Hukumar (NITDA) Za Ta Gabatar Da Shiri Na Musamman Domin Taimakawa Ƴan Nageriya Masu Son Fara Kasuwanci
Hukumar (NITDA) Za Ta Gabatar Da Shiri Na Musamman Domin Taimakawa Ƴan Nageriya Masu Son Fara Kasuwanci
Hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), ƙarƙashin jagorancin Malam Kashif Inuwa Abdullahi (CCIE), da haɗin gwiwar ƙungiyar duniya mai fafutukar kawar da matsalolin ƴan kasuwa masu shirin farawa, da masu tasowa, gami da fatan bunƙasa cigaban masana'antu, (MassChallenge U.S, A Global Network of Zero-Equity Startup Accelerators), su na farin cikin gayyatar ƴan kasuwa masu tasowa da masu son fara kasuwancin a kowane fanni su hanzarta su cike buƙatarsu ta neman shiga cikin shirin na wannan shekara ta 2021 wanda za su ƙaddamar a Nageria, (B2MC Nigeria Programme). Apply here.
Shirin na (B2MC) a Nageriya, gasa ce ta ƙasa gami da ba da horo ga masu son fara duk wani nau'in kasuwanci da masu tasowa tayadda za a taimakawa waɗanda su ka yi nasara a haɗa su da kasuwar duniya domin samun cigaba.
Duk wani ɗan kasuwa mai tasowa da mai shirin fara kasuwancin, ka da ya yarda ya rasa wannan dama, ya hanzarta ya ziyarci wannan adireshi na:- Apply here domin ya gaggauta cike buƙatarsa ta neman shiga cikin tsarin tayadda zai kai ga samun damar ɗaukaka fiƙirarsa ko masana'antarsa zuwa ga samun mataki nagaba na cigaba mai girma.
Za a rufe karɓan bayanan masu son shiga cikin shirin a daren ranar 15 ga watan Oktoba, 2021.
Ku hanzarta domin samun nasarar cin moriyar tsarin. Allah Ya taimaka Ya ba da sa'a da rabo.
ALLAH yasa mudace Amin
0 Response to "Hukumar (NITDA) Za Ta Gabatar Da Shiri Na Musamman Domin Taimakawa Ƴan Nageriya Masu Son Fara Kasuwanci"
Post a Comment