-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Illolin Bilicin Ga 'yamace

Illolin Bilicin Ga 'yamace

Illolin Bilicin Ga 'yamace 



Dabi’ar shafe-shafen mai dake canja launin fata a tsakanin mata da ma wasu mazan na kara dada zama ruwan dare. Wata kididdigar da sashen kula da lafiya na Majalisar Dinkin duniya ya fitar ta nuna cewa kashi 70 daga cikin 100 na mata a Najeriya sun amince suna amfanin da mayukan da ke sauya launin fata duk da irin illolin da ke tattare da hakan.


Hajiya Habiba wata mace ce a Kano da ta shafe sama da shekaru sama da 20 tu a lokacin tana shafe-shafen man dake canza launin fata. Ta fadawa wakiliyar Muryar Amurka Baraka Bashir dalilan da yasa ta daina wannan dabi’a inda tace, “Na ga mutane na yi ne shine nima nace bari in yi, kuma idan na kalli kaina a madubi sai in ga kamar na yi kyau. Amma dana bari sai nake ganin kaina kamar dodo.


To amma abinda yasa na bari shine, dana bari sai wasu abubuwa suke zubowa daga jikina masu kaikayi, na je asibiti aka bani magani. Tunda na warke sai nace bari in bari, kuma ga kurajen da ke yawan fitowa a fuska nace wannan ba abinyi bane”. Wani likitan fata a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano mai suna Dakta Shehu Yusuf, yayi bayanin illolin wannan dabi’a.


Ya bayyana cewa ita fata tana da wani rubi a samanta wanda ke kare shigar rana kai tsaye cikinta da hakan zai iya haifar da matsala. To su kuma man shafe-shafen canza launin fata suna koke wannan sinadarin ne na kan fatar su maida ta siririya ko kuma su kashe karfin fatar ko da kuwa ba ta maida fatan mutum shara-shara ba.


Idan aka ji ciwo zai yi wuya fatan ta warke da wuri. Wata kuma in bata yi siririya ba to daga baya in aka dade sai fatan tayi baki da tauri ko kuma ta yi nankarwa harma cutar kansa na iya shiga da wuri. Idan fatan tayi siririya wato kaurinta ya ragu to za a ga kamar jijiyoyin jinin mutum sun fito fili ana gani ko kuma wasu gashi-gashi su dinga fitowa a kan fuskar mutum.


Jijiyoyin fatar idon mutum takan saki ta yadda zai iya jan matsalar haifar da hawan jini na ido da zai iya haifar da hakiya ido da makamantasu duk a sakamakon shaf-shafen man da ke canza launin fatan mutum. Wannan duk ya fito ne a jawabin Likita Shehu.

0 Response to "Illolin Bilicin Ga 'yamace"

Post a Comment