-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tarihin Jaruma Fati Muhammad

Tarihin Jaruma Fati Muhammad

Jaruma Fati Muhammad

Fati Muhammad (An haife ta 15 Yuni 1982) tsohuwar jarumar finafinai ce a masana'antar finafinai ta Arewacin Najeriya wadda akafi sani da Kannywood.

Asalin mahaifan Fati Fulani ne daga jihar Adamawa. An haife ta a ranar 15 ga Yuni, 1982 a unguwar Tukuntawa ce kin Birnin Kano. Tayi Firamare da Sakandare a Tukuntawa.

Fati ta fara harkar fim ne tun daga lokacin da ta gabatar da sha'awar ta ta shiga harkar finafinai a lokacin tana da karancin shekaru. Ta fara da nuna ma Tahir Muhammad Fagge wani fitaccen mai shirya finafinai a masana'antar Kannywood sha'awar ta ta shiga harkar finafinai. Shi kuma Tahir ya haɗa ta da Ishaq Sidi Ishaq an acclaimed image maker in the industry. Daga nan ne Ishaq Sidi Ishaq ya fara saka Fati a fim dinsa mai suna "Da Babu", irin rawar da ta taka da kyawu da salon ta sune suka kara fito da ita a fim din inda nan take daga fitar fim din aka san ta. Wanna ya kara jan hankalin sauran producers na masana'antar inda suka yita saka Fati a finafinan su. Fati ta yi finafinai da dama. Daga cikin su akwai; Sangaya, Zarge, Marainiya, Mujadala, Kudiri, Tutar So, Garwashi, Tawakkali, Gasa, Abadan Da'iman, Zo mu Zauna, Tangarda, Hujja, Al'ajabi, Halacci, Samodara, Zumunci, Murmushin Alkawari, Gimbiya, Bakandamiya, Taskan Rayuwa, Nagoma and Babban Gari.

Fati tace a yanzu ta daina fitowa a finafinai amma kuma tana cigaba da shirya finafinai

Fati ta yi aure inda ta auri wani jarumi a masana'antar Kannywood mai suna Sani Mai Iska. Inda ta bar masana'antar tabi mijin ta suka koma London. Bayan wasu shekaru da auren su kuma sai auren ya lalace, daga nan Fati ta dawo gida Najeriya. Bayan dawowar ta nan ma ta tsunduma cikin harkokin finafinai, saidai bata dade ba ta dakatar bisa ganin wasu sauye sauye da tace ta gani a masana'antar. Fati ta sake aure kuma inda ta auri Umaru Kanu wani mai shirya finafinai a masana'antar Kannywood kuma yaya ga mawaƙi Ali Jita. Bayan wani lokaci kuma auren su yazo karshe. Fati bata haihu ba a iya rayuwar ta ta aure.

A 2019 anga fati a tarukan siyasa. Kuma Fati ta tabbatar da cewa ta shiga harkokin siyasa

Wasu daga cikin hotunan Jaruma Fati Muhammad


0 Response to "Tarihin Jaruma Fati Muhammad"

Post a Comment