-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Cikakken Bayanin Yadda Ake Kowace Miya A Kasar Hausa (Koyi Da Kanki)

Cikakken Bayanin Yadda Ake Kowace Miya A Kasar Hausa (Koyi Da Kanki)

Cikakken Bayanin Yadda Ake Kowace Miya A Kasar Hausa"Koyi Da Kanki"

        MIYA KALA KALA


KPOMO PEPPER SOUP(GANDA)

kisamu gandarki ki yankata , ki kankare ki wanketa sai ki dora har sai t dahu sai kisa niqaqqen tumatir d tattasai , albasa , gishiri maggi, spices, albasa sliced, d green pepper, yankakkiyar albasa , ayanka carrot slice a zuba aciki a bari su dahu sai a sauke aci d shinkafa ko cous-cous


MIYAR OHA

nama tsoka zalla

Ganyen oha, stock fish

Maggi, gishiri

Busasshen kifi

Cry fish, gwandar masar (melan)

 Manja Ki tafasa naman kizuba stock fish maggi albasa thyme tafarnuwa kayan qamshi su kuma dahowa ki yanka gwandar masar qanana kamar yankan maggi ki zuba akan namanki zuba busasshen kifi dakakkaken cry fish ki yanaka ganyen oha ki wanke ki zuba kisa soyayyen manja ki rufe idan tayi 15min sai ki sauke in ganyen yayi laushe aci d sakwara ko amala.


MIYAR UGU

kayan ciki 

Nama, manja

Ganda, agushi

Stock fish

Cry fish

Ganyen ugu

Tafarnuwa 

Thyme

Maggi , curry, gishiri Ki gyara ganyen ugu ki yanka qanana  ki wanki ki ajiye ki tafasa nama d kayan miyar aciki ki wanke stock fish kisa gandarki t dahu sosai ki yanka qanana k I zuba naman kayan ciki maggi gishiri curry ko kayan qamshi dakakken cry fish 2 spn ki barta t tafasa sosai sai kizuba ganyen ugu mai yawa ki rufe y tafasa zuwa 10minute sai ki sauke aci d sakwara ko tuwon shinkafa baya ma sakwara in t dawo tayi santsi


馃彽fish source cream馃構


馃彽kifi

馃彽tattasen Leda

馃彽albasa da tafarnuwa

馃彽magi, Cory, tym

馃彽man gyada

kisabtashe kifin kisoyashi sama sama kikwashe. 

Kimarkada tafarnuwa da albasa kisoyashi saiki soya tattasen ledan kizuba ruwa saiki bare kifin kifidda kayoyo da fatarsa, saikuma kisaka tsokar aturmi ko blander kidakeshi yayi luqui saikijuye a tukunyar kizubasu magi dasuransu Idon kaurinsa yaimiki dai- dai  saiki sauke


     馃構馃構馃構yanada dadi kina iyaci daabunda kikayi ra'ayi


MIYAN KIFI

______________

Sukumbiya Danye Me Kyau 1

Tattasai 2

Attaruhu 3

Cabbage

Albasa 1

Curry

Maggi 

Mai

:

   Zaki Wanke Kifinki Da Lemon Tsami Ko Toka Domin Fidda Karninsa Da Kuma Yaukin Dake Jikinsa Sai Ki Yanyankashi Amma Sai Kinyi Sauri Domin Idan Kankarar Jikinsa Ta Narke Zai Iya Dagargaje Miki Wajen Aikinsa, Sai Ki Barshi Yasha Iska Domin Ya Tsane,in Ya Tsane Sai Ki Barbadeshe Da Magi Ki Jerashi A Farantin Gashi Kisa Shi A Oven Idan Kuma Baki Da Oven Din Sai Ki Soyashi A Mai Amma Karki Yawaita Juyashi Gudun Dagargajewa,


Idan Yayi Sai Ki Aje Ki Ki Dauko Attaruhu Albasa Tattasai Da Cabbage Da Kika Yanyanka Kika Wanke Ki Dora Kasko A Wuta Kisa Mai Ki Soyasu Kisa Maggi Da Curry Idan Sun Fara Hade Jikinsu Sai Ki Dan Sa Ruwa A Ciki,sannan Ki Kawo Kifin Kisa A ciki Yayi Kaman 10minutes Saiki Sauke,ana Ci Da Bread Ko Haka Kawai Da Dan Juice.*MIYAR ALBASA*


*Ingredients*

_Albasa_

_Tsokar nama_

_Attarugu_

_Tomatoes_

_Curry_

_Thyme_

_Man gyada_

_Salt_

_Maggie_


*Method*

_Da farko zaki tafasa nama tare da albasa da spices da seasoning bayan ya dahu saiki kwashe shi ki daka shi saiki yanka albasa amma mai yawa akeso kamar ukku amma manya manya saiki sanya tomatoes kamar biyu  saiki sanya attarugu shikuma kamar ukku ita albasar grating dinta zakiyi saiki soya mai ki zuba albasar tare da jajjagaggun attarugu da tomatoes saiki sa Maggie da salt da curry idan ta dahu saiki zuba naman ki wanda kika daka saiki motsa shi zuwa kamar 5mnts shikenan saiki sauke_MIYAR KANTU (RIDI)*


*Ingredients*

_Kantu (ridi)_

_Nama_

_Kifi busashshe_

_Albasa_

_Attarugu_

_Ugwu or Alayyahu_

_Maggie_

_Salt_

_Thyme_

_Spices_

_Mai_


*Method*

_Zaki tafasa namanki da seasoning da spices saiki soya kayan miyarki acikin mai saiki zuba namanki wanda kika tafasa ki sanya har da ruwan da kika tafasa naman acikin kayan miyar saiki sanya kifin ki busashshe bayan kin gyara shi da ridin ki bayan kin daka shi watau (kantu) wadda akeson yanwan shi yakai kamar  one cup saiki rufe tukunyar ki barshi ya dahu zuwa kamar 20 mnts saiki yanka ganyenki ki xuba ki barshi zuwa kamar 5mnts shikenan kin gama_*MIYAR OFFORIRO*


*Ingredients*

_Tattasai_

_Attarugu_

_Albasa_

_Nama_

_Stockfish_

_Crayfish_

_Man ja_

_Kayan ciki_

_Seasoning_

_Spices_

_Alayyahu_

_Garlic_

_Maggie_

_Salt_


*Method*

_Zaki wanke stockfish saiki dafa shi ajeshi a gefe saiki tafasa nama da kayan ciki ki sanya albasa garlic seasoning da spices saiki yanka tattasan ki da tomatoes da onions amma a tsaytsaye saiki daura man ja kan wuta saiki zuba kayan miyarki  ki soya saiki zuba crayfish dakakke da naman da kika tafasa tare da stockfish saiki sa maggie da salt da spices saiki rufe idan komai ya dahu saiki sauke dama already kin dafa alayyahunki bayan kin gyara shi kuma ba tare da kin yanka shi ba saiki hadashi da miyar saiki motsa._


*MIYAR ZOGALE*


*Ingredients*

_Tattasai_

_Attarugu_

_Albasa_

_Zogale_

_Maggie_

_Gishiri_

_Garlic thyme_

_Seasoning spices_

_Nama_

_Kifi busashshe_

_Man ja or man gyada_

_Gyada_


*Method*

_Zaki tafasa nama ki sanya thyme da maggie da albasa bayan ya tafasa saiki sanya mai a tukunya ki soyashi da albasa saiki zuba kayan miyarki ki kuma sanya naman da kika tafasa tare da ruwan da kika tafasa naman saiki zuwa gyadar ki wadda kin riga kin gyarata kin daka ta da busashshen kifin ki shima bayan ki gyara abunki saiki sanya curry da maggie gishiri saiki barshi yayi kamar 10mnts saiki zuba zogalen ki bayan kin gyarashi anaso ki zuba zogalen da yawa domin anfiso miyar tayi kauri saiki barshi kan wuta yayi kamar  15mnt shikenan saiki sauke_


Miyar Awara


馃彽Kayan  miya

馃彽Awara 

Uwar gida zaki hada miyarki yanda kikeyin miyar dage dage sai miyarki tahadu saiki yanyanka Awara ki kanana saiki zuba acikin miyar kibata 5 to 6 mnts saiki sauke zaki iya ci da kowane abinci aci lpya.


馃彽miyar kwai da dankali馃構


馃彽poteto

馃彽kwai

馃彽kayan miya

馃彽albasa

馃彽nama ko kifi

馃彽man gyada

馃彽magi da Cory

馃彽tym onga


馃彽zaki soya namanki kijajjaga kayan miya kisoya saiki zuba ruwa, saiki feraye poteto kiyanyakashi kanana kizuba saiki zubasu magi da Cory da tym kirufe Idon yanuna saiki fasa kwai kizuba onga kikada sannan kijuye amiyar saiki yanka albasa kizuba, kinadan motsa miyar donkarya kama had kwan yanuna kisauke.馃構馃構馃構MIYAR GYADA*


*Ingredients*

_Kayan miya_

_Nama_

_Tantaqwashi_

_Gyada_

_Alayyahu_

_Kabewa_

_Daudawa_

_Mai_

_Kayan qamshi_

_Spices_


*Method*

_Zaki tafasa nama da kuma tantaqwashi da albasa maggie saiki sanya kayan miyarki acikin man da kika soya ki barshi zuwa kamar 10mnts kina soyawa saiki zuba ruwan da kika tafasa naman da tantaqwashin saiki yanka kabewa ki dafa ta saiki daka ta ko ki markada ta saiki zuba acikin kayan miyar da kika daura akan wuta saiki dan qara ruwa saiki zuwa gyadarki wadda kika daka tah sai kuma ki sanya kayan qamshi da daudawa da maggie bayan ta dauki kamar 25mnts tana dahuwa saiki zuba alayyahu shi kuma saiki barshi ya dahu zuwa kamar 5mnts saiki sauke shikenan kin gama miyarki ta gyada_      Kici da shinkafa ko kuskus  taliya 

ko makaroni. 


MIYAR HANTA

By Ameenah sidi

Ingredients


Attaruhu

Albasa

Tafarnuwa

Danyar citta

Curry

Mai

Maggi

ki wanke hantar ki yankata kanana ki sa a tukunya ki dafa da

albasa da citta da magi,ki jajjaga attaruhu da albasa da danyar

citta da tafarnuwa da mai ki zuba akai idan hantar ta dahu,kiyi

ta juyawa kisa magi da curry da gishiri,in tayi ki sauke,idan tayi

miki kauri zaki iya kara ruwa kan ki sauke.


Ameenah Nasidi's Kitchen馃崠馃崡馃嵅


SPICED CHICKEN PEPPER SOUP

BY Ameenah Nasidi

Ingredients

Zabuwa

Kaza

Water

Pepper soup seasoning

Mint(chopped)

Garlic(crushed)

Chillies(chopped)

Crayfish(ground)

Onion(chopped)


Yadda Za'a hada

Wash d meat(zabuwa da maza) and put it in a pot with a little water, season with salt, chopped onion, chillies and crushed garlic and boil for 20 minutes. Add d pepper soup seasoning and continue to cook for another 20 minutes to till chicken becomes tender, add d crayfish and mint leaves, stir and simmer for 8 minutes add season to ur taste and bring it down. Aci Dadi lafia make u no forget Meenah...馃構馃槣


miyan jajjage


_Ababen bukata_

*tattasai

*Attarugu

*Albasa

*carrot

*mai

*maggi

*Nama ko kifi(optional)

*peas

*dakkaken barkono

*curry

*tafarnuwa


       _yanda zaki hada_


Zaki jajjaga tattasai da taruhu da albasa da tafarnuwa wuri daya,a daya bangaren kuma kin tafasa namanki,daganan saiki daura manki akan wuta idan yayi zafi sannan saiki kawo jajjagagun kayan miyanki ki juye idan suka fara soyuwa saiki juye namanki da kuma ruwan tafasan namanki aciki ki saka magi,gishiri,curry,thyme da kuma dakkaken yajinki sannan sai carrot,shikuma peas dinki dama kin tafasashi yayi laushi saikawai kijuye acikin miyan kibasu 10 to 15 mnt zagika manki yafito Saika wai ki sauke miya ta hadu saiki dubawa oga dakuma maman Nu'aiym 🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲🍲


       Banhana a aikawa yan uwaba amma plss kar a canjamun komai idan kuma anyi ban yafeba.


BITTER LEAF N EGUSI


馃崚Sai kin wanke bitter leaf yfita dai dai to yr test OK

Sai kikawo agushinki nikeke sai kifara haza mai a huta inyayi zafi kidama agushin ki kaman zaki dama koko sai ki zuba a tukuyar da kika haza a wuta da mai sai KIZUBA damai mai agushi da kika dama sai ki suya kaman 3to5 min sai kizuba nikeken kayan miya ki hada su kisoya lokacin ki Riga kin tafsa naman ki sai kizuba a agushin kida kayan MIYA da tun dah kiriga kin soya agushi da kayan MIYA sai KIZUBA nama kisa komai naki su maggi , curry gishiri, da duk abunda kikeso OK Sai last of all bitter leaf naki kibarshi for some time ki kwashe馃構馃構馃構馃崚       *chilled tomato soup*


*kayan hadi*

TUMATIR MANYA 5

ALBASA BIYU

MANKUDI

GARIN YAJI CHOKALI BIYU

CURRY POWDER

MAGGI DA GISHIRI

TAFARNUWA UKU

THYME


*yadda ake hadawa*

1) zaki wanke tumatir dinki da albasa,tareda sauran kayan hadinki harda tafarnuwar,,saiki markadesu a blender dinki,,karki zuba ruwa dayawa daidai misali.


2)zaki zuba manki atukunya,ida yy zafi saiki juye wannan markadannaki,rufeshi zuwa minti biyar,,saiki.zuba maggi gishiri da corry dakuma wannan garin yajinnaki,saiki juya harkomai yahadu,,saiki rufeta kibata kamar minti 5, saiki sauketa insha Allahu lokacin tadawo,kinyi miyarki ta tumatir a saukake👌🏻


*_POTATO SOUP_*

_INGREDIENTS;_

_Fish._

_Potatoes._

_Carrot._

_Salt._

_Maggi._

_Butter._

_Onion._

_Pepper._

*_PROCEDURES;_*

_Zaki wanke kifin saidin a saka a tukunya kisa Maggi,salt da albasa ki rufe sai a daura a wuta,a kankare  carrot a wanke,a feraye dankali a wanke sannan a yanka da carrots kanana a zuba a cikin kifin._

_Ki wanke pepper da onion Ki yanka a zuba a ciki su dahu suyi laushi sannan Ki sauke, Ki saka mixer Ki farfasa yayi laushi sosai ko Kuma Ki zuba a blender ki markadesu._

_Ki Sami mazubi mai zirfi ki zuba ki sa butter kadan sai a Sha ko Kuma a ci da biredi._

*_HEALTH TIPS._*


SOYAYYAR MIYAR KODA DA CARROTKODA

ALBASA

TUMATUR

CARROT 

KOREN WAKE

ATTARUHU

TATTASAI

 

Dafarko zaki sami kodarki ki yayyankata ki wanketa kisa gishiri maggi kayan kamshi ki soya kodar inta kusa soyuwa seki yanka albasarki akai seta fara soyuwa seki barbada fulawa akai saiki zuba ruwa dan kadan seki jajjaga kayan miyarki ki zuba  ki cigaba da juyawa sai ruwan yakusa konewa saiki zuba karas din dasu koren wake dasu maggi saiki rufe kibata wuta kadan da haka zata karasa nuna se aci da shinkafa ko sakwara😋😋FRIED PEPPER SOUP

 (Obe Ata Dindin)INGREDIENTS:


1.Kayan ciki,Eggs

2.Albasa, attarugu, tumatir, tattasai

3.Manja/mangyada

4.Maggi, salt

5.Curry, thyme, crayfish, garlic powder, ginger

powder da sauran kayan kamshi.

PROCEDURE:

Ki sami tukunya ki sa manja, idan ya narke sai ki

sa tafashen nama ko kayan ciki ki soya shi, idan

yayi sai ki kwashe, sai ki juye yankakken

albasanki, sannan ki juye nikakken kayan miyanki,

yayi ta soyuwa. Idan kayan miyan ya nuna, sai ki

zuba su maggi da sauran kayan kamshi, ki barshi

yayi 2mnt.

Daga sai ki juye kayan cikin, ki jujjuya ki bashi

kamar 5mnt, a can kuma already kin dafa kwai ko

guda nawa kike so, sai kawai ki tsumbula su a

ciki idan miyar ta nuna.

Za a iya cin miyar nan za da rice, yam, cous cous

da duk abinda zaki hada shi dashiWasu lokuta za ki ga kabeji ya cika gari ya yi

araha sosai har mu rasa yadda zamuyi da

shi. Akwai hanyoyi da dama da ake sarrafa

kabeji wanda yawanci arowa mukayi daga

wasu kasashen, saboda muma bai kamata a

bar mu a baya ba duba da dimbin amfanin da

yake da shi a jiki

Abinci masu kayatarwa da akan yi da kabeji

sun hada da

1- Doluman

2- Miya kala kala

3- Salad

4- Coleslaw

6- zuba ssi a cikin wani abincin domin ya

kara armashi

Da sauran su.

A yau ina dauke da Miyar Kabeji ne. Sai a

biyo ni.

Abubuwan Bukata

1. Nama

2. Kabeji

3. Albasa

4. Attarugu

5. Karas da duk wani kayan lambu da kike

bukata a ciki

6. Man gyada ko zaitun (wanda ake miya da

shi) banda manja

7. Garin Corn flour

8. Ruwan naman kaza wato stock

Yadda ake yi

Za ki yanka Kabejin ki bayan kin cire gurin

taurin, sai ki yayyanka shi yadda ki ke so.

Manyan yanka ya fi saboda kanana yana

narkewa. Ki zuba kabejin cikin ruwan gishiri,

kina iya wanke shi a take ko ki bar shi na

dan wani lokaci.

Ki dora tukunya a wuta ki zuba mai dan

kadan kamar karamin cokali 4 haka. Idan

yayi zafi sai ki sa danyen naman a ciki. Ki

bar shi ya soyu sai ki juya dayan gefen shi

ma ya soyu.

Sai ki zuba Albasa (ki yanka ta san ran ki),

ni markada nawa nayi. Ki dafa ta har ta

koma fara sai ki zuba Attarugu ki juya. Ki

dauko karas ki zuba. Kina iya ba shi dan

lokaci kafin ki zuba Kabeji din ko kuma ki sa

kai tsaye.

Za kiga Kabejin ya cika Tukunya. Kar ki

damu idan bai shiga duk ba, ki juya ki rufe.

Idan ya sauka ki kara har ya shige duka.

Ki dauko ruwan naman kaza (stock) ki zuba

ki jujjuya. Ki kara ruwa kadan idan bai isa

ba. Ki rage wuta ki ba shi kamar minti 30 ko

nama ya dahu.

Saura garin corn flour, shi za ki zuba shi

bayan Albasa ko Attarugu, kuma, ki na iya

bade naman da shi. Kar ki damu idan ba ki

da shi, kina iya kwaba garin fulawa kamar

cikin karamin cokali 1 da ruwan sanyi ki zuba

bayan kin sa attarugu.

Kin lura ban ce ki sa kayan Dandano

(seasoning) ba ko? Ki sa duk abinda kike so.

Gishiri, maggi, ganyen parsley, Curry, har da

daddawa in kina so. Ni ban cika sa

seasoning ba a cikin kayan Lambu amma na

saka ganyen Persley.

Zaki iya cin shi kadai ko da biredi, shinkafa

ko taliya ko da abin da ranki ke so. Tare da

fatan kun fahimta?         CABBAGE SAUCE


Barkanmu da wannan lokaci mai albarka a cikin wannan wata na rahama da ibada, da fatan Allah ya karbi ibadun mu. Wannan girki dai na masu karamin karfi ne irinmu domin mu samu damar canjin dandano a bakunan mu a wannan lokaci mai falala dan haka idan uwargida ta koyi wannan girkin to ko gidajen masu wadata ba zasu nuna mata jindadin buka baki ba saboda tsabar dadi da kamshin dandanon wannan girki sannan ko a ido wani ya kalla sai ya fara santi._


ABUBUWAN DA AKE BUKATA*


1- Kabeji

2- Albasa

3- Koren tattasai 

4- Jan tattasai

5- Magi

6- Gishiri

7- Man gyada

8- Nama kadan (idan da hali)

9- Kayan dandano (seasonings)


*YADDA ZA A HADA*


_Uwargida ta samu kabeji babba mai kyau sai ta yanke wannan jijiyoyin masu kauri na jiki sai ta yayyanka shi ta zuba a ruwa ta wanke sannan ta tsame ta ajiye, sai ta kuma dauko albasa ta bare ta yayyanka ta yanka mai kyau a kwance sannan ta wanke ta ajiye daban, sai ta kuma dauko tattasai kore da jan duk ta yanka su kanana suma ta ajiye daban_.


Sannan sai ta dauko kaskon suya ta dora a wuta ta soya nama amma naman bada yawa ake sakawa ba (kamar yanka goma kanana) idan kuma babu ma shikenan, bayan ta soya naman sai ta tsame shi ragowar wannan man dake kasko sai ta juye yankakkun albasa da tattasan nan ta soya su amma ba soyawa sosai ba_.


Sai ta dauko wannan wannan kabejin ta zuba akai sai ta dauko magi da gishiri da kayan dandano (seasonings) ta zuba akai sai ta dauko ruwa a kofi ta zuba sai taci gaba da soyawa sannan ta dauko wannan naman ta yayyanka shi kanana sai ta zuba akai, sannan taci gaba da jujjuyawa tana soyawa bayan mintuna zata ga kabejin yayi laushi sosai sauran kayan hadin ma suna hada jiki sun soyu gaba daya, sannan sai ta sauke ta dauko faranti (Plates) ta zubawa magida da iyali ta hada da lemon sha ko kunu mai dadi._


0 Response to "Cikakken Bayanin Yadda Ake Kowace Miya A Kasar Hausa (Koyi Da Kanki)"

Post a Comment