-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Dubarun zama da uwar miji

Dubarun zama da uwar miji

Dubarun zama da uwar miji

Uwar mijinki ta na da mutukar mutunci da daraja, domin mijin da ki ke takama da shi danta ne, ita ta dauki cikin shi wata tara, ta haife shi, ta raine shi, ta yi wahala da shi, har ya girma kika aure shi da hakoransa cif a baki, kafin ya aureki uwar shi ya sani da ‘yan’uwansa, yanzu kuma ga ki kin shigo cikin danginsu, sai ki ce uwar shi ita ce abokiyar gaban ki? Wannan babban kuskure ne.


Yanzu ‘yan mata har sunaye suke sama iyayen mazajensu, wai uwar miji musifa ce, uwar miji bala’i ce, uwar miji hawan jini ce, waiyazu billah, wacce ta haifi uban ‘ya’yan ki ita ce musifa, lallai kuwa kin dauko hanyan rusa auren ki. Dole ne ki mutunta ta, dole ne ki so ta, kuma ko kin ki, ko kin so matsayin uwa take a wurin ki.


Ya ke ‘yar’uwata! mai shirin shiga dakin mijinta ki sani, uwar miji mutumiyar kirki ce, uwar miji masoyiyar ki ce, uwar miji tana da mutunci a idon ki, idan kin dauke ta a haka to ga wasu dabaru nan da za ki yi amfani da su wurin mallakar uwar mijin ki ba boka ba malam.


Dabarun su ne:


1. Mutunta ta, idan za ki gaishe ta ki gaishe ta da mutuntawa, idan za ki yi mata magana ki yi mata magana da mutuntawa. Wannan shi zai saka mata soyayyanki a cikin zuciyarta.


2. Kyautata mata, Ki yi kokari wurin kyautata mata, kyauta wane yin mata dinki idan kina hali, yi mata girki, idan tana bukatar wani abu ki siya ki bata, idan abinci ne abin da ta fi son shi za ki rinka bata, idan ma ba unguwar ku daya ba, sai ki rinka yi ana aika mata da shi lokaci zuwa lokaci.


3. Idan ki na son ki sami karbuwa to fa ki kula da irin maganganun da za ki rinka furtawa a gabanta, ka da ki sake ki yi maganar da ba za ta so ba, idan ma kin yi ne kika ga bata so ba to sai ki nemi afuwarta.


4. Ki rinka ambata ma uwarsa abin da danta ya ke yi na alkairi, misali idan yana tallafawa wata makaranta, ko taimakama wasu gajiyayyu, kada ki rinka ambata mata yana siya miki kaza da kaza domin wata uwar mijin sai ta fara hassada ta kamata ta tada hankalinta, ta ce kin mallake shi, ai sai abin da kika ce ya ke yi, shikenan sai ta tsaneki.


5. Ki rinka kwadaitar da mijinki a kan ya rinka ziyartar su, ko da kuwa a gari daya suke.


6. Sannan ki rinka kwadaitar da shi akan daukan ki da ‘ya’yanki ku je ku wuni mata, kin ga za ta ji dadi, kuma ki kwabi ‘ya’yanki kafin ku je, domin kada su yi ta mata dambe da rashin kunya da barna, su sa ta ji haushin ki ta ce baki ba ma jikokinta tarbiyya ba.


7. Sannan duk kawayen uwar mijinki ki rinka girmama su suma, kuma ki rinka musu kyauta daga lokaci zuwa lokaci, hikiman yin haka shi ne duk abin da ki ka ba su za su bata labari, kin ga za ta ji dadi ta kara sonki.


8. Idan mijinki zai siyawa mahaifiyarsa zani, to kada ki yi mugunta, ke ki sa mai tsada ita kuma ki ce a siya mata mai arha wanda ba zai kai ko ina ba zai kode, idan ya siya miki mai kyau itama ki ce ya siya mata mai kyau.


9. Ki rinka tunatar da shi wurin siya musu kayan abinci,da yi musu sutura akai-akai, domin da ban tausayi ka ga namiji gidansa ana cin kaji amma miyan mahaifiyarsa kamar ruwan wanke kai, wallahi sai Allah ya saka mata, idan ya siyo kaji goma ko bai ce ba, ki ce wane zan cire biyu inyiwa Inna miya muje a kai mata, kuma shi ma zai kara sonki.


10. Sannan ko da wasa ka da ki sake ki rinka zagin uwar mijinki, domin wallahi magana fa yana zagayawa, za ki yi mamakin jin maganganun banzan da kika yi ya kai kunninta, babu ruwan ki, ko da ki na kyautata mata amma bata sonki ki cigaba wata rana za ta soke, idan har kina kyautata mata.


11. Sannan idan kin je yi mata wuni, to fa kada ki zauna baki komai, daki yayi datti amma ki ki gyarawa, immason samu ne kina zuwa ki fara mata hidima, ki kwaso kayanta ki wanke, ki share ciki da wajen dakin, ki mata gogye-gogye, wata ma idan ta iya kitso har tsefe kan uwar mijinta take yi, ta wanke mata ta rangada mata kitso, ko kuma ta ce a kira mai kitso ta biya kudin a yi mata.


Wannan duka muna daukan su abin wasa, amma ba haka bane, rashin kula da su shi ya sa iyayen mazajenmu suke takura mana, suke tsanar mu, kuma wani lokacin suna da gaskiya, domin wadansu suna daina zawa gaishe da iyayensu tun daga lakacin da suka yi aure, ke kuma baki iya kwadaitar da shi ba. Wannan shi zai saka ta fara cewa ke ce kike hana shi.


Wadansu matan ma har zagin uwar miji suke yi duk inda kika zauna sai ka zagye ta, idan za ai mata zani mai tsada ki hana, baki zuwa gaishe ta, kin je mata wuni kina cika kina batsewa dole ta tsaneki. Suma ‘yan’uwansa dole su tsane ki domin mahaifiyarsa ba ta sonki.

Yan uwa mata sai mu dauki darasi domin mu sai irin dubarun da zamu zauna da uwar miji da kyau.


0 Response to "Dubarun zama da uwar miji"

Post a Comment