-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman So da Kauna

Kalaman So da Kauna

Kalaman So da Kauna

So Tamkar Wata Irin Wutar Dajice Mai Fara Ruruwa Ahankali Daga Bisani Saita Mamaye Ko Ina

SoTamkar Wata Irin Rijiya Ce Mai Nisan Zurfi Wanda Har Yanzu An Gagara Samun Wanda Zai Kureta

So Tamkar Duhun Dare Ne Wanda Idan Harka tsinci kanka acikinsa Bazaka Taba Gane Hanyar Fitowa Ba

So Tamkar Wata Nau'in Giya ne Mai Matukar Sanya Maye Da Zaran Ka Kwankwadeshi Bazaka Taba Dawowa Kan Hayyacinka Ba

So Tamkar Wani Katon Gulbi Ne Mai Tsananin Girma Da Zurfi Da Tsawo Da Fadi Har Zuwa Yanzu Ba"a Samu Wanda Ya Iya Kai Kurewar Karshensa Ba

So Yanada Matukar Wahala Amma  Yafi Komai Sauki Idan Har Aka Dorashi Bisa Kan Alkiblar Daya dace.

 So yanada yawan Gaske Wanda Har Zuwa Yanzu Babu Wanda Zaice Yataba Hango Iyakar Karshen Sa

So Tamkar Tafasasshen Ruwan Shayi Ne Mai Zafin Gaske wanda Bazaka Taba Sanin Yaya Yakeba Sai Alokacinda Ka Sanyashi Acikin Bakinka Anan Ne Zaka Gane Yanda Yake

So Yanada  Launi Kala-Kala Har Yau Bqbu Wanda Zai  Iya Suffanta Maka Yanayin Yanda Kalarsa Take

So Yana Sanya Nishadi Acikin Zuciya Amma Yafi Komai Tafarfasa Zuciya Da Sanya Rashin Sukuni Acikin Ruhin Wanda Ya Kamu Dashi

So Tamkar Ruwa Yake Ayayinda Yake  Shiga Ta Cikin Siririyar Kofar Zuciya A Hankali Yake Narkewa Ya Daskare Cikinta.

Kyautar Kalaman So Daga Bakinda Baya Gajiya Da Ambaton Furucin Harafin Dake Fitar  Da Sakon Gaisuwar Girma Agareki. 

Budemin Nashigo Kofar Zuciyarki Da Sannu Zan Zamo Dauwamammen Farin Cikin Da Zai Bunkasa Dukkan Wani Farin Cikin Rayuwarki

Assalamu Alaiki Yake Hakikar Halittar Da Bayananina Suke Nufi. Nazo Da Murna Zuwa Murmushi Da Farin Cikin Shaukin Samun Damar Ganin Kyawun Nasabarki

Kicemin Marhabun Yaka Taho Dan Gata Zuciyata Kazo Zan Baka Ruwan Hawayen Idanuwana Suna Kwaranyane Sanadin Nemanka

Annashuwa Da Shauki Ne Zasu Biyo Baya Farin Ciki Marar Misalin Adadi Shine Zai Rufe Dukkan Wasu Kofofin Damuwata

Zuciyata Tana Miki Sallama Ta Masoya Jinin Dake Kara Kuzari Ajikina Shima Yana Ladabin Gaisuwa Agareki

Yar Asalin Kyau Mai Dirar Hanci Siriri Matsakaici Kinada Kyawun Halitta Da Tsarin Iya Kwalliya Akan Burgewa

Sonki Ne Kadai Akan Tsarin Dukkan Tunanina Komai Nisan Dare Da Tsawon Wuni Iya Wuya Tunaninki Ne Akan Kwakwalwata

Kallon Tsakiyar Idanuwanki Suna Saukar Da Sabuwar Ni,ima Acikin Jikina Ta Hanyar Hakane Nake Kara Kaimi Wajen Ganin Nasamu Ganinki Akowace Rana

Dauki Ki Amsa Sunankine Nake Ambato Tsananin Sonkine Yake Tsuma Zuciyata Shiyasa Bana Gajiya Wajen Yaki Da Dukkan Wata Damuwarki.

                                                                                                                 

0 Response to "Kalaman So da Kauna"

Post a Comment