-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tallafin AFJP Farmers : Manoma za su yi murmushi da tallafin Gwamnatin Tarayya

Tallafin AFJP Farmers : Manoma za su yi murmushi da tallafin Gwamnatin Tarayya

Tallafin AFJP Farmers : Manoma za su yi murmushi da tallafin Gwamnatin Tarayya.

Gwamnatin tarayya za ta raba kudin da ya kai Naira biliyan 12.3 a matsayin tallafi kwanan nan wa manoma fiye da miliyan biyu da tallafin Naira Biliyan 12.3.

Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa manoma miliyan biyu a daminar shekarar nan Andrew Kwasari ya ce za su fara ne da ba manoma miliyan 1.2 tallafin Biliyan 6.15

Daga baya ana sa ran wasu manoman fiye da miliyan daya za su ci moriyar tallafin Jaridar Punch ta ce sama da manoma miliyan 2.2 gwamnatin tarayya ta ke shirin raba wa kudi domin su bunkasa harkar gonarsu a wannan shekarar.

 Gwamnatin Tarayya za ta tallafa wa manoma miliyan biyu a daminar shekarar nan Andrew Kwasari ya ce za su fara ne da ba manoma miliyan 1.2 tallafin Biliyan 6.15 a matsayin tallafi kwanan nan.

Jami’an fadar shugaban kasa sun fada wa jaridar cewa shugaba Muhammadu Buhari ya amince a fitar da tallafin Naira biliyan 6.15 da za a ba manoma.  Manoma miliyan 1.2 za su amfana da sahun farko na wannan tallafin da gwamnati za ta bada. 

Andrew Kwasari ya yi magana Babban mai ba shugaban kasa shawara a kan abin da ya shafi noma, Andrew Kwasari ya bayyana cewa an tantance manoman da za a ba wadannan tallafin. Kwasari ya ce shugaban kasa ya amince da fitar kudin, sannan NIPSS ya tabbatar da lambobin BVN na asusun banki na wadanda za su amfana da tallafin. 

“Manoma miliyan 1.2 za su fara jin shigowar kudinsu a banki nan ba da dade wa ba. Wasu karin manoma miliyan 1.1 za su samu karin Naira biliyan 6.15.” 

“Mu na da karin wasu (manoma) fiye da miliyan 1.1, kuma NIPPS ta tabbatar da bayanansu, kuma za a aika sunayen na su ga shugaban kasa domin ya amince.” “Mun tattara sunayen manoma fiye da miliyan shida a ofishina, za mu bada umarni a fara biyan wadannan manoman da mu ka yi wa rajista tallafin kudi.”

Hadimin shugaban Najeriyar ya yi kira ga duk wadanda za a ba tallafin, su yi abin da ya kamata wajen bunkasa nomansu, yace za a sa ido a ga abin da sukeyi.

4 Responses to "Tallafin AFJP Farmers : Manoma za su yi murmushi da tallafin Gwamnatin Tarayya"

  1. Muna matukar farin ciki da wannan tallafi da gwamnatin shugaba BUHARI ke niyyar bayarwa ga manoma karkashin AFJP FARMERS, Allah ya tabbatar Mana da wannan alkairi a ciki asusun na ajiya a banki.

    ReplyDelete
  2. Meyasa mutalakawa bama samunidai nacika Amma Shri bawani lbr

    ReplyDelete