tabbas na yi nasara na samun ki a matsayin mosoyiyata abun alfaharina. A tsawon lokacin da zan rayu ina numfashi, ina son ki so mara iyaka.

Ina bukatar tallafinki cikin wannan babbar rana mai dauke da tarin sirrikan albarka nake neman agajinki domin kibudemin kofofin zuciyarki hakan shine zaisa naji dadi wajen isar miki da Sakona

Aminci agareki tare da gaisuwa mai fitowa cikin masarautar fadar zuciyar dake miki soyayyar Gaskiya

Hakikanin Ainihin suffar motsin bakina yana juyawa tare da murmushin kallon halittar kyawawan Madaidaitan labban Bakinki

Farin cikine mai fitowa daga sansanin tsakiyar ruhina yan zubewa a gabanki domin nuna isa da martabarki na mukamin sarautar gimbiyar yan Mata

Jarumta da hikimar iya launin bakinki wajen iya murmushin alfarma shine jagora wajen sanya zuciyata kamuwa da shauki na Musamman

Kin Halittu: surar jikinki tana burge zuciyata hasken sinadarin shaukin murmushin fuskata Tananan tare da kyakkyawar halittar surar Jikinki

Fararen hakoranki sun jeru daidai misalin kallon burge idanuna INA sonki

SO shine fitilar dake haskake duhun kowane irin Ruhi sanna shine wakilin dake wakiltar damuwa mai gusar da dukkan wani farin ciki a rayuwar kowace irin Zuciya

Iya kallonda nake yiwa kyakkyawar halittarki ya isa ya gamsardani cewa ke kykkyawace kuma wadda babu irinta a duniyar masoya. 

Kwalliya, tafiya, kwalisa sae yan mata masu aji suke iya yin wanda zasu burge namiji, amma kuma ke ba iya burgewaba har numfashi take kusa da dauka domin dacewarsu.

I luv yuh mah abar kaunata soyayyarki abun alfaharice agurina domin babu abunda nake nema in rasa idan na farin cikine.

 Masoyiyata Allah ya halicci zuciya be domin soyayyah zan kasance Mae yiwa soyayyarki bauta tamkar bawa agareta, ina mai matukar godiya ga Allah da hotemin ke amatsayin masoyiya.

 A duniya duk Wanda yasameki a matsayin masoyiya wallahi yagama yin babbar nasara a rayuwa, domin kin kasance mace wadda ta mallaki duk abunda wata mace takeda shi, samunki ba karamar nasara bace.

 So dayawa wasu masu yiwa soyayya mummunar fahimta sukance mace batada tabbas akasin basu samu wadanda ke kaunarsu da gaskiyaba, nikuma inada ke kuma nagamayin babbar sa'a a rayuwata, ke macece wadda babu irinta a rayuwa.

 Haskenki tamkar hasken farin watane mai haskaka sararin samaniya Wanda take dauke wani sanyi mai ratsa jini da jijiya, haskenki tamkar hasken zinariya Wanda yake sheqi da walwalin haske marasa misaltuwa.

Muryarki tamkar sarewa ce wadda idan ana busata tamkar anayinta ne a cikin karkashin zuciyar mai sauraro, ina matukar alfahari da ke a rayuwa.

 Ke farar macece wadda ake yiwa alkunya da alkyabbar mata, gaki fara zuciyarki fara gaki da farar aniya, ina sonki kuma ina kaunarki kuma aurenki shine cikon muradin rayuwata.

1 Response to "Sababbin Sakonnin Kalaman Soyayya"