Menene Amfanin Lalle Ga Mata
Menene Amfanin Lalle Ga Mata
AMFANIN LALLE GA MATA
2)-Yin lalle a kafa na zuqe cutar dake kafa
sannan yana maintaining dumin mace, bi ma ana
yana inganta ni’imar mace ba tare da ya gushe
ba.
3)- Ga duk mace mai infection, ta tafasa lalle
in ya dan huce sai ta yi sit bath dashi na sati biyu
in Allah ya yarda zata warke
4)- Ana iya sha ruwan lalle cokali 1 don wankin dattin ciki
amma banda masu ciki.
5)- Don gyaran Fata; lalle dai ba karamin
tasiri yake dashi wajen gyara fata ba, domin shi
natural toner ne wanda ba bilicin yake yi ba amma
yanasa haske mai kyau kuma yana goge dattin
fata,
6)- A bangaren gyaran fuska, tana sa fuska tai kyalli,
laushi, da haske in an kwaba da ruwan Kwai amma
banda kwaiduwar kwan.ki kwaba ruwa ruwa amma
ba sosai ba ki lizimci shafa shi kullum 30 mins kafin
wanka sai Kinga bambanci a cikin sati biyu Insha
Allahu.
7)- Ga masu son hasken fata, ki kwaba lalle da
ruwa, ki shafe a jikinki inya bushe ki dirje da man
zaitun za kiga canji
8)- Ga masu fama da pimples, yar’ uwa
ki hada lemon tsami da lalle kwabi mai dan
tauri amma ba sosai ba kina shafa wa a fuskar ki
bayan watanni kuraje zasu mutu sannan tabo bazai
zauna ba ga hasken fuska da laushi.
9)-sannan gamai son kamshin fata,
Ki kwaba lalle da turaren ki mai kyau na ruwa
wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a bucket
ki sa garin lalle ta jika tai já zir sai ki tsiyaye
ruwan ki diga turaren ki mai kamshi ciki Bayan
kinyi wankan sabulunki sai ki dauraye jikinki
dashi inkin lizimci haka to bake ba rabo da
kamshin jiki in sha Allahu
10) Sannan ga Amare Kafin kiyi dilke na aurenki
ki kwaba lalle mai kyau tare da turare mai maiko,
turaren gargajiya mai mai, ki jika kamar bucket daya
kada yayi ruwa ruwa sosai kamar dai kunu, kullum
sai ki shafa a dukkan jikinki sai ki zo ki saka turaren
wuta akasko ku burner ki rufu akai ki turara jikinki har
sai hayakin turaren nan ya shiga jikinki sosai sai ki fita
kije kiyi wankan ki,za kiga canji a fatar ki rapid canji kuwa.
Fata za tayi laushi, haske da kuma santsi. Two months before
bikin ki zaki iya wannan kedakanki kuma zakiji dadin hakan.
11) Lalle nasa cikan gashi,
ba yasa gashin kan mace ya zube, yana da matukan amfani
wajen gyara gashin mace, inda wasu ke tura (steaming) gashin
su dashi ma’ana
12) A karshe mata na yin ado da lalle wajen kara kyaun kwalliyar su.
wanda su ke zanawa a jikin su.
0 Response to "Menene Amfanin Lalle Ga Mata"
Post a Comment