-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tallafin Work Experience Programme(WEP): Ma'aikatar Matasa da Cigaban Wasanni ta Tarayya Ta Fitarda Da Naira (N80,460,000) Ga Matasa (2,682) Da Zasuci Gajiyar Sharin

Ma’aikatar Matasa da Cigaban Wasanni ta Tarayyar Najeriya ta ce za a fara biyan Alawus ga ma’aikatanta na Shirin Kwarewar Aiki wato Work Experience Programme(WEP) a wannan watan bayan an kammala bin diddigi da sasantawa kan kudaden da za'a bayar.

Ma’aikatar ta bukaci matasa da wadanda zasuci gajiyar shirin da suyi hakuri da jinkirinda aka samu kuma su bawa zukatansu hakuri akan matsalolin da suka kawo tsaiko a harkar.

Ma’aikatar ta biya Naira Dubu Tamanin da Naira Dubu Dari Hudu da Sittin (N80,460,000) zuwa ga matasa Dubu Biyu, Da Dari Shida da Tamanin da Biyu (2,682) wadanda suka shiga horo a karkashin wannan shirin a watan Agusta da Satumba. Wadannan kudaden sun shafi mahalarta a Arewa da Kudu.

Shirin Ƙwarewar Aiki (WEP) Ƙaddamarwa na Ma'aikatar Matasa da Ci Gaban Wasanni na Tarayya shiri ne na horo na watanni uku wanda ke ba wa mahalarta damar samun ilimin da ya dace, haɓaka ƙwarewa da ƙwarewar wurin aiki wanda zai inganta aikin su.

Sa hannu:

Sashen Cigaban Kasuwanci da Ƙaddamarwa,

Ma'aikatar Matasa da Cigaban Wasanni ta Tarayya

0 Response to "Tallafin Work Experience Programme(WEP): Ma'aikatar Matasa da Cigaban Wasanni ta Tarayya Ta Fitarda Da Naira (N80,460,000) Ga Matasa (2,682) Da Zasuci Gajiyar Sharin"

Post a Comment