-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

SADAUKI BOOK Hausa Novel

SADAUKI BOOK Hausa Novel

 SADAUKI BOOK Hausa Novel 1 Complete

MARUBUCI: Abdulaziz sani madakin Gini

Posting by Abubakar Saleh Quyraemey

Admin @ Top Hausa Group WhatsApp 

Phone number : 08138873799Zamanine Na Kashin Dankali Wato Babba Asama,karami Akasa. Mafi, akasarin Mutane Sun Dogara Da Tsafi Fiye Da Addini. Sarakunan Kasashe Na Wannan Lokacin Basuda Burin Dayafi Sukai Mamaya Ga Makwattansu, walau Na Kusa Ko Nanesa, badon Komai Sedan Sufadada Kasashen Su Babu Abin Da Kowanne Me Mulki Yake Tsoro Fiyeda Mutuwa,domin Itace Kai Abar Datake Katsemusu Jindadin Duniya. Awannan Zamani Akwai Wata Kasa Da Ake Kira *NURUL DALHI.* Wannan Birni Yana Karkashin Mulkin Wata Sarauniya Mesuna *MURKISA,* ita dai Murkisa Tagaji Wannan Sarautane Tun,ahannun Kakanta *HUBUSUL SABARI.* Wani Kasaitaccen Matsafi, wadda Ya Shahara Aduniya, saboda Haka Murkisa Tazama Gagarau Awannan Zamani Domin Duk Kasar Data Yaka Setayi *GALABA* Akanta. Murkisa Ta Tara Manyan *BARADE* Gwarzayen Yaki Ta Hanyar Amfani Da Tsafi Ko Basu *DUKIYA* Komai Nisan Gari Idan Taji Labarin Jarumi Seta Aika Masa Da Sakon Dukiya Me Yawa Yadawo Karkashin Mulkinta Idan Kuma Yaki Seta Tsafanceshi Yadawo Koda Bay...Duk Daganin Tasamu Wannan Biyan Bukata Hankalinta Be Kwanta Ba, Ita Burinta Aduniya Shine Yaza,ayi Tayi Tsafin Dazata Cigaba Da Rayuwa Har abada. Watara Murkisa Ta Shiga Dakin Tsafinta Tafadi Bukatarta Ga Abin Dogaronta Wato *ALJANINTA KALKULU.* Kalkulu Ya Bushe Da Dariya Yace, Yake Sarauniyar Duniya Kin Sani Cewa Ina Tareda Ke Tun Kina Cikin Mahaifiyarki *IYAYANKI* Sunyi Mulki Metsaho Shekara Da Shekaru,amma Ba Su Sami Ikon Aiwatar Da Irin Wannan Bukata Taki Ba.Cikin Mamaki Murkisa Tace Mene Dalilin Dayasa Suka Kasa?Kalkulu Yace Indai Bakyaso Ki Mutu Sai Kinyi Wani Tsafi Me Wuyar Gaske Shin Ko Kin Taba Yin Nazari Akan Gunkin Dodon Dayake Kofar Gidan Sarautarnan? Murkisa Tace A,a Ban Taba Asalima Bansan Dalilin Yin Saba, nidai Tun Ina Karama Nataso Nake Ganinsa Bansan Muhimmacinsa Ba.Kalkulu Yace To Tsaya Kiji Shi Wannan Gunki Dakike Gani Ba Gunki Bane, dodo Ne Na Gaskiya Kakanki Ya Tsafanceshi Yazama Gunki, muddin Gunkin Yana Kofar Gidannan Baza,ataba Cimmu Da Yaki Ba. Kika Lura Zakiga Yanada Alamar Kaho Akansa To Yazama Dole Ki Tura Adauko Miki Kahon Wannan Dodo Yana Can A, ajiye Akogon *KUSUGU.* Kodajin Haka Sai Murkisa Tace Yakai Kalkulu Kasani Cewa Ba Mahalukin Daya Taba Shiga Kogon Kusugu Yafito Araye Taya Zan Tura Wasu Suje Su Dauko Mini Kahon Tsafi Acikinsa?. Kalkulu Yace Sarauniya Ai Bakisan Abin Damu Aljanu Muka Sani Ba,ina Tabbatar Miki Idan Har Kika Tura Mutum 5 Dazan Lissafa Miki Zasu Iya Zuwa Su Dauko Miki Kahon Sihiri Mutum Na Farko Shine Babban Jarumi Dake Kasar *JULHAIRI* Ana Kiransa *SADAUKI* Mutum Na 2 Shine Sarkin Yakin Ki Wato IMRAN,mutum Na 3 Shine Tsohon Matsafi *KAN,ANU* Matsafin Dakika Gada Agun Kakanki, mutum Na 4 Mace Ce Anakiranta Da Suna *LUWAISA.* Ita Luwaisa Budurwa Ce Yar Shekara 18 Tananan Atsare Agidan *SARKI DUNGU* Na Kasar *BULBANIYA* Luwaaisa Ta Taba Cin Dan Itace Ba Kuma Babu Wani Namiji Daya Taba Kusantarta Itakadaice Zata Iya Taba Kahon Sihiri Dayake Ajiye Akogon Kusugu. Mutum Na 5 Shine *ZULMU* Masanin Hanya ....Shine Kadai Mutumin Da Ze, iya Nuna Hanyar Dazaabi Aje Kogon Kusugu,shikuma Yana Zaune Akasar Julhairi Ya Kebe Kansa Daga Cikin Mutane Yana Bautar Gunki Abayan Gari. Koda Murkisa Taji Wannan Bayani Sai Tayi Shiru Tana Tunani Daga Bisani Ta Amsa Dacewa Yakai Kalkulu Zanje Nayi Shawara Tukunna. Kalkulu Ya Busheda Dariya Yace, haba Murkisa Sarauniya Yar Sarakai Ki Tuna Fa Kin Gaji *MULKI DA TSAFI* Tun Kaka Da Kakanni Mezesa Kiji Dar Azuciyarki?. Murkisa Tayi Murmushi Tace Ba Tsoro Nakeji Ba Amma Kasani Na Taba Aikawa *SADAUKI* Da Dukiya Mai Yawa Don Yadawo Karkashin Mulkina Amma Yaki,shikuma Sarki *DUNGU* Kasan Cewa Mashahurin Matsafine Karbar Luwaisa Daga Hannunsa Ba Karamin Abu Ba Ne. Kalkulu Yasake Bushewada Dariya Yace Akwai Hanyar Dazaki Ribaci Sadauki Ya, amince Da Bukatarki Sadauki Yanada Mace Wadda Ta Mutu,yau Shekara Guda Kenan Kuma Yayi Imani Cewa Zata Iya Dawowa Kinuna Masa Cewa Zaki Dawo Masa Da Matarsa Tabbas Ze Amince Shikuma Sarki Dungu Babu Mutumin Dayake Shayi Fiyeda Sadauki Dole Yabashi Luwaisa sarki Dungu A duniya Babu Mutumin Dayake Shakka Samada Sadauki Dole Yabashi Luwaisa Idan Ya Bukaceta.Wannan Bayani Na Kalkulu Yasa Murkisa Taji Sanyi Aranta Tace To Shikenan Zanyi Duk Abinda Kace Domin Biyan Bukatata. Dakata Sarauniya Kwai Babban Hadari Guda Daya Wanda Zaki Kiyaye Bayan An Dauko Kahon Tsafi. Cikin Mamaki Tace Menene Hadarin.? Kalkulu Yace Yazama Dole Ayankawa Dodo Luwaisa Yasha Jininta Dazarar Ansa Masa Kahon Tsafi Ajikinsa Inbahakaba Kuwa Ruhinsa Zedawo Jikinsa Ya Hallaka Kowa Agarin Nan Ke Kuwa Take Zaki Mutu. Murkisa Tayi Murmushi Tace Bakomai Zankiyaye.*******************************************************************************************
Acikin Turakarta Musamman Ta Kebe Tareda Sarkin Yakin Ta Imran Murkisa Ta Sanarda Imran Dukkanin Abinda Yafaru Tsakaninta Da Kalkulu, Kodajin Haka Se Imran Yayi Ajiyar Zuciya, Sannan Yace Ranki Yadade Ashirye Nake Na Sallama Rayuwata Don Biyan Bukatarki Amma Ina Tsoran Wani Abu. Kinsani Cewa Nidake Muna Soyayya A Sirrance Babu Wanda Ya Sani Agarinnan Kuma Kinyi Alkawari Zaki Aureni Ina Tsoron Kada Ki Sauya Alkari. Murkisa Tayi Murmushi Tace Kaima Kasan Haka Bazata Yiyuwa Ba,katuna Yau Shekara Goma Kenan Muna Soyayaya Bamu Taba Samun Sabani Ba,kana So Na Ina Son Ka!.Yaza, ayi Wani Yazo Daga Baya Yashiga Tsakanin Mu Na Rantse Da Tsafin Iyayena Bazanci Amanar Kaba. Imran Yayi Murmushi Yace Shikenan Ranki Yadade Yanzu Hankalina Yakwanta, abinda Zaayi Zanje Na Sanarda Kan,anu Sarkin Tsafi Domin Muyi Shawara Akan Abinda Yakata Mufarayi Bisa Wannan Bukata Taki.Nandai Imran Yayiwa Sarauniya Sallama Yatafi. Yana Shiga Harabar Gidan, ya iske Kan,anu Azaune Ya Kunna Turaren Tsafi,hayaki Nata Bulbula Daga Cikin Wani Karamin Kasko Imran Yazauna Agefe.Bayan Kananu Yagama Surutansa Na Tsafi Seya Juyo Ya Dubi Imran Suka Gaisa Yace Rufe Bakinka Ansanar Dani Komai Kaje Kayi Shiri Kawai Gobe Zamu Tafi. Duk Da Imran Yasan Matsayin Kan,anu Aharkar Tsafi Seda Yayi Mamakin Wannan Al,amari. Dasafe Aka Shiryawa Imran Da Kan,anu Guzurin Tafiya Ta Dubi Imran Tace Idan Harkun Dawo Da Kahon Tsafi Zancika Alkawarin Danayima. Tasake Duban Tsoho Kan,anu Tace Kai Kuma Zan Raba Garina Biyu Nabaka Rabi Ka Mulka. Cikin Farin Ciki Imran Da Kan,anu Suka Kada Linzamin Dawakansu Suka Nausa Daji, Sarauniya Tabisu Da Kallo Har Suka Kule Sannan Tajuya Tareda Dakarunta Takoma Gida. Kwanansu Biyu Suna Tafiya A Jeji Sannan Suka Yada Zango Abakin Wata Korama Dayake Dare Ne Kuma Iska Me Sanyi Tana Kadawa Sesuka Kunna Wuta Suka Zauna Jin Dumi Imran Yayi Hamma Wadda Ke Nuna Tsananin Jin Yunwarsa. Koda Ganin Haka Se Tsoho Kan,anu Ya Busheda Dariya Nantake Yadaga Hannunsa Sama Yai Tsafi Sega Farantin Abinci Ya Bayyana Nan Take Suka Ci Sukai Hani,an.Wai Shin Yanzu Ina Zamu Fara Dosa?. Imran Ya Tambaya Cikin Yanayin Damuwa. Kan,anu Yayi Murmushi Yace Yanzu Kasar *JULHAIRI* Zamu Fara Zuwa Domin Mu Nemi Uban Tafiya Wato *SADAUKI,* inbashi Bukatarmu Bazata Biya Ba. Habadai Kan,anu Ina Zaton Dai Shi Sadaukin Yana Takama Da Jarumatane Kawai Nifa Inaganin Duk Abinda Zeyi Nimazan,iya.Kan,anu Yasakeyin Murmushi Yace Wane Kai Jarumtar *SADAUKI* TWuce Saninka....Imran Ya Bata Rai Shidai Kawai A Zuciyarsa Cewa Yake Nikuwa Sai Na Jarraba Karfina Akan Sadauki Nan, nifa Yanzu Aduniya Banga Wani Da Namiji Dazanyi Shakkarsa Ba, saidai Afini Karfin Tsafi Amma Banda Na *KWANJI.* Kan,anu Ya Katsewa Imran Tunaninsa Dacewa Daganan Zuwa Birnin Julhairi Tafiyar Kwana Talatin Ce Amma Zamu Yita Ayini Daya.Tayaya Hakan Zata Faru Imran Ya Tambaya.Maimako Kan,anu Yabashi Amsa Sai Kawai Yarintse Idanuwansa Yayi Tsafi Nantake Wata Irin Iska Ta Fara Kadawa Iskar Ta Taho Daga Sama Daga Can Se Imran Yagano Wata Halitta Ta Doso Su Halittar Nazuwa Sai Yaga Wani Irin Doki Ne Mai Kan Mutum Amma Jikinsa Da Kafafunsa Na Dokine Yanada Manyan Fukafukai,kuma Ido Daya Ne Dashi Manne Agoshin Sa.Dokin Ya Sauka Agabansu Yadubi Kan,anu Yace Ya Shugabana Mekake Bukata Daga Gareni.? Kan,anu Yadubi Halittar Yace Yakai *ZANGALU* Zamuyi Tafiya Tareda Kai Ta Tsahon Lokaci Inaso Duk Inda Muke Son Zuwa Kakaimu. Zangalu Ya Busheda Dariya Yace Ya Shugabana Ni Bawankane Idan Duniyar Kake So Mu Kewaye Ashirye Nake. A,a Yanzu Dai Inaso Ka Dauke Mu Ka Kaimu Birnin Julhairi Inda *SADAUKI* Yake. Angama Ya Shugabana. Zangalu Ya Durkusa Kan,anu Da Imran Suka Hau Bayansa Ya Tashi Dasu Sama Cikin Yan Dakiku Ya Lulaka Dasu Cikin Gajimare.*******************************************************************************************Murjejen Kato Ne Na Gaske Mai Matsakaicin Tsaho Kyakkyawan Ne Kuma Shekarun Sa Baza Sufi Talatin Da Uku Ba Kai Da Ganinsa Kasan Karkarfane Yana Tsaye Shikadai Adokar Daji Yana Saran Bishiya.Tun Bayan Mutuwar Matar Sa Salsima Ya Kebe Kansa Daga Cikin Mutane Ya Koma Jeji Da Zama Kullum Bashi Da Aiki Sai Yin Farauta Da Yin Itace, Ko Wanne Bayan Kwana Bakwai Yake Shiga Gari Ya Sayarda Fatun Dabbobi Da Ya Kamo Dakuma Itacen Daya Tara Adaidai Wannan Lokaci Ne Sadauki Yagama Sare Wata Katuwar Bishiya,tafadi Kasa Koda Yaga Magriba Ta Doso Sai Kawai Ya Dauki Sungumin Bishiyar Ya Dora Akafadarsa Ya Nufi Inda Bukkarsa Take. Yana Cikin Tafiyar Ne Yaji Iska Daga Sama Yana Daga Kai Yai Yanadaga Kansa Sama Yai Arba Da Kan,anu Da Imran Kawai Sai Ya Yar Da Bishiyar, ya Zare Takobinsa Ya Tsaya Yana Jiran Isowarsu. Zangalu Ya Rufe Fukafukansa Saadda Ya Sauka Nesa Kadan Da Sadauki, Kan,anu Na Cike Da Murmushi Shikuwa Imran Ya Kurawa Sadauki Ido Kawai Yana Kallon Kirar Karfinsa Tabbas Yasan Karon Su Bazaiyi Kyau Ba,kodai Ayi Kare Jini Biri Jini Kokuma Daya Ya Kashe Daya. "Gaisuwa Gareka Babban Jarumi,Ya Sadaukin Duniya.Kan,anu Yafadi Har Yanzu Bedana Murmushi Ba. Sadauki Yadubi Kan,anu Sannan Yadubi Imran Dakyau Sannan Yace wanene Kai Meke Tafe Daku.? Nine Kan,anu Sarkin Tsafin Nurul Dalhi Wannan Kuma Imran Kenan Sarkin Yakin Mu, Mai Girma Gimbiya Murkisa Ce Ta Aiko Mu Gareka. Sadauki Ya Sauke Takobinsa Kasa, sannan Ya Zauna Bisa Wani Dutse Dake Gabansa Yace. "ina Fatan Dai Baakan Waccan Bukatar Tasake Yowa Aike Gareni Ba.Yakai Sadauki Hakika Akan Wata Bukatarce Wadda Kaima Zaka Samu Cikar Burinka Na Duniya. Sadauki Yayi Murmushi Yace, aini Bani Da Sauran Buri Aduniya. SADAUKI Yace Domin Na Rasa Babban Abinda Nafi So Fiye Da Komai Arayuwa Ta. Kan,anu Yace Nasan Da Haka,amma Ka Sani Muddin Ka Baiwa Sarauniya Hadin Kai Zata Dawo Maka Da Wannan Daka Rasa. "Ta Yaya? Duk Duniya Babu Wanda Zai Iya Dawo Min Da Salsima.Kan,anu Bekara Cewa Komai Ba Sai Yayi Tsafi, Kawai Sai Gata Ta Bayyana Agabansu Mace Ce Mai kyawun Gaske Tana Sanye Da Fararan Kaya,Kayan Da Sune Ajikinta Sa,adda Da Ta Rasu, Zoben Dake Jikin Dan Yatsanta Shine Zoben Da Sadauki Yasa Mata Lokacin Dazai Binneta. Sadauki Ya Bude Baki Kawai Don Mamaki Yakasa Magana Ya Karaso Dafda Ita, tana Mai Yimasa Murmushi, ahankali Yadafa Kafadunta, sai Yaji Tabbas Ita Ya Taba.Sadauki Ya Rungume Salsima Yana Kukan Farin Ciki Yana Mai Cewa Salsima Kin Dawo Gareni Bazan Sake Yadda Mu Rabuba. Yana Rufe Bakinsa Salsima Ta Janye Jikinta Daga Gareshi Tadubeshi Tace Yakai Mijina Ka Manta Ne Cewa Ni Matacciya Ce Idan Har Kana So Na Rayu Na Dawo Gareka, saika Biyawa Murkisa Bukatarta Domin Ita Kadai Ce Zata Iya Dawo Min Da Ruhina. SADAUKI Yace Domin Na Rasa Babban Abinda Nafi So Fiye Da Komai Arayuwa Ta. Kan,anu Yace Nasan Da Haka, amma Ka Sani Muddin Ka Baiwa Sarauniya Hadin Kai Zata Dawo Maka Da Wannan Daka Rasa."Ta Yaya? Duk Duniya Babu Wanda Zai Iya Dawo Min Da Salsima. Kan,anu Bekara Cewa Komai Ba Sai Yayi Tsafi, Kawai Sai Gata Ta Bayyana Agabansu Mace Ce Mai kyawun Gaske Tana Sanye Da Fararan Kaya, Kayan Da Sune Ajikinta Sa,adda Da Ta Rasu, Zoben Dake Jikin Dan Yatsanta Shine Zoben Da Sadauki Yasa Mata Lokacin Dazai Binneta. Sadauki Ya Bude Baki Kawai Don Mamaki Yakasa Magana Ya Karaso Dafda Ita, tana Mai Yimasa Murmushi, ahankali Yadafa Kafadunta, sai Yaji Tabbas Ita Ya Taba.Sadauki Ya Rungume Salsima Yana Kukan Farin Ciki Yana Mai Cewa Salsima Kin Dawo Gareni Bazan Sake Yadda Mu Rabuba. Yana Rufe Bakinsa Salsima Ta Janye Jikinta Daga Gareshi Tadubeshi Tace Yakai Mijina Ka Manta Ne Cewa Ni Matacciya Ce Idan Har Kana So Na Rayu Na Dawo Gareka,saika Biyawa Murkisa Bukatarta Domin Ita Kadai Ce Zata Iya Dawo Min Da Ruhina Salsima Na Gama Fadin Haka Hawaye Ya Zubo Mata Sannan Tace Yakai Masoyina Na San Kana So Na, don Haka Kayi Duk Abinda Sarauniya Ta Umarceka,domin Na Dawo Gareka Mu Karasa Rayuwarmu Tare. Nan Take Salsima Ta Bace Sadauki Kuwa Ya Hau Kala Mata Kira Amma Shiru Bata Amsa Ba. Kan,anu Yadafa Kafadar Sadauki Yace To Sadaukin Duniya Ka Kwantarda Hankalinka, kayi Abinda Sarauniya Take Muradi Daga Gareka."me Take So?. Abu Na Farko Tana So Muje Mu Karbo Luwaisa Yar Sarki Haris Daga Hannun Sarki Dungu Na Kasar Bulbaniya Sannan Muje Kogon Kusugu Mu Dauko Mata Wani Kahon Tsafi Acikinsa,wanda Luwaisa Ce Kadai Zata Iya Tabashi. Sadauki Yayi Ajiyar Zuciya Yace Amma Kasani Cewa Babu Wanda Yasan Inda Kogon Kusugu Yake, kuma Babu Wani Mahaluki Daya Isa Ya Shiga Kogon Ya Fito Lafiya. Kan,anu Yace Karka Damu Da Wannan Alhalin Yanzu Akwai Mutumin Daze Nuna Mana Hanya, shine *ZULMU* Shima Yana Zaune Akasarnan, a Bayan Gari Yana Bautar Gunki Ina Tabbatar Maka Mu 5 Dinnan Zamu Shiga Kogon Kusugu Kuma Mu Fito Lafiya SADAUKI Yai Shiru YaCikiin amarin Wannan Tafiya Me Hadarin Gaske Daza Suyi, daga Bisa Yai Nasa Tsafin Yaga Akwai Alamun Nasara, "shikenan Na Amince Amma Zaku Kwana Awajena Inyaso Gobeda Sassafe Sai Muyi Haramar Tafiya. Kan,anu Da Imran Sukayi Murmushi Suka Dubi Juna Sukayi Murmushin Farin Ciki Danganin Sadauki Ya Amince. Tun Kafin Gari Ya Waye Suka Gama Shiri,sadauki Ya Kwashe Kayan Yakin Sa Yazuba Awata Jakar Fata Ya Dora Bisa Wata Farar Taguwarsa, sannan Ya Haye Bisa Taguwar Yai Gaba Imran Da Kan,anu Suka Bi Bayansa. Tafiyar Sa,a Guda Sukayi, suka Hangi Bukka Bisa Wani Dogon Tsauni, sadauki Yadubi Imran Da Kan,anu Yace Kuje Wancan Tsaunin,ku Samu Zulmu Inya Amince Sai Ku Taho Mutafi. Kan,anu Da Imran Suka Dubi Juna "Ya Sadaukin Duniya Ka Taimaka Kayi Masa Magana Dakanka Tunda Mu Be Sammu Ba. "kan,anu Yafadi Cikin Sassanyar Murya."ni Sanina Kukayi Kukazo Kaitsaye? Ai Kunyadda Da Kanku Me Kuke Shayi...Zulmu Ze Amince Kuwa? Wanne Irin Masifu Zasu Hadu Dashi Akan Hanyasu Ta Zuwa Kogon Kusugu? kodajin Haka Sai Imran Yakada Linzamin Dokinsa Ya Nufi Tsaunin, shima Kan,anu Sai Yabi Bayansa Sadauki Yayi Hakane Don Yafara Jarraba Jarumtakar Imran, ya Sani Cewa Zulmu Babban Matsafi Ne Kuma Mutum Ne Me Taurin Kai, dole Ne Ayi Tababada Shi,kafin Ya Amince. Dagowarsa Kenan Daga Sujada Agaban Gunki,sai Yaji Karar Sawun Dawakai, zulmu Ya Mike Zumbur Ya Ruga Waje Daga Cikin Bukkar Tasa, kawai Sai Ya Hango Su Su Biyu Sun Nufo Kan Tsaunin Zulmu Ya Mikar Da Hannayensa Biyu Yayi Tsafi Sai Ga Wani Abu Kamar Tsawa Yana Fita Daga Cikin Yan Tsunsa Biyu Tsawar Ta Doki Kasa,nan Take Kasar Ta Fara Tsagewa Tana Ruftawa Tamkar Ana Girgizar Kasa, dokin Imran Da Na Kan,anu Suka Fara Turjiya Da Haniniya,suna Zamewa Suna Fadawa Cikin Rami. Koda Kan,anu Yaga Zasu Halaka Sai Ya Kira Zangalu Ya Bayyana Fukafukansa Abude Yana Shawagi A Sama Nan Take Suka Haye Kansa Ya Tashi Dasu Sama Ya Haurar Dasu Kan Saman Tsaunin Ya Dira Agaban Zulmu. Bayan Imran Da Kan,anu Sun Sauka Sai Suka Matso GuKU Bayan Imran Da Kan,anu Sun Sauka Daga Kan Zangalu, sai Suka Matso Gun Zulmu"gaisuwa Agareka Zulmu Masanin Hanya ''kan,anu Yafada Yana Murmushi. "ku Suwaye.? Kuma Me Ya Kawo Ku Nan Wajen.? Nan Take Kan,anu Ya Gabatar Da Kansu Agareshi, dakuma Dalilin Zuwansu,sannan Ya Nuno Masa Sadauki Don Yasan Cewa Tare Suke, zulmu Yayi Shiru Yana Tunani Daga Can Yace To Naji Kuma Na Amince Amma Ina So Nasan Menene Sakamakona Bayan Mun Sami Nasarar Dauko Kahon Tsafi A Kogon Kusugu. Imran Da Kan,anu Suka Dubi Juna Sukayi Shiru,domin Sun San Cewa Sarauniya Murkiya Batayi Alkawarin Komai Ba Ga Zulmu Kamar Kiftawar Ido Sai Ga Sadauki Agabansu "naji Abinda Kace Zulmu Karka Damu Ni Zansa Sarauniya Tayima Goma Ta Arziki. Zulmu Yayi Murmushi Yace Godiya Nake Ya Sadaukin Duniya.Ko Yanzu Mu Tafi Na Amince. A,a Zamu Kwana Anan Wajenka, inyaso Da Sassafe Sai Muyi Harama. Saida Rana Ta Fito Sannan Suka Dora Guzurinsu Abisa Ababan Hawansu Suka Nausa Cikin Dokar Daji. Kwanansu Uku Suna Tafiya Acikin Dokar Daji Zulmu Na Ta Nuna Hanya, batun Cin Abinci Da Shan Ruwa Kowa Tsafinsa Ne Ke Bashi. Arana Ta Uku Ne Imran Yadubi Zulmu Yace Wai Kai Seyaushe Ne Zamu Isa Birnin Bulbaniya.? Zulmu Yayi Murmushi Yace Ai Ko Rabin Tafiya Bamu Yi Ba, amma Babu Mamaki Nanda Kwana Tara Muyi Rabin. Daga Wannan Ba Wanda Yakara Magana, har Suka Iso Wani Bakin Daji Me Yawan Surkuki Zulmu Yace "to Kowa Ya Shirya Munshigo Dajin Kwankwamai, kusani Akwai Mugayen Aljanu Masu Shan Jinin Mutane Awannan Daji. Dole Ne Mu Kiyaye Dokokin Dajin, duk Wanda Ya Kuskure Yayi Daya Daga Cikin Abubuwannan Guda Uku Sunansa Matacce. Abu Na Farko Kada Kowa Yaci Ko Yasha Duk Abin Dake Cikin Wannan Daji Sannan Babu Waiwaye Kuma Ba, amagana. Nantake Gabadayansu Suka Kara Nutsuwa Suna Cikin Tafiyar Ne Suka Iso Wani Wuri Wanda Wani Katon Rami Yaraba Hanyar Kasan Ramin Kwazazzabo Ne Na Matattarar Ruwa Mai Tafiya Zurfin Ramin Yakai Zira'i Tamanin Fadin Kuwa Yakai Kafa  Dari Nanfa Kowa Ya Tsaya. MUHADU A SADAUKI NA 2

1 Response to "SADAUKI BOOK Hausa Novel"