-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yan bindiga sun sace dalibai da dama a harin Yauri jihar Kebbi

Yan bindiga sun sace dalibai da dama a harin Yauri jihar Kebbi

Yan bindiga sun sace dalibai da dama a harin Yauri jihar Kebbi

Bayanai daga jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga sun sace dalibai da dama daga Kwalejin Tarayya da ke garin Yawuri.

Ganau sun ce 'yan bindigar sun tafi da dalibai da yawa sannan suka harbi wasu daga cikinsu.

Wani mutum da ya ga lokacin da lamarin ya faru ya gaya wa BBC cewa 'yan bindigar sun ci karfin 'yan sandan da ke gadin makarantar kana suka kwace motoci kirar Toyota Hilux daga wurinsu suka zuba daliban sannan suka tafi da su.

Wasu mutane sun ce an kai dalibai da dama asibiti domin yi musu maganin harbin bindiga sakamakon raunukan da suka samu yayin da suke tserewa daga harin na 'yan bindiga.

Dan majalisar da ke wakiltar yankin a majalisar dokokin tarayya Muhammad Bello Ingaski ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun sace dalibai maza da mata da tsakar ranar Alhamis.

'Yan bindigar "sun ci karfin 'yan sandan Mobile da ke gadin makarantar wadanda sun fi 20, sun sassari wasu sannan suka harbi wasu. Akwai 'yan sandan da aka sara an tafi da su asibiti, yayin da su kuma 'yan bindigar suka wuce da wasu yara."

Rahotun BBC

0 Response to "Yan bindiga sun sace dalibai da dama a harin Yauri jihar Kebbi"

Post a Comment