-->

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL
To continue receiving our daily updates on news, jobs, and opportunities, please follow our new channel above, Thank you for your continued support Haskenews Media & Publishing Services
Kotu ta dakatar da babban bankin kasa CBN daga cire harajin hada-hadar kudade

Kotu ta dakatar da babban bankin kasa CBN daga cire harajin hada-hadar kudade

Kotu ta dakatar da babban bankin kasa CBN daga cire harajin hada-hadar kudade

Babbar kotun tarayya dake zamanta a Awka dake jihar Anambra ta bayyana sabon tsarin babban bankin kasa CBN na hana tafiya da kudade wato (Cashless Policy) a matsayin musgunawa al'umma.

CBN dai ya aiwatar da tsarin ne a jihohi 6 tare da birnin tarayya Abuja inda abokan cinikayyar bankuna ke kokawa kan yawan cajinsu kudaden a kowace hada-hada.

Wannan ya biyo bayan karar da wani masanin shari'a a jihar ya shigar a gaban kotu ya na kalubalantar sabon tsarin na CBN yadda ya sabawa sashi na 42 a kundin tsarin mulkin kasar nan.

A na shi bangaren, Lauya mai kare babban bankin Jackson Iragunima ya ce an fito da sabon tsarin ne don saukakawa al'umma bawai don a musguna musu ba.

Source: Freedom Radio Nigeria

0 Response to "Kotu ta dakatar da babban bankin kasa CBN daga cire harajin hada-hadar kudade"

Post a Comment