-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Miliyan 5 zuwa 25: Gwamnatin Najeriya Za Ta Fara Bawa Matasan Da Suka Kammala Digiri Da HND Bashin Miliyoyin Kudade Daga Miliyan 5 Zuwa Miliyan 25 Domin Dogaro Dakai

Babban Bankin Najeriya ya sanar da sabon shirin lamuni ga wadanda suka kammala karatun jami'a da kwalejojin fasaha da ke son kafa kasuwanci, yana mai cewa matakin wani bangare ne a kokarinsa na yaki da rashin aikin yi a kasar.

Bankin ya ce za a aiwatar da shirin lamunin ne a karkashin shirin sa na Tertiary Institutions Entrepreneurship Scheme (TIES).

A cikin wata sanarwa da babban bankin ya fitar ta shafinsa na Facebook ya ce: “Babban bankin na CBN, a matsayin wani bangare na manufofin sa na magance hauhawar rashin aikin yi ga matasa da zaman banza, ya bullo da Tertiary Institutions Entrepreneurship Scheme (TIES) don samar da canji mai kyau tsakanin daliban da suka kammala karatun digiri na kwalejojin kimiyya da jami’o’i a Najeriya, daga neman ayyukan gwamnati zuwa kasuwanci.

"Shirin na da nufin samar da sabon tsarin kudi wanda zai habaka samar da ayyukan yi, habaka kasuwanci, da tallafawa ci gaban tattalin arziki."

Lamunin zai kama daga Naira miliyan 5 a fannun ayyukan daidaikun mutane/kebabbun kamfanoni/kananan kamfanoni, zuwa miliyan 25 ga ayyukan hadin gwiwa/ayyukan cikakkun kamfanoni.

Ana sa ran masu neman lamunin na zabin farko su kasance sun kammala karatu daga kowace jami'a ta Najeriya ko kwalejin fasaha a cikin shekaru bakwai da suka gabata.

1 Response to "Miliyan 5 zuwa 25: Gwamnatin Najeriya Za Ta Fara Bawa Matasan Da Suka Kammala Digiri Da HND Bashin Miliyoyin Kudade Daga Miliyan 5 Zuwa Miliyan 25 Domin Dogaro Dakai"