Kasuwar 'yan kwallo: Osimhen, Jesus, Raphinha, Suarez, Bale, Cavani, Kounde
Kasuwar 'yan kwallo: Osimhen, Jesus, Raphinha, Suarez, Bale, Cavani, Kounde
Arsenal ta tattauna kan cinikin ɗan wasan Napoli da Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 23, kuma suna ci gaba da kokarin ganin sun yi farautar ɗan wasa daga Brazil Gabriel Jesus, mai shekara 25, daga Manchester City. (Goal)
KocinChelsea Thomas Tuchel na shirin kashe fam miliyan 200 a kakar badi, yayin da sabon mai ƙungiyar Todd Boehly ke shirin karbe harkokinta nan ba da jimawa ba. (Telegraph, subscription required)
Ɗan wasan Brazil Raphinha, mai shekara 25, ya shaida wa darakta a Leeds United cewa yana son ya buga wa Barcelona, wanda a baya ya yi watsi da tayin fam miliyan 30 da ta gabatar masa a farkon wannan shekarar. (Sport)
Ɗan wasan Uruguay Luis Suarez, mai shekara 35, na iya komawa ƙungiyar David Beckham ta Inter Miami bayan kammala zama a Atletico Madrid. (Independent)
Ƙungiyar Serie A ta Italiya Salernitana za ta so ta daidaita da dan wasan Manchester United da Uruguay Edinson Cavani, mai shekara 35, a cewar shugaban Salernitana Danilo Iervolino. (Manchester Evening News)
Mbappe bai fitar da ran buga wa Real Madrid tamaula ba
West Ham ta tuntubi United kan batun Lingard
Ɗan wasan gaba a Belgium Eden Hazard, mai shekara 31, ya nuna ba zai bar Real Madrida yanzu ba, ya jaddada cewa yana son nunawa duniya zai iya bayan raunin da ya samu. (Goal)
Everton da Crystal Palace duk na zawarcin ɗan wasan Watford asalin kasar Senegal Ismaila Sarr, amma Newcastle ta kawo karshen nata farautar kan matashin mai shekara 24. (Football Insider)
Mai buga wa Wales gaba Gareth Bale, ɗan shekara 32, ya gabatar da tayi ga Atletico Madrid, amma aka yi watsi da bukatarsa. Bale a wannan kakar zai yi bankwana da abokiyar hamayyar Atletico wato Real Madrid.(Marca)
Mai tsaron raga a Slovakia Martin Dubravka, ɗan shekara 33, na son ci gaba da zama a Newcastle, duk da cewa ana alakanta kulob din da yunkurin dauko mai tsaron raga a Manchester United da Ingila Dean Henderson, da na Chelsea da Sifaniya Kepa Arrizabalaga. (Chronicle)
Jules Kounde da ke tsaron baya a Sevilla da Faransa da kuma ɗan wasan Croatia da RB Leipzig Josko Gvardiol na cikin jeren 'yan wasa takwas da Chelsea ke farauta. (Telegraph, subscription needed)
Newcastle United ta matsu ta sayo ɗan wasan Leeds UnitedJack Harrison, mai shekara 25, kuma ta iya saye ɗan wasan Lille Sven Botman, mai shekara 22. (Telegraph, subscription needed)
Aston Villa ta bi sahun Everton a farautar ɗan wasan Burnley James Tarkowski. (Times, subscription needed)
Mai buga waArsenal da Faransa William Saliba, na cikin tawagar Gunners a sabuwar kaka bayan nuna bajinta a lokacin zaman aro a Marseille. (Evening Standard)
Ɗan wasan baya a Ingila Ryan Fredericks zai yi bankwana da West Ham bayan gaza ba shi sabuwar kwangila har lokacin cikar wa'adi. (Football Insider)
West Ham na son ta dauko ɗan wasa daga Nottingham Forest Joe Worrall, mai shekara 25. (Evening Standard)
Manchester United za ta saye ɗan wasan Norwich Citymai shekara 22 Max Aarons, a cewar tsohon ɗan wasan United Rio Ferdinand. (Independent)
West Ham na ci gaba da tattaunawa da Rennes kan ɗan wasan Morocco Nayef Aguerd. (90 min)
Renan Lodi mai shekara 24 ɗan Atletico Madrid da Brazil na cikin 'yan wasan na Newcastle United ke son dauka.(Chronicle)
Copy Daga Shafin BBChausa
0 Response to "Kasuwar 'yan kwallo: Osimhen, Jesus, Raphinha, Suarez, Bale, Cavani, Kounde"
Post a Comment