-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Cikakken Bayanin Yadda Ake Dambun Nama

Cikakken Bayanin Yadda Ake Dambun Nama

Cikakken Bayanin Yadda Ake Dambun NamaDAMBU KALA KALA


Dambun shinkafa 

  Shinkafa

  Carrot

  Green pepe 

  Cabbage

  Oil

  Maggi 

  Curry 

  Spices ...


Za'a barza shinkafa, a tankade, tsakin shinkafar a wanke da ruwan zafi, idan yadanyi laushi kadan a tsane a matsami, inya tsane, sai ajuye a roba mai fadi, ayayyanka cabbage axuba, agurza carrots a xuba akai, ayanka g/pepe axuba, asa mai kadan, asa maggi, curry da spices, da  dan gishiri kadan, agarwaya su atare, azuba a leader asa a madambacci atoshe ko ina arufe adora a wuta, inyayi zaifara qamshiiiiiiiii.


Dambun cous cous 馃崨

Cous cous

Carrot

Nikakken Nama

Alayyaho

Mai

Onion

G/pepe

Attarugu

Curry

Maggi

Spices..


Za'a juye cous cous a roba, ajuye n/nama akai, ayanka carrot cute asa akai, ayanka onion da tarugu axuba akai, ayanka g/pepe asa akai, asa mangyada yadda zai isa, asa maggi, curry & spice aciki, ayanka alayyaho asa akai, sannan agaurayasu, adinga xubawa acikin fararen leader ana kukkullawa, asa a tukunya aturarashi kamar alale...


Dambun ACCA 

ACCA

Carrot

Cabbage

Kifi

Onion, g/pepe, tarugu

Mai

Maggi, curry, spices..


Axuba ACCA a roba a yayafa masa ruwan dumi kadan , sai ayanka cabbage kanana axuba akan accan, agurxa carrot axuba akai, ayayyanka onion, tarugu, g/pepe, kananan yanka axuba akai, adafa kifi da kayan kanshi amarmasa kifin akai, asa man gyada, asa maggi curry, & spices akai, sai a garwaya su, sannan axuba a madanbacci a turara,,, inyayi xaifara qamshiiiiii.


Dambun Alkama 馃崨

Alkama

Cabbage

Carrot

Zabuwa

G/pepe

Onion, tarugu

Curry, maggi spices

Mai..


Asamu alkama a barzata a wanke da ruwan dumi a tsane a matsami, inya tsane, ajuye a roba, adafa zabuwa da kayan qanshi yadafu ligib, sai a ciccire tsokan naman a guggutsurashi axuba akan tsakin alkamar, ayanka cabbage da carrot azuba akai, ayanka onion, tarugu da g/pepe axuba akai, asa mai, asa maggi, curry da spices aciki, sai a garwayasu axuba a madanbacci a turara...


Dambun Tsakin Masara 馃崨

Tsakin masara

Rama

Gyada

Kanwa 

Mai

Tafarnuwa

Gishiri

Danyar citta

Albasa

Qarago

Kifi ( banda )


Za'a samu T/masara a wankeshi da ruwan dubi, sai a tsaneshi da matsami, inyatsanu a juye a roba, ajuye banda a roba ajuye ruwan zafi akai, inyayi laushi a gutsutsura bandan a kan tsakin, sai a daka gyada axuba akai, adafa Rama sama sama axuba akai, asa ruwan kanwa kadan 馃憣馃徎akai, abarbada garin tafarnuwa kadan 馃憣馃徎, ayanka danyar citta axuba aciki, asa mai yadda zai isa, asa gishiri kadan 馃憣馃徎, asa maggi da ajino aciki, asa curry da spices, sai a garwaya azuba a madanbacci a turara, idan yayi asauke azuba garin Qarago da mai kadan 馃憣馃徎...


Dambun Zogale 馃崨

Zogale

Cous cous

Kifi

Onion, tarugu

G/pepe

Mai

Curry, maggi & spices..


Adafa zogale sama sama 馃憣馃徎 atsane a matsami, inya tsanu, akawo cous cous ajuye akai, akawo sardines fish a marmasa akai, ayayyanka onion da tarugu akai, asa mai, asa curry, maggi & spices akai, sai a garwaya, adinga zubawa a fararen leader ana kullawa, aturarashi kamar alale.....


DANBUM DANKALI

*

ABIN BUKATA

Tumatur

Kwai

Gishiri

Magi

Kori

Dankali

Albasa

*

HADI

Zamu fere dankali a soya amma kada ya soyu sosai, idan ya dauko soyuwa sai a dauko kwai, tumatur da albasa. To dama munriga mun yanyan ka kasu sai mu xuba a kai dankali sai murika xuyawa yana dagargajewa idan kwan ya soma yin yellow sai a sauke.

*

misali:- Dankali goma albasa biyu tumatur hudu kwai uku.


馃尭DAMBUN KIFI馃尭ABUBUWAN BUKATA SUNE:-馃憞馃徎馃憞馃徎
馃尭kifi

馃尭maggi

馃尭gishiri & curry

馃尭attarugu

馃尭albasa

YANDA ZAKI HADA SHINE:- 馃憞馃徎馃憞馃徎馃憞馃徎


Ki gyara kifinki kitafasa kicire kaya kiwatse kifin kizuba maggi da curry da Albasa d tarugu 

Sai ki aza mai a wuta kisoya shima isan yafara watsewa toh ya soyu shikenan sai kikwashe.


(DAMBUN NAMA)


1-Nama

2-attaruhu da albasa

3-mai dandano dadi

4-citta

5-mai

6-turmi

7-kaskon suya

     YADDA AKEYI

  da farko zaki sami namanki mai kyau mara kashi da kitse se ki wanke ki zuba a tunkaya ki sa albasa da citta da mai dandanon dadi sae ki barshi yayi t dahuwa in ya dahu sae ki sauke ki kirba tare da attaruhu da albasa sae ki na kara maggi da onga in ya kirbu sae ki zuva akasko ko tukunya ki sa mai sosae ki soya in ya soyu ki kwashe zaki iya sa hannunki ki danna inba kyasan mai


    DAMBUN NAMAN TUKUNYA


Shima hk zakiyi anma shi daga tafashen naman zaki runga kara ruwa yana dahuwa daman kin hada attarugu da albasar gun dahuwar kinsa maggi da gishiri da citta sae ki ta kara ruwa har sae kinga ya farfashe sae kisa muciya ki bubbuga sae ya dagargaje sae ki zuba mai ki soya shikenan kingama


DANBUN COUS COUS

ABUBUWAN DA AKE BUKATA :-

馃崋Cous Cous

馃崋Nama/Hanta ko mince meat

馃崋Maggi

馃崋gishiri

馃崋Green beans

馃崋Albans a

馃崋 attaruhu

馃崋zogale ko Alayyahu


YADDA ZAKI HADA :-

Ki tafasa nama ki sa ruwa da dan yawa, in ya dahu, ki yanka shi

'kanana, duk kayan hadinki ki yanka su 'kanana, sai ki juye ruwan

naman akan Cous cous, ki sa maggi, curry, gishiri ki juya sosai kisa

murfi ki barshi zuwa 5mnt,

Sai ki 'dauko madanbaci ki dora a wuta ki zuba Cous Cous kisa leda ki

rufe kamar yadda ake dambun tsaki, 5mnt sai ki kwashe Cous cous

din kisa duk kayan hadin da mai ki juya sosai ki Mayar a wuta

zuwa minti 3 ki sauke.

zaki iya sa bawon kabeji. Yana da dadi


Dam bun naman kaxa.

Abun bukata

*kaza

*man gyada

*kayan maggi

*kayan miya


Yadda akeyi:-

1 zaki tafasa kaxan ki da citta da maggi,sai albasa,in tayi laushi ki sauke ki soya sama-sama,saiki juye aroba ki cire tsokan,ki wanke kayan miya attarugu,tattasai,albasa ki jajjga aturmin kisa maggi curry,san nan ki juye naman  ki daka duka.

(karki manta ki fara soyawa sama-sama).

Inya daku ki juye afaranti ki barbaxashi san nan ki sa mai awuta ki rinka diba kadan kadan kina xubawa kina soyawa harki gama.

Note wan nan hadin yanada kyau ki gwada ki gani.

0 Response to "Cikakken Bayanin Yadda Ake Dambun Nama"

Post a Comment