-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yau 14 Ga Watan Yuni: Muhimmiyar Sanarwa Game da “Physical Verification” da “PPA Letter” Na Npower Batch C Stream 2

Yau 14 Ga Watan Yuni: Muhimmiyar Sanarwa Game da “Physical Verification” da “PPA Letter” Na Npower Batch C Stream 2

Yau 14 Ga Watan Yuni: Muhimmiyar Sanarwa Game da “Physical Verification” da “PPA Letter” Na Npower Batch C Stream 2

Da yawan mutane sun damu akan suna duba “Dashboard” nasu amma basuga ansa musu “PPA Letter” ba. Jama'a ku kwantarda hankalin ku, wannan ba abin damuwa bane ba, domin kuwa duk wanda baiyi “Physical Verification” ba bai rigada ya zama Beneficiary (wanda zaici gajiyar tallafin) ba.

Har yanzu duk wanda ya duba “Dashboard” ɗin sa a can sama “Appicant” zai gani ba “Beneficiary” ba... Wannan yana nufin kenan har yanzu Npower basu tantance mutum ba, kuma shi “PPA Letter” ana turo shine kaɗai ga wanda anka tantance domin ya fara zuwa aikin sa a inda aka tura shi.

Saboda haka idan lokacin da aka ayyana za'a fara “Physical Verification” yayi, wato 14th June 2022, ko mutum yaga “PPA Letter” koma bai gani ba kawai duk wanda yasan yayi “Thumb print” yaje yayi Verification ɗinsa a LOCAL GOVERNMENT ɗinsa (LGA ɗinda akayi amfani dashi lokacin cike Npower). Daga baya idan mutum yayi passing verification ɗin zaiga “PPA Letter” in sha Allah!

Allah yasa mudace. Amen

Wanda yaga wannan saƙon yayi ƙoƙarin turawa ƴan uwa da abokan arziki domin suma su amfana.0 Response to "Yau 14 Ga Watan Yuni: Muhimmiyar Sanarwa Game da “Physical Verification” da “PPA Letter” Na Npower Batch C Stream 2"

Post a Comment