-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kimanin manoma milyan 2.2 ne za su samu tallafin noma na naira bilyan 12 da millyan  3 daga gwamnatin Tarayya

Kimanin manoma milyan 2.2 ne za su samu tallafin noma na naira bilyan 12 da millyan 3 daga gwamnatin Tarayya

Ga Alamu Manoman FMARD, AFJP Zasu Dara 

Manoma Miliyan 2.2 ne a Najeriya za su samu tallafin gwamnatin tarayya 

Kimanin manoma milyan 2.2 ne za su samu tallafin noma na naira bilyan 12 da millyan  3 daga gwamnatin Tarayya.

Fadar shugaban kasa ta bayar da tabbacin cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya riga da ya amince da ware naira bilyan 6 da milyan 15 domin tallafawa manoma milyan 1.2 na rukunin farko da zasu ci gajiyar shirin.

Mai taimaka wa shugaban kasa na musamman a 6angaren noma, Andrew Kwasari, ya bayyana wa majiyar mu cewa bankunan da ke da alhakin kula da shirin, ya zuwa yanzu sun fitar da rukunin farko na wadanda za su ci gajiyar shirin.

Ya bayyana cewa, manoma milyan 1.2 na rukunin farkon wadanda su ka samu nasarar samun tallafin, za su kar6i kudaden su nan ba da jimawa ba, haka kuma ya ce wasu rukunin na biyu na sama da manoma milyan daya su ma za su sake samun tallafin kudi na kimanin naira bilyan 6.15.

A yayin da aka tambayeshi yawan adadin manoman da za su iya samun tallafin, ya bayyana cewa za abayar da tallafin ne rukuni-rukuni kuma kowanne rukuni za a bayar da kimanin naira bilyan 6.15 kowanne."


Sharhi:

Ina kuke Manoman rani da damina tabbas ga duk alamu wannan tallafin gwamnatin tarayya bata nesa gabawa talakawa manoma shi. Addu'armu itace Allah yasa tallin mai tsoka ne tayyada manoma zasu amfana dashi su sayi taki, iri,kayan aiki da dai sauransu. Allah yasa mudace Amin

0 Response to "Kimanin manoma milyan 2.2 ne za su samu tallafin noma na naira bilyan 12 da millyan 3 daga gwamnatin Tarayya"

Post a Comment