-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Me Yasa Ilimin Sakandire Ya Tabarbare A Arewa

Me Yasa Ilimin Sakandire Ya Tabarbare A Arewa

Me Yasa Ilimin Sakandire Ya Tabarbare A Arewa

Shi ilimi shine gishirin rayuwar dan  adam, kuma jigon cigaban jama'a da kasa baki daya. Tabarbarewarsa ka jawo akasin haka:-

(1) GWAMNATI

Gwamnati itace ke da Alhakin samar da hukumar ilimi don kula da makarantu da malamai, haka nan samar musu da kayan aiki da kuma bibiya, don ganin komai yatafi kan tsari wanda sabanin hakan ka iya jawo nakasun ilimin a cikin al'umma.

(2) MALAMAI

Nagartar malamai itace ke samar da nagartartun dalibai. Sabanin haka ka iya jawo nakasu ga dalibai da ilimi da kuma sauran tarbiyya ta dalibai. Don haka malamai a karo ilimi; tunda baka iya bayar da abunda baka dashi.

(3)DALIBAI

Karsashin dalibi/daliba wajen son ya/ta koyi karatu itace kololuwa wajen samun nasarar ilimi. "Zaka iya tursasa doki ka kaishi bakin kogi, amma bazaka iya tursa sashi yasha ruwaba". Don haka dalibai kalubale gareku; da gwamnati da malamai da duk sauran ma'aikata na bangaren ilimi, nasararsu na ga jajircewarku. Kuna iya sayan:

iPhone, I pad, I pod, Android, Tabs etc. Amma bazaku iya sayan:

Text books, dictionaries etc ba.

Kuna iya whatsapp, Istagram, Zoom, IMO, Facebook, Twitter, Skype, e.t.c amma bakwa iya samun lokaci don nazarin karatunku. Shifa ilimi ba'a gado; sai kayi kasamu. Manufa na taimakon kudurin dalibi wajen karatu, Karkuyi karatu don neman aiki kawai; ilimi baya tabewa. 

(4) IYAYE

Iyaye kuna mahimmiyar gusun mawa akan 'ya'yanku musamman a kasar Hausa. Sai abinda iyaye suka Dora yaro akai yakeyi, idan iyaye suka kasa kwabar 'ya'yansu to tun suna yara sukabarsu ba kwaba. Idan sun girma sannan ace za'a kwabesu, shikuma ice tun yana danye ake tankwarashi.

Kukan kurciya jawabi ne ! Nagode.

Daga: Yahaya Ado Wasai 

PG Guidance and Counselling, @B.U.K 2022.


0 Response to "Me Yasa Ilimin Sakandire Ya Tabarbare A Arewa"

Post a Comment