-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tarihin Jaruma Hadiza Aliyu Gabon

Tarihin Jaruma Hadiza Aliyu Gabon

Jaruma Hadiza Aliyu Gabon

Hadiza Aliyu an fi saninta da Hadiza Gabon (An haife ta a 1 ga watan Yunin shekara ta 1989) a kasar Gabon, Hadiza Aliyu ta kasan ce shahararriyar yar wasan kwaikwayo a hausa film a Najeriya, a ƙarƙashin masana'antar fim ta Kannywood

An haifa Hadiza Aliyu Gabon ne a kasar Libreville dake kasar Gabon, ta dawo Najeriya daga bi sani domin wasu dalilai, inda tayo karatu, sannan ta fara harkan fim, Haifaffiyar garin Libreville, Jamhuriyar Gabon, Hadiza Aliyu ‘yar gidan Malam Aliyu ne wanda dattijo ne. A bangaren mahaifinta, Hadiza dan asalin kasar Gabon ne, kuma a bangaren mahaifiyarta, asalin ta Fulani ne daga jihar Adamawa, Najeriya

Hadiza Aliyu ta halarci makarantun firamare da sakandare a kasar haihuwarta inda ta rubuta jarabawarta ta A-Level tare da burin zama lauya sannan daga baya ta zabi Lauya a matsayin kwas din da ta fi so. Ta fara karatun jami'a a matsayinta na daliba, amma dole ta daina zuwa makaranta saboda wasu matsaloli da suka dabaibaye karatunta. Karatun nata ya tsaya a lokacin kuma hakan ya ba ta damar halartar shirin difloma a cikin Harshen Faransanci kuma daga baya ta zama malama mai koyar da Faransanci a wata makarantar sirri

Tana daya daga cikin manyan jaruma mata a masana'antar fim ta kannywood

Hadiza Aliyu ta shiga Kannywood ba da dadewa ba bayan ta shigo daga Gabon zuwa jihar Adamawa, Najeriya . Ta tashi daga Adamawa zuwa Kaduna yayin da take sha'awar shiga masana'antar fim ta kannywood tare da dan uwan ta. Ta samu damar ganawa da Ali Nuhu kuma ta nemi taimakonsa don kaddamar da ita a matsayin 'yar fim. Hadiza ta fara fitowa ne a shekarar 2009, inda aka sanya ta a Artabu, ta samu shiga masana'antar fim ta kannywood a matsayin daya daga cikin manyan jarumai mata tare da taimakon Ali Nuhu da kuma jagorancin Aminu Shariff . Takasance shahararriyar yar'wasan Hausa ce. Mutane da dama na gani da daukan ta amatsayin jarumar yar'wasan Kannywood kuma abar koyi musamman yadda take fitowa cikin sutura na al'ada da kyau.[5] Hadiza takasance itace jakadiyanda ya daga cikin Camfani sadar na Nijeriya MTN Nigeria da kuma kamfanin abincin Indomie, ta karbi kyautar Best Actress Jury Award a 2nd Kannywood Award wanda kamfanin MTN Nigeria suka dauki nauyi bayarwa. Itace wacce ta kafa gidauniyar HAG Foundation

Wasu daga cikin hotunan Jaruma Hadiza Aliyu Gabon
0 Response to "Tarihin Jaruma Hadiza Aliyu Gabon"

Post a Comment