-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

SANARWA: Abubuwanda ake buƙata a wajan gudanarda "Physical Verification" na Npower batch C 2, a yau Talata 14th June 2022

SANARWA: Abubuwanda ake buƙata a wajan gudanarda "Physical Verification" na Npower batch C 2, a yau Talata 14th June 2022

SANARWA: Abubuwanda ake buƙata a wajan gudanarda "Physical Verification" na Npower batch C 2, a yau Talata 14th June 2022 

Ofishin shirin Npower na ƙasa sun bayyanarda ranar Talata 14th June 2022 a matsayin ranar da za'a fara aikin tantance wa ƴanda zasu amfana da tallafin zango na biyu (Physical verification batch C2). Kowa yaje kan dashboard ɗin shi domin ganin inda aka turashi!

Aikin zai gudana ne a cikin kwanaki 12 kacal. Saboda haka duk wanda yasan sunan sa ya fito kuma yaje an ɗauki shatan yatsun sa (Thumb print), ya hanzarta a cikin wa ƴan nan kwanaki 12 da aka tabbatar domin a tantance shi.

Kwanakin zasu fara ne daga Talata 14th ga wannan watan zuwa 25th, duk a cikin wannan watan na June da muke ciki.

Abubuwan da ake buƙata aje dasu;

1- Lambar shedar samun tallafin Npower (wadda take a cikin takardar da akayi print a lokacin cike tallafin na Npower).

2- Alamar sheda ta mutum (National ID Card, Voters Card ko kuma wani katin da yake yarjaje a ƙasa).

3- Takardun shedar karatu (Takar dun makaranta wa ƴanda mutum yayi amfani dasu a lokacin cike Npower) da kuma takarda sheda ta ƙaramar hukuma (Certificate of indigene).

Allah ya bada sa'a. Amen!

Wanda yaga wannan saƙon yayi ƙoƙari ya sanarda sauran ƴan uwa da abokan arziki.

0 Response to "SANARWA: Abubuwanda ake buƙata a wajan gudanarda "Physical Verification" na Npower batch C 2, a yau Talata 14th June 2022 "

Post a Comment