-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Dalilan Da Kesa Mace Ta Rasa Mijin Aure Dakuma Hanyoyin Magance Matsalolin Rashin Maji

Dalilan Da Kesa Mace Ta Rasa Mijin Aure Dakuma Hanyoyin Magance Matsalolin Rashin Maji

Dalilan Da Kesa Mace Ta Rasa Mijin Aure Dakuma Hanyoyin Magance Matsalolin Rashin MajiCikin Muryar takaici ta dube ni, duba me son samun mafita tace, “Kawata meye mafita?, aure nake so wurjan Jan kamar na kai kaina dakin miji wallahi, kowa ya zo rimi rimi kwana kadan sai ya gudu, Abin ya ishe ni “,Kawata Zarah tayi shiru daidai inda ta fashe da kuka cikin tashin hankali. Na bi ta da kallo cikin tausayi ,ya yin da na shiga tunano irin rayuwar da muka yi da Zarah tun daga kuruciya har girman mu ,a inda yanzu ni ina cikin shekara ta Bakwai da aure, yayin da Zarah ke zaune a matsayin Budurwa har yanzu.


Tsugunawa nayi daidai kafar zarah, na dafa kafadun ta, cikin yanayin Rarrashi na fara yi wa Zarah magana cikin sanyin murya nace, “Kiyi hakuri Zarah, komai yana da wa’adi a rayuwa, aure lokaci ne, sanin kan ki ne baki da wata makusar halitta da za’a ce an gaza auren ki, sannan kina da ilmi, Asali da kyak….. “ “Dakata “,a fusace Zarah ta dakatar da ni, wanda har sai dana tsorata. Ta cigaba da cewa, “Tabbas ina da kyau, Asali, Nasaba, Ilmi, amma sanin kan ki ne cewa Kubra duk wannan abubuwan dana mallaka shirme ne domin nayi asarar Babban abinda ya dace na mallaka, wato tarbiyya.” Ta yi shiru daidai inda ta sake fashewa da Kuka mai dauke da Gumjin takaici da Danasani. A wannan lokacin kasa cewa komai nayi, jikina yayi sanyi kwarai, sannan kuma na shiga tunanin irin zaman da muka sha yi da Zarah akan dacewa da yayi ta gyara tarbiyyar ta yadda ya kamata sabanin yadda take rayuwa kara zube babu tsari.


Ginshiki

Tabbas haka ne cikin rayuwa komai yana da lokacin sa, yayin da komai yana wanzuwa ne cikin tsarin Allah subahanahu wata’ala.Hakika Aure na da lokaci tabbas, amma duk da haka akwai wasu abubuwa da mata ya kamata su dinga dubawa kafin furta cewa sun ki auruwa, ko Mazan da suke son nasu sun ki fitowa su aure su, duk kuwa da soyayyar da ke wanzuwa a junan su.Akwai wani abu da Mata ya dace lallai su dinga lura da shi kafin koka cewa namiji ya ki auran su, ko bayan duk doguwar soyayyar da suka yi ya gudu ya auri wata.,Abin kuwa shine….


•Yaya Ku Ka Hadu Ko A Ina Ku Ka Hadu Da Shi Kansa Namijin?


Abin nufi anan a ina kuka hadu da mutum, ma’ana waje ne nagartacce ko wajen Banza?, sannan kuma kuma a cikin wanne yanayi ya gan ki ganin farko, ma’ana a nutse cikin tarbiyya ya gan ki ko a yanayin rashin tarbiyyah??. Gurin haduwar farko da yanayin da namiji ya gan ki a farko yana da matukar tasiri da amfani cikin neman aure, Hakan ya sa mata ya dace lallai su kula da wasu abubuwa kamar haka…


•Kamun Kai


Mace ta zama mai kamun kai da mutumta kan ta tare da nuna kyakkyawar tarbiyyah a ko’ina take ,Domin maza kaso 90% cikin 100% abinda suke bukata a macen aure shine tarbiyya da kamun kai ba kyau ba.


•Surutu


Lallai ya dace ga mace ta zama in har zata bude bakin ta, to ya zama maganar da zata yi ta zama maikyau ta tarbiyya. Sannan maganganun su zama takaitattu, ba mace ta zauna tayi ta surutu babu kai babu tsari ba, babu nutsuwa da nuna kunyar ‘ya mace.


Sutturar mace ma wata jigo ce babba a rayuwar ta, wanda mace ya dace ta dinga sanin irin sutturar da zata sa don suturta jikin ta. Domin yadda mace ke sa suttura ma na bata damar samun miji. Wani shirme da mata ke yi wajen tallata jikin su, wai a tunanin hakan ne zai sa maza su kwadaitu da su, su aure su, tabbas shirme suke tafkawa domin lallai Macen da take suturta jikin ta maza sun fi sha’awar ta da daukar musu hankali, saboda kullum tunanin su wace irin kira ce dauke cikin sutturar nan?, sabanin macen data gama fallasa surar ta kowa ya gama gani.


•Ciye-Ciye


Lallai mace ta sani ba ko’ina mace ya dace tayi ta ciye ciye ba a gaban maza, Ka ga mace tsakiyar maza tana ta ciye, babu kamun kai. Tauna da ciye ciyen rashin tsari kan zubar da mutumci da kimar mace.


•Yanar Gizo


Kafar sada zumunci ba illah ba ce ga mace matukar zata tsare darajar ta, sabanin wasu matan da suka mayar da abin dandalin su na shaidana da rashin kamun kai. Ka ga mace na turo wasu sakonni da kana gani ka san rashin tarbiyya ya gama keta jikin ta.


•Instagram


Ita ma wata kafar sada abota ce, wadda y’an mata da dama ke amfani da ita ta hanya maras kyau, inda mata ke turo hotuna marasa tsari ciki, ka ga wata ta turo kirji, Baki, Mazaunan ta, kai dadai sauran sassan jiki na rashin kamun kai.


•Jami’a


Karatu yana da mahimmanci kwarai ga maza da mata, wanda yanzu kai ya gama wayewa wajen Bazama neman ilmi, wanda hakan tabbas yana dakyau. Amma abin mamaki wasu matan sun mayar da jami’ar wajen kashe Ahu da zubar da tarbiyya da al’ada. Ka ga mace ta fito daga gidan iyayen ta da shigar mutumci, amma tana isa Jami’a zata cire, ta shiga nuna kirar jikin ta, da hulda da maza da wasa da su, tare da wasu halaye marasa tsari.


Kafin na karkare filin zan yi kira ga mata akan lallai suyi duba ga wannan abubuwa dana lissafo a sama wanda akasari su ke janyo musu rashin kima gun maza, Ballantana ma su aure su. Za su ga mazan na soyayya da su, amma in aka zo kan maganar aure sai su ki auran su, su je su auri y’ar mutumci mai tarbiyya.

Manzon Allah (SAW) da kan sa cewa ya yi namiji na iya auren mace, don abu uku

•Kyau

•Asali

•Addini

Amma daga karshe ya hore su da auren mafi alkhairi daga cikin su, wato mai Addini. Ashe kenan mata dacewa ya yi su jajirce wajen kwatanta kyakkyawar tarbiyya sabanin kaucewa hanya, wadda babu inda zata kai su sai tashar danasani.

Mu sani Kyau komai girman sa wataran yana gushewa…

Kudi duk yawan su wataran suna iya zama tarihi…

Amma Addini baya gushewa har Abada, sannan wanda ya rike shi ba ya tabewa.

Mu hadu mako mai zuwa Insha Allahu.

Natural 

0 Response to "Dalilan Da Kesa Mace Ta Rasa Mijin Aure Dakuma Hanyoyin Magance Matsalolin Rashin Maji"

Post a Comment