-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

2023 Kalaman Soyayya

2023 Kalaman Soyayya

2023 Kalaman Soyayya Zazzafa 

My Inason ganin fuskar ki ta cika da farin Ciki, inason naga

annashuwa a tare dake, inason naga kina walwala na jin

daɗi, banason naga bacin rai naki, bana son kiyi kuka, kukan

ki tayar min da hankali yake, hawayen ki zazzabi suke

sakani, nakan dimauce idan bakya farin ciki. Burina ni dake

mu Kasance abokai na har abada, mu Kasance Aminai, mu

Kasance ma'aurata, ni dake mu Kasance hanta da jini. Mu

Kasance kamar ƙarfen jirgi dan ƙarfi, mu zamo kamar zinare

ko ina aka kalle mu an ga mata da miji cikin Soyayya. Mu

kasance masoyan juna na haƙiƙa.

MY Zanzo gareki domin warkar da raɗaɗi da xogin da zuciyata

keyi akan kaunarki, ciwon ƙaunarki ne abinda ke fisgar

xuciyata ta jefani cikin duniyar tunaninki, Shalele ƴar lele

sarakiya mamallakiyar xuciyana mai sarautar zuciyata sakon

ƙauna mai ɗauke da tambarin zuciyata zuwaga Queen ɗina kina Zuciyata.

Masoyiyata abar kaunata ki sani ina sonki ina kaunarki son da nake miki har ya kai ga…..ko da idanuwana a rife suke ke nake gani idan na bude su ke nake son gani. Ko da ba na tare da ke ina jin motsinki a cikin jikina Lokachin da nake tinaninki, kadaici shi ya fiye min komai dadi. Me ya sa kina rayuwa a cikin jikina ni ma ina rayuwa a cikin jikinki amma duk da haka nake jin tsakaninmu da nisa?

Sarauniyata taho gare ni ki kama hannuna ki furtamin kalmar kauna a cikin kunnuwana…na rayu saboda ke ki zo ki mutu a kai na…ki sani ni fa ko a lahira idan an tashe mu to ke nake so a matsayin matata….na samu biyayyarki me kuma ya rage zan roka a wajen ubangiji?

kawai numfashi nake so ga ubangiji don mu yi soyayya mai dorewa ni da ke….fatana Allah.ya tsawaita mana rayuwa ya ke abar kaunata…wacce nake ganin sunan ‘ya’yan da zan haifa a cikin idanuwanki….fakina da idanuwana ba za su iya fada miki ko kwatanta miki adadin son da nake miki ba don tuni na shide a cikin sonki, na zama ke. I Love You Mai Sona

Kece kadai acikin zuciyata,kece waddarashin ganinki kemai dani maraya.

Tunda idanuna suka kalli kyakkyawar fuskar ki,kunnuwana sukaji daddadan sautin muryar ki zuciyata ta fantsama cikin kogin kaunar ki ya sahibata abin alfaharina.

Idan ina tare da ke ko,online ko a Gidan ku ko a

Gari farin cikina bayamisaltuwa na kanjikamar kada na tafi gida domin

irin yadda nake son kasancewa tare da ke a kowanne lokaci ya mamaye dukkan wani burina.  Hakika yawan sauraron muryar ki kadai ka

iyasawa naso abani daki na tare a gidan ku, bana tunanin matsalar komai in har

idanuwana nayin arba da kyakkyawar fuskar ki mai

cike da annuri da haske kamar wata dan daren 14,

ki kasance tauraruwa mai haskake gani na, nakan ji

dadin muryar ki a duk sanda kika furta man Kalmar so.

Lallai ni yau na zama bawan soyayya wanda nake ta fangima da fangan

fangan a cikin tafkin dausayin soyayyah wadda rasa ta zai iya tarwatsa dukkanin wani fatana da farin cikina.

A duk sanda na kwanta bacci zuciyata zata shiga shiryo mani irin daddadar soyayyar da ya wakana a tsakanin nida ke, sai kawai in ga ina wani irin murmushi jin dadi saboda dace da nayi dake a matsayin masoyiyata.

Amincin Allah ya tabbata ga amintacciya, Wacce zuciyata ta

aminta da amincinta, Wacce nakeyiwa SON da bana yiwa

kaina, wacce tazamto sarauniya me isashshen iko datake

tafiyar da mulkinta a yalwatacciyar fadar zuciyata, Ina

Tabbatar miki bawata bayanki, Ke kaɗai ce tawa.

Soyayya na iya chanja mutum, domin ita Soyayya ba'a ganin,

balle a koreta ko a hana ta shiga zuciya. Ba'a Cewa Soyayya

ga yadda ake so, sai-dai kayi yadda take so. Ba'a Shiri wa

Soyayya, ko babu shiri Idan taxo kamar mutuwa haka zata

shiga Zuciyar mutum. Duk wanda yayi so dan Allah to shine

keda riba, cikin Soyayyar ki babu sirki, na gani kuma na

gamsu kuma na Tabbatar da ke me ƙauna tace ta hakika, ki

sani, ni bazan taba son wata ƴa mace wacce bake ba, domin

zuciyata bazata taba jindadin zama da wata ƴa sama dake

ba, duk wani jin daɗin duniya bai damen ba indai babu ke.

Rayuwata Fansarki ce, Zuciyata Tini ta Rikirkice, Kunnuwana

Sun ƙi Karban zance, idanuwa na sun so su makance, duk

sanadin Soyayyar da kika amince mini, Mulkin zuciyar Shine

aiki na, samun farin cikin ki jindaɗi nane, Murmushinki

Annashuwa Ce ga zuciyata, Duk ranar da kikai fishi Dani

banida kwanciyar hankali, Ni Bawa ne ga Zuciyar ki.




0 Response to "2023 Kalaman Soyayya"

Post a Comment