-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YAN ABUJA hausa novel

YAN ABUJA hausa novel

  πŸ’…πŸΌ YAN ABUJAπŸ‘°πŸ»πŸ’…πŸΌ


       


   BY HAERMEEBRAERH
Ina farawa da sunan Allah azza wa jal, mai rahama mai jin qai.Allah ka taimaka na isar da saqon alkairi kamar yadda nai niyya. Ameen


Wannan labari qirqirarre ne, ban yi dan cin fuska ko taba mutuncin kowa ba, zan yi domin samun qyara a al'umma musamman ma ma'aurata, dan haka nake roqon duk wanda Allah yasa ya karanta ya daure yai amfani da abinda yaji na alkairi a ciki, kuskuren daya riska , yai qoqarin kauce masa. INA GODIYA DA DIMBIN MASOYAN NOVEL DINπŸ‘΅πŸ» WATA UWAR πŸ‘΅πŸ» BAN FARA WANNAN SABON BA SAI DA ROQO DA

 KWARIN GUIWAR KU, INA ROQON KU DA KUCI GABA DA MIN ADDU'A ALLAH YA RABA MU LFY DA MEDIAπŸ˜‚  HAERMEEN HAMMAERH LOVE U ALL❤
Page 1: 

Gidan malam Baballiya, gidane mai girma na qasa, a tsakiyar garin kano, wanda ya qunshi mata biyu, Sarai itace uwar gida, sai Bilkisu, itace amarya, malam Baballe yana da yara guda hudu dika mata, wanda yake ta burin Allah ya azurta shi da da namiji, mai albarka, wanda ko bayan ba shi zai kula da wannan zuri'a tashi mai cike da rikici, domin tin yaran nashi mata na qanana gidan yake a cikin rikici, wanda Goggo ce sanadin komai wato Sarai, ita Mama Allah ya sa mata sanyin hali, amma kome za ai bata yarda a taba mata yar ta tilo ba, dan haka in aka ji rikicin ta to fa akan yar tane, ko shi ma ba zata tsaya aita bala'i ba , za dai ta tabbatar ta karbar wa yar ta 'yanci sannan ta ja ta su bar wajen, a haka Allah ya raya masu yaran su guda hudu, Goggo Sarai nada, Suwaiba mai shekara 19, Saudat tana da shekara 18 wanda da watanni, sai  Salma me shekara 16, Mama  Bilkisu na da Juwaira wadda take sa'a ce ga Salma kwana uku ne tsakanin su, yanzu ta na dauke da tsohon ciki, wanda gashi nan haihuwa ko yau ko gobe. Sai dai mui fatan Allah ya amsa adduar Abba Baballiya domin kullum fatan shi Allah ya dube shi ya bashi namiji, mutum ne shi mai sanyin hali amma yana iya qoqarin shi na ganin ya isa da gidan shi, badan ma qoqarin da yake ba da tabbas Goggo Sarai zata zama itace mijin a gidan.

" wash Allah na, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Juwaira, taimaka ki kira min Abban ku a waje" da sauri ta dau mayafin ta da ke kan qofa ta yafa ta fita " Abba Maman mu na kiran ka,kai sauri Abba bata da lfy kamar haihuwa zatai ina jin" da sauri ya shiga takalmin ma yaqi qarasa shiga qafar tashi, " Subhanallahi Gimbiya, haihuwat ce?" ( yana kiranta da Gimbiya ne don a ilimin shi na addini ya san cewa kiran sunan mata da suna mai dadi sunna ne, inda yake kiran Goggo Sarai Sarauta) " Malam taimaka min na samu na kai uwar daka bana son zama a nan na haihu a rumfa" kamata yai ya kaita daki " amma mun shigo daka ko dai muje asibiti ?" Murmushi tai sanin cewa qarfin hali yai dan ya kwantar mata da hankali ya fadi hakan ta san bai da kudin yin hakan, ko na mota basu da shi, shi kuma ba mai kwadayi ba ne da zasu samu a wajen Goggo Balki, dan yayan ta kyawawa inji ta da fada YAN ABUJA ne su sai mai kudi, dalilin wannan ne yasa take samun kudi sosai, duk da fadan da Abba Baballiya keyi akan su daina biyewa samarin banza, amma sukai kunnen uwar shegu , da ya musu wuta2 kuma ya fara kulle sai ta saka su Islamiyya,daga sun fita zasu bi gidan qawaye su canja kayan su, su qara gaba neman mazan da zasu aure su su kai su Abuja, gaba daya basa hulda da qawyen su na unguwar, sai 'ya'yan masu kudi, saboda anan suke saka ran samun nasara. Kukan jariri ne ya dawo da Abba daga tinanin ina zai samo kudin kai ta asibiti ta haihu lfy? Da hanzari ya qarasa taimaka mata ta haihun ya kuma gyarata ya aje jaririn ya fita qofar gida, "Juwaira doran ruwan zafi in ya yi ki kirani" to Mamana sannu" cikin zumudi da washe kyawawan haqoran ta farare masu dauke da hushirya a saman su, fita tai taje dora ruwan taga ba iccen, amma duk da haka sai ta je ta dakko tukunya ta wanke ta zuba ruwan ta kawo wajen murhun ta aje, zata juya kenan ta ga mahaifin ta na shigowa da icce a hannu da kuma leda, da hanzari ta isa ta karba, tana mai sannu, komawa tai ta hada wutar ta dora shi kuma yai dakin, tsaki taji anyi a gefen ta, qin juyawa tai dan tasan ba zai wuce daya daga cikin yan uwan ta ba" aikin banza sai rawar qafa ake, duk dai abun mutum mace ya qara haifa balle ai mana wani rawar kan uwa ta haihuπŸ™„" hmmm Allah ya kyauta ya kuma shiryar da ku dika, to bari kiji yan baqin ciki, wannan karon namiji Mamana ta haifa a cikin gidannan, dan haka baqin ciki ya kashe duk wani dan hassda" wani uban ashar Salma ta saki ta tashi da hanzari zatai dakin su cikin rashin sa'a bokitin gaban ta ya bige tukunyar da take dafa abu, ai ko tini ta zube nama ne na kaza cike da tukunyat wanda yafi qarfin kaza daya, ko kulawa ba tai ba ta shiga dakin da gudu tana "Goggo ! Goggo ! Wai ni kina ina ne wannan mummunan labari ya same mu?" Da saurin su suka fito dikkan su an qule a daka ana hasafin kudin da suka samo, suna bata labarin mazajen da ke son su turo ai zancen auren su, " ke meye haka duk kin fadar min da gaba kamar Bilki ta haofi saurayi" hmmmm ai kinji ashe ke kikai mana mugun fata baki da tinani sai wannan, gashi nan to ya tabbata ai" damqo ta tai da qarfu cikin zare ido take tambayar ta" me kk nufi salma?" Ina nufin Mama Balki ta haifu saurayin da kullum kk mana mugun baki akaiπŸ˜™" ai wurgi tai da ita gefe, ta qume kai da hannun kujera sukai gaba ita da sauran yammatan nata, sai dakin Mama Balki" me nake ji? Me nake gani? " Abba ne ya baje ma Mama Balki nama balangu sai shayi daya hada mata da madara ta gwangwani da bred, "No i cant belive this, what is going on here, ina jaririn yake?"A cewar Suwaiba yar boko kenan,  don tana da NCE ita sai Saudat me kwalin secondary a hannu wanda duk daya take da su Maryam sai dai Juwaira tana son ta cu gaba ba halin ne yasa ta hakura, amma sakamakon ta yayi kyau sosai, both WAEC & NECO, " Haba Sarauniya ta ya zaki shigo daki haka ba ko sallama? Kuma bama ki tambayi ya ta haihu lfy ba? Aa tambaya kuke ina jaririn?" Eh ban ga zan iya ba ne shiyasa ban ba, tambaya daya ko da zan yi shine me aka haifa?" Na miji Allah ya bani, me zai faru? Allahn da ya ban ba wai dan ya manta ki bane kema ai, in kin kwantar da hankalin ki kema naki na tafe, dan haka ku fita min a daki tinda ba arziqin yi min sannu ne ya kawo ku ba"Hahaiiiiii Cassssss, eh lallai ne, kinyi da na miji shine zaki fara min kitifi ko, to bari na baki wani labari, a da kam na damu amma yanzu wani tinani ya wanken damuwa ta, Shi Uban yaran me ya ke da shi ya tara da zan damu raina akan namiji? Bayan ga Yaya mata Allah ya bani na zuwa Abuja ? Yarana kowanne namiji mai lafiya ya gansu sai ya yaba, dan haka bama zan bar labarin nan ya kwana ba: bakin ta suwaiba ke son rufewa tana" Goggo ki bari ba yau ba kin sanar da su, ko kin manta halin yan baqin ciki ne?" Aa Suwai ba Banni na fada masu suji dan baqin xiki ya mutu, yarana guda biyunnan sun samu mazajen aure mazauna Abuja, dan haka sai ka bude kunnen ka kaji, zan basu izinin cewa su turo magaba tan su a zo ai komai," hmmmm Sarai kenan wato kece ma mijin yau ni ne matar ko? Umarni kk ban akan mazajen auren si ko? Ba bincike ba komai kawai su turo b to bari ki ji na fada maki zan ba yayan ki mijin da suke so amma komai yaje yazo ki kuka da kanki kina jina ko? Fitsarartiya mara kunya mai raina mijin ta gaban Yayan ta dan su koya suma" ranshi bace ya matsa kusa da Maman yana bata naman a baki" Shewa Saudat tayi tace " ikon Allah wai na kwance ya fadi" dariya Suwai ba tai da Salma suka tafa har da uwar tasu suka fice suna dariya, can qasan maqoshin Goggo balki kuwa kishi ne damfare, kada kai tai a ranta tace" Hmmmmm to ai ku gama da yayana sun tafi ABUJA aure kashin ku ya bushe a gidannan.

Bayan kwana arba'in da shida ne, anyi suna da kyar wanda ba wani tari da akai an sama yaro Ammar, yaro kaykkyawa kamar iyayen shi, amma yafi kama da Juwaira, ba qaramin so da gata yake samu ba a wajen su, musamman Juwaira din ma, yan zu haka wasa take mai ta shimfida tabarma a tsakar gidan inda ya sha shara ko ta ina yayi fes da shi, dakin su kuwa ba abinda ke fitowa sai qamshin tirarwn wuta na tainke, Sallama Abban su yai  shigo jikin shi a mace, amma dik da haka sai da yai masu wasa ya sumbaci Ammar ya shafa kan Juwaira ya shiga cikin dakin Goggo Balki, kwalama Juwaira kira yai yace ta kira Mama.........

[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ   YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ   BY HAERMEEBRAERH

Page 2:

Da isa da qasaita ta shigo palon, hakan ne yasa Abban murmusawa duk da qunan da ran shi ke masa na abin da take yi mishi" Sarauta kenan yi ki qaraso mui abinda zamui na fita sallah"isowa tao tana hura hanci ta zauna a gefen damar shi inda Mama Bilki ke zaune a gefen hagun shi," da farko dai zan ma Allah godiya daya kawo man wannan rana danake ta buri, domin manema auren yaran nan ne Suwaiba da Saudat suka zo, kuma mun karbe su a gidan Yaya Balarabe cikin aminci da mutunci, inda suka damqa mana dukiyar auren yaran, Suwai ba kudin auren ta sadaki, na gani ina so da kudin da zata hada lefe dika, an bamu million daya da dubu dari biyu, sai na Saudat Ita kuma Million daya, a gaskiya na so naqi karba saboda kudin sunyi yawa, kamqr wanda zamu saida yayan?....... Abban su ina fatan dai bakai mana baqin cikin iyayen zamani ka sa an rage kudin nan ba?" Ta fada tana cike da tsoron ko dai an rage kudin ?" Amma dai na rasa me yasa baki da da'a wallahi? Ya ina magana ban qarasa ba zaki katse ni? Har kina ikirarin zan ma yayana baqin cikin iyayen zamani? Anya rayuwar da kk na da kyau kuwa? Gaba daya kin sa tarbiyyar yarana a lalace? Kin raina ni baki ganina da qima da mutunci? Kedai harka in ba ta kudi ba baki san komai ba? Na gode Allah da yasa ina iyakar qoqarin riqe gidana, ke kam na san da karuwanci zaki saka yayana yi su na kawo maki kudi, haba, bai ishe ki misali ba da Balki? Yarta daya amma ta tsaya wajen bata ilimin addini dana zamani daidai iyawar t, ke kuwa in ba Salma ba da tai sauka yarannan biyu ba zasu iya bude qur'ani sui karatu mai kyau ba, Salman ma gashi nan ne kawai, to ina mai maki nasiha da kiji tsoron Allah akan abinda kk, ina jiye maki ranar kuka, ranar dana sani, ranar ni yasu,........ " Aa faaaa, bafa zaka sani a gaba ba kana min mugun fata da kuma maganganu na nuna baqin ciki qarara a wannan al'amari, Yaya dai nawe ni nai naqudar su na haifa, ba wanda ya taya ni lokacin danake qafa daya lahira, daha duniya,ko akwai? Dan haka sai wanda naga damar su aura sannan zasu aura, nifa takura ce bana so tammm, yanzu ka bamu kudin lefen da sauran dan musulunci bai yarda kowa ya taba dukiyar auren yara ba sai su ehe" hmmmmm Sarai kenan to ai bari kiji iya kudin lefe zan baku, sauran kuwa sai sanda akai auren su zan baki su, da ke a taki qaramar kwakwalwar sai na dauku kudin na baki dika? Haka kawai aje wani abu ya faru bana fata ba ai aure ba ku barni da biya da tashin hankali? To bazai yu ba" Bala'i ta miqe tana zazzagawa son ranta ita sai an bata kudin, tashi yai ya kade rigar shi ya fice dika a gidan, daidai lokacin da Mama Balki ke cewa" Ubangiji ya sanya alkairi da albarka, Allah ya kare dukkan abinqi ya basu zaman lfy" Hahaiiiiiiiii Cassssss, ni zaki wa bariki? Zuciyar ki cike da baqin ciki amma wai kk addua mai dadi haka, dama ba daga bakin ki ta fito ba dana ce ameen" sa kai tai ta fice ta shiga madafin su ta hau aikace2, tana yi tana masifa kamar wadda ta zautu, yaran ne suka dawo daga yawon tazubar din su da sunan Islamiyya, " wai Goggo me ke faruwa ne gaba daya muryar ki har qofar gida" hmmmm wannan sallamammen uban naku ne mana, an kawo kudin auren ku sun riqe shida Balarabe, to wallahi ni ba zasu nuna min isa da iko ba, sai sun kawo kudin dika" Goggo kwantar da hankalin ki tashi mu shiga ciki ki gani" inji Suwaiba, daki suka shiga ta dakko mata maqudan kudi.a jakar ta saida tai baya dan yawan su," waya baki wannan kudi haka?" Alhaji Salihu mai tumbin Nera  kk ji, cewa yai ga su ko zan qara wsu abubuwa a lefe yaso bayar wa a can ya fuskanci za a iya cewa sun yi yawa, shi kuma yana ganin ko nawa ne zai iya kashewa ya samu yar zuma, ( Sunan da yakan kirata kenan lokacin watsewar su) dariya Saudat tai " Aaaaa kice Adda Suwaiba Alhaji yaji zuma yau" dariya sukai dika har uwar tasu suka tafa, baqin cikin ma da take ciki ta manta shi, ba sallah ba salati suna zaune ana maida tanda akai da yanda za ai.

Juwaiirah  ce na hangi goshin asuba ta na ta ibada, kamar wata babbar mata, Maman ta ta saba mata da tashin dare, dan ta sanar da ita cewar duk abinda bawa ke so ya roqi Allah zaibiya masa buqatar shi musamman a lokutan karbar addua wanda qarfe uku zuwa asuba Allah na amsa adduar bayin shi dan lokaci ne mai mahimmanci ga bayin Allah, " Ya Allah kaine masanin abin da ke zuciyata Allah ka biya min dikkan buqatu na na alkairi Ka sa Yaya Jabeer ya zama shine mafi alkairi a rayuwa ta duniya da lahira" wannan addu'ar ce tafi daukan hankali na, nace tooooo waye kuma Yaya Jabeer? Adduar ta ta ci gaba wanda tai wa iyayen ta da yan uwan ta da dikkan muslmi, bayan ta idar ne ta hau karanta Qur'ani da zazzaqar muryar ta, har aka kira sallah ta gabatar ta dora da azkar da karatu har gari ya waye, a sannan ne ta samu ta dan koma bacci zuwa qarfe takwas ta tashi, ta fara taya Maman ta aiki, bayan ta gama gyara gidan dan ba su ke girki ba balle ta taya ta aikin girki, wanka ta shiga ta fito,haka nan taji tana son yin kwalliya yau dan ita ba ma'abociyar yin ta bane sai dai tai kwalliya sama2 kawai , ta saka wata rigar ta doguwa ta atampa rigar na da fadi ta qasa unda ta sama aka dan tsuke ta da dogon hannu yanda rigar ta zauna mata abin kallo ne domin Juwairah  akwai shape mai kyau, gyara gashin kanta tai da kyar dan yawan shi da tsaho, bayan ta gama ne ta kafa dauri me kyau, ta samu tiraren ta ta fesa, tana gamawa ta je wajen Maman ta zata dau Ammar, Maman ke tsokanar ta" Aa kaga Juwairere saraunuyar mata,Juwairere  diyar Mamanta" ni mama na ce maki bana son Juwairere  Allah dariya qawayena suke in suka zo sukaji kina fada musamman Nafeesa" to in banda abinki Nafi ai qanwar ki ce kin fa bata kwana bakwai masu kyau" kin ga kuwa data tsokane ki sai ki murmushi saboda yarinta ce ba wani abu ba" dariya suka saka sosai suke dariya saboda sarai ta san maman nata na tsokanar ta ne again, basuji sallama ba sai ji tai an kama hancin ta," wannan dariyar taku Mama ba zata bari kuji komai ba , musamman wannan Juwaiirahn da ta bude wannan qaramin bakin nata take cikawa mutane gida da yar muryar nan ta ta"tsalle tai na murna ta kama hannayen shi dika" Yayana, wayyo Yayana kaine da gaske? I missed u so much Yayana, yaushe ka dawo? " Oh Juwaiiraah ko zama bai ba fa wannan zumudi a bari ya dan zauna ya huta mana" Mama rabu da ita nima ba qaramin Missing din Juwairere na nai ba, ban ga laifin ta ba dan ta nuna murnar ta na gani na" murmushi Mama tai ta fita debo masa dan ruwa ya sha dan gidan haka suka tashi ko na karyawa ba a miqo masu ba, jawo ta yai kusa da shi " Amma da Juwairere kin san na hana kwalliya ko?what if wani ya zo ya gan min kwalliyar mata? Ko a aike ki a haka kowa ya kallen ke? A gaskiya ni dai bana so, anyways yanzu ai ta qare tinda ga angon ki nan ya gani" πŸ˜‰πŸ˜‰ duqar da kan ta tai murna na ratsa ta daya kira kanshi angon ta, ga hannun ta dayake murzawa a hankali, karbe hannun ta tai ta canja mazauni tana turo baki, ita a dole fushi take,Mama ce ta shigo dauke da kofi a hannun ta ta aje mai a gaban shi ta samu wajen zama," Mama kin ga wannan yar rigimar ta turo baki, lallai akwai magana yau" Aaa ni kam ba ruwana ina gefe ba a shiga tsakanin ku ai ku" komawa yai kusa da ita ya dago kanta" Juwairere na me ya faru?"to ba ga shi nan ba wai JuwairereπŸ˜₯ ni Allah bana son sunan nan,gaba daya ka sa Nafee na tsokana ta, Kullum ta ganni sai ta hau ce man Juwairere ta qarasa yar kwallar ta na fita baki a gaba, dariya ta bashi ba kadan ba wauta da shagwabar ta na burge shi sosai" ki kwantar da hankalin ki princess ba zan qara fada ba inshaa Allah sai munyi aure" harara wasa ta mai tare da jin kunyar kalmar aure da ya ce ta fita a dakin da gudu tai tsakar gid tana dariya, kada kai Mama tai tace "Allah dariya kuke ban yaran nan ba kadan ba kun iya wauta" Mama kenan ba wauta bane da gaske auren ta nake son yi in Baba zai ban ita, itamma ba Abujan za a kaita ba, dan dalilin zuwana kenan, naji an kawi kudin wadan can marasa kunyar" hmmm haka ne Jabeer amma kasan ni ba ruwana da wannan kalmar ta yan unguwar nan ko, na cewar yaran gidan nan YAN ABUJA NE ba zasu auri kowa ba sai dan can, in su suna fda kuma sun yarda zasu aure su ni ban fada ba kuma ban ba yata izini ba , in da rabon can ne gidan auren ta yake Allah ya zaba mafi alkairi in ba can bane ni ko ina albarka na ke nema mata kullum" haka ne Mama, Allah ya shige mana gaba" Jabeer dan gidan Yaya Balarabe ne ya dawo daga bautar qasa inda aka tura shi illorin, ya kammala karatin shi bangare kasuwanci, to a yanzu haka yana taba saida jakunkuna da takalma, ba wani arziqi ne da shi ba, yayun ta sun so matuqa ace me kudi ne da sun aure shi ko dan kyaun shi, amma inaaaa talauci a cewar su ya dakushe tauraruwae shi.A yan kwanakin nan kusan kullum sai ya zo, ana haka Salma tai wani saurayi mai kudi shina ya fada mata a Abuja yake da zama, kuna shi sana'ar saida motoci yake, kullum in zai zo ya vaza uwar riga ya shigo mota mai tsada ya zo amma fa ba ko sisi, wataran ne ma zai dan samu ya siyo mata yar shawarma kamar mayya tana rawar kai saurayi ya siyo mata abu ta amshe ta shigo,itama tini ta i sahun manyan ta amsar kudin maza da basu jiki ai tabe2 , alhajin dai dake son ta shima ya matsa zai turo sanda ya turo magabatan shi sun sha mamakin ganin daya daga kayan da ya taba zuw da su da motar, amma suka basar, a tinanin su wata qila anko sukaiπŸ˜†.........

[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ   YAN ABUJA.  πŸ’…πŸΌ
   BY HAERMEEBRAERH
Page 3:

A haka aka karbi kudin auren inda gaba daya aka saka ranar auren su nan da wata daya, gori kam da baqaqen maganganu ba irin wanda Juwairah.bata karba ba wajen yan uwan ta, tin tana kuka har ta kai ta daina sai dai ta kauda kai sui tayi ranta na quna, takanji kamar ta ce Ya Jabeer ya fito ai auren. Wata rana ta na zaune tana yanka alayyahu ma Maman ta sai Adda Suwaiba ta fito ita da Salma, " hhhhhhh Adda dan Allah ki ga yarinyar nan, a kyau dai duk gidanan albarka tafi kowa, ta tsaya ta mori kyaun na ta amma tanaiwa kanta baqin ciki tsabar mugunta , ban taba ganin irin wannan yarinya va" hmmm ina ruwan ki uwar kinibibi taje ta auri wanda ta gadama ma ba Jabeer ba, danni wallahi ba kyau ba ba ilimi ba in baka da farare bugun Abuja, sannan ba zaka auren ka kaini Abuja ba wallahi kayi kyaun banza da kyaun halin wofi, dan ba su zan ci ba" dariya sukai sina riqe baki, alamun sun ma ta rashin mutuncinnan, girgiza kai tai tace" Adda Suwai kenan, ina kyautata zaton kun manta wa keyi, sannan kun manta dawa kuke jayayya, wanda duk zai wa wani gorin talauci to y sani ba da wannan bawan yake ba da ubangijin bawan yake, beside ba fa kusan sana'ar mazajen ku ba gaba ki dayan ku damuwar ku kawai a kai ku Abuja, ku matan Abuja ne, matan manya, bana maku baqin ciki, zanfi murna ace kuna gidan hutu dan nima ina ma kaina fata, amma zan baqin ciki ace baku da alkibla saita kudi da son abun duniya, Allah ya kyauta, ammmm for ur information, ni haka nake son Ya Jabeer ba dan dukiyar shi ba ba dan komai ba , Son shi ni kaina ba zan ce ga daga in da ya fito ba, na tainci kaina da So da qaunar shi ne kawai dan haka wannan matsalar ku ce wai rashin kudin shi, tinda ya zama jinin jikina ba zan iya rayuwa ba shi ba kun ga ko ko a wanne hali yake zan iya zama da shi" Tafi taji ana yi mai cike da shauqi idon Jabeer tap kwallar dadi da murna, Mama na daka tana mamakin yar ta ta, lallai yau an kaita maqura,daga kai tai tagan shi yana qarasowa gaban.ta, wata irin kunya taji ta lullube ta da ko guduwa daga wajen ma kasawa tai, dan tinda suke bata taba zayyane mai yanda take son shi ba, wanda da damar masoya shi ke dakushe ma su amashin soyayyar su, kafadun ta ya riqe ya juya ya kalli su suwaiba, inda suka qame qam suna wurga idanu, " Princess wadannan kalaman naki sun qara dasa man zazzafar qaunar ku da son ku akan na da, ba zan iya rayuwa ba ke ba, dan haka nake roqon Abba da ya taimaka ya auran ke nima a hada gaba daya da na wadannan fitsararrun marasa tarbiyya, ba dan komai ba sai dan a kafa tarihi tare kar muzo lissafi yana kwace mana" murguda baki Suwai tayi tana qunquni tai daki, tsugunnawa yai ya ci gaba da taya ta aikin ita dai kunya ta ishe ta a haka suka gama yiwa mama girki ko leqawa gaida maman bai ba ita kuma ta kasa fitowa dan komai akan kunnen ta akai, Abba ne ya shigo da sallama bayan sun amsa ne yace" Aa Juwaira Jabeer yau kune kuke mana abincin daren? " yana fada yana dariya, sosa qeya yai ita kuna ta rufe fuska ta je ta amshi ledar hannun shi, tai dakin Mamar ta da yasha gyara yake qamshin tiraren wuta na tsinke, Maman ce ta zo ta wuce su da ruwa a bokiti kanta a qasa dan yai yaran sun bata kunya sosai, Jabeer ne yai dariya yace" Hajiya Maman mu yau kuma kunya ta kk ji ne? Shiyasa sai yanzu kk fitowa da kk ji Abba ko? Ai dana sani to tafiya nai da muka gama hirar tamu" sosain hannun ta ta wurga mai tana " wannan danneman tsikannen yaron wato duk kauda kaina sai ka nunan kai dan zamani ne ko? Ai gashi kun ja min makara yin wanka sai da Abban nasu ya dawo" dariya sukai dika Abban ke tambayar me ya faru da hanzari Juwaira tace" ba...ba..komai Abba" dariya Mama da Jabeer sukai Mama ta wuce su Jabeer yace "Abba ka huta akwai magana a bakinnan nawa, ni dai in ke ba ki da abin cewa ni ina da shi" roqon shi take da ido ya bari sai gobe yau kuyar zata mata yawa, amma kanne ido daya yai yana mata kwalo sai ya fada yau, tura baki tai tai daki, bayan sun gama komai tayi wanka sunci abinci, in da wajen cin abincin ma Jabeer rashin ta ido ya so yi ta qi yarda, wai da sai dai suci a kwano daya, da taqi sai ya zauna kusa da ita, in ya faki idon kowa sai ya zura hannu a nata ya diba ya kai bakin shi yana lumshe ido, can sai yace" ke ni fa ban yarda ba ya akai naki ya fi dadi? " Kai Ya Jabeer da rigima kk, ni duk daya ne kai ne ka ji haka" to kawo mu canjen kwano in haka ne" miqa mai nata tai ya bata nashi daya ci gaba da ci ya qara zura hannu a wancan, " Tab in ba sai an qara canjawa ba me kk fakar idona kk sawa naki?" Yahhhhh" ta fada tana turo baki cike da shagwaba, " wai ni da kk wannan maganar ta ya akai kasan nata yafi dadi?" Saurin tashi zatai ya danne hannun ta da nashi, " Abba loma daidai nai a dikka" Allah yafi loma daya" πŸ˜”πŸ˜™ " Hmmm Abban su dan allah ka rabu da shirgin yaran nan mu ci abincin mu bana son kana wasa da cin abinci kar wani ciwon ya kama mana kai" kashe mata ido Jabeer yai ya matsa kusa da ita, daidai kunnen ta" to kinji yanda ake wa miji ko, sauran mui aure kina raba mana kwan irin haka" dariya ta gimtse," hmmmmmm bariki, har da Yayan ake zaune ake iskanci a tsakar gida, sannan in nawa sun fita ace masu yan iska, to ai bahaushe yace, qazantar da baka gani ba tsafta ce" muryar Goggo Sarai kenan, "Subhanallahi, me kk fada ne ke ko  agaban yara gasu gaba daya kin jawo su kun fito kun sani a gaba?" Eh abinda kaji na fada mana ko maimaici kk buqata na qara karanto maka?" To bari kiji mara kunya, Jabeer ya tabbatar man da auren Juwaira yake son yai, yana son a hada dana sauran ayi, dan haka wannan shirirtar taki da goregoren naki ya qare dan duk ina ji" Aiko ba wanda ya isa ya hada mana aure da wadannan yan maulan" kan ta rufe baki taji fauuu an make bakin da qarfi, saida bakin yai jini," kan uban nan Jabeer me suwaiban tamaka zaka mata wannan dukan, ko uwar ka Hansai ba zatai ma yata hukun ci ba balle Uban ka Balarabe" wani dukan ya kaiwa Saudat dake kusa da shi sosai mai qarfi saida ta kifa, " duk rashin kunyar da kikai ma Abba kan su zan huce ita kuma waccan hikuncin rashin kunyar da ta min ta karva" sannu uban su" inji Salma, aiko takalmin qafar shi ya cire ya murde hannun ta yaita maka mata, sai ihu take, Goggo ce taje da niyyar kwace ta, wani kallo ya mata da hantar cikin ta ta kada tai baya da sauri tana " Allah ya isan su baqin mugu kawai" sakin ta yai ya sa takalmin shi yai waje, Abba da Mama sai Juwaira da idon ta ya cika da hawaye suka shige daki suka rufe qofa suka bar su nan.


Washe gari sai ga Baba Balarabe yazo batin auren Juwaira da Jabeer, sadaki dubu ashirin, a taqaice dai dubu Hamsin ya miqa masu kudin komai dan iya su ya ke da,  take ita ma aka shaida hada bikin su dana yan uwan ta, sunyi murna sosai, inda suka sha gorin cewar " dadin ta kudin auren ma kamar anje siyan yar tsana a gwanjo dan ko matsayin kasuwa ma ba a samu ba" suna yi suna dariyar rainin hankali, ba wanda ya kula su, sauran dubu darin da yake da ita kayan gado masu sauqin kudi yaje ya siyo mata da kujeru, irin na talakawannan, Jabeer yai qoqari sosai Abba na ta hana shi, yace Abba dama ai a musuluncu haqqin miji ne duk wadannan amma al'ada ta sauya abun, dan haka na bar ku da siyan yan kayayyakin kitchen, Allah ya hore mana mu samu aiki mai kyau Abba kasuwancin nawa ya bude, komai zai zama tarihi, addua sosai Abban ya mai da godiya. Daki aka gyara mata a main house din su ya kewaye mata guda biyu da dan wani qaramin waje a matsayin kitchen sai wani budadden bandaki mara rifi daga cikin kewayen nasu dai, ba laifi daidai talaka, yanzu jiran ranar biki sike nan da tan satika.
A yau ne dimbin mutane manya masu manyan motoci da qanan mutane marasa abun hannun suka shaida daurin auren wadannan bayin Allah kamar haka, Suwai ba da Alhajin ta Salihu mai tumbin Nera, Saude da Alhaji Kalla na Abuja, Sai Salma da Alhaji Mansur, sannan kuma qaramar su Juwaira da Jabeer din ta, surutu kala2 ke yawo a tsakanin mutane wasu na sanya alkairi, wadan da suke bin bashin magana kuma suna gulmammaki akan su Suwaiba sun dakko ruwan dafa kan su ne basu sani ba, Salma kuwa bata da wayo, duk kyaun ta ta buge da auren talaka? Kowa dai da abinda yake fada, a haka aka tashi daga daurin aure, inda mazajen su Suwai ba suka ce su fa basu yarda ai komai a kano ba Abuja za a wuce ai dinna babba mai qayatar wa da abokan su, sai matan abokan su, ko dangin su ba za a dauki ko daya ba, shi dai mijin Salma shima cewa yai a bashi matar shi ya wuce da ita Abuja domin shi ba abokin mijin su Suwaiba bane, sun roqe shi akan yaje ai komai tare yaqi, dan haka kawai kauda maganar yai yace zasu tafi ba damuwa dangin shi da abokai na jiran shi za ai dinner, Ita kuma Juwaira sun yi yar walima kafin dare aka gama, YAN ABUJA KUWA jiki na rawa da daren nan, aka shirya su Goggo na kuka suna kuka aka fita aka daga sai ABUJA. Da dare kuma Juwaira na gaban Innar ta da tazo biki Inna Dije tana qara bata yan kayayyakin mata natural, wanda ta hada madara da zuma da ta sha dakakken kayan qamshi cikin babban kofi tace ta shanye, dama ta yini da yunwa tini ta shanye tsaf, ta qara mata da dafaffiyar kaza da ta sha kayan qamshi itama ta ci iya itawar ta, ( ita ni'imar mace ana son ta da dumi yan uwa, ba a son ni'ima da sanyi, dalilin haka ne ake sin muna yawai ta amfani da kayan qamshi su citta kaninfari masoro, da dai sauran su, suna saukar da dumi ga jikin mace, ko hadin su kankana da su cucumber korake mutum zai yana hadawa da wadannan, suna qara mai dadi da qamshi da amfani a jiki,) a haka aka sa ta gaba tai wanka me kyau da dan tiraren su na wanka dan duri, dan basu da arziqin siyan mai tsada, ta samu ruwan dumi mai hadin ganyen magarya da kaninfari kadan a ciki tai tsarki da shi sai qamshi ke tashi ko ta ina, tana fitowa Inna Dje ta bata misk mai kyau ta sa ta shafa a HQ, sannan ta miqa mata brush din ta ta wanke baki duk tana tsaye a kanta, ita ko kunya duk ta dame ta ga mutane ba a gama tafiya ba, ai ko tana gama wa ta sata tai alwala sukai daki batansa ta shafa wani kwalliya mai nauyi ba, iyaka ta gyara ta ta samata qanan kaya daga ciki riga da skirt masu matuqar kyau, sannan ta sa mata laffaya, ga qamshi na tashi ko ta ina, kunshin nan ya zanu kannan ya dau gyara na musamman , yan daukar amarya ne suka zo a mota biyu, tana kuja tana komai aka fiddata, wata goggon Su ce mai suna Kareema tace" yanzu Bilki ba wata yar nasiha haka za a fiddata baku mata ba ke da yaya?"" Hmmm Kareema kenan, ai Juwaira bata buqatar wannan, duk zaman ta tana nufin bata koyi komai ba a wajen mu? Ai ba zai mata amfani ba a yau ina jin taje da sawar  albarkar mu a rayuwar su dika" a haka ta tafi daki ta zauna sai hawayen rabuwa da yarta take abar son ta, an kai Juwaira lafiya kuna kowa ya kama hanya ya dawo, an barta daga ita sai halin ta tana ta zare ido dan hawayen sun qare mata......

..

.....

[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA    πŸ’…πŸΌ  


  


 Page 4: 
Tana cikin wannan yanayi na tinanin Maman ta da Ammar taji hayaniyar maza na shigowa, sauri tai ta dawo palo ta zauna dan bata yarda wasu qarti su shiga mata har dakin baccin su ba da sunan abokan ango a daren farko, zama tai ta nade qafafun ta a kujera, ta rufe kanta har fuskar ta, Sallama sukai suka shigo, akwai wasu daga abokan shi da basu san ta ba dan ba garin suke ba, amsawa tai da muryar ta mai dadin sauraro, kanta a qasa, tana tsaka da jin dadin ba wuta ba zasu ganta sosai ba aka kawo wuta, haske ya gauraye ko ina, ai ko da sauri ta qara duqunqunewa, dariya sukai gaba dayan su" to amarya ki kwantar da hankalin ki mu ba zamu takura sai kin bude fuska ba, angok ki zai bude maki da kanshi in mun tafi, sai dai akwai wasu shawarwari da nake son baki, wanda na san kin san da dama daga abubuwan zamab aure, amma wannan mata da maza sun rasa su shiyasa ake samun sabani mai yawa a gidan aure, na farko dai akwai son zuciya, miji da an kwana biyu ya daina dokin amaryar shi sai son zuciya ya shige shi, ya fara fito mata da halayen shi mara kyau na kwadayin son ya zamana ta fara taimakawa gidan dan ya samu sauqi, ba a ce mace karta taimaka wa mijin ta ba hakan abune mai kyau, dan zai qara mata samun lada mai yawa, sannan zata samu soyayyar mijin ta da yawa, amma abinda ba a so miji ya sa son zuciya ya dinga especting din matar da hakan,in batai ba a zo rai na baci, yana jin haushin ta, daga nan an samu matsala, ita kuma mace son zuciyar ta shine kwadayin abun da mijin ta baida hali, dan ta gani a maqota kama daga sutura, abinci, da abin hawa, sai ta fara nuna halaye na sin zuciya wataran har ya kai ga tana sabon Allah dan ta samu kudin wadannan , kinga kenan ta biye wa son zuciya daga nan aure sai ya lalace azo ana samun matsaloli, zan barku anan saboda dare nayi kuma na san amarya ta gaji tana buqatar hutu ko ba haka ba?" Murmushi tai mai sauti tace"Mun gode Allah ya saka da alkairi" Ameen" suka amsa gaba daya, anan wani abokin su kuma ya amsa yai masu addua mai yawa wadda zatai masu matuqar amfani a rayuwa in Allah ya amsa masu, a haka ne suka ce bari su tafi, ya tashi zai raka su, yana miqewa ya bige da jikin kujera, yar qara yai ta shagwaba kamar wani mace, tai sauri ta dago tana mai sannu, ido abokan shi suka zuba mata suna mamakin kyau na qaramar yarinya haka, nan gaba ta qara girma ya zata koma?πŸ€” ganin haka ne yasa yai sauri yai gaba yana "to kuzo mu tafi mana"😠 ( wai kishi ana kalle mai mata lolsπŸ˜‚) fita sukai suna zuwa soron gidan yace "to guys ni zan koma na gode Allah ya bat mana zumuncin mu da amana" Ameen" suka amsa, wani ne a cikin su yace " kai dai ba sai ka kore mu ba muma sauri muke , dan na kula ko second uku.ba ka son qarawa anan" dariya sukai yai wuf ya shige yana daga masu hannu. Zaune take ta hade kai da quiwar qafa taji shigowar shi, bayan yai sallama ta amsa ne ya je kusa da ita ya tsugunna, yanda nungashin shi ke sauka a kan hannayen ta daya riqe sai da ya sa zuciyar ta sauri, ga tsoro ga wani feelings sabo da ke shigar ta, " Princess kin ga ya da kkai kyau kuwa? Ba dan kar nai qarya ba sai nace tinda nake ban taba ganin kyakkyawa irin ki ba" Kai Yah Jabeer wannan kowa yaji yasan dadin baki ne kawai" matsawa ya qarayi sosai fuskar ta na saman tashi, amma kusancin su ba mai yawa bane daya qara matsawa hancin su zai hadu, sannan yace" Hmmm ke kk ga hakan amma ni iya gaskiya ta na fada" wani irin abu taji ya bi qafar ta har kanta, bata taba jin wannan feelings din ba" wannan shine auren dama" My Goodness, this is going to be awsome, da na zaci wata azabar ake sha kamar yanda qawar ta shamsiyya da akaiwa aure wata uku da suka wuce take fada masu," me kk tinani haka" ya fada a jikin leben ta da ya qarasa kai bakin shi jiki, da sauri ta miqe tsaye tai breaking kiss din da yaso ya mata, ta hau kame2 tama rasa ina zata shiga, daki zata ko waje zatayi, kamo kafadun ta yai dika ya hade ta da bangon da take tsaye kusa da bed room din su" calm down my princess, is not like i am gonna hurt u or something" murmushi tai na yaqe tace" Yah bacci nake ji jikina ciwo yake" " Ok to muje ki alwala mui nafila sai ki samu ki rage kayan jikin ki mu kwanta zan maki tausa ma" baki na rawa tana sauri cike da in-ina tace" Aaaa..... bama....bama sai .. ka min tausaaa ba " dari yai ganin yanda hankalin ta ya tashi kamar wadda yai wa wani abun already, he just almost kissed herπŸ™„, alwala sukai sukai salla raka'a biyu bayan sun idar ne ya kama kanta, ya fata kwararo adduoin da suka zo a sunna, na ma'aurata kamar haka" Allahumma innee as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha a laihi wa a'udhu bika min sharri ha wa sharri ma jabaltaha alaihi" bayan sun gama ne ya koma palo ya dakko ledar da abokan shi suka aje mai, ya dawo da plate da cu daya, juye masu kaza yai a ciki da chips din da yasha hadin hanta da kayan kamshi, ga attaruhu da albasa, an mata yanka mai kyau, kamshi je ya karade dakin daya motsa mata da yinwar da take tare da ita, ga kumaadara mai sanyi a gefe da jus din exotic na Dansa, niyyar ta ta qi ci, dan qawayen ta sunce in an bata kar ta ci, in taci sai ta biya shi da jikin ta, inaaaa yunwar ta ta motsa" Allah yana ban amshewa zan me yai zafi, iyaka na fara kuka nasan zai hakura" πŸ˜™ aiko yana miqowa daidai bakin ta cikin jin kunya ta amshe, tana are ido dan dadi, a haka ya na bata yana ci suka gama, bayan sun gama ne ya fara qoqarin rage mata kayan jikin ta, bayan ya dakko mata na barcin da zata saka, wuga ido ta fara ko ta ina, ga shi sun ciko da hawaye taf, "Yah Ka bar ni nai da kaina" OkπŸ€—" ya ja baya yaje ya cire nashi ya saka na bacci a gaban ta, lokacin da ya cire rigar da wandon ya cire vest da sauri ta juya,tana kwalalo ido wajeπŸ‘€ hankalin ta ya tashi gano yanda jikin shi yake, take jikin ta ya fara bari," like what u see? " d hanzari tace " no i don't infact banga komai ba" murya na rawa, " gaskiya Naseer ya kyauta danai wanka kan mu zo amma da bnsan ya zan ba yanzu dan a matse nake zuwa wankannan batan lokaci zai" zaro ido ta qara kamar su fadi qasaπŸ‘€ " Yah to kaje toilet mana tinda ka matsu?" Hmmmm gama ki ga me nake nufi" yana kashe mata ido dayaπŸ˜‰ take hankalin ta ya tashi dan ta gano shi yanzu, a hankali ta dau kayan tai palo ta canjo ta dawo yanzu kam she is crying like a bby, zuwa tai ta kwanta a hankali dan tai wa Inna Deeje alqawarin bazata giji mijin ta ba , zata bashi duk abinda ta nema mudin bai sabawa Allah ba, janyo ta yai jikin shi, yana shinshina qamshin ta, " kaiii amma princess gaba daya qamshin nan ya sa na qara qaguwa na kusanta da ke" shafa ta ya fara yana mata salon da ita kanta ba zata so ya daina ba, a wannan lokacin Yah Jabeer ya fara qoqarin cika aiki, addua taji ya fara ta saduwa da iyali, kamar haka" Bismillahi Allahumma janibna shhaidana wa jannibasshaidana ma razaqtana" kukan da take son yi ta mayar ta hadiye, bata qaunain da zai bata ranshi ya fasa, kuka da roqo da komai tayi mashi a ranar, har cewa tai tama fasa son nashi, tinda haka ne πŸ˜™ bayan komai ya dawo masu daidai ne ya mannata da qirjin shi yana mata adduoi da saka albarka, sannan yana nuna mata mahimmancin kawi mai budurcin ta da tai , da illar da zata same ta da bata kawo ba din, kuka take qasa qasa, tashi yai ya saka kayan shi ya fita ya hada mata ruwa mai dumi ya kaita bayin su ja su kadai a sata ciki taji dadiin ruwan sosai bayan sun gama sukai wankan tsarki suka fito suna zuwa zama. Tai dan lokacin qarfe 3:30 sallolin nafilar ta tai ta fara bacci  a wajen,sai shi ya daga ta bayan ya idar da nashi, sukai baccin su.


'YAN ABUJA kuwa bayan sun isa wani katafaren hotel suka sauka mai suna Chelsea hotel.................

[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA    πŸ’…πŸΌ

    


    BY HAERMEEBRAERH

Hey guys, i want u to know that i really and truelly apriciate ur love, Allah ya barmu tare, as for those of u that ar requesting for this novel ta prive dan Allah kui hakuri na kai page 5 as u can see wayata riqewa zatai in ina tura novel da yawa abun ba mutum daya ba, so dan Allah ai hakuri da ni.Tanx.I dedicated this page to all it's fans, and WATA UWAR's fans. ANA MUGUN TARE. ME LOVE U XOXO❤

Page 5:

Tinda suka je farfajiyar wajen bakunan su Suwaiba yaqi rufuwa, ganin irin manyan motocin da suka gani, wasu sai a American movies suka taba gani, wasu ma basu taba ji ko ganin su ba, ( abun ku da masu idon cin nera) hankalin su ya kai qololuwa wajen kwadayin son suga mahallin su, sun shiga wajen da ake gabatar da dinner, inda suka qarasa wajen hight table din su hudun su, iya ganin su iya ganin jajayen hulina ne, sai fararen kaya da sirkin ja, daga matan har mazan shigar kenan, sune kadai suka saka baqin lace da ratsin baqi, mazan su ma farin shadda da jan aiki a jiki da jar hula ne akan su, wani mutum babba suka gani a gefe mutane kowa ya shiga sai ya gaida shi, ya hakim ce a wata qatuwar kujera, suma tashi sukai suka kai mai gaisuwa sannan suka koma mazaunin su an fara gidanar da dinner lfy, inda daga baya aka umarci kowa yake yai serving kan shi abin da zai ci wajen maza daban wajen mata daban, wani irin nama ne na daban da aka zo dafawa aka mai dahuwar laushi sosai duk abin mutum ba zai gane na meye ba,  matan kuwa kaji ne da sauran tarkace abinci kala2 a wajen har da na qasashen waje, sunci sun sha, daga baya akai ta rabawa mazan wani ruwa a wata kwalba mai duhun kala, jikin su har rawa yake dan murna, kowa ana bashi ya kafa kai tas suka shanye, suka aje kwalbar, bayan an yanka cake ne da sauran bidi'o'i aka tashi daga wajen inda angwayen suna shiga mota suka bama matan wani ruwa a cups masu kyau da sirkin wani magani a ciki, suna sha take bacci ya dauke su, madadin su yi gidajen su da su sai naga sun dauki wata hanya kamar za a bar garin, wani katafaren gida ne suka isa mai gate guda uku manya, katangar gidan duk maitar mutum na ya gudu ba zai samu dama ba, suna isa wasu qattai ne naga sun fito murdaddu sun sha baqaqen kaya da neck tie red, daukar su Suwaiba sukai a hannu suka shiga da su gidan a wani qaton falon nan anan suka aje su kan kujeru suka juya zasu fita, ji sukai wata qatuwar murya tai magana, kai min ko wacce daki, ka hada su a gado daya, wani turmusheshen mutum ne ya fito ba riga daga shi sai gajeren wando, i have been wondering were on earth do they found his sizeπŸ€” God he is huge😱 ga tsaho ga qiba, ga tumbi, ga sanqo, ga gashin baki, ga hammatar nan cunkus, ga idonnan jawur, ga ga ga....... my goodness, i can not describe this guy, kawai gashi nan dai, haka ya tako da fataken qafafun shi ya kalle su suka duqa, alamun gaisuwa, daga masu kai yai ya ce" kuje sai nan da sati biyu ku dawo,dan ban taba ganin mata masu kyau irin wannan ba" yana lashe baki, daga kai sukai suka amsa da " to oga zaks, fita sukai kowa hankalin shi kwance dan sun san samun su zai rubanyu da yawa, Nicon hotel suka wuce su hole abun su, dan su dama sunyi auren ne dan gudun maganar mutane, amma ba dan sun damu da auren ba, tinda a cewar su mata na nan kamar jamfa a jos.

Shigar Oga Zaks dakin keda wuya ya isa gaban gadon, yana lashe baki, kashe wutar yai ya kunna bed sid lamp, cire masu kaya yai ya dakko wani magani ya shaqa masu, maganin bacci ne, wanda zai kai su kwana bakwai cif suna bacci ba tashi, ina ganin zai zame rugegen gajeren wandonnan nai gaba da gudu πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀.Ba shi ya fito daga dakin nan ba tin daren sai qarfe tara na safe hamma yake yana miqa yai wani bangare ya shiga wani daki, waya yai naji yana " ku shigo, ya aje wayar ya shiga wanka, wasu mata ne dattijai suka shigo, dakin da su Suwai ba suke nan suka shiga, gyara su suke, suna tausaya masu, amma dayar tace" hmmmm wama ya sani ko garin shegen son abun duniyar su ne suka hadu da su, ai kinga ban ga laifin su ba kwadayi mabudin wahala" haka ne kam" tafiya sukai bayan sun kammata, a palo suka hadu da shi yana zaune, ya baza uban tumbi yana kwasar girki, " daga yau duk wata shegiyar tsohuwa a cikin ku da ta qara gulma akan matan da suke shigowa gidannan sai na mai daku matana kuma ta inda baku tsammata ba tana zan na amfani da ku, munafukan banza da wofi" jiki na rawa baki na kyarma suka hau bashi hakuri, korar su yai ya barke da wata mahaukaciyar dariya.
Salma matar me saida mota kuwa, wani qaton gida aka kaita a wata unguwa a gwarinpa, wani qaton gida ne mai kyau, ya tsaida motar, fita yai ya je ya bude gidan da kan shi, ya dawo ya shigar da motar fitowa sukai yana riqe da ita a jikin shi, bayan sin shiga ne take ta zare ido ganin dukiyar dake gidan, wani daki ya kaita mai kyau, suna shiga ya janyo ta ya fara aika mata saqinnin shi, dan shi dama bai wani more ta ba sosai, kuma ba laifi tana tare da budurcin ta, ba sallah ba salati ba godiya da Allah na daren farko na ma'aurata ba adduar komai haka ya maida ita mace, yasha kuka da zagi, dan ashar sai wanda ta manta, bayan sun kammala komai ne yai ta rarrashin ta, qasan zuciyar shi yana " zakici uban ki ne wannan zagin da dukan da kk mun duk sai na rama na fanshe abuna, yar me kwadayin tsiya" amma a fili wani lelen ta yake kamar kwai, a cikin sati dayan nan ya nuna mata gata sosai, wanda ta dinga hango gidan su tana ayyanawa a ranta" tab haka rayuwar Abuja take dama, ga miji gangariya na samu, ga kayan alatu na ci na sha na kwanta miji namin hidima, tab amma an bar Juwaira a baya ina tausaya ma rayuwar ta" " tinanin me kike haka ?" " ba komai, ina tinanin ka ne kawai" ta fada tana wani karairaya ta haye cinyar shi, " woww karki damu ai gani kome kk so naki ne, nema kawai zaki a baki" dariya tai tana shafa jikin shi tana limshe ido, " da gaske Alhaji na?" Da gaske mana tambayi ki ga aiki da cikawa" hmmm ni dama dubu dari biyu kawai nake so zan je na dan siyo kayan sawa na gida, dan na ga ba a kawon kayana nan ba, kace a bari inna zo gidan ka akwai amma ka hana ni shiga dakuna ukun can, sannan kuma in da nake ba wasu kayan kirki" ( yarinya wannan lokacin nake jira da zaki nemi wani abu a wajena) amma a fili cewa yai shirya muje na kaiki ki siyo kayan" da sauri ta sauka tana murna ta saka kaya ta dau jakar da tazo da ita ta fito, tsaf ta ganshi a tsaye yana mata shegen murmushi,  fita sukai suka dau hanya, suna tafiya taga suna barin gari," ina zamu ne sweety?" Wani waje zan kai ki in kk ga wajen zaki ji dadi sosai" wooow u ar so romantic babe, i love u" I love u more dear" kiss yai wa hannun ta, a haka yana tuqi tai bacci, bata bude ido ba sai a wani qauyen da bata san ina bane, wani gidan qasa ne mai girman gaske, ko ta ina mata da yara qauyawa ne a ciki sai wasu dattijai a gefen wata bishiya, sina cin wani tuwo baqi miyar koriya sharrr da ita, da sauri ta miqe ta fara murza ido, a zaton ta mafarki take, " babe ina ne nan? Me muke yi anan? Ko mafarki nake ne?" Hhhhhhhh ba mafarki kk ba Salame, nan shine ya dace da ke, kuma nan ne gidan ki, na asali, can gidan gidan oga na ne daya karban auren ki, anyway , karki damu bangaren ki yafi na dika gidan kyau, da taimakon ogana, harda TV an sa maki, tin da ko gidan uwale da ubale ai babu su ko?" Ya fada yana wani shu'umin murmushi, ita ko ta dade da fara kuka harda majina, kuna take tana bashi hakuri ya maida ta ma Goggon ta ita ta fasa auren, wanka mata mari yai," dan uwar ki mai kwadayin nan an gaya maki wawa ne ni? Na kashe maki yan kudadeb nawa kice na maida ki gida, ai ke da gida sai kin haifi biyar a qalla, sai dangin ki sun manta dake , ba dai Abuja kk so ba, to ai nan ma Abuja ce, dan haka baki da damuwa,inna fita ku tabbatar kin biyo ni in ba haka ba gaban su zan fara ballaki, danni ba sabon abu bane wajena dukan mace" daga kai tai dan yanzu wani irin tsoron shi take ji ba kadan ba, hankailin tq in yai dubu to ya tafi yawo, musammab da ta shiga taga daki daya ne dakin nata da wata yar TV da kayan kallo, sai gado qarami da kujeru biyu, da yan kwanika da ledat daki, kai abun dai kamar wata mara gata, haka ta shiga tana kuka kamar ta suma, biyo ta yai yace ta biyo shi daki mai kallon nata, amsawa tai ta abishi kamar raquma, wani daki ne mai cike da tarkace da tsohon gado, sai wata uwar datti da aka tara a gefe na kayan wanki, ga poo din kashin yaro ba a zubar ba qazanta dai ta qarshen qarni kawai, wasu yammata ne a gefe an ci ma an yi fari ta fuska an dashe har fuskar tayi wani kampala kampala, ba kyaun gani, sun sha bra ta dame su anyi daurin qirji da yan wayoyi a hannu, manyan yayan shi ne, a qauyen da Talle aka san shi, mijin marka, markan ce ta fito kamar wata baqar mahaukaciya, futu2 da ita tana goge hanci da zanin ta, ido yai jawur, alamun girki take kenan, duk qauri da warin hammatar ta ya bude wajen, " dalla malama ki sauri yau zan koma ni" shigowa tai tana bin salma da mugun kallo, "wannan fa Talle?" "Qanwar ki ce, dama na zo ne na kawo ta zan koma, ki kula da ita in ta bar gidannan kashe ku zan , kuma haka" sa kai yai zai fita, " ina zaka rabon ka da nan wata uku kenan, sannan yau kazo ko kwana ba zakai ba zaka wuce"  " jarababbiya muje na maki ko sau daya ne ba dai jarabar ki in ta motsa har gabam yayan ki sai kin nema ba" eh naji din muje" a gaba ta sa shi sukai daki yaran na dariya suna tafawa, ita ko salma qafafun ta taja tai dakin da yake nata,gado ta fada tana kuka mai ban tausayi, ga mijin da take so cannda wata qazama yana mu'amalar aure da ita duk suna jiyo wa, ga talaucin da ta hango tsabar shi a gidannan, yau ina zata saka kanta😭😭😭 Oh Yau meye ranar kwadayin na ta? Kuka take sosai taji an banko qofar" Malama kije ki qatasa mana abincin tin da baba ya qule daka da marka, yunwa muke ji , dan yanzu kan su fito sai an gan su" shewa sukai yaran suka tafa, "Hahaiiiiiiiiiiii casssssssss " suka fada a tare, miqewa tai ido yai mata jawur tace" ni na sa uwar taku shigewa daki da ubam naku da zaku nuna min ku fitsarraru ne?" Ke malama yau zamu daga maki qafa ko dan darajar Baba na gari, amma ki kiyaye mu nan gaba mu zane matan baba muke ki tambaya kiji, sakarai kawai, kema ba zai wuce tarkon baba kika fada ba" dariya suka saka suka sake tafawa, wata ce da bazata wuce shekara 14 ba ta shigo dauke da bokiti akai na markaden koko, kallon su tai ta kauda kai , " ke jummala je ki qarasa abinci marka  bata kusa," " ku me kuke yi tin dazu baku je ba? Ba in da zani sakarkaru kawai" wucewa zatai huwaila ta janyo ta ta kwada mata mari, kuka ta saka tana" Allah ba zan ba mugaye kawai sai dai ku kashe ni, baku da aiki sai dai kuci kui wanka in su yaya Baban gida sun zo suita lalibe ku da sunan wasan abokan wasa kuke yi, ko ji kuke ban sani ba ne?" Shiru sukai suka sake ta suka kama hanyar shiga madafin nasu, kuka taci gaba da yi, a hankaki tai shiru ta daga kai taga Salma " laaaaa kece amaryar Baba da za a kawo dama?" Daga mata kai tai ta shige daki, shigat ta ke da wuya Talle ya fito daga daki...........[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ     ' YAN ABUJA  πŸ’…πŸΌ
      BY HAERMEEBRAEHPage 6: 


Yana gyara wandon shi riga a kafada, ita kuma ta fito da daurin qirji, sai miqa take bakinnan wani wari kamar an bude shaddar gidan haya, hammatar ta har wani kore2 brown2 take, qafar nan fururu da ita kan ya danqare, ba a qanin tsagar kitson ma, kuma gashi ita mace ce mai cika da tsahon gashi, yawu ne cike a bakin shi ya je ya zubar, yana masifa" ke ba a binda kk iya kuma kk si sai ki wanta a biya maki buqata baki san ya ake gyara ba sannan in na nema a wani wajen ki fi kowa kishi, to wallahi ba zai yu ba, ko ki canja hali ko wannan karon inna tafi sai na yi wata shida.ban.dawo ba" " kai hakuri Talle amma dai kasan ba laifi na bane ko, kana ganin baka bar mana komai kk tafiya, ni nake wahala na ma yara nai ma nawa yayan, sannan ga wadannan shegun 'ya'yan da iyayen su ba sa nan, duk a kaina, yaushe nake da lokacin gyara? Kawai hakuri xakai, in ka gyara kaga gyara, in baka gyara ba ka ga dan gundun uban qazanta a gidan ka" ta murguda baki ta wuce tana kada manyan duwaiwakan ta" ga mace har mace da mutum zai huta amma an kasje kai da qazanta Allah wadai" zib da yawu ya qara yi har zai fita ya tina da salma, leqawa yai yaga tana kwance har lokacin sai kuka take, dakin ta ya tura qofa ya hau gadon yandago ta, saka ta yai a cinyar shi taji wani amai ya taso mata sakamakon warin da yake na hammata ga warin yawu, da gudu ta fita waje ta kasa aman ga wahala duk ta ishe ta, kuka ta fashe da shi na takaici," ke dan uwar ku mai kwadayi ni zaki wa iskanci? Ni zaki fito kina toshewa hanci kina qoqarin haras wa? Yau zaki ci uban ki kan na tafi kuwa" janta yai da qarfi yai dakin da ita yaran nashi manyan suna labe suna jiyo kukan ta, ya wurga ta gado ya cire kaya ya hau aiki, kuka take tana kakarin amai amma saboda yunwa ba komai a cikin ta sai wahala kawai take kwasa, " ni ka daga ni kaje kai wanka kasan ba zan qi ka ba, wannan warin zai kashe ni in baka tashi ba,nimfashina kamar zai dauke" mari ya sakar mata ya ci gaba yana cewa" kema sai kin shaqa dan uwar ki niba a haka aka sani nai har sau biyu ba ban tsinci komai ba? Dan haka dole na sauke akanki dan inna tafi ban san randa zaku ganni ba" a haka ya gama abinda zai ya tashi gajiya fal jikin shi, ba wankan tsarki balle na daudar daya kwasa haka.ya fice ya sa kai yai cikin garin Abuja,inda ya barta nan kamar matacciya, ita kuma Marka ana can gabam murhu, anyi goho ana hura wuta, ko wanka bata damu da ta je tai ba, gaba daya murna ce fal cikin ta, yau talle ya cika mata aiki, hankalin ta kwance, dan ta sani talle ba qaramin gwarzon maza bane, ya qi tsayawa ne kawai ya kula da ita da iyalin shi dika, ga girma na kama su, dan shi zai yi shekara 47, ita kuma zatai 38,  lokaci ne da ya kamata su zauna su mori rayuwar su amma inaaa, kowa da nashi matsalar, tin asali ita ta bazama shi, qazantar ta da rashin sanin ya kamatan ta, shine sanadin kwadayin matan waje da yake, musamman in ya gansu fes da su, daya shigo ya ganta duqun2n ji yake kamae ya rufe ta da duka, a hankali ya fara da marin ta in ta cika mai ciki, sai duka ya biyo baya, a haka har halayen shi suka munana, lokacin da take son ya gyara lokacin shi kuma idon shi ya bude da matan waje, still ita kuma bata gyara ba, ga yaran su da suka lalace duk a sanadin muguwar tarbiyyar iyayen su, tinda in suka tashi kusantar juna ba ruwan s da yaran zasuji ko baza su ji ba,zasui abun su kamar dabbobi su fito suna zagin juna ko yabon juna a gabam yaran, ta haka Huwaila babbar yar su ta fara miqawa Baban gida cousen din su jikin ta yana lalubewa, domin so take itama taji.me Marka kewa ihu tana nuna jin dadin ta akai, ana haka Badamasi shima ya ke jan Jummala sui nasu, kafin kace me yara idon su ya bude, Haule ce kawai Allah ya sawa nutsuwa a yaran Talle kaf, dan ita har makaranta take zuwa, kuma mamar ta daban a gidan,bata san ta ba, shi kanshi bayace ga uwar ta ba, dan tinda ya saki uwar ta aje masa Haulen ba ta sake juyowa ba, dan gani suke gidan shi ba abin son hada zuria bane ba sam, haka rayuwar gidan Talle take, yana tare da iyayen Badamasi da Baban gida.wanda Yayan shi ne, iyayen su sun rasu,  suma Su Badamasin Mahaifiyar su bata da rai sai mahaifin su, watan ta shida da rasuwa, sun rasu ita da jaririn ta da tazo haihuwa, dan haka daga su sai uban su da yaqi aure sai bin 'Yayan jama'a sa'annin su Jummala, gidan Talle gida ne na marasa da'a da tarbiyya, ko kadan ba mai kwaba a gidan, lokuta da dama Marka na leqawa dakin Yayan mijin ta su watse tare,sakamakon nesa da mujin na ta keyi da su, wataran sai yai wata shida, bakwai baya nan, yana cikin garin Abuja, wannan ta'asar da ake ta tafkawa yaran basu sani ba,.domin a fili nunawa suke su ko gaisuwa basu ishi juna ba, amma da dare yayi in wani na buqatar wani zasu qwanqwasa qofa a bude su shige su gama su fice, wannan shine Gidan TallesiousπŸ˜‚πŸ˜‚


A bangaren amarya Juwairere kuwa, suna shaqar amarcin su cikin jin dadi so da aminci, a gefe ga qawar ta kuma yar uwar ta Nafeesa na debe mata kewa, da taya ta aiki in Yah Javeer ya fita kasuwa wajen jakunkunan shi, a haka dai ana cin dadi zara bata barin dami, sai ibtila'in talauci ya ziyarce su, anan haka Juwaira bata taba nuna mai wani sauyi ba sai ma qara mai qwarin gwuiwa da take kulluma, ana haka sai ta fara fuskantar canji daga wajen Surukar ta wato Hansai wadda suke kira innarmu, bata nuna mata a fili sai dai a qasa, da habaici, domin ba qaramin kwarjini Juwaira ke mata ba, badan haka ba tana jin zata iya furta mata abun da ke ranta, ( bankomai ke jawo wa bawa kwarjini ba kaga yana da maqiya amma su rasa ya zasui da shi face tasbihi,zikiri , da yawaita hailala da istigfari, komai maqiyin ka zaiyi, nafarko Allah zai kare ka ko abun ya same ka ka sani yana daga cikin jarabawar rayuwar ka shiyasa u can not escape it, iya hakurin ka iya lada da daukakar ka, na biyu yana sa maqiyan ka suji tsoron ka ka gagare su, ga soyayyar Allah da malaiku da bayin Allah managarta, mu riqe ambaton Allah a koda yaushe, kina tuqa tuwo ne, kina shara ne, kina tqfiya ne, kina ma megida wanki ne ko guga, kina ma yara wanka ne, ko zaki sauke tukunya ne, ki bismillah, komai zaki ki sa ambaton Allah a ciki rayuwar ki zata zama abin so wajen kowa, sannan Allah zai so ki ya ambace ki a tsakanin mala'ikun shi). Wannan dalilin ne yasa ta fito da dabarar yi maya zagon qasa wajen Yah Jabeer.

Wata rana ta zo za tai abinci sai ta share madafin ta ta gyara, ta qara dauraye tukunyar ta , sannan ta hada wuta ta dora ruwan zafi, ta fara gyra wake, ta gama da waken kenan ta wanke ta zuba sai ta yanka albasa a ciki dan yai laushi da qamshi, dama tasan ba su da kayan miya man ma manage za tai masu da shi, kuma da dikkan alamu in suka ci wannan nandare sai dai ai hakuri, ta kammala kenan tana shirin dakko shinkafa ta rege ta wanke ta nema ta rasa ko sama ko qasa, hankalin ta ya tashi sakamakon duba lokacin dawowar Yah Jabeer da ya kusa, " Oh ni Juwairah yanzu in ya dawo me zan bashi, ya wuni kasuwa, sannan ya bada kudi daidai gwargwado a mai girki, ince ina ta tafi to?"  " kin kusa gama abincin ne ? Dan na fara jin yunwa , innar mu ma na can tana neman abinci yunwa take ji sosai" " na shiga uku, kinga anan na aje shinkafar na kewaya bayi kan na fito na rege na saka ban ganta ba" baki ganta ba fa" inji Nafeesa, kuka Juwairah ta fara ta koma daki tai tagumi ta rasa abin yi, dabata ce ta fado mata, tashi tai ta samu wannan waken ta rage ruwan sosai, ta samu dan man daya rage masu, da dan wani magi da take da guda uku, sai gishiri ta zuba a ciki ta qara albasa sosai, inda suke shuka alayyahu ta je ta yanko mai yawan gaske ta zauna ta cinke ta gyara ta wanke sosai ta zuba, nan da nan abinci ya hadu murna tau tana godewa Allah da wannan dabarar da tai, duk da qarancin shekaru irin nata, bayan ta gama ta zubawa kowa ta kai masu, kan ta fita taji Innarmu da wani yaro tana "ka siyar shamusu nawa ya baka?" Bata jin me yaron yace," amma dai bai kyauta ba gaskiya, a fa wajen shi Juwairah ta sai shinkafar amma shine ya rage har nera saba'in dan nema mai kan buta" mamaki ne ya cika Juwairah, dama ita ta dauka??????

[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ
  

      BY HAERMEEBRAEHPage 7:

Bata qarasa mamaki ba taji innar mu na cewa, " shegiyar yarinya, daga zuwa komai na mu ya fara tabarbarewa, gaba daya Jabeeru ya tare a qasan ta, ko shigowa gida yai da mun gaisa wuf ta tafi wajen ta, ya dan zauna mui hira ma yanda muka saba  amma inaaaa an janye mai hankali, to ni ba zaki mulkar min da kamar yanda uwar ki tai ba, in dai ina raye, hqka kawai, ke na haifarwa dan? To mu zuba shege ka fasa" kuka ne ya kusa kwace ma Juwairah jin kalaman surikar ta, wannan wace irin rayuwace kuma?" Ya Allah help me" abinda ta iya furtawa kenan ta share hawayen ta ta koma ban garen ta, qarasa gyara wajen tai tai wanka, tai brush, ta gyara gashin ta da ta wanke, ta daure bayan ta shafa mai mai ta taje, ponytail tai ma gashin, ta dakko daga qanan kayan ta da, Inna Deejee ce ta siyo mata su yan gwanjo ne, amma masu mayuqar kyau, tin da basu da halin siyan sabbi, kalar shigar ta, kalar pink da black ne, riga da wando pencil, sun amshe ta ba kadan ba, fita tai ta debo garwashi ta saka tiraren wuta, sannan ta fesa jikin ta da tiraren, ta shafa humra, kyautar Goggon ta Kareema kenan, kafin kace me da ka kalle ta zaka dauka yar wani hamshaqin me kudin ne, ko matar wani attajirin, Nafeesa ce ta shigo" dadina da matat Yaya kina burgeni, ko ta wacce gaba aka latsa ki kina nan, a shekarun mu kina da kaifin hankalin da babba ma bai da shi, duba kiga yanda kikai mana dabara dazu, Innar mu da ta koma daki da ta ga abincin ban san me ya razana ta ba, dan naji harda ashar ta baza mana a dakin dazun" ta qarasa cikin dariya, " kai sisto irin wannan fasa kai haka, in kk fashe man kan nawa yayan ki ya dawo kin masa bayani ai" Sallamar shi suka ji da sauri Nafeesa ta fito zata bar wajen, tsayawa tai ta gaida shi sannan ta wuce, tana jin Nafee ta fita ta taso cikin yauqi da tafiya mai daukan hankalin masoyi, wani lumshe ido naga tana yi kamar mai jin bacci( duk a cikin salon daukan hankalin Yah Jabeer ne😜) tana isa wajen shi, ledar hannun shi ta karba, sannan ta jawo hannun shi zuwa daki, suna shiga kamar jira yake duk yar qibar nan tata da manyan duwais dinnan baya jin nauyin su, dagata yai ya manna ta da jikin bango,dariya take mai sanyin sauti, ta zagaye wuyan shi da hannayen ta , dora fuskar ta tai a kan tashi, tare da hade bakin su waje daya, sai da tai mai kiss mai tsayawa a rai, sannan ta kai bakin ta wajen kunnen shi tana mai sannu da zuwa, " Jarimin maza ina maka barka da dawowa, ina fatan yau kasuwa da mutanen cikin ta basu wahal min da kai ba ko? Dan in haka ta faru akwai hukunci mai tsanani akan su daga wajena" hura mai iskar bakin ta tai a kunnen tare da yin kiss a ciki ba shiri ya nemi wajen zama da ita a hannun shi, " a gaskiya samun mace kamar ki Juwairiyyana akwai wahala, u ar one in billions, samun kamar ki ancikin mata million zai wahala, ke ce daya tamkar da dubu, in zance zan tsaya fadan wacece ke bakina zai running out of words, so kawai ke kadai ce , kuna ke daya Yah Jabeer din ki ke so" wani irin dadi ne ya lullube ta, kamar yanda kullum take son faranta mashi, shima qoqarin shi kenan, basu da arziqi, ba su da abubuwan more rayuwa, amma suna da junan su, tashi zatai daga cinyar shi amma sai da ta goga mazaunan ta a jikin shi da yasa shi sakin yar qara, gwalo ta mai ta tafi da sauri zatai daki, binta yai a baya yana" ai baki isa ba, ki tsokanen ki gudu, haba yarinya, tsayawa zaki ki qarasa ladan ki kawai" dariya take tana bashi hakuri " dan Allah Babe ka bari kaci abinci kai wanka, sai namaka tausa kamar kullum, in yaso in ka samu qarfin jiki yau till down zamui" tana kaiwa nan ta rufe fuska tana dariya ta zagaye shi ta fita da sauri, zuwa tai ta hada mai ruwan wankan, ta dawo shi kuma ya shirya wanka, shiga sukai bandakin a tare bayan ta je ta rufe qofar bangaren su, wanka ta mai da kyau ta sa mai toothpast a brush din shi( mata da yawa suna cewa wai mijin su yana warin baki baya son yin brush da sauran su, shawara gare ki sister mai wannan matsala shine, ba a ce ma na miji je kai brush ko wani abu makamancin haka, dik da akwai mijin da in shaquwar ku ta kai qololuwa kina iya sanar da shi kuma ba zai damu ba dan yasan duk amfanjn ku ne ke da shi, so in ba irin mijin nan gare ki ba dabara zaki, ki hada maku ruwan wanka tare kafin wankan ki tabbatar kin gama gigita shi yanda ba zai maki musu a komai ba, daga nan sai kui wankan tare, in ba  kui tare ba saboda maybe yanayin gidan naku, sai saka mai ruwan ki kai masa da kayan wanka, sannan ki saka mai toothpast a brush ki aje mai a kusa, ba yanda za ai ya qi musammab yaga kin saka maku tare, kinga ba zai zargi kina jin wari bane daga wajen shi, har yai feeling bad kuzo kuna samun sabani) bayan ta mai wankan yayi brush daki suka koma, ta gyara mai jiki tare sa feshe shi da tirare, palo ta dawo da shi yana biye da ita kamar raqumu da akala, abinci ta zaunar da shi ta bashi, yana ta santi" kaiiiii amma ba qaramin birge ni kkai ba, kin san rabona da faten wake har na manta kuwa?" " naji dadi da yabawar ka Hubby" " kusa da ita ya matso" ke din ta daban ce, komai naki daban ne,Allah ya barmu tare" murmushi sukai dika, kiran sallar magrib ne ya katse su suka tsaya suka saurara sannan suka bi suma, bayan an idar ne sukai adduar da ake yi ba yan idar da kiran sallah, Allahumma rabba hadhihidda'awatittammah, wassalatil qa'ima, a ti muhammadal  wasilata wal fadeela waddarajatirrafee'a wab'athhu maqamam mahmudan lladhi wa adtah, innaka la tukhliful mi'ad, sannan suka dora da salatin annabi ingantacce, addua suka daga hannayen su sama sukai a tare ita da shi, suna idarwa suka tashi sukai alwala, shi ya tafi masjid ita tai a gida, bayan ta idar ne tayi azkar din bayan kowacce sallah ne, sai ta samu tai kuma azkar din yamma, tana idar wa ta miqe ta je tai wanka ta dawo dan ragowar abincin nasu ta juyo masu ta kawo ta hado da ruwa da komai ta aje a gefe, daki taje ta saka rigar baccin ta mai matuqar kyau da daukan hankali, sai ta dora zani akai, da hijab tana jiran sallar isha'i bayan tayi sallar ne da minti 15 ya shigo, sai da ya biya wajen Innar mu ya gaida su, baban shi na ta sa mai albarka, ita ko ta cinkishe fuska tana hura hanci, daya tambaye ta sai tai qaryar kanta ke ciwo, dan yau wuni tai da yunwa, can sai ta saki fuska " kasan da yake bana son faten wake, kuma bana son bawa yar albarkar nan aiki shiyasa, amma da shinkafa zan bata ko gwangwani dayar nan ne ta dafa min, tinda Nafee ita har yau bata iya tsantseni irin na Juwairah ba" ba komai Inmar mu kawo na kai mata za tai maki ai, ba zai yu ku kwan da yunwa ba" da sallama ya isa daidai Juwairah ta fito daga daki ta cire zanin ta da hijab din ta, tana qarasa shafa mai a cinyar ta, ko da ya higo tini ta sauya salon shafawar, sake baki yai kamar dolo yana kallon ta, qarasa shigowa yai ya aje ledar still idon shi a kanta, juyawa tai ta koma daki tana tafe tana juya bayan ta tana waigowa tana mai wani kallo da murmushi, ni dai tin da ya shiga suka ja qofar bam qara ganin me suke aikatawa ba sai dai kunnuwa na sun jiyo man Jabeer na  sambatu da bana gane yaren da yake, sayyarar qafa ta na ja nai wajeπŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀


Qarfe hudu na asuba suka fito sukai wanka tare da alwala mai kyau suka koma, bayan sun shirya ne suka fara habatar da nawafeel, kowa ya fara addu'ar shi, Jabeer ne ke hango baqi, a gefen shi dan ba wuta sai ta wayar shi suka kunna, miqa hannu yai yaga meye, dagawar nan da zai yaga shinkafar da Innarmu ta bashi ce jiya a dafa mata, " Ya salam ! Tab lallai da safe na shiga magana wajen innarmu, aiko ni tai na kawo ki dafa mata wai yunwa take ji, tin safe bata ci komai ba, bata cin faten wake, shine gaba daya na manta" " haba Yah Jabeer bai kamata ka manta da wannan mahimmin abu ba kuwa, domin yunwa ba ta da mahadi" a qasan ranta kuwa jinjina wa Innar mu take wajen iya hada makirci, matar da taci ta tande kwano, har ta aiko wai a dada mata in akwai, tace babu shine take cewa ba ta ci, ikon Allah, lallai Allah mai jin qan bawan sa mai tinawa da shi a kiwanne hali yake, da bata zama mai neman taimakon Allah a kimai ba da bai taimaka mata jiya ba da bama ta san me ake shirin kulla mata ba, kiran sallar asuba ne ya katse su ya fita masjid an yi sallah, ya dawo, ita kuma tayi tata a gida tai azkar tai karatun asuba da take yi kullum ba fashi komai aikin da ke gaban ta sai tayi ko rabin shafi ne kan ta tashi, tana rufe qur'ani ya shigo, lokacin gari ya dan waye, miqewa sukai akan zasu maida bacci, dan Nafeesa ke abin karyawa a gidan, in ba arziqin abin karyawan ma da dama koko kawai zasu dama su sha, sallama sukaji anyi..........

............

....

[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA.  πŸ’…πŸΌ     BY HAERMEEBRAERH


Page 8: 


Nafeesa ce ta shigo," Yah Jabeer Innarmu tace ka bada shinkafar tin da tayi wuyar dahuwa" πŸ™ˆ " inna lillahi, ni gaba daya mantawa nai shaf dana shigo, dan Allah ki bata hakuri kice yanzu za a dafa" tace in ka fadi haka na amso ka bata ta fasa wataran an dafa" "My goodness, yau ya zan na je gaida Innar mu, yq kk ga fuskar ta tai fushi ko?" 😱 " hmmmm ba kadan ba kuwa Yah, amma tace kar na fada maka tai fushi" Juwairah a ranta tace" ina fa zata so ya sani tinda tana son nakasani ta qarqashin qasa"πŸ™„ dauka yai ya miqa mata, yace ta bata hakuri sosai kan ya shigo, fita tai da ita tana mai dariyar zaka amsa ne in ka shigo. 

Bayan sun taba baccin su ne sun tashi wanka sukai sukai brush su ka shirya, hijab ta dora akan kayan ta matsattsu da tai ma mijin ta kwalliya da su kan ya fita, sun shiga bangaren na su Innar mu lokacin ta gama.raba abin karyawa, tace akai masu sai ga su sun shigo, duqawa Juwairah tai har qasa suka gaisa," Ya jikin Nafeesa tace bakiji dadi bane yasa ya aje bai baki ba" zare ido tai cikin duqar da kai," da sauqi Innarmu na ji dama sosai" to Allah ya qara lfy, yasa amarya za ai min ko ango, danni na gaji da lfy sa banga qaho ba aure wata na biyar kenan shiru ba magana" ta fada in a form of wasa take, amma duk wanda ya kula ya san magana take fada mata, murmushi tai sosai tace" Innar mu karki damu komai lokaci ne amare za a samo maki masu yawa da masu kawo cefane har sai kince sun isa haka" tana fada ta miqe tai wajen Baba Balarabe ta gaida shi, sake baki Innar mu tai, shiko gogan be gane magana suka sakar wa juna ba, dadi yake ji wai Innar shi da matar shi akwai shaquwa, har suna magana irin wannan a gaban shi, matsawa yai yana" akwai abinda zan taya ki ne Innata?" Murmushin qarfin hali tai ta ce eh ba a rasa ba, dan dai kawai kar ya koma wajen da matar shi take, " Baba ina kwana?" Lfy qalaou diyar albarka, kina lf" " lfy qalaou babana" " to madallah, Juwairah ina son ki ta hakuri da wannan Innar taku, wani hali ta dakko d ni kaina ta canja min kwata2 ba kamar yanda na santa ba, dan haka kema sai kinyi hakuri, abotakar ta da Goggon ku ba abu ne mai kyau ba, na yi nayi na raba su amma abun yaqi" " Ba komai Baba , ai uwa ce a wajena Innar mu ko da ba matar ka bace, mahaifiyar Yah Jabeer uwa ce a wajena, tinda ita ta haife shi, kuma shi din mijina ne, in ban so mahaifiyar shi a tawa ba ni kaina ba zan samu kwanciyar hankalin gidan aure ba, rikicin yawa zai min, da mahaifiya ma ana samun sabani dan haka ita ma a hakan na dauke ta, watarana ba zatai ba" " Allah ya miki albarka , halayyar mahaifin ki da mahaifiyar ki ba wanda kk bari" murmushi sukai dik, bayan sun gama gaishe2n su suka koma suka karya ," to ni zan wuce sai na dawo, ki kular min da kanki, kar ki wahal da kanki " tasowa tai ta zagaye hannayen ta a wuyan shi shi kuma ya zagaye qugun ta sukai ma juna kiss sosai, da kyar ta kwace kanta, sai wani shinshina ta yakeπŸ™„ " Yah zaka makara fa, ka tafi cikin amincin Allah, Allah ya bada kasuwa mai yawa mai albarka, ya kare ka daga haramun komai qanqantar ta, Allah ya hada ka da halal komai qanqantar ta, ka kular min da kan ka, ka tsaida sallah akan lokaci, in kaji yunwa ka taimakeni kaci abinci, kaga yanzu ba da bane ba abubuwan da sai na ci gaba da dafa maka kana tafiya da shi, karka barmin kan ka da yunwa kaji?" " Karki damu an gama ur higness" ya dan duqa alamar gaisuwa, dariya sukai ta raka shi har waje, ta dawo daki ta hau gyara wajen da suka ci abinci.


" kai jama'a wai dan tsabar baqin ciki na aje flask din nan anan an kai min shi can, ko uban wa ya ce a tavan kaya oho, shikenan mutum in yana haushin talaucin da yai mai katutu sai ya dinga taba kayan da ba nashi ba yana canja masu waje? Oh ni sarai na ga abin da ya ishen yau" kamar ba zata amsa ta ba amma taga dacewar bata amsar" Hmmmm Allah nawa inji bamaguje, to ai dai har yau wata kusan biyar ban ga daya daga YAN ABUJAN sun yi koda waya bane balle nace ko an yi maki wani aike na azo a gani, ana nan dai yanda ake, ba wani hura hanci da za ai mana kuma " haba kamar ta ari baki dan masifat da ta taso mata lokaci daya ta yunquro,sai bala'i take tana gore2n ai abinci ma wataran ita ke taimakawa, Mama tace daga yau in ta haifu karta qara taimakawar taga in bazata rayu ba ita da danta? Ammar ne ya kama hannun maman shi yana kuka, dan baya son hayaniya shi sam, daukar shi tai sukai daki sika bar Goggo na kumfar baki.

Oga Zaks na gani sun fito daga wani daki mai duhu sosai, Alh Kalla dauke da Saudat 

Alh Salihu dauke da Suwaiba, suna fitiwa, " to ku maida masu sabbin kayan da kuka zo da su kuyi gida,nan da awa uku zasu farka, kuma ku kwanta gefen su a matsayin bacci kukai, domin wannan magungunan da sukai ta sha zasu sa masu kasala da ciwon jiki, na kammala duk wani aiki da za ai akan su, kudi kuma sai kun ce sun ishe ku, dan mahaifar su na da kyau sosai, Dodo yayi farincikin samun ta, ba a taba kawo mata irin wannan ba, nima kuma shaida neπŸ˜‹, hahhahaahhha" godiya sukai suka canja masu kaya sukai mota da su sai cikin.garin.Abuja, kowa ya dau hanyar gidan shi, fadar kyau da tsaruwar gidajen nasu bata baki ne kawai, readers ku hango kowanne gida mai kyau kawai a idon ku, a gado suka aje su suka kwanta gefen su sukai ta baccin asara, basu suka farka ba sai wajen lq'asar, miqa Suwaiba tai, tana hamma, tana kallon dakin nata, ko ta ina dakin ya ruda ta, ko tunanin komai ba tai ba sai na bari taga wannan gidan na ta mai dimbin kyau, tashi tazo yi taji wani.ciwo a cikin ta komawa tai.ta zauna, tana "wasssshhhhhh Allahna, me ya samen a ciki kum? Duk jikina ciwo yake" kamar a tare suke wannan maganar da Saudat domin tafi Suwaiba raki harda kuka, a rude mazan suka tashi kamar ba abinda ya faru" me ya same ki Sweetheart?" Cikina" dagawa yai ya gani," Ayya kiyi hakuri zai warke a hankali hatsari muka samu a hanya, ke da yar uwar ki kwalbar cup din da kuke shan drinks ta cake ku a ciki, amma mun kaiku babban asibiti an dinke wajen, so a hankali zamu jira ya warke mu ci gaba da shan amarcin mu ko" ya fada tare sa jawo ta jikin shi yana shafa ta, kwantar da kanta tai a jikin shi kamar ba ita ba, tashi yai ya je ya hado mata abinci tana daga gadon ya aje mata, ya zauna yana bata a baki, wani dadi ne ya lillibe Suwaiba yau mafarkin su ya zama gaske, tana gama wa ta dau waya ta kira Goggon ta, wayar a kashe take ta kunna ta tanakiran ta ko bugu daya ta dauka kamar jira take, " haba yar nan yau wata biyar da kwana uku, kun tafi shiru ba magana ba aike" wata biyar da kwana uku??????............

[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ     'YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ

        BY HAERMEEBRAERH
Page 9:

  Tinani ta ke son tayi, amma kanta ya kulle sai pounding yake, nan da nan ciwon kan da take ya qaru sosai, komawa tai ta kwanta, tai qoqarin daina tinanin" Babe what us wrong?" " kana ke ciwo sosai, so nake na tina abubuwan da suka faru a tsakanin wannan watannin da akai auren mu gaba daya ban sani ba" " ki dena yawan tinani likita ya hana, saboda zai jawo maki ciwon kai mai tsanani, ki kwantar da hankalin ki kinji, aikin da akai maku ne yasa kuka kai wadannan watannin ba tare da sanin inda kan ku yake ba, nj dinnan da kk ganni sai da nai sati uku a asibiti, abokina kuma wata daya da sati biyu, kafin mukaji sauqi" tausayin kansu ne ya kamata, lallai ashe hatsarin babba ne? A haka bacci ya dauke ta shi kuma yai palo yana murmushin samun nasara, waya sukai da Alh Kalla, " aboki ya ka qare da wannan 'yan rigimar?" Komai ya tafi as planed, ban samu matsala ba, wannan shegiyar uwar tasu ce taso sawa mata ta tinani, na kawar da shi, yanzu haka bacci take" dariya suka.saka, " ai ni tashi tai tana min shagwaba naji kamar na manta da ciwon na dan more ta kadan, dan sai ta min kyau sosai" " shegen sama, ana halin neman yanda za ai a rufawa kai asiri kana neman kayan dadi" dariya sukai tayi" anyway na mata dabaru irin namu na manya ta bar zance fatan ta Allah ya bata lfy, kasan har yanzu maganin bai gama.sakin su ba, bacci take tayi" " haka ne, to sai dare in mun hade a gidan Oga, yau akwai meeting" k to ba damuwa sai daren" kashe wayar sukai kowa na jinndadin samun nasarar da sukai, yanzu tinanin su bai wuce yanda zasuna samun jini da aka ce suna kawo wa duk wata ba daga matan nasu, dan su ba sa son suna satar yayan mutane, ana tsafi da su, aikin zai basu wahala, kuma kar wataran a kama su, dabara ce ta fado mai na yanda zasu na samun jinin daga wajen su, murmushi yai sosai, " dan ta rashin haihuwa me sauqi ne, tunda ba ni aka cirewa mahaifa ba bare na damu, 'ya'ya dama takura ne, sanda na so haihuwa na nemo matar da zan haihu da ita, dariya.ya dingayi kamar mahaukaci sabon kamu. Ni ko nace hmmmmm kwadayi mabudin wahala. " Ni dai marka na gani da yin abinci kullum nai na talla nai na gida ?" " nima haka gaskiya,  wannan yar rainin kullum sai dai mu dafa mu bata, ga Baban ma ya tafi har yau bai dawo ba " tab ai ko yau ita zatai tuwon dare ko taji a jikin ta, ni hutu ya samen, dan ba zai yu.na nemo na tuqa kuma na bata ba inaaaa" "sai Markaaaa, uwar gidan Talle, an buga an  barki" yaran suka fada cikin hada baki da dariya da shewa, ita kuma ta wani dage qafa tana zaune a qasa ta turo dankwali gaba, tana kada qafarta da tai fururu, " je ki kiran ita Huwaila" da hanzari ta miqe tana gyara daurin qirjin ta, tana tafe tana banqaro qirji, qugun kamar an daurawa tabarya zani, " Amarya ki zo Marka na son magana da ke"  kamar ba zata amsa ba da dan duk.tana jin su, ga wani mugun tsoron su da take ji yanzu, dan duk wani rashin mutunci da yake faruwa a kunnen ta, yau da gobe duk tana jin su, fitowa tai dan ta tsira da jikin ta, dan yanda suke ikirarin dukan ta kullum tasan za su aikata, " kinzo ba zaki magana ba ma?" " gani" " to ki bude kunne da kyau ki ji, daga yanzu ke zaki dinga girkin gida, su yaran sj ji da na siyarwa, ba zai yu nai ta wahala ba a gidannan, ke kina nade a gado, saidai na dafa na miqa maki, ki cinye ki gyara daki ki wanka ki koma ki kwanta, ai ba abinda ya kawo ki kenan ba, bautar aure kika zo, dan haka kula da yaran tsakar gidannan ma yana ciki, tsarkin kashin su da masu wanki, duk naki ne yanzu, in dai hutun amarci ne sati daya budurwa, bazawara kwana uku, ke ko ban san ame zan saki ba, tsabar adalci irin nawa wata biyar da kwana hudu na baki kika huta, dan haka daga yanzunnaj ba sai anjima ba ki dau aikin ki" " wo ke wo ke markan Talle" yaran suka dauka suna ta mata kirari tana kada qafa tana hura hanci su kuma suna dariya, " banji kin amsa ba " " to" ta ce ta juya zata tafi taji wani daga yaran yana " Naaa gaaamaaa" wani kuka ne ya taso mata, tinawa da tai tinda take bata taba daukan Ammar ba balle ta kai ta ga mai tsarki, gashi yau za taiwa dan wasu, kuma an maida hakan aikin ta, " bakiji bane sai kin gama qamar da dan mutane?" Sim sim sim ta wuce zata wanke amai,Haule ce tace" Aunty bar shi na wanke mai" " ke uwar kitifi uwae kinibibi, ina ruwan ki da hukuncin dana yanke? To a hir din ki kar kina min haka ranki zai mummunan baci, ita na ga dama ita zata wanke" " na gode Haule zan masa kije kawai" wanke mai tai zuciyar ta na matuqar tashi, tanafitowa suka kwashe da dariya har uwar suka tafa, murhu ta nufa, ta hura wuta ta dora ruwan tuwo, ranar dai na taqaice maku ba ita ta kwanta ba sai goman dare, jikin ta ba inda baya mata ciwo, tuwo ta tuqa yan kwano biyu, dan haka tana kwanciya ta hau bacci kamar matacciya." Dan Allah Juwairah ki sauri mana, duk wannan wankan naki na qa'ida sai ya sa ba mu fita da wuri ba" Nafeesa ke jiran Juwaora da ta gama girkin rana wajejen qarfe sha daya na safe,ta kammala gyaran gidan tsaf tana son yau taje ganin Maman ta , Nafee tace zata, ita har ta shirya amma Juwairah na wanka ne ma, can bayan kamar minti takwas ta bude ta fito daga bayin" kin san Allah, ba dan kina jirana ba sai na qara five minutes, ya zan nai wanka jikina bai fita ba, kowanne bangare a jikin mace fa ana son amai wanki mai kyau, musammab lunguna da saqon jikin mace ke har kunne da cikin kunne sai na wanke ni haka kurum Yah yazo min soyayya a kunne yaji dacin datti" "iyyee iyayen love, aiko ba zan gangancin wanke kunne na ba ruwa ya shige min a banza a barni da zuwa asibiti da jin azaba" " hhhhhh dadina dake komai baki iya ba, in zaki ai dabara zaki, tinda kinga yawan goge kunnen nan likitoci na ta hanawa bai da kyau, to saiki samu ki karkata kunnen ki gefe daya, ki wanke ta baki bakin da lungu da saqon shi, in kk gama kk dauraye saiki saka towel ko zani ki tsane ruwan tas, in kk gama da bari daya sai ki wa bari dayan ma haka, kinga ba ruwan da zai shiga kuma kin wanke shi fesss" " kaiii Juwairah wayon ki da sanin yaiamatan ki na ban mamaki, dan na kula wataran Mama Bilki ma mamakin ki take sosai akan halayyar ki" hmmm tashi to mu wuce na gama" tashi sukai suka tafi bayan sun leqa sum ma Su Innarmu sallama ita da Baba Balarabe, qara masu kudin mota yai yace su gaida mutan gidan in sunje, kar sui magariba a can, amsawa sukai sukau godiya suka tafi.


Da sallama suka shiga gidan, cikin zumudi ta fada dakin nasu, Mama Bilki ce ta fito dauke da fara' a sakamakon gane mai sallamar da tai, a hanya suka hade suka rungume juna suna ta murna, Ammar ne a gefen maman, da sauri ta dauke shi tna mai kisses ko ta ina," i missed u so much my bby broth, how ar u doing dear?" Dariya yake tayi kamar ya gane ta yana ta surutai irin na yara masu son yin magana, dariya tai ta aje shi a cinyar ta suka hau gaisawa, Nafee ma gaida su tai, tana mai jin dadin yanda taga soyayyar 'ya da uwa, da kuna dan uwa, " Aa mutanen kano ta dabo ci gari jalla babbar hausa, ne a gidan namu" Goggo ce ta fafa tana dariya," Kano ko da me kazo an fika ba, in mutum ya fadi alkairi yanzu mu bashi amsa dan gidan ya tarar amma in ya kuskure nan ma sai muje maqota mui aron rashin mutunci mu bashi amsa" Nafee ce tai maganar, " kul Nafeesa, ai uwa ce Goggo a wajen ku, kome zatai karku tanka, ku barni da ita nice daidai ita" Hahaiiiiiiiiii Casssssss a hakan? A hakan ne kk daidai ni? Dga shekaran jiya da yarana suka min waya zuwa yanzu kudin da suka shigo mun ta akawun ( account) ba qanana bane, ke kuma fa? Me ta kawo maki, tuwon dusa muyar lalle?" Dariya ta kwashe da shi sosai harda riqe ciki" kedai anyi sallamammiyar mace, yanzu me kk kenan? Kin tsaya kina rashin mutunci gaban yara, ke da baki da kamun kai, baki son a zauna a gidannan lfy, kullum sai kin nemi tijara ina sane, yauma ba zaki sawa kanki salama ba kenan" Abban su Juwairah kenan da ya dawo lokacin da take masifa, " oyoyo Abba da gudu taje wajen shi, ta rungume shi, shima rungume ta yai ya kama hannun ta suka zauna, qasa ta duqa ta gaishe shi, Nafee ma haka amsawa yau cikin nishadi" Ehhhhh lallau ne yau yar so ta zo, ka balbale ni da bala'i a gaban su mana, yarana tunda suka tafi baka neme su ba, amma wannan nunar ranar kullum sai ka tambaye ta, yau kuma ji yanda kk rungumar yar cikin ka kamar a gidab qabila" ke malama in baki da abin fada mai kyau fita ki ban waje, Jahila kawai wadda bata san e ake kira da musulunci ba balle ta san abin cikin shi" magana za tai ya daka mata tsawa, fita tai tana qunquni, ci gaba da gaisawa sukai sosai sukai ta hira, a haka dai har lokacin tafiyar su yayi, Mama ta tashi ta hau dan har hada mata wasu abubuwan iya qarfin ta dai, sallama sukai tana kuka suna lallashin ta suka koma gida, suna isa sun zaci Innar mu ta dora girkin dare amma inaaa, murmushi Juwairah tai ta shiga ta canja kaya, ta hura wuta ta dora taliya a cikin kayan da mama ta basu, ta hada da ganyen alayyahu da albasa, ta daka yar daddawa kadan dan ba isasshen maggi to daddawar zata taimaka abincin yai dadi , nan da nan ta kammala ta fada wanka , (Hikima r gyara daki kenan a wajen mace kan ta fita, in kk gyara gidan ki tsaf in da hali ma ki girki kan ku fita, da kin dawo to wanka zaki ki zauna ki huta, ba ruwan ki da zama cikin qazanta, da kuma taraddadin aiki a gaban ki) tana fitowa daga wanka Jabeer ya dawo, fita tai ta amshi ledar hannun shi ta ajiye sukai barka da dawo war su yanda suka saba, sannan ta ja shi bayi, sabon wanka ta sake domin cewa yai bata fita ba sai ya sake mata, tana dariyar gano wayon shi da tai tace" to shikenan ka gama nima sai na maka naka muje muci abinci dan na gaji yau da wuri zan kwanta" " tab yarinya ku daina zancen vacci ma in zaki bari" yana yi yana matsa cinyoyin ta da yake wankewa, yar qara tai ta shagwaba ta fada jikin shi, tana goga cinyar ta a jikin shi," Yah Jabeer akwai zafi fa" yanda tai maganar a saitin kunnen shi wani abu yaji har tsakiyar kanshi da qafat shi, janye ta yai ya kiqa mata soson" yi sauri ki wanke ni, nima ba zan iya jira ba, dariya tai ta amsa tana mai wankan cikin wani salon da ya amshe soson ya aje gefe ni dai ganin halin da yake neman jefasu yasa ji fecewa πŸ˜±πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀πŸƒπŸ»‍♀

[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ     'YAN ABUJA    πŸ’…πŸΌ

       BY HAERMEEBRAERH

This page is for u our missing Sawwama Qawwama, i and all ur fans ,tum hari yaad aa rahi hoo, we wish u will be back soon dearπŸ˜₯❤
 Darene yanzu a cikin garin Abuja, a wani hotel da su Alh Salihu suka maqale wa, tare da 'yan matan su da bazan iya tantancewa arna ne ko musulmai ba, wata naji an kira da 'yar Gwal, daga nan na gane hausawa ne, amsawa tai ta juya, dayar ta mata nuni da ido, murmushi naga sun sakamr ma juna, " mene ne naga kuna wani dariya kamar wasu wadan da suka cinci damin kudi a qasa?" Inji Alhj Kallah kenan da ya ga sanda sukai hakan," 'Yar gwal ce ta hau cinyar Alhj Salihu tana wani karairaya tana shafa shi" Alhaji na kudi muke so, gaba daya qawayen mu sun wucemu a komai, bayan muna tare da ku, gaskiya zai zama abin kunya ace ko motar hawa bamu da ita" tana magana tana kai bakin ta jikin nashi, wani irin nunfashi Alh ya fitar da bai san yana ruqe da shi ba," Haba 'Yar gwal yanzu dan wannan shine kuke wani abu kamar baqi, ai in kuna son abu kamar umarni zaku bamu kuga an cika, dan haka,..... kan ya qarasa kamar jira suke suji zaa biya masu biqatar su, suka miqe tsaye suka ja su daga clube din dake cikin hotel din zuwa dakunan hotel din , tin a hanya suke romancing din su, naje leqawa sukai slamming qofar a fuskataπŸ˜₯ haka nai baya na koma gidan Suwaiba naga wainar tmda take toyawa.


Hango ta nai tana zaune ta baza kaji a gaba da fresh milk a gaba tana diba, hankalin ta kwance, tana danna wayar ta, bayan ta gama taje tai wanka tai brush, ta saka kayan hacci, amma sam bata jin bacci, komawa tai palon ta kunna kallo, tqna kallo tana duba lokaci, wannan rayuwa, ace miji ba zai dawo da wuri ba sai dare ya raba? Tashi tai ta dakko fruit salad data hada ta saka a fridge, ta zauna tana kallo tana sha, bayan ya qare ne, ta aje bowl din a gefe, dai hamma take tana miqa, duk ta gaji da zaman shirun, wayar ta taji tana ringing, miqa hannu tai ta dauka, "Saudat love" shine sunan da ya fito akan wayar, " Hey sis"

"Hey" 

" ya kk, da yayan nawa?"

" muna lfy, Ya Alhjn ki?"

"Muna lfy"

"Dama kiran ki nai naji ko Baby na gidan ku, tsoro nake ji, gidannan ya min girma, duk dare sai naji kamar kirana ake," ta fafa cike da tsoro,

" Sis kiyi hakuri baya nan, nima zaman jiran mine nake, duk yanda akai suna tare, ki kwantar da hankalin ki ki mori abinda ya kawo ki, tin kan lokaci ya qure maki" amsawa tai da"to" sallama sukai suka kashe wayar Suwaiba ta tashi tai daki, bata jima da kwanciya ba, lokacin qarfe 2:45am ya shigo bakin shi duk warin giya, tsabar kwarewa da sukai ba sa layi, sai dai a gane ta idon su, da saurin fushin su,Suwaiba ce ta miqe ta nufe shi, " wai wannan wanne irin wulaqanci ne Sweethert, tinda nazo gidan nan i can't remember d last time we had xxx, amma da nai magana kace lokacin ban da lfy ne, yanzu danaji sauqi ka kasa sauke nauyin dake kan ka, amma kai da dikkan alamu har yanzu kayi auren ma wasu kk bi a waje, ga giyar da kk sha wadda ni ban san kai din dan giya bane, wannan ai iskanci ne" ta fada tana daga murya tana masifa" ni kk kira dan iska? Ni kk kira dan iska ko, ba dai ni kk cewa dan iska ba ? Yau zakiga iskanci ganin idon ki Suwaiba" miqewa yai ya janyo ta ya hau duka kamar an aiko shi, a haka ya cire mata kayan ya wurgar duk ya yaga su, aiki ya fara akan ta full time, and non stop, gaba daya jikin ta yai tsami ga duka , ga xxx din da ba tai niyya ba, kuka take tana" kai hakuri nice yar iskar ba kaiba, ba zan qara ba , ka taimaka min, ka duba auren soyayyar da mukai da kai" kwade bakin ta yai yace " auren soyayya ko auren kwadayi?auren kudi? Karki zaci ban san kr da uwar ki kwadayayyu bane da yan uwan ki? Ina sane da komai, ni ba qaramin mutum bane" qara wurgata gadon yai da take qoqarin guduwa ya kwanta a jikin ta, nan da nan bacci ya dauke shi, kuka take sosai jikin ta na ciwo, haka ta tashi ta ja jiki da kyar, ta tafi toilet, ruwan zafi ta hada mai zafi sosai, ta shiga, tana shiga tai qara dan azaba, a haka ta gasa jikin ta taji dadi sosai, nan da nan bacci ya fara diban ta a xaune a ruwan, fita tai taje ta saka wasu kayan ta koma daya dakin ta kwanta, ta rufa, nan da nan baccin wuya yai gaba da ita, da asubar fari Saudat ta kira ta a waya tana kuka, Ta sanar da ita irin cin mutuncin da Alhn ya mata itama, sata yai tai ta mai tausa, har wayewar gari, data fara gyangyadi ya zabga mata mari, ta dora daga inda ta tsaya, kuka sukai tayi, ba mai lallashin wani, itama Suwaiba labarin nata ta bata, sannan sukai akan gobe zasu hadu in mazajen sun fita, qoqarin shigowa ake ta danne wayar ta kwanta tai lamo kamar me bacci, qarasa shigowa yai ya zauna kuda da ita, " Haba my Suwai hakuri zaki, ke ma kin san in rai na y baci bana son a cika tambaya ta musamman maganganu na rainin wayo, auren kudi kikai kuma ga kudin nan, to meye na damuna sai na maki wani abun?" Kuka take ta gefen ido bata ce komai ba, janta yai jikin shi yana shafata, take ta fara saukr ajiyar zuciya tana hamma, don bacci take ji sosai, kiss ya mata ya maida ta ya kwantar yace shi zai fita, daga mai kawai tai ta koma ta lumshe ido, bayan ya fita ne tai baccin awa uku ta tashi tai wanka , ta hada abin karyawa mai rai da motsi da tea mai kauri ta ma manta jibgar da ta sha, taci tai nak abinta, Wayar ta ce tai ringing ta amsa da " ku barta ta shigo qanwa ta ce" ta kashe, Wajen kamar minti 5 Saudat ta shigo, cikin shiga ta alfarma, ga wata arniyar mota da ta zo da ita driver na tuqata, ta ci gold ko ta ina hannu da qafa da kunne, dan harda sarqar qafa suke daurawa, isa tai itama kusa da sister din ta akan dinning table ta ja plate ta zuba chips da kwai da farfesun naman kan rago, sai tea da ta hada itama mai kauri ta hau sha, sai da ta gama sannan ta yada kai baya ta zame kadan daga kujerar tace" Sis ina cikin tashin hankali wanda da dikkan alama kema haka ne, dan ga jikin ki ya nuna, dubi fuskata" ta fada tana mai nuna mata fuskar ta da tai jawur ta kumbura, sai rufewa tai da mayafi da ta shigo," ga zaman yunwa da nai dan jiya kwata2 kasa cin komai nai" 

" yar uwa bari kiji, ki cire komai a ranki shawarar da zan bamu shine mu cire rai a son sai sun zama mutanen kirki, tin da dai ba halin su bane, mu zauna mu mori dukiyar da muka zo Abuja domin ta, mu xama manyan hajiyoyi,mu bawa maqiyan mu kunya, dan ni kam kin ganni nan, in ba jiya dana sha jibga ba, bana wasa da abin ci ko wani nau'i na jin dadi, sannan kuma da kk ganni nan haqqina na aure in daga yau ya ce ya daina ban ba zan damu ba, domin kuwa akwai hanyoyi da dama da zan iya maganin matsala ta, wanda na san kema kin dan su ba sai na tsaya bayani ba, i hope ba zasui gangancin turamu wannan stage din ba, zasu na daure wa ko once in a while ne suna biya mana buqatun mu, to kinga ba mu da matsala da bin matan su ko kuma wani abu mai kama da shan giya, sun dade ba suyi baπŸ™„ dan ba zan qara yarda a taba lafiya ta ba, an gama daga jiya" " kaiiiii yar uwa wannan shawara tayi wallahi" tafawa sukai suka koma palo duka debo dambun nama da juice suka dawo palo suka kunna kallo, sunayi suna hira qarshe waya suka dauka, suka hau kiran Goggo Sarai, suna waya,  a lokacin suna tsakar gida dikkan su, Mama Bilki, Abban su Juwairah, Ammar, da ita kanta Goggon, wanki Mama Bilki keyi na kayan Abban su da na Ammar, ita kuma tana girki, wanda ta dade da dena cin abincin gidan sai dai tai nata, su kuma suci nasu, hakan da tai yada Abban sun ya samu ragi daga dawainiya, shiyasa ma wataran suke samun abinda suke aikawa Juwairah dan Mama ta kula da rayuwar da take ciki a zuwan da tai sau daya, amma da ta tambaye ta, qeqasa qasa tai tace ita lfy lau komai yake tafiya masu, addua tai mata kawai amma tasan akwai wata a qasa, cikin firgici ta daga kai daga tinanin ta sakamakon......


...............

[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ      'YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ

       BY HAERMEEBRAERH
Hey guys i am sorry yesterday i fogot to number the page, it suppose to be page 10 and this is page 11. Thanx me love u XoXo.

Page 11:
  Wata qara da Goggo Sarai ta sake da sunan dariya, dan kawai ta ja hankulan su,"Hahhhhaaaaa kaiiii amma naji dadin haduwar ku gaba daya tare, ikon Allah ana can ana cin amarci sai yau aka samu haduwa kenan, to ya masu gidan? Ya rayuwar hutu da jin dadi?" 

"Lfy qalaou Goggo, ina Abba?" 

" Hmmmm ga shi can wajen waccan sallamammiyar matar tashi da ta shanye shi"

" Bashi mu gaisa kar yace bamu neme shi ba"

" Aiko bada wayata ba ehe ku kira shi a yar rakani kashin shi kawai"

Tana fada tana hura hanci tana turo dankwali gaba irin na fitsararrun matan nan? Kada kai Abban nasu yai yace" Allah ya kyauta" murguda baki tai kamar wata qaramar yarinya, irin na rashin kunyar nan,( dan kunsan murguda bakin ma kala2 ne, akwai sexy murguda baki mai daukan hankalin oga, yaji dole sai ya kai nashi bakin a naki sabida yanayin yanda kikai yi shi da salon jan hankali, sannan akwai na rashin kunya kamar na Goggo sarai dai)  miqewa yai da niyyar fita sai wayar shi ta hau ringing, dagawa yai da sallama, su Suwaiba ne, gaida shi sukai kamar ba sa so ya amsa tare da tambayar su gidajen su," hhhhhh Abba do u really have to ask ? We ar fyn, komai normal kamar dai yanda ka sani Abba mazajen mu masu kudi ne, so ina ganin ai bamu da wata matsala mu" 

" Suwaiba ni mahaifin ku ne ba zan gaji da maku nasiha akan ku bi duniya a sannu ba, yau in kaine gibe ba kai bane, dukiya da abinda ke cikin duniyar nan ba komai bake face rudin shaidan ga wanda ya mai da su abin bauta, kuji tsoron Allah a lamarin ku, Hello ! Hello..... shiru yaji ashe sun dade ma da kashe wayar tin da ya fara wa'azi suna ta surutan yanzu zai takura masu, mamaki je cike da zuciyar shi, " yarannan ni suka kashewa waya?" " Abban su kai hakuri komai zai daidai ta da qarfin addu'ar da zaka dinga wa iyalan ka, Allah zai shirya maka su inshaa Allahu, adduar iyaye amsasshiya ce a wajen Allah, Allah ya shirya mana zuria" " hmmmmm Ameen Gimbiya ta Allah ya albarkace ki da zuriar mu duka" dadi ne ya kamata mara musaltuwa  a duk sanda ya mata wannan adduar" Ameen a bin sona" murmushi sukai, nan da nan yaji baqin cikin shi ya tafi, ruwan wankan da ta saka mai yaje ya shiga yai wankan shi, ita kuma ta fara qoqarin dora madu abinci.( magidan ta ku na qoqarin yi wa matan ku godiya da addua musamman ta nema masu albarka a wajen Allah, in albarkar nan ta wanzu a garesu ta shafe ku, da xuriar ku kenan, mata ku dinga dukkan abinda kk san zai faranta masu rai sui maku adduar, soyayya bata tsufa sai dai masoyan su tsufa).Nafeesa ce ta shirya tsaf cikin riga da skirt na atampa, tayi kyau sosai ta taho bangaren su Juwairah" matar Yayah ya naga baki shirya ba kin saka dan guntun wando da vest an faka gashi gefe?" " Nafeesa kenan ina ga alama kin manta yau Yaya da wuri zai dawo sannan yau ranar dana ware domin gyaran lambu na ne ko? Ga girki da zan da wasu aikace2n, kuma sanin kan ki ne ni fa yawon shiga nan shiga can dinnan ba son shi nake ba, shike kawo mace ta daina kula da iyalan ta da gida tana qarewa a titi" " hakane kam gaskiya, ni dai zan tafi gidan Shamsiyya na gaida ta, dan na mata alkawarin zani yau din, na zaci zamu tare ne tinda naga ke kin dade baki je ba, sai na dawo to" " to ki dawo lfy, ina gaida ta da yaran" fita tai ta tafi, ta je gidan Shamsiyya inda ita shamsiyyar yaran ta biyu mace da namiji, Farha da farhan, goyo take tana goyon macen , gaba daya gidannan sai a hankali, komai da kan shi yake zama, bai da muhalli, shiga tai palo ta zauna da sauri ta miqe tana duba skirt din ta daya jiqe, hannu ta kai hancin ta taji wani mugun xarnin fitsari, da sauri ta kauda kanta ta fita tsakar gidan,ruea ta sa ta wanke hannnun ta saka a skirt dinta tana masifa" ni gaskiya shiyasa bana son zuwa wajen ku shamsiyya, ga gida har gida Allah ya hore maki amma sai uwar qazanta, duba dan Allah daga zuwa na xauna akan fitsari , ko da Juwaira bata haihu ba na san.abin da ba za a taba samun ta da shi ba kenan, yanzu haka saboda gyaran gidan ta da kula da haqqin mijin ta yasa taqi biyo ni, Juwairah nada lokutan yin komai, tinda ba za a hadu ace kullum zaka hada kowanne aiki kayi ba zaka gajiya, sai wanda suka zama aikin yau da gobe, dan Allah ki gyara, dan yana daya daga abinda yasa Baban Farhan yake neman aure duk.da ya fada maki amma kinqi gyarawa" kaiiii hajiya bala'i daga zuwa.sai wannan dogon karatu? To dan Allah ya kuke so nayi? Ga aikin gida gana miji gana 'ya'ya" sai ta fara hawaye wai ita a dole komai ya mata yawa, kama hannun ta Nafeesa tai suka koma palon ta zaunar da ita a kujera, sai da ta laluba wata taji ba jiqa ta zauna ta fiskance ta, " qawata ni ba wai ina maki fada dan ranki ya baci bane" " to dan meye? Saboda kowa ya tsane ni sai a dinga ce min qazama ? Kalmar qazama fa na da ciwo tsakani da Allah" majina ta sharba tana gige hancin da zanin ta, " to yanzu kingq hakan da kikai ni ba zan yi shi ba, da na goge majina da zani gwara na je na wanke hancin, ai in kk ji ance qazama akwai kalmar tsafta kuma ko? To ni so nake ki cire kalmar da kowa ke kiran ki da shi na qazan ta ki mai da shi mai tsafta, yanzu ki fa duba kiga  Mama Bilki, kullum kk dhiga wajen ta kinga dai ta tsufa ko, amma tsabar qamshi da tsafta bazaki so barin wajen ba, come to think of it ba fa ta da kudi da wadata kamar ki? Dan Allah ki gyara ki rage son jiki,son kallo da karancr2n nan na zamani har sai kin gama komai sannan ki dauka ki fara,ina fatan wannan ya zama na qarshe da wani zai baki shawara ko za a zage ki akan tsafta, in baki gyara ba Abban Farhan yace maki zai qara aure kuma ya fara nema in kk gyara nasan bari zai dan matsalar shi dake kenan ba wani abu ba" " Na gode qawata, ba wanda ya taba zaunar da ni ya min bayanin ya shige ni" " ba godiya a tsakanin mu" murmushi sukaiwa juna shamsiyya ta miqe ta fara tattara kayan wajen data loda a kujera, nan da nan Nafeesa ta taya ta suka gyara gidan ya dau hake da qamshi, girki sukai mai rai da lfy kala2, wajejen la'asar Nafeesa ta bar gidan cike da tsaraba daga wajen shamsiyya, a ranar ta sha wanka da gaye, Abban Farhan daya dawo ya sha mamaki amma bai nuna ba, sai ya nuna mata matuqar jin dadin shi, dakuma yabawar shi tashi yai yaje dakin shi yace " ina xuwa" wata sarqace ta gold mai kyau ya zagaya ta bayan ta ya daura mata suna kallon madubi, dan harda koyawa yaranta baccin wuri sai da Nafeesa ta koya mata, godiya tai ta masa shima yana godiya, ba a jima ba taji zancen aure ya rushe, sai dai ya sanar da ita cewar" Baby ki kwantar da hankalin ki dan ni ba mai ra a yin mata biyu bane ko sama, tsaftar ki da rashin tsaftar ki in ni me ra ayi ne ba zata hana min yin aure ba, na fada maki ne dama dan ki gyara mu more ratuwar auren mu yan da ya kamata" taji dadi sosai inda ta qudurta ma ranta xama mace mai tsafta ta bugawa a jarida, yan dakowa ya mata tambarin qazan ta sai an buga mata na tsafta in Allah ya yarda. Ni ko na ce to Allah ya yarda ya shiryemu mu gane tsafta na da kaso mafi tsoka a rayuwar aure.

Bayan Juwairah ta gama komai ta yi wanka ta kwanta tana hutawa, tasbihi take ta yi ga Allah bacci ya dauke ta, tafiyar tsutsa yake mata a qafar ta ta farka idon ta na qara lumshewa, juyi tai ta cusa kanta a cinyar shi ta ci gaba da baccin ta, a hankali ya janye ta dan ya kula a gajiyae take, yaje ya cire kayan shi ya aje inda take aje masu kayan wanki bayan ya ninke, ya tafi wanka dan har da ruwan wanka ta aje mai, bayan yai wanka ne yaga kamar bata ci abinci ba ya shirya ya zo ya qara tashin ta sai magagi take bacci ne sosai a idon ta a haka ya daga ta ya zubo abincin yana bata yana ci duk abinnan da ake idon ta rufe yake, " Yah Jabeer ka dawo?" " Eh na dawo princess" " Sannu da xuwa" "yawwa, meke damun ki ne yau?" " bacci nake ji na gaji ne sosai, ga jiri danake ji, tin shekaran jiya kuma sai naji cikina na ciwo, kamar ana min motsi a ciki" har yanzu ta qi bude idon," Subhanallahi, gobe zamu asiniti mu ga likita dan shiyasa kk ji kwanaki ina ce maki sai naga kamar baki da lfy, abinda ke kwantar min da hankaki kawai ganin yanda jikin ki ba wani damuwa sai kyau da kk qarawa ma, nan din ki har wani kyalli suke" hannun shi ya kai saman rigar ta yana shafawa, a hankali ta janye hannun shi ta juya baya ta ci gaba da baccin ta, wani yawu ya hadiya, ganin yanda hips din ta suma suka ciko sosai kamar sui magana, tashi yai ya maida plate din ya wanke bakin shi da hannu ya rufe ko ina ya dawo" princess ko dai fushi kk ban dawo da wuri ba yanda na saba? Shi ne kk share ni kk son yin bacci?" Shiru yaji, matsawa yai jikin ya ya janyo ta, bacci yaga tana yi sosai, bai so haka ba, gaba daya ta rikita shi, amma haka ya hakura dan yasan ba halin ta bane kyale shi koda tana cikin fushi ne, ja masu abin rufa yai yai masu addua ya shafa masu, suka kwanta........

[11/26, 12:34 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ
       BY HAERMEEBRAERH


Alhamdu lilLAAH ala kulli halin, naji sauqi sisters na gode da kulawa, Allah ya barmu tare da alkhairi mara yankewa. ME LOVE U XOXO❤Page 12:


   Da asuba ta tashi ta duba taga har ya fita masjid, addu'ar tashi daga bacci tai " "Alhamdu lilLAAHi alladhi ahyani ba'ada maa amatani wa ilaikannushour" sannan ta sakko daga gadon ta je tai alwala ta dawo ta gabatar da raka'atanil fajr tai sallar subh,tai azkar din safiya, tana idarwa tai azkar din ta, tana gama wa wanka taje tayi ta sake yin brush, gaban madubi ta zo ta warware kitson da tai da yamma, guda biyu akan ta sakamakon ba ta son kitso sosai kuma shima Yah Jabeer din nata yafi son tana mai adon gashin haka ba tare da ta kitse ba( yana da kyau mace ta iya yin kitso biyu irin na indiawan nan da muke gani ana raba kai biyu a kwantar gefe da gefe a dame shi a kitse sai yai matuqar kyau in ke mai santsin gashi ce ma zakiga har sheqi yake da dare ake wannan kitson bayan kin gama wa oga kwalliya, ma'anar yin wannan kitson na farko dai zaki bacci ba tare da kanki yai buyaya ba, kinyi muni, da safe zaki tashi kan ki tsaf da shi, bai barbaje ba, sannan kuma in ma kun samu kusantar juna da me gida kin yi wanka kanki ba zai na lalacewa ba nan da nan kiji mata suna kai yasha ruwa gashi na.zubewa, akwai fa'ida sosai akan yin hakan da sai kin fara zaki gano su da kan ki) da sauri take yin komai ba son jiki, dan ba ta son sai ya dawo ne zatai wadannan abubuwan, ya na dawo wa daga masjid ya tsaya wajen Innar mu su gaisa, kamar kullum, riqe shi tai d surutai na ba gaira ba dalili, daga baya ne ta fara tura mai saqon dake ranta a wayon ce" Allah sarki Juwairah yarin yar nan akwai hakuri, kaga fa yanzu wata na wajen.shida kenan.da auren ku, qawayen ta sun haihu amma ita ko batan wata bata taba yi ba, amma bata damu ba, ko dake dama yaran zamani.ai ku ba ruwan ku, mu ne dake son yan jikoki mu za mu damu, waya sani ma ko maganin hana haihuwa take sha" wani irin faduwar gaba ne ya samu Jabeer ido ya zaro waje yace" Haba Innar mu Juwairan nawa take d zatai wannan tinanin? Kuma har ta aikata hakan? Inaaaa sam ba zatai haka.ba kima daina wannan tinanin dan Allah, kuma da kk zancen sa'o'in ta Innar mu Nafeesa ma fa sa'ar ta ce ita kinga ai har yanzu ma batai aure ba, in da zaki gane komai nufi ne na Allah ko" habaaa kamar ya watsa mata wuta, bala'i ta fara kamar ta ari baki" iyeeeee lallai e Jabeeru ka nuna min mata tafi 'yar uwa ko? Har qanwar ka zaka duba kaiwa gorin aure? To bari na fada maka abin da nake boye maka, nifa na fara gajiya da wannan yarinyar, tin da ka aureta ka daina bamu lokacin ka, ka daina zama ai hira kamar ta da da kai, sannan gaba daya soyayyar ka da kulawar ka ta koma wajen ta, akqn me?" " akan shi ne mijin ta, kuma hakan da yake shine yake nuna ya haifu dan sunna ne, yanzu dan Allah bakiji kunya ba? Kk hada kan ki da surukar ki? 'Yar ki kuma ta wani bangaren? Habaaaa Hansai, wace irin rayuwa kk daukar wa kan ki yanzu, abinda ba halayyar ki ba kina neman shaidan ya maki huduba ki fara, to bari na fada maki abinda mata kan ku yake toshewa akai, kowacce mace dangin miji ce, kuna uwar miji ce wataran in ranta ya kai, dan haka in kikai wa matar dan ki adalci, kema sai wata taiwa taki yar, in kk kyautata wa matar wanki ko matat qanin ki, kema naki qannen mijin da matan yayun sa zasu tausaya maki su miki adalci, in kuma duk kin kiyaye amma ana maki abinda bai dace ba, to ki sani kowanne dan Adam akwai jarabawar shi, wataqila taki anan take, sai ku hakuri ki qoqari kuma ki cinye jarabawar taki, dan haka in kk kula, tin da Jabeeru yai aure kulawar da na ke ba ki ta qaru, ba dan komai ba sai dan kula da nai kin kai idon ki gidan matar dan ki, ki gyara hali ko kun samu rabauta a lahira, baki tafi da haqqin kowa ba, haihuwa ta Allah ce, ko bata haihuwa haka yaga zai zauna da ita ke baki isa ki ce dan me ba" Baba Balarabe kenan da ya dade a tsaye yana jin maganganun Innar mu, wata irin nadama da kunya ce ta kama ta," Malam ka yi hakuri, Jabeeru ka yafe min sharrin zuciya da shaidan ne, ina ganin tin da ta zo komai namu yaja baya, ga shi kana nuna mata tsantsar so, idona ya rufe akan hakan na manta nima nawa mijin yana iya qoqarin shi akaina, ku yafen ba zan qara ba" nan ta zayyano yan sace2n da tai tayi wa Juwairah dan ta hada su fada amma sai taji shiru, saka makon iya zaman duniya da Juwairah ke da shi da ta kula hakan ta faru zata san dabarar da tai ta bashi hakuri, da jikin ta da kalaman tq, " Ba komai Innar mu ya wuce ke uwa ce a wajen ta, da bata dauke ki uwa ba uwar miji ta dauke ku da ita kanta zaman sai ya mata wuya amma tasan ko da uwa da uba ana sabawa fiye da haka ma a kuma ci gaba da zama, dan haka na san ba ta qullace ki ba, jiya kwana tai ba lfy, asibiti xamu ma" Subhanallahi" suka hada baki dika ukun har da Nafeesa, " meke damun ta?" Inji Innarm mu, " Da ciwon jiki ta kwana ga zazzabi da ciwon kai, ciwon mara, da kasala, dan jiya wani irin bacci ta dinga yi" murmushi Innar mu tai tana" ikon Allah ai ya kamata a kaita ta ga likita bokan turai a fada mana wata nawa ne, na fara tanadin kayan kwalliya dan da alama bana zan yi ango nima, in kishiya ce na samu na gyaran daki,kar ta zo ta fini. Wajen Malam" Innar mu me kk nufi hakan?" Inji Nafeesa kenan, Jabeer kuma a ranshi cewa yake" Allahumma ameen" " Innar mu bari na wuce naga ko ta shirya mu tafi" " to Allah ya qara afuwa" tashi yai baki a washe kamar gonar audiga, ya isa, qamshin da yaji ne ya qara kwantar masa da hankali, ga nutsuwa da qaunar matar shi da yake ratsa shi, sallama yai ta amsa, durqusawa tai ta gaida shi, ya amsa tare da jawo ta jikin shi, daga kanta yai yana kallo, wata riga tasaka shara2 ko ina ana hangowa a jikin ta, sai wando guntu rigar bata gama rufe mata cibiya ba , tai parking gashin ta in to ponytail, fuskar ta tai fayau kyaunta na qara fitowa, the more yana kallon ta the more yana qara ganin kyaunta, bata cikawa fuskar ta makeup ba, iyakar ta powder da lipstick, sai tirare da ta fesa ta shafa mai, zame rigar yai yana shinshina wuyan ta, ita kuma maida kanta baya tai tare da miqa mai qirjin ta gaba, nan take hannun shi na rawa ya daga ta tsaye ya zame rigar ta ta yana qare mata kallo, duk wata tsiga a jikin shi ta gama tashi saboda wani irin kyau daya ga ta qara" Babe ni dai bana son wannan kallon da kk man yai yawa, tin da ka shigo kk kallona" ta fada cikin shagwaba da sake narkewa a jikin shi tana wani dan zame wa shi kuma da sauri ya janyo ta, gaba daya ta gama rikita shi, daukar ta yai cak sukai daki, bam qara sanin me ake ba sai da naje na wajen Innar mu na sha kokon safe na dawo😜 a gadon na hango su suna manne da juna, " My princess , jiya kin manta yau munyi zan kai ki asibiti ne? Gaba daya naga yanda jikin ki yake jiya da yamma yau kin tashi garau da ke" Eh My dear, kaga in banda da asuba dana tashi naji kaina na dan ciwo kadan, sai da na zo brush warin toothpast din ya sani amai, tin da nai aman nan naji dadi, yanzu inajin na warke ba sai mun je ba ma" " Aa ba haka za ai ba, ya kamata mu je asibiti muji me ke saka motsin da kk ji ko ya daina" yana fada yana shafo cikin nata da tausayawa, nan da nan idon ta ya ciko da kwalla" Yah bai daina ba, dazu ma ya min, ga tsoro da yake ban in ya motsa din, sai naji kamar wani abu ne a ciki" ta qarasa tana mai yin kuka" Here, here my baby, stop crying , ba komai inshaa Allahu sai alkairi, u don't have to worry ur self babe, koma meye zamu samu maganin shi tashi muje mui wanka mu shirya muje" tashi ya fara, ya miqa mata hannu ta kama, a hankali ta miqe, sai yanzu ya qara ganin qirman da qirjin ta yayi, ga cikin ta ya dan tasa ta qasa, ta yi wani fari sosai, kamata yai ya  zura mata doguwar riga da dan hijab din da take zuwa wanka, tinda gidan akwai suruka, sannan kuma safiya tayi, shima ya zura tashi rigar , qofar su yaje ya rufe sannan suka shiga wankan bayan sun gama ne suka dawo suka shirya, suka fita, saida ta biya wajen Innar mu ta gaida su sannan ta tashi zasu tafi" Juwaireren Mama ki yafe wa Innar ki laifukan da ta miki domin Allah, sharrin shaidan ne ya shige ni da son zuciya, amma in Allah ya yarda ya wuce ba zan sake ba" wata kwalla ce ta fito mata ta godewa Allah da ya kawo mata komai da sauqi kuma da wuri," Haba Innar mu ai ba komai, ni fa yar ki ce, ke uwa ta ce, ban dauki hakan.a komai ba, face gani.nake nice bana kyautata maki yanda ya kamata, nima ki yafe min"Baba balarabe na daki yana jin dadin kasancewar Juwairah a matsayin surukar shi, yarinyar dan uwan shi, da yake so, yarinyar data samu tarbiyyar iyaye na gari. 


Sun isa asibiti bayan layi da suka bi, gwajin farko aka gano tana dauke da cikin wata hudu da sati biyu, zaro idanu take kamar mara gaskiyaπŸ‘€ ga murna ga kunya duk sun ishe ta, ta rasa ya zatai, janyo hijab din ta tai ta sunne kan ta a ciki tana dariya qasa qasa, Jabeer ta gani ya tashi yai sujjadar godewa Allah yana kwallar murna, itama a cikin ranta take maimaita" Alhamdu lilLAAHi ala kulli halin, hamdan katherran ya rahman, murna take sosai taji hannun shi ya janyo ta jikin shi, hada fuskar su yai waje daya suna shaqar nunfashi junan su," Juwaireren mama kin ga ikon Allah akan mu ko, ya mana kyauta mai dadi da sanya farin ciki ko?" Daga masa kai kawai take tana murmushi, Doc. ne ya ce" to  Lovey-Dovey sai a tsaya a saurare ni kuma in anje gida an qarasa murnar, ina da wasu masu jiran a waje" yana fara'a da jun sun burge shi yake maganar, shawarwarin da zasu taimaka masu ya basu, ya rubuta magani inda yace su je su nuna takardar kawai za a basu kyauta ne,godiya sukai mai yawa sika fita, he locked there hands together, dan ji yake kamar ya dauke ta karta wahala, he is happy, kula da hakan da yai ne yasa ta tsada su a wani wajen da ba mutane sosai tace" Babe can i ask u a favour?" " Anything for u my love,just say it, inshaa Allahu in baifi qarfina ba i will do it for u" murmushi tai ta sunkuyar da kai qasa" Yah pls don't tell anyone that i am pregnant plssss" ta qara damqe hannayen su" But why, abun murja ne fa? Don't u want them to be happy for us, and must importantly to pray for us, and our baby" ya qarasa cikin rada, " Yah is not what i meant, kawai ni kunya nake ji, kowa ya san me nai na samu cikin nan, har da Abba😱 " kiran Abban ta da tai wata kunya ta qara kamata kamar yama gani, dariya Jabeer yake sosai yana riqe ciki, " amma kema baki da wayo na kula, to bari kiji, tin kan a kawo ki aka san in an maki aure zamui abin da zaki samu ciki, come on mu wuce gida rana da dukar min ke" maqale kafada tai tana turo baki, " what again?" " i am so hungry" but we just ate?" " yeh i know, but i am still hungry" yatsina fuska take kamar in bata ci ba wani abu zai same ta ne, " k then me kk so?" " Yah ga me agwaluma can ita nake so, kuma ina son waccan zogalen dafaffe" "ikon Allah, ashe kwadayin da kk ta min kwanaki bbyn mu ce ke saka ki" ya maqale murya" Yah ka taho mun da gyada mai gishiri, ka tahon da rake, kazo man da akwaluma mai yawa" kukan shagwaba zatai yai maza ya kama bakin shi, alamar yayi shiru" yi hakuri ba zan sake ba kin ga a titi muke duk da katangar nan ta kare mu kinga masu agwalumar zasu maki dariya" narke fuska tai" Oh ni Juwairah yau naa ga tsokana da ranar Allah""Auuuuu kin fi son a tsikane ki da dare kar ki damu wannan ma ba a barmu a baya ba ai" da sauri yai wajen masu agwaluma yana dariya, zura hannun ta tai a riga tana shafa cikn ta dayake a lafe kamar ba komai, amma tana jin motsawa kadan kadan, " Ikon Rahman, wato wai ni Juwairah ke dauke da ciki ban sani ba, Allah na gode maka, kasa duk abin da zan haifa ya zama musulmi mumini salihi, Allah ka sani na bi dukkan yanda Annabin ka ya tsara mana don samun 'ya'ya na gari, tin kafin aure na har yanzu da ka ban wannan arziqi, Allah ka sa su zama wadan da muslunci da musulmai zasui alfahari da amfanuwa da haihuwar su, Allah na gode maka ka ba wadan da basu da shi, ka sauqaqa min wajen haihuwa" hannun shi yasaka ya ce" Earth to Juwaireren mama, tinanin me kk haka? Na dawo ina tsaye baki ji ba, wato har zaki fara manta ni ko" ya fada yana shagwabe baki kamar yaro" ba komai muje gida nayi na sha abunnan yunwa ta qaruwa take" dariya yai suka kama hanyar fita suka samu abin hawa sai gida, lokacin da yake fadawa innar mu gudu ta saka tai bangaren su tana dariya, kowa murna yake a gidan kamar me, labari nan danan ya bazu a dangi Juwairah na dauke da cikin wata hudu da sati biyu, kowa na murna da saka albarka, jin wannan labarin da Goggo Sarai tai ya daga mata hankali, domin tunanin ta ya tafi akan dama yaran ta ne, ko dan samun wani kaso nadukiyoyin surukan nata,nan take tinanin Salma ya fado mata, wayar ta ta dakko, taita zabga kira ana mata turanci, hankalin ta ya tashi sosai, mayafi ta yafa ta leqa ta kira Abban su, ta bashi ya ji me ake fada, ce mata yai wai layin baya aiki yanzu," wai ni wa kk kira haka ne, Malam wannan Yarinyar Salma mana, duk Yan uwan ta sunyi waya anji daga wajen su amma ita shiru, ga wannan kabarin da ya iske ni na samun cikin wannan kodadiyar"  " hmmmm Sarauta kenan A gabana kk sok ki ciwa 'yata fuska wai kodaddiyar 'ya na gode, Allah zai raba su lfy, ita kuma Salma Allah ya sa ki same ta a wayar, in kun yi magana kin sanar da ni" yai shigewar shi ciki, wayar suwaiba ta kira ta dauka itama tambayar ta tai tace bata ji daga wajen ta ba, Saudat ma amsa daya ta bata, hankalin ta suka kwantar akan cewa ta yu ma sun fita qasar waje d mijin ne shiyasa, wani farin ciki ne ya maye damuwar ta.
Salma wadda ta koma Salame kuwa, ana can qauye, jikin ta qaura yai la'asar, ba kowa ne da yasan ta zai gane ta ba, duk ta kode ta jeme.Yau ne ranar karbar jini a wajen su Suwaiba wanda Oga Zaks ya buqaci ko a kai su, ya qara dana su, ko akai jini........

..

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ     'YAN ABUJA    πŸ’…πŸΌ

              BY HAERMEEBRAERH

page 13: Mijin Suwaiba ne Alhj Salihu yai wa mijin Saudat magana akan yanda zasu aiwatar da qudirin su na samun abinda suke so cikin sauqi, dariya suka bushe da shi suka tafa, a tare suka furta" 'YAN ABUJA"   lokacin suna dawowa gida,dan daga wajen Oga Zaks clube suka wuce as usual amma yau basu dade ba dan sha dayan dare suka dawo gida , cikin kwalli kowa ya tadda iyalin shi, an sha kayan ado, fatar nan har wani sheqi take sabida jin dadi da hutu, sai dai suna isa kowacce ta tanadi magana a bakin ta da ta ja masu jibga, Suwai ba ce ta fara gabatar da uzurin ta kamar yanda Goggo sarai ta sa ta fadi" Mine " "Na'am" tana fada tana wani tauqi tana manne mai a jiki, " dama cewa nai ko zamu asibiti a duba mu ne, lfyr mu qalaou kuwa? Har yanzu fa ban taba koda barin wata ba, ga qanwar mu na da ciki, kuma zai zama mana abin gori mu da mahaifiyar mu ace mu uku ba mai ciki" wani wawan mari ya antaya mata, ya hankada ta qasa sai da ta kifa, " dan uwarki ni zaki mayar qaramin mutum qaramin yaro? Wanda bai san me yake ba? OHHH wato ki haihu na samu magaji ko? Ko ki kashe ni ki karbe dukiya ta ko? To bari kiji wani abu, wannan dukiyardaga karuwai sai masu saida giya su zasu more ta, ba tsarin yara a rayuwar nan tawa, ban sani ba ko gaba, amma as of now ban da wannan burin da kwadayin yaran da ke zaki sani neman haihuwa" " dan Allah ka saurare ni ka kuma fahimce ni" kan ta qarasa ya rufe ta da mugun duka ko ta ina yana " baki yarda ki daina sa in sa da ni ba ko, ina fada kina fada kema , aiko xaki ci uwar ki yau, sai soyayyar yara ta fita a zuciyar ki yau", waya ya ciro ya dinga zabga mata, tin tana kuka har ta rufe idon ta a qasan wajen ta daina mitsawa, a haka ya samu damar ida qudirin shi na mata allurar bacci, ya debi jinin ta dan mugunta har keda biyar, yana gamawa yai ma mijin Saudat magana ta waya, yaji yana haki, tambayar shi yai ko lfy, ya bashi amsa da " sai da jakar taci duka tukunna, wai ni zatai wa zancen haihuwa" " kalla rabu da su wannan shegiyar uwar tasu ce zata zugo su ai gashi ta ja musu duka , ni leda biyar na diba dan uban ta, ai ta gina jikin da kayan kudin" dariya Kalla yai sosai," ni kuma hudu da diba" to sai mun hadu yanzu zan fito,tsallake ta yai ya fice dakin shi ya saka jinin a inda aka basu su saka, wata jakar fata da akai mata ado da ja, da ratsin baqi a jikin ta ta ratayawa ce, ba a son su aje ta a qasa ko da da mistake ne sai sun ba da wani wannan ya tashi aiki, in ba haka ba sai an kaiwa Oga Zaks matan, domin ko kusantar su yai jinin nasu diban shi ake, sun isa wajen Oga zaks, suna isa suka miqa mai jinin wata dariya ya barke da ita kamar an yaga zani, ba ko dadin saurara" aikin ku na kyau, shiyasa kuka fi sauran abokan harka shanawa, bakuda tsoro, bakwa jinkiri, ku gaggauta maza muje a ba Dodo jinin kyawawa ya sha" ta shi sukai suka shiga wani daki, dan tsoro ina leqawa nai baya a 360 ba zan iya dakko maku rahoton komai ba anan, gidan Saudat na je, tana kwance rabin jikin ta na kujera, rabi na qasa, fuskar ta ta kumbura tai sintim, dan tafi ta kwanaki hayewa, jikin ta ko digon duka babu, a zuciyata nace wanan Alhj Kalla shi na shi hukuncin Kalla mari ne kawaiπŸ€” mari kam iya mari ta shashi da dikkan alamu, dan ina jin shi ya sata suma ma, ruwa na yayyafa mata na labe, a firgice ta miqe tana" ni bana son Yaran ma har abada, kayi hakuri ka daina kallan mari" tana fada tana kuka fuska dagaje2 da hawaye ga majina da yawun azaba" dube2 ta hau yu taga ba kowa, ga wani irin jiri dake dibar ba, da tsananin ciwon kai, komawa tai ta kwanta, tana maida nunfashi, suwai ba ko vata farka ba sai da suka koma gida wajen qarfe hudun asuba, yana isa daga ta yai toilet da ita ya hada ruwan zafi ya saka ta, ihu ta saka na azaba, dan jikin ta duk ya farfashe," kayi hakuri mai sunan Annabawa na tuba, ba zan qara maka zancen yara ba har mu mutu, ka yafeni sharri shedan ne" rife mata baki yai yana hawayen munafurci, yana bata hakuri shima, harda in ya sake ko taba hannun ta da sunan duka ne, duk.hukuncin da taga za ta mai ta masa, runtse idon ta tai.tana jin yanda zafi ke shigar ta, nan take zuwa Abuja ya sire mata a rai, wannan wace irin azaba ce, in kaci dadi na wata daya sai an zaizaye maka shi a kwana daya? Yanzu yanda take jin ta kamar wadda akaiwa yasar wani abu, bata da qarfi ga cuwon kai da take ji kamar kan ya fice, barin ta yai ya tafi kitchen ya samu fruits ya markade ya tace ya kawo mata ya sa mata abaki yace ki sha zaki samu qarfi sosai a jikin ki, bangaren d masu aikin su suke yaje,ya tas mai girke2 dan ya mata farfesu, ko na naman meye ma a samu ta samu kwarin jiki, ai ko ba komai ta maida mugun yawu, sannan abinda ya kawo ta kenan, inji shi, farfesun naman rago yai mata da yaji kayan hadi, irin farfesunnan ne wanda mutum zai zaci gashi ne, yasha kayan lambu a ciki, qamshi da maiqo sai tashi.yake, fresh milk ya hadi mata da shi, ya koma toilet din bata shanye jus din da ya mata ba dika, dakko ta yai ya dawo da ita gado ya cire towel din ya samo riga iya guiwa mai dan fadi ya zura mata, kanta ta jingina da frame din gadon idon ta lumshe, zuwa yai ya dakko wannan hadin ya shigo da shi, ai tana jin wani qamshi mai dadi sai ga idon Suwai a bude, wani yawu ta hadiya na kwadayi, Alhj Salihu yace" shegiya dangin maita, ji fa uban ta da taci amma ta ga nama har ta miqe" a ranshi yake wanan maganar, isa yai gaban ta ya aje mata ya fara bata taga baya sauri, daga mai hannu tai.ta saka nata dayan hannu ko ta kan spoon din bata bi ba, ta hau ci kamar tsihuwar mayya, ci take ba ko tsayawa sai da tai nak, ta kora da fresh milk, ta zame ta kwanta, lokacin Subh payer ta yi amma ko a jikin su, haka suka kwanta bacci, manne mata yai yana shafa ta, abin ku da wadda ta dade miji na gabza in ta nemi haqqin auren ta, yau.ta samu a bagas dik da zafin da take ji haka ta miqa mai kanta, ranar ta murna ba iyaka, tini ta nemi zafin ciwon ra rasa, kusan abinda ya faru kenan a gidan Saudat,sai dai akwai wani plan da Suwaiba ta hada a qasan ranta na ganin me yasa ba su son su haihu, suna son su san me ya hana su haihuwa????


Cikin dare Salma taji kamar buga qofa ake, a hankali ta miqe ba tare da tai wanai kwakkwaran motsi ba, dan tare suke kwana da Haule yanzu, leqawa tau ta qaramar qofa ta bular ta hango wan mijin nasu na waige2 yana kwankwasa qofar Marka, mamaki ne fak cikin ra dan duk yan kwanakin nan mark ke zuwa, yau fushi take da shi, daren jiya ya hana ta dari da hamsin da ta roqa yace bai da su, shine tace yau ba za ta ba, shi kuma gashi a mugun matse yake, hannun shi na kan wandon shi, haka yake kwankwasa qofar, budewa tai tana magana qasa2" Dalla can sai ka tada yaran ma sun gan ka, ni shigo kayi ka gana ka tafi" jawo shi ciki tai ta wandon shi, aiko akan idon salma, kame baki tai tana fadin " tab ashe wannan matar munafuka ce? Ba ta da maqiyi da rana kuma bata da masoyi da dare da ya wuce Babam bangis, lallai ran da Su Badamasin suka sani akwai case" tana cikin wannan tinani ta fara jiyo qarar dan qaramin gadon na Marka irin na qarfen nan, sannan ga sambatun ta nan da bata iya shiru ita sai ta tona masu asiri, yaran akwai nauyin baccin tsiya, to an wuni shiririta kuma anyi bacci  late dole in sun kwanta kamar gawwaku, Marka a wayon ta hade yaran take dika daki daya saboda irin haka, kafin Salma ta zo ne dakin ta yake na Yammatan, amma kawo ta yasa aka hade su, motsin qofa Salma ta ji zai fito sai da ya fito Marka ta biyo shi tana miqa tana gantsaro girji, shi kuma yana qara shafawa" kamar na koma mui ta yi sai asuba na tafi" " lallai Yaya kaima a gaida ka, duk wannan aikin da garar da ka diba bai ishe ka ba, in kana son ka koma ciki qaron nera daru kacal" murmushi yai haqoran shi jajaye suka bayyana" Aaaa dari tab na gama baki dari ukun yau, ni dai gaskiya ban da su"  " to kuwa kama gaban ka ka wuce ya ishe ka haka a barwa gobe" yana qarasa fitowa gaba daya Salma ta fito da buta a hannu ita ma , hankalin su ne ya tashi, gaba daya da ganin ta" Salame dan Allah ki rufa mana asiri, kar kowa yaji labarin nan" suna hada baki suka fada" a nawa zan shiru ko ko haka nan zan rufe bakin nawa kuke nufin" kudi ya dakko dari biyar guda biyu ya miqa mata" sauran naki kema, da sauri ta shiga daki ta dakko dari biyar ta hada dana hanun ta ta bata, " sannan ina son ki sani Talle ya kusa dawo wa dan jiya baki nan kina yawon ta xubar Badamasi ya fada sun yi waya, in ya dawo kk kuskura na ganku tare har kk hada jiki da shi warin ki ta mannu a jikin shi saina fada mai, dan ba zaki sa yanda ni na tsare aure na ba ina juran ya dawo mu raya sunna ki ja min amai ba kuma ba biyan buqata, kinji ni ko, wani yawu ta hadiya na yau ta shiga uku an raba ta da gwarxon maza, tace" na gane kiyi wa Allah ki rufa mana asiri" " baku da matsala in ma komawa zakui sau asuba din zan iya maku gadi" Aaaaa ni na ma ta fi yannan" fakam fakam Yayan Talle ya bar sashen nasu, ita kuma ta koma daki ta bar Marka da cizon yatsa an amshe yan kudaden kuma ba wai itama ta qoshi da abun bane, yau tayi biyu babu, tura qofar tai ta koma, Salma me zatai ba dariya ba yanzu sun dawo hannun ta kenan da taji tana son kudi zata neme su kuma dole su bayar ko ta tona su, wani muna tai ta dale gadon ta ta miqe.
Yau shamsiyya qawar su Juwairah da Nafee ta kawo ma Juwairah ziyara dan tana son ta qara bata wasu shawarwarin game da yanda zata gyara nonon ta da suka lamushe kamar an yi gobara ta ciki an yashe komai sai fata, sannan ga kanta dake yawan karyewa gashin ta na zuba, abu mafi mahimmanci da zai kaita ta taya su murna dan Nafeesa ta bata labarin samun cinkin da tai, murna take sosai itama da jin hakan. Shiryawa tai bayan ta gyara gidan ta tsaf kamar ba ita ba ta fito ta hau abin hawa har gidn su Juwairah da Nafeesa bayan ta sauka ta sallami mai adaidaita sahun ne ta shiga ciki, bangaren innar mu ta fara shiga, bayan sun gaisa ta mata murna ne ta shiga ciki , wajen Juwairah, a can ta hango Nafeesa tana alwalar la'asar, Juwairah na daka tana gabatar da sallah.........

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ   ' YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ

       BY HAERMEEBRAERHThis page is for u SWEETHEART, Sis Juwairiyyah, u ar d best sister that one could ever ask for, i love u so so very much dear, u ar d best.❤❤❤❤❤❤❤❤

Page 14:


Itama sallah tai domin da alwala ta baro gidan ta, tasan lokaci zai mata hakan, bayan sun idar ne suka hau gaishe gaishe, Juwairah na tsokanar Farha akan ta girma ta isa yaye," hmmm ke dai bari sis abinda na ke son ki ban shawara akai sis, ya zan dan nan da sati uku nake son yaye ta, nono gaba daya ya koma slipas b kyaun gani, ya barni da fata, duk nankarwa a jiki, ga cikina ma nankarwa tun na haihuwa, dan ma Allah ya san Abban su mutum ne mai kawaici baya son ya bata raina amma ba namijin da zai so hakan, dan kan ya koma hakan na kula yana matuqar son wajen"   " sister kin ko kawo kuka wajen maganin ki" dariya suka saka Juwairah tace" Nafee kina ban matsayin da bai kai nawa ba Allah" " no ba haka bane dear a gaskiya kina burge ni wajen hangen nesa wallahi na san ba komai bane ya jawo sai mai da hankali da kikai kk koya wajen Mama Biliki da muna ganin kina 'yar ta amma tana baki wahala ke ke komai a gidan gashi yana maki amfani"  haka ne kam, dan ko ni a da watarab sai naji na gaji bana son taimaka mata, data fahimci haka bata mun fada amsa take tayi takan ce jiki da jini, ti tanzu dai kin san me zaki yar uwa na farko ki nemo wadannan garin maganin ki fake su waje daya ki samu alkama ji qarin ta kina kunu kuna zubawa ko da madara ko ba madara, zaki iya sha, ke ko a ruwa xaki iya sha amma yafi kyau a alkama da madarar musamman ta shanu, magungunan sune kamar haka, NONON KURCIYA, GANYEN BAFULATANA, GADALIN NONO,  su ne abubuwan ana samu a wajen masu saida maganin mata, sai kuna na biyu mai sauqi kuma yana yi sosai shima, wanda zaki samu farar shinkafa, ki wanke ki jiqa akai markade ta zama kamu, sai ki daka bagaruwa da ake tsarki da ita, ki na dibar kadan ba mak yawa ba kina yin kunu kina sha, zaki iya saka madarar shanu ko ta ruwa in babu zaki iya shan shi haka, banbancin su wancan in ya karbi mace yana dadewa a jikin ta, sosai, sannan kuma ba a son qiwa kiyi yau kiqi gobe sannann ana son ayi kamar na wata daya, zuwa yanda nonon ki ya lalace, bangaren nankarwa kuma ki samu, man kade(wanda ake shafawa faso ko kaushi) sai kina shafawa a cikin ki da kuma nonon da dai in da kk san akwai nankarwar(stretch marks) kinji wadannan a sauqaqe kenan"" kaiiiii amma wallahi yar uwa na gode sosai, Allah ya saka miki da alkairi, Allah ya sauke ki lfy, ya bamu bby mai albarka," sunkuyar da kai tai a ranta ta amsa, " Dalla in zaki amsa ki amsa ba ma son gulma kikai cikin ma" " sannu Nafeesa sarkin rashin kunya na gode dani kk wannan maganar tin da ni nayi" cikin kaduwa Nafee ta hau zare ido, tama kasa magana, su kuma dariya da kunya ce ta kama su musamman ma Juwairah ashe Yayan ta duk yana jin su, tashi tai ta ja labulen ta fita wajen shi kai a qasa" sannu da zuwa mine" " yawwa princess, how ar u feeling,now?" " i am kind of k, amma fa kaina yanajuyawa kuma cikina na motsawa sai nai ta jin tsoro kuma abin na min daban haka" " ki ta hakuri kinji princess u will be fyn inshaa Allah, kawai hakurin nan naki dana san ki dashi zaki ci gaba zamu iya komai we can get thiugh it all" murmushi tai, shima haka yai kissing bayan kunnen ta a hankali, sai da yasa tsigar jikin ta tashi, " yanzu tinda shamsiyya ta zo bari na je wajen Innar mu na yi hirata nima" gai da shi shamsiyya tai ya yi ma Farha wasa ya tafi, Nafeesa ta aika da abincin shi da komai, da kyar ta karba dan kunya da tsoron Yayan nata, dariya suko sukai ta mata,bayan ta dawo ne ta ce" laaa Matar Yayah na hada mana zogalen da ramar?" " kaiii amma Allah ya miki albarka, pls do" ta shi tai suka je Nafee na hadawa suna hira ta saka komai zata yanka albasa kenan, Juwairah ta dakatar da ita" Nafeesa kar ku sa mana albasa sai dai a naki dan mu muna da masu shinshinar bakunan mu, ehe, baki san ba a son in yamma tai mace ta ci albasa ba? Dan haka ki kiyaye ko ke zaki in miji na gida ki hakura da albasa,in ko kinci ki tabbatar kin wanke bakin ki tass yanda ba yanda za ai ya ji warin ta" godiya suka sake mata dikkan su shamsiyya tace" lallai zan yawai ta zuwa gidannan don na samu sirrin da yasa baki taba fada da mijin ki ba kuma kk iya controlling din shi haka"  " hhhh haba shamsiyya ai mace bata controlling miji sai dai ya zamar mata bawa a lokacin da itama ta zamar mai baiwa, na miji ba ya sanin ya zama maki bawa sai dai yaji mutane na cewa ya zama mijin hajiya, ko mijin kan tace, da sauran su, babban abinda ke jawo ma mace hakan kuwa shine, neman soyayyar Allah makadaici, in mace ta nemi soyayyar Allah, ta kuma samu ta gana da na miji, wanda hakan yai qaranci a cikin mu mata, daga wajen boka sai dora rai akan, maganin mata, bayan ba su kadai ne ke riqe zaman aure ba, wallahi in Allah ya so mace ta gama samun dacewar duniya da lahira, dan haka ni sirrina na zaman gidan aure shine son Allah da neman Allah  ya so ki, saka soyayyar namiji a saman ta Allah shi ke saka mata fadawa halaka, daga zuwa wajen boka, zuwa zinace2, da dikkan abin da ya kauce hanya dan haka ina horon ku da neman soyayyar Allah, wani irin dadi ne ke ratsa su dikkan su, musamman Jabeer da ya kawo kwanuka da niyyar yin alwala yai tafi masjid, wani irin dadi yaji yakuma godewa Allah a zuciyar shi sosai da samun mace kamar Juwairah, suma sallah sukai, suka raka ta ta hau abin hawa ta tafi, tana cike da farin cikin samun qawa kamar Juwairiyya.Kui hakuri da wannan sisters dan nayi alqawarin typing ne yau ma da ba zan samu yi ba, tanx alot. Me love u xoxo.❤

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA    πŸ’…πŸΌ

  
      BY HAERMEEBRAERH


page 15: 


Yaune ranar da Suwaiba da Saudat suka hada akan zasu je asibiti su ga meke faruwa har yanzu ba su samu ciki ba balle a kai ga sa ran haihuwa, sun shirya tsaf inda suka yi ma mazajen qaryar zasu tafi shoping ne, Dunes Supermarket suka nufa cikin isa da qasaita, da nuna su wasu je a Abujan ma, Alhj Salihu ne ya biyo su a boye ya tabbatar da ina zasu je, ganin sun nifi nan ne ya sa hankalin shi kwanciya, ya kira Alhj Kalla ya sanar da shi cewar da gaske shoping suka tafi, Suwaiba ta kula da bin ta da yake duk da qoqarin boyewar da yake shine dalilin ce ma driver ya kai ta can tai ma Saudat message akan su tafi can din, bayan sun isa ne sukai sauri suka fita ta baya suka je wani private hospital dake kusa, ta shin farko likitar ta gane ai ba ma mahaifa a tattare da su an cire ta, hankalin su ba qaramin tashi yai ba, kuka suka saka kamar wasu yara, jikin Saudat sai rawa yake dan ta fi Suwaiba son yara, dan Suwaiba dama ita ba wai ta wani damu da su ba ne, amma kasantuwar yanzu taji bata da mahaifa kwata2 hankalin ta ya dagu sosai, tashi sukai bayan sun gama biyan komai suka dawo supermarket din suka debi wasu daga abubuwan da suke buqata musamman na gyaran jiki, Suwai ba kuwa acici kayan kwalam fa maqulashe ta jida," da mu zauna ba mahaifa ba kayan more rayuwa ai gwanda mu kwashi rabon mu muci tin da bamu da magada" fadan hakan ke da wuya Saudat ta saka kuka," Malama kar ki taran jama'a, meye na kukan kuma a cikin mutane, daga cewa mu more rayuwar mu, dan haka ni dai kinga, in ba zan haihu ba ba kuma zai hana na more rayuwa ta ba,come to think of it, ba mahaifa ba haihuwa ba kudi, wahala ta kama mu fa kenan, kuma mazajen mu suka san bama haihuwa mun shiga uku, in gaba suka so qara auren su za sui, ba gwanda mu ware ba mu saki ran mu mu tatsi abinda muka tatsa, tin da mun taba zaman Abujan munji abinda ke cikin ta, kinga sai mu canja sheqa" gyada kai tai kamar qadangaruwa, amma wannan zancen rashin mahaifa kuma ita da yar uwar ta a tare akwai wani abu a qasa wanda sai ta binciko ta san mene shi, bayan sun kammala kowa ta kama hanyar gidan ta.Yau gidan Talle shar da shi domin ta shi kawai sukai suka ga Salma na bada umar ni ko ta ina kuma Marka bata ce komai ba, da farko sawa tai manyan sukai shara sosai, suka share ko ina, suka wanke bayin su, aka fito da wanki narke da daki kowa ya duqa har yaran sukai ta wanki, da kudin da ta karba a wajen su da shi aka siyo sabulun wanki, bayan sun gama ta sa su wanka, gidan yai fes da shi, Marka ma sai da tai wanka ranar, Salma tai wanka ta tafi daki ta kwanta, dan ta bada kudi a siyo kayan miya ai girki, kwanciyar ta ke da wuya, Huwaila da Jummala suka shiga dakin mamar su da ya sha gyara suka hau tambayar ta wai me ke faruwa ne" Um Um Um Um Um" shi take maimai ta wa kawai tana kama baki, alamar sui shiru maganar babbace , kame bakin nasu ko sukai ba su qara tambaya ba,Marka ko cikin zuciyar ta cewa take, "yarinya ni ce fa uwar shedanu, ki gama wannan mulkin naki na yan kwanaki, kiga abinda zai.faru nan gaba, dani kk zancen" da yamma suka ji qarar mota fita sukai da gudu, Huwaila na can Ita da Baban gida a wani lungu na gidan suna sana'ar tasu, sukaji qarar, ai a firgice suka saki juna sukai hanyar fita daga lungun kowa na zare. Idon, Talle kenan mai gayya mai aiki, shine ya iso, Salma da jin haka ta miqe tana rangwada ta je.ta taro shi, dawowa sukai ciki yaran nata gaida shi, yana amsawa, dakin Marka ya leqa ta ganta tai wanka dakinnan fes, wata uwar dariya ya saki" Shegiyar sama wato ganin amarya ta kyakkyawa ya nutsar dake, yo ni dana san haka ne ai dana dawo da jimawa, da ban tsaya wajen qadangarun bariki suna amshen kudina ba" leqawa zai ya shiga Salma ta tsaya a bayan shi tana kallon Marka, da sauri Marka ta miqe ta ja baya," Aa Talle in ka zauna dakin nan ba ai wa yarinyar can adalci ba kuma, wancan karon ai a wajena ka fara zama ina ganin wannan karon wajen ta zaka fara zuwa" tsantsar mamaki ne ya kama shi ya sake baki, qarasa yai wajen ta ya taba wuyan ta yaji lafyr ta qalaou kuwa? Ya jita daidai, amma abun nan akwai mamaki, kada kai yai ya juya yai dakin Salma dan tana ma Marka kallon nan ta juya, hira ya dinga mata da ba wai ganewa ta ke ba, dan gaba daya tsami yake yi, dabara ce ta fado mata, ruwa ta saka a bokiti babba, ta dakko brush guda biyu ta saka toothpast jiki ta je kusa da shi zuciyar ta na tashi amma ta jure ta zauna a cinyar shi tana shafa shi, " Babe taso muje mui wanka magariba na yi, kaga in munyi munyi sallah sai muzo nai maka tausa dan da alama ka gaji ko" gyada kai ya dinga yi kamar qadangare ya daga ta yana son ya dauke ta, da sauri ta sauka dan in ya sata a kafadar nan sai tai amai dan tsamin zufar da yake, nuna mai tai akwai yara kawai yaje ya fara shiga zata biyo shi ta mai wankan, tafiya yai yana washe baki, rabon da a mai haka tin tana amarya a cikin garin Abuja, wanka ta mai sosai, ta bashi brush ya wanke bakinnan fes,sai ga Talle an yi shar, shima kar ba yai ya mata wankan ta wanke bakin ta, ta fara leqawa taga ba yaran maza ta fito, daga baya shima ya biyo ta dakin, shirya shi tai tace yai alwala ya je masjid" ka ji min yarinya da ke kk sani nai sallar? To banga dama ba hadawa zan da isha'i"  " Aa Allah ya baka hakuri, ni so nake dama kayi da wuri saboda in na zo maka tausar nan bana son abinda zai sa na tsaya" cikin yauqi da kwarkwasa take maganar,tini ya washe baki kamar dolo, miqewa yai zai tafi masjid, yajiyo maganar ta," Babe in kaje ka jira sui isha'i kawai ka ga in ka shigo sai asuba zamu sarara ko ya kace" ta na kashe mai ido daya, " maganar ki duce sweety na" ai ko ana idar da isha'i sai gashi ya shigo fakam fakam, yana shigowa ya tadda ta tai gayu sosai da yan kayan da take da su, ta dan fesa turaren ta da ya kusa qarewa dan kale ma take yi, yana shiga daga ta sama yai yana juyi da ita,ita ko dai dariya take tana sakewa, kisses ya fara aika mata da shi tana mayat mashi, suna tsaka da wasannin su ya katse ta da "ni fa yunwa nake ji, mu fara cin abinci kannan yarannan sun yi bacci sai mu dora daga inda muka tsaya, dan yau sai na saki kiran sunan tsohuwar ki" dariya ta ke sosai a haka ta dakko masu abinci suna ci suna hira, " Babe me yasa ka amshen waya ta ne, tinda naxo yanzu kusan wata bakwai da wasu kwanaki ban ji muryar kowa nawa ba" wani mugun kallo ya buga mata daya sa cikin ta kadawa, dan dai Tallen Tallen ne fa, sunkuyar da kai tai tace" ka yi hakuri ba zan sake zancen ba" wasu hawaye masu zafi suna sauka a fuskar ta, hannu tasa ta share su kamar ba ita tai kuka ba, ta dakko cokalin abincin ta kai bakin shi, amsa yai ya dan sake rai kadan, a haka har suka gama, Huwaila da Jummala kamar yanda suka saba sun fita zance amma zancen da su Badamasi ne, ana can ana latse2 da tabe2  da tsotse2, ita kuma Marka sun gama shirya duk abinda ya kamata cikin duhun nan ita da Yayan Talle, da zata wuce ne ya daki duwais din ta ta baya, juyo wa tai ta hau masifa" kaifa yayan nan jarababbe ne, kwana dayan nan da akai ba ai abun ba duk ka zama kamar ka dauke ni mu gudu, to ina sanar da kai ka iya takun ka, kasan Talle ya fika wayo ko dan ba soko bane kamar ka, zai iya gane wa" kada mata kai yai alamar zai kiyaye, shigewa tai, Salma amarya ana can ana soyewa ita da me gida, Sun yi nisa ba sa jin kira, komai ya kankama, har ya fara aiki, suna cikin yi ne sukaji motsi ana sanda, gaba daya Talle ya cika wajen na su da gurnanin shi, Marka kamar ta mutu dan kishi, ga wani irin feelings da take ji, sai matse qafa take ta kai ta dawo, ta kuma kaiwa ta dawo, tana jin motsin tace," Alhamdu lilLAAH"  ai ko ta manna kan ta a jikin qofa taji ya za a kaya, " Salame bude qofar mana na iso, me kk yi ne baki riga kin bude ba sai na zo ina bugawa sun ji kamar rannan, so kk wannan shegiyar kishiyar taki mai baqin tsiya taji ta leqo irin na rannan, Salame ya dai naji ki shiru, dan Allah ki sauri mana ki bude muyi mu gama na tafi a matse na zo yau" Talle da ya gama jin komai wani shaqa yai ma Salma da idon ta ya firfito waje, amma da sauri ya sake ta ya sauka , ya saka wando jin da yai ba a daina taba qofar ba,kuma ba a daina kiran Salma ba, ai ko mai maganar da ya leqa ta bular da yake hango su yaga yana ta howa da gudu ya kwasa yai waje, ya fito da hanzari yaga an gilma da gudun tsiya komawa yai dakin, dan ya san laifin ta ne koma wane, kan yaje ta zura rigat ta tana ta kukan wannan masifa da ake neman jefa ta, " Marka" shine abin da ta furta,dafe kan ta tai, da ta sani da bata tsuye ta ba ta bat su da halin su, gashi yanzu ta jawa kanta,dukan ta ya fara ko ta ina tana ihu tana ya tsaya yaji me ya faru, ba ta da laifi, inaaa dukan ta yake tin tana kuka tana bashi hakuri sai da ta koma ajiyar zuciya, sai da ya tabbatar ta kasa motsa ko da ya tsan ta ne sannan ya futa dakin Marka, tana bude qofar ta wani azababben mari ya maka mata, " Dan uban ki kin san hakan na faruwa ashe kk munafurcen baki gayan ba ko da ta wayar yarannan ne? Ga shi kwarton na ta ya ce kin gansu" kuma ta fara dan marin ya matuqar shigar ta" inna fada maka ba yarda za kai ba cewa zakai kishi ne, shiyasa nace Allah ya nuna maka da kan ka ka gani" kwafa yai yace zata ci uban ta na san maganin ta ai,komawa yai ya kwanta, a dakin markan, nan take jarabar ta ta motsa, musamman d ta gan shi ba riga,matsawa tai da zummar kwanciya gefen shi, da dabara ta goga qirjin ta a bayanshi, wata ajiyar zuciya ya sake ya finciko ta, da zafi zafiya ya fara aika mata saqonnin shi cikin huce haushi, marka tun ana na dadi tana kukan dadi, sai da ta fara kukan wuya, roqon shi ta ke Allah Anna bi ya kyale ta amma inaaa yai nisa, sai da ta gwammace ba tau wa Salma mugunta ba ranar, fadi yake yana" duk sai kunci uban ku, zan maganin kowa a cikin ku, ki min shiru abin da kk so nake baki ko na farfasa maki baki" ya kaiwa bakin ta duka, dip tai bata qara kokawa ba sai kukan zuci, da sassafe ya shirya ya daukar wa Salma kayan ta suka wuce cikin garin Abuja, Marka kamar ta mutu dan haushi, ita da ta so a barta ta zauna da su amma shine aka tafi da ita, kai wannan abin haushi da yawa yake.
Sun isa Cikin garin Abuja da rana wajen 12pm, gidan Alhjn shi ya kaita, sun qara yin tafiya, amma wannan karon dakin shi na gidan nan ya kaita, ya aje ta , yai ficewar shi, miqewa tai fuska ta kumbura sintim da kyar take gani, ta jingina da ginj ta rungume guiwowin ta tana kuka mai bam tausayi, nadamar zuwan ta ABUJA kam ta yi ta ba iyaka, wato in baka iya kama barawo ba ya kama ka, wannan shine ya faru tsakanin ta da su Marka.


Jabeer ne yai sallama ya shigo fuskar shi cike da fara'a kamar wanda yai tsintuwar dimond...........[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA    πŸ’…πŸΌ    


    BY HAERMEEBRAERH

Hey guys thank you so very much for everything. Na ji dadi sosai da kulawa da nuna damuwar ku, na ji sauqi sosai. πŸ’ƒπŸ» Alhamdu lilLAAH. Love u da yawa❤

Page 16:Shiga yai hannun shi buyu boye a bayan shi, ita kuma ta sowa tai da niyyar mishi sannu da zuwa yanda suka saba, sai taga ya maqale a jikin gini yana mata dariya, daga girar ta daya tai tare da lumshe cikin wani salon daukar hankali" me kk boyewa baka son na ganiiii" " matso kusa ki gani to" matsawa tai, kusa da shi sosai, in ta matsa yace ta qara, haka har saida jikin ta ya zama gaba daya a nashi, sannan ya fidda hanneyen shi ta bayan ta, ya rungume, yai kissing din ta sosai, sannan ya kama ta suka zauna, miqa mata leda yai ya tallabe fuskar shi yana kallon ta da murmushi, bude ledar tai itama tana murmushi tana kallon shi tana kuma kallon ledar, tana budewa taga wayar da zatai dubu sha biyar, bude baki tai cikin murna da tsalle, ta dane shi tana mai kisses ko ta ina, kama ta yai ya riqe kafadun ta, " My princess ki nutsu kina girgiza mana bby, so kk kuji ciwo?" " Kaiiii amma mine na gode, na gode , na gode, Allah ya saka maka da alkairi, Allah ya sama dukiyar ka albarka da rayuwar ka gaba daya, Allah ya jiqan iyayen ka ya sa su cika da imani" " Shhhhhhh wai wannan godiya haka kamar na sai maki mota?" " hmmmm kai ka ga bai kai ai.wannan godiyar ba, kai ma kasan ina da son waya, a matsayina na wacce ba ta taba riqewa ba yau na samu ai sai godiya ko, beside macen kwarai dole ne ko tsinke mijin ta ya kawo ya bata ta nuna mai godiya da murnar ta, in ba haka ba taiwa kanta baqin ciki dan gaba ba zai ci qwarin guiwar kawo wa ba" " wannan haka yake macen kwarai, mace daga cikin matan aljanna, Juwairah in dai ta dalilin miji ake shiga aljanna na maki alqawarin na yarje maki" wani irin hawaye mai dumi ne ya ke bin fuskar ta na tsantsanr farin ciki da nishadi, ga wani son shi da ke ratsa shi, " Yah Jabeer, na gode sosai Allah ya bar mu tare , mu je aljannar tare, domin kaima ka shiga cikin alqawarin Allah duk mai kyautata wa iyalin shi zai shiga aljanna, kana daya daga cikin mazan da suke koyi da halayen Annabin rahama da sahabbai" haka sukai tai ma junan su dadadan kalamai, ( abinda aka rasa a wannan zamani kenan, saurayi zai tai ma budurwar shi daddadan zance kan aure, amma da anyi kwanaki ya daina kenan, itama haka, sai a dawo kowa na dana sanin auren dan uwan shi, auren duk da muke ganin yana dadewa wallahi ba sa dai na neman junan su kamar ranar suka fara haduwa, kowa a kullum yana son ya fidda sabon salon da zai faran ta ran dan uwan shi ne, dan haka mu ci gaba da nemawa juna farin ciki sai auren mu yai qarko).

Bayan an kwana biyu Suwaiba da Saudat sun fara sabawa da wannan mummunan labarin da suka juyo wa kansu, Saudat ta fara neman dalilin da zai sa ta san me ne ne silar rashin haihuwar su, watarana Alhj Kalla  zasu tafi meeting gidan Oga Zaks , domin a wannan yana yin da ake ciki ta fuskanci ko su su waye, sai dai ta qi gayawa Suwaiba dan ita akwai wauta, da ta sani zata fasa kowa ya san sun sani, ta ko jawo masu masifa, sai da ta gama jin komai wani member suka samu da zai shiga qungiyar tasu amma bai san location ba, take Alhj Kalla ya fara bashi address, Saudat na kwafewa, tana gamawa zata tura riga Alhj Kalla ya fito, gaban ta ya fadi amma ta dake, ta ci gaba kamar tana gyaran rigat ne," Ohhh mata kenan, daga kwalliya sai saka kayan ado, sai gyare2 kawai kar dai aga munin ku" dariya sukai gaba dayan su," ina ta kiran ki ina palo banji kin amsa ba" take ta gane wayo yake son mata," ai ban jiba Alhj na, ni da nake nan kana can,wataqila ma da ka daga murya dana jiyo ka, tinda kai ba zakai amfani da waya kana kirana ba , sai kai ta kira in ban ji ba kace nai laifi" murmushi yai a ranshi ya tabbatar bata ji komai ba, "k shikenan je ku dakkon ruwa na sha anjima kadan zan fita"  tashi tai tana kada jiki tana yauqi tana isa kitchen ta qarasa da hanzari ta ciro takardar ta wulla a bayan fridge din dan ya fi kusa, motsin shi ta ji ya biyo ta, budewa tai kan ya qaraso ta dakko ruwan da cup, yana isowa tace" hmmmm Alhj na kana sona da yawa na kula 'yan kwanakin nan kamar ka maidani rigar sawa ko ina zaka sai dani" murmushi yai yace" ai ke kk koma haka shiyasa na koma hakan" ya karbi cup din ya hade da hannun ta, ya matse saida tai qara, ya zaro mata idon shi jajaye yace" ki kiyayi bincike domin yana kai maiyin shi ga halaka" " Bannnn......ban ganee...baaa" " dalla malama rufen baki, ji kk ban san kina bin waya ta ba? Ko in da na fita, ki gani? Ina nake zuwa me nake yi? Me kk son sani yau na sanar dake? Dan ba tsoron ku muke ji ba? Auren kwadayi auren kudi kukai, kuma kuna samu, to meye na sai kun ji kwakwaf?" Jikin Saudat sai rawa yake wani ruwa2 taji na tsattsafo mata ta qafart ta batai aune ba taji ya kwada mata bari" Dan uban ki fitsari kikai a tsaye? Ji yanda kk batan takalmi ni da zan fita? Me kk sani game da mu?" " Alhj ban san komai ba, sai dai zargi da nake" aje cup din yai ya zaunar da ita a kujerar dinning dake kitchen din " ehen ina jin ki zargin me kk?" " dama ina zarkin ko ku yan damfara ne, kai da Alhj Salihu" " kin tabbata zargin da kk kenan?" "Allah shine" " to bari kiji, zargin ki ya tabbata, amma idan na ji wannan maganar ko a wajen waccan doluwar yayar taki da ba abinda ta sani sai barin zance, da soj kudi, kin mutu, kinji ko baki ji ba" cikin tsawa ya qarasa zancen," Nnnnaaajii..."" Good,ni na fita, miqon takardar da kk boye kan na karya ki" tashi tai ta dakko ta miqa mai, ficewa yai ya barta ta durqushe tana ta kuka, lallai yau data gaya mai abin da ta gano game da shi da fa shikenan kashe ta zasui, yanzu ta gudu ma nan ma har gidan su zashi wataqila ma ta jawa uwar su a hada da ita a kashe, ta zauna tai shiru sui ta cin kudin haram kudin jini, "kaiiiiii wannan Abuja ba tai ba, inaaaa" ni dana sani a Damaturu nai aure na ma" ta fada tana share majina.

Salma ido ya kumbure dga zaunen tai baccin wuya ba shi ya dawo ba sai wajen la'asar, riqe da koko da qosai dan yamman nan da ake yi, sai wata leda mai kaya a ciki kala uku da takalmi kala biyu sai jaka daya, da yan kayan kwalliya da ba a rasa ba, miqa mata yai, ta tashi ta isa ta karba, leqawa tai ta yamutsa fuska, " baki daku ba kenan ko, gar da zan baki abun da ban sai wa Marka a shekara goma ba, ke kin samu ma kk kyabe baki ko" a tsorace tace" na gode" ta tashi ta shiga dan bandakin dake maqale a dakin tai wanka ta canja kayan ta fito, koko da qosan ta dauka ta ci ta sha, sannan ta koma ta zauna, " kin iya cewa wani yai sallah amma ke bata dame ki ba, ji kk ban gane ki ba, wa'azi a baki amma ke baki aiki da shi munafuka, irin kune kuna da yara kuna sa su sallah su qi, to basu ga kuna yi ba" miqewa tai zalo zalo taje tai alwala tai sallar ta koma ta zauna," zuwa gobe ogana zai dawo shi kadai yake zama anan, matan shi suna maiduguri, aiki ke kawo shi nan,  dan haka in ya dawo da yamma ki shirya muje mu gaida shi, in muka dawo na gan ki a waje ko kusa da wajen dakinnan kin mutu ranar, dan na san ki idon ki idon kudi, kice zaki maqale ma bawan Allahn da bai san neman mata ba, na kula akan kudi komai yi zaki, tinda an iya bin qattin qauye masu bada dari da hamsin" hawaye take sosai sunqi tsayawa, haushin ta bai wuce yanda yama qi ya saurare ta ba sam, ya tsaya ta mai baya ni yaqi, kawai sai ta maida kanta ta kwanta, bata qara furta komai ba har ya shirya ya fice, kuka take mai ban tausayi" Oh ni Salma na saiwa kaina wahala daga yar shawarma da motar dana gani duk na rude ga inda na kawo kaina, Abuja ko wahala?"

Da kyar Marka ta miqe ta je ta hada wuta ta shiga ruwan dumi ta gasa jikin ta, komawa tai ta ci gaba da kwanciya, wani qaramin yaro ne shafi'u daya daga cikin yaran da Talle ke auri saki ya shigo zai kai shekara goma, baya jurar yunwa shi, dan ko da su Huwaila na baccin gajiyar iskancin su da suka sheqewa da dare, ita Marka takan tashi tai abin kari da wuri, to yau sunji shiru kowa dif a gidan, tura kai yai ta ware qafafu tana ta firfita da mafici," Marka yunwa muke ji" da sauri ta sake zanin ta juyo kan shi," me kace?" " cewa nai yunwa muke ji" habaaa ina wuta na saka wannan yaron, inji Marka, kiran shi tai tace zo ka karba, yana isa data damqe shi ta hau duka, tana" sai na fashe dukana akan ka, dan uban ka, banda wannan ta'annutin da uban ka ya min, har abinci kk tambaya? Ga shi tinda ya dauke waccan jaja amaren sai da na gan shi kuma, to ko xaka ci abinci har ka qoshi, amma na duka" dim dim dim kk ji" Marka lfy me ya miki haka" cewar Haule kenan, tana qoqarin kar bar shi, wani mari itana ta karba, kai na taqaice maku duk wanda ya shiga sai ta saki wani ta kama wani haka tai tayi kamar mahaukaciya, sai da ta gaji jikin ta yau laushi sannan ta kwanta tana kuka, ita ta shiga uku, ta hada sharri kuma ya zame mata tsiya......

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ   ' YAN ABUJA  πŸ’…πŸΌ
       BY HAERMEEBRAERH
Masoya novel din 'YAN ABUJA  dan Allah ku min hakurin jina da bakuyi akai2 yanda na saba, inshaa Allahu in komai yai normal zan ci gaba ba da tsaya ba har sai na gama dika. Na gode. Love u all❤


Page 17:


" wa'alaikumussalam shigo shigo yar uwa kiga me yayana ya saimin" Juwairah ke fadin hakan cikin murna da kuma zumudi, Nafeesah ce ta qara sa shiga itama cike da dokin ganin me za a nuna mata, sanda ta gani itama yar qarar murna tai ta haye kujerar da Juwairah take" kaiiiii amma Allah ya saka ma Yah Jabeer da alkairi, ya sai mana waya mun daina leqen ta qawaye" " to malama ba wai an sai mana waya ba na dinga neman ta ina rasawa" " hhhhhh Allah baki hakuri ai wannan wayar inna dauke ta yanda kk san jariri sai kin nema na miqo maki, ko in tana buqatar a sa mata kudi" dariya suke sosai, " yauwa wai ni ruwan meye wancan a butar qarfe na ga kin saka a garwashi?" " Oh ban cire ba dama je ki sauken dan Allah ki dawo na fada maki hajiya tambaya" " ah to dan kin san in baki fadan ba baki da zaman lfy yau" fita tai ta sauke mata butar ta dora ruwan wankan ta , ta koma dakin, xama tai tare da tanqwashe qafa agaban Juwairah tace " To malama a bamu darasi, dan zama dake akwai diban ilimi" " ke ko, ke ko, hmmm kina raina sanin da Allah ya baki ne amma kin fini ilimi ai, kefa duba ki gani yanzu ci gaba da karatun ki kike ni fa ina zaune a gida kullum" " kema zaki ci gaba ne komai lokaci ne sis oya ina jin ki meye wancan a butar qarfe?" Dariya Juwairah tai sosai sannan tace" ke dai ba ki mantuwa to magani ne, maganin infection musamman na masu ciki, Mama Bilki naga ta yi lokacin cikin Ammar shine nayi, Oh har naji ina son ganin yaron nan wallah" " to naji magani ne amma ai baki fadan ya ake hada shi ba ko" haka ne, kinga dai da fari zaki samu ganyen garahuni, da 'ya'yan hulba ki tafasa su sosai sai ki bari ya sha iska sai kina tsarki da shi, da yawan masu ciki suna fama da infection sosai, mai fidda ruwa kala2, amma da zasuna amfani da wannan zai masu magani duk da ba wai yana dauke shi dika bane kwata2 amma yana ragewa sosai, in aka hada da wasu magungunan na sanyin" " yauwa ko ke fa ba ga shi kin qara min ilimi ba ni ina ma san wannan abun,in ba yanzu ba, yauwa rannan naji kina fadama shamsiyya wani abu lokacin na fita ban ji me kuke cewa ba game da warin gaba" " Oh k wannan, dama muna magana ne akan macen da take fama da warin gaba na farko dai akwai na lalura, akwai wanda mace da kanta take jawo wa kanta" "hhhhhh kaji Matar yaya wai mace ta jawo wa kanta kamar yaya? Kana sane kabar jiki yaita tsami"  dariya sukai sosai suka tafa, " Allah da gaske nake, yanzu misali Nafee, ke ce kin tashi a rana kin wuni da pant daya a jikin ki, kin je fitsari kin yi fitsari baki wanke wajen sosai ba kin maka pant kin mayar, kin yi bayan gida kin maka kin mayar, sannan da jiqar da komai kk mayar wa, ki fadan pant din dan uwan ku ne da zai qi wari?"  " hhhhhhh wallahi dole yayi amma dai misalin nan dama ba dani aka buga shi ba a canja gaskiya a saka Salma" " wulaqanci yayar tawa, Allah sarki mutan Abuja ana can ana shan dadi an manta da dangi" " hmmm ke dai bari buri ya cika, Allah muma ya sada mu da mafi alkairi" " Ameen dai" " to yanzu fadan ya za ai ai maganin wannan warin dan Allah dan akwai yar makarantar mu, kin zauna kusa da ita sai kinji wannan warin, dan ba zanji kunyar fada mata ba, da azo ana ta gulmar ta tana jin haushi" " Allah sarki, aiko gwanda ki sanar da ita, dan aboki na gari ke wayar da kan abokin shi, kina ji ba, a rana a baki canja pant a ki canja sau uku, ya zama na kina da tsimma ko towel qarami a toilet din ki wanda in kikai fitsari ko bayan gida zaki tsane wannan ruwan, sannan in kin zo tsarki ki fara da gaba ko da baki komai ba, sannan baya, karki hade wajen wajen wankewa, in kk gama kk goge wajen sai ki maida pant din ki, in rana tayi kikai wanka sai ki canja, da dare ma haka, ba yanda za a same ki da wari ko da baki shafa misk, balle a same ki kina wanke wajen da ruwa mai dumi da kk zuba zuma asalin me kyau, wannan wanke gaba da ruwan zuma ya samo asali ne daga Annabin rahama yana daga taskar magungunan daya bayar muna amfani da shi, bake ba warin gaba in dai kina wanke wa da ruwan zuma kina saka misk, kina tsanewa in kinyi bayan gida, ina fatan na amsa tambayoyin ki Hajiya tambai" " hhhhh wallahi kin biya ni kin amsa har da wanda ban ma zata ba ke dai Allah ya barki da yaya, ya sauke ki lfy" cikin jin dadi tana shafa cikin ta ta amsa, tashi tai ta tafi bayi da butar ta a hannu, bayan ta fito ne take ce ma nafee" Nafee gobe ne kin san ranar gyaran jikina ina zan samu dankalin turawa pls na wa ya qare" karki damu zan samo maki kan gobe, ji cikin ki ya fa girma amma kk maganar gyaran jiki, ki bari ki haihu mana" " Tab aa ni dai ki samo min, in babu ma ina da zuma da sugar kawai ki samon lemon zaqi ko daya ne ko biyu" " to Allah ya kaimu, bari nai wanka na fita makaranta" "to Allah ya bada sa'a, bari na dan huta nima".
" Alhj wannan itace mata ta da kuka karba min auren ta a garin kano, dama na dawo da ita nan ne dan na dinga samun kulawa, zama ni dayan ba dadi" Talle kenan ya fada yana sosa qeya, murmushi uban gidan na shi yai yace" Allah sarki ai ba damuwa, hakan da kai kayi tinani, kuma ka kyauta, ina maku fatan alkairi, Allah ya bada zuri'a dayyiba" " Ameen" gaida shi salma tai kanta a qasa tana wasa da gyalen ta, ya amsa ba tare da ya kalli in da take ba, kudi ya qirgo dubu goma ya bata, yace gashi ta sai wasu abubuwan da take buqata, amsa tai hannu na rawa, rabon data riqe kudi haka ai ta manta, tashi sukai suka fito, suna isa daki ya miqa mata hannu, fuskar nan ba walwala," me zan maka kuma" ta fada cikin tsiwa, " dan uban ki ni kk tambaya me zaki min, to in baki san me zaki min ba bari na fada maki, kawo su nan" alamun da ta gani na ba wasa yasa ta miqa mai tana hawayen baqin cikin ga samu ga rashi, murmushi ya fara yi jin dumus da yai," Ko ke fa salameme na, yanzu ai kin ga ko dari biyar na baki ai yafi na qattin qauye masu baki dari da hamsin ko" juyo wa tai cike da bala'i tana kallon shi kuma sai ta fasa dan wani tsoron shi daya kamata, gani tai yana cire kayan shi, ita ko bata shirya ba, ga ciwon jiki da take fama da shi, gashi shi in ya fara abu bai san ya bari a huta ba, sai ya gajiyar da mutum, kuka ta fara tana" ni na barma dari biyar din dan Allah ka bari sai nan da kwana uku, na gaji banda lfy" dariya yai sosai ya maida kayan shi" da kyau matar manya matar Dan Abuja kenan, ku baku da buqatar kudi ai, ni na fita to ga wannan ki leqa waje akwai shago ki siyo kwaki da sugar ki sha, ina jin har canjin gyada zaki samu ma" nera dari ya wurga mata ya fice yana wata tafiyar yan duniya a shagide, kuka ta durqusa tana yi, " wai ni ina yan uwana ne, suna can suna jin dadin su sun manya da rayuwa ta, basu san a halin danake ciki ba,Oh Allah ka kawon dauki, na tuba, Juwairah kin huta, dabaki zabin aure ina zaki ba, gani ina cin ubana a garin da na taso da kwadayin yin aure cikin shi" kuka take mai ban tausayi, yunwar dake cin ta ce ta dawo da ita daga tinanin da take, tashi tai ta wanke fuskar ta, ta saka mayafi ta je ta siyo garin ta da sugar da gyada, hadawa tai tana sha tana kuka,ganin duk talaucin su ba su shan gari a gidan su amma yau gata da gari, share hawayen ta tai, ta jingina da katifar su, a haka baccin wuya ya dauke ta." Adda Suwaiba ya kamata fa mu je ganin gida yanzu haka, haba tinda muka zo yau watan mu na takwas kenan fa, muna cikin na tara, bamu taba zuwa gida ba, ba a taba zuwa mana ba, ga labarin Salma shiru, har yanzu" " hakane kam ya kamata muje muga ya su Goggo suke, batun Salma ki daina damun kanki tana can suna cin amarcin su, kin san mijin ta ma ba laifi akwai kudi, wataqila ma basa qasar nan" " haka ne Allah ya jiyar da mu alkairi, amma nikam na tambaye ki?" Ina jin ki" " dan Allah baki zargin komai game da mazan nan namu kuwa?" Kamar ya fa?" Tina wa da tai in ta sake Suwaiba ta san me ake ciki kashin su ya bushe ya sa tai saurin kauda zancen ta basar tace" ba komai yanzu dai mu tambaye su, yaishe zamu gida" " Ba rana balle wata" amsar da suka ji kenan ana basu bayan an bude qofa an shigo, " ke tashi mu tafi gida, ai an sada zumuncin haka, ku da kuke son Abuja kamar ran ku, in ban manta ba, Saudat kan mui aure cewa kikai, in Allah ya baki miji kuka tare a Abuja sai kin shekara biyar baki je ganin gida ba, ko ba ai haka ba?" Cikin qunar rai da kwallar da ta maqale mata tace" anyi haka, amma a da ai ban da isasshen sanin ya Abujan take kuma gani nake zan iya amma ni yanzu gaskiya gidan mu nake son zuwa naga uwata" wani hatsabibin kallo ya watsa mata, ba ta san sanda ta durgusa ta dau jakar ta ba tai hanyar fita, sallama yai wa abokin shi wanda daga jin warin da suke sai da suka biya sukai tatul, nikam nace Saude Allah shi kyauta karki daku yauma.......πŸ˜‚

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ     'YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ

         BY HAERMEEBRAERH 

MAMAN YOUSUP 

Mutan Gwambe ina godiya sosai da nuna so da qauna, kuma saqo daga Salamemen Talle tace a sanar dake bata da qawa sama dake tana son ki sai kin isa ABUJA  adama da keπŸ˜‚πŸ˜ ME LOVE U XOXO❤

Page 18:Goggo Sarai ce ta qame kan kujera tsabar ba a iya samun wajen ba ma, da nuna ita bata gaji arziqi ba, iyakar wajen ta aka shata aka gyara, baqin cikin da kanta da kanta take, dan ko ba wanda ya kula da ita, ita amma gani take all eyes on her, ita a dole ga uwar masu kudi, mijin Salma kawai take jira su dawo daga waje a yo mata kabakin arziqi na waje, Ammar na hango yana tafiya dugui2, dan ba wai ta gama kwari bane, ya zo wajen randar ruwan Mama Bilki, da dikkan alamu qishirwa yake ji, Mama Bilki na daka tana baccin tsakanin azahar da la'asar( bacci ne da in bawa yayi shi yake samun lada daga wajen Allah) ita ko hakimae ana zane ana kora jus da meatpie, ga mafici a hannu irin wanda ake kamar zuge shi dinnan ta kwama uban baqin glass a ido na ba mutunci dinnan, Abban su shi ke da bangaren ta yau amma gudun wulaqanci sai dare yake shigowa, kan tace ita ke ci da gidan, ko makamancin haka, dan haka yana qofar gida, Ammar ne ya dakko cup yai ta buqawa a jikin randar," Yauwa yaro fasa wa uwar ka dan arziqin da ya rage mata ka huta gadon mugun abu kawai" bata gama rufe baki ba ya saki fitsari, gangarowa yai qofar ta, habaaa ai kamar an watsa mata ruwan zafi, ta miqe kafin ta isa ya fara qoqarin tafiya yana kuka, da alama ba iya fitsarin zai ba, daidai fitowar Mama Bilki da shigowar Abban su, hannu ta sa ta wanke Ammar da wani lafiyayyen marin da ko Maman akai wa sai jikin ta ya gaya mata," ganin wannan kini babbun iyayen naka masu son abin duniya da har suke ganin Da namiji ya fi Ya mace daraja ba zai hani cin uban ka ba, in banda baqin ciki da aka koyawa yaro qarami tin yana ciki, duba fa ku ga yanda ya tsanyaran fitsari a qofata yai gaba, to ba zan lamunta ba" Ammar tsabar kuka ya gigice sai ga kashin ya biyo baya, zuciyar Mama Bilki tafasa kawai take ba iyaka, tin da Abban su yake da ita bai taba ganin bacin ranta haka ba, ita kanta Goggo Sarai ta tsorata , wandon Ammar Mama Bilki ta cire ta wurga a jikin qofar da aka canja wa Goggo Sarai, qofa ce irin ta qarfen nan mai kauri milk color, ta aje Ammar din ta isa jikin qofar ta samu wandon ta goga sosai har labulayen, sannan ta dawo ta daga hannu zata wanka mata mari, amma sai naga ta tsaya,( nace kash dama kin qarasa mun sha kalloπŸ’ƒπŸ») me ya tsaida ta oho, daukar Ammar tai da yake ta kuka yaqi shiru ta je ta fara gyara shi sai da ta gama taje ta dauke wandon nashi ta wanke ta shanya, sannan ta qara wanke mai jiki dika, ta bashi ruwa da abinci ta goya shi sai bacci, yana yi yana ajiyat zuciya, wata irin wuta aka dauke a gidan gaba daya , ba mai iya cewa komai, Goggo Sarai na tsoron tace kanzil yanda Mama Bilki ta bata rai bata san me zai je ya zo ba, ita kuma Mama Bilki ta fasa marin ta ne ganin datajar Abban su dake bayan ta, shi kuma ya fuskanci hakan, sannan ya yi shiru ne saboda kar ya bata damar magana ya san kuka zatai dan zuciyar ta cike take da baqin ciki, sai da ya tabbatar ta fara sauka tinda ta ci gaba da yan aikace2n tsakar gida sannan yace" kin ban mamaki Sarai ba kadan ba, ki duba kiga abinda kk aikata, yanzu marin da kk wa yaron nan ko ni ki kaiwa ai sai naji a jikina ba shi ba ma, dubi yanda yatsunki suka kwanta a kan fuskar shi, kamar quna, haba dan Allah, kin kyauta kenan, baki taba ganin fushin Bilkisu haka ba , to ina mai tabbatar maki ki kiyayi sakata a irin fushin nan bana kusa, dan duk abinda ta aiwatar akan ki ke kk jawo, kinga misalin hakan ai dazu ko?" A sannan ne ta samu bakin magana, " eh tinda kun haifi dan gwal, dole mana ku fifita shi akan komai, to da dan da uwar na san meye matsalar ku, baqin ciki, kuma nan gani nan bari dumamen mayya in dai nice ni da Yayana yan albarka" juyawa tai fuuuu ta hau cire labulayen dika aka watso su tsakar gida ta dau daya ta goge qofar dakin da shi, ta saka ruwa ta wanke, ta qara gogewa da labulen masu kyau din, da su ta gyara wajen, duk kyau da tsadar labulayen haka ta saka hijab din ta ta fita waje ta watsar ta dawo, tana wani isa da taqama taje ta canja wasu," a hayyyeeeeee ayyuuuuririiiiii, to bari kuji sau goma wannan shegen tsinanne yana bata qofa sau go........bata ida fadin me take so ba ji tai qummmmmm a bakin ta, ludayin hannun Mama Bilki ne ta saita shi a bakin Goggo Sarai, ihu ta saka, ita kuwa ta je ta durqusa ta dau abin ta ta juya ta ci gaba da aikin ta, Abban su mai zai in ba dariya ba, " Kai amma Gimbiya yau kam sai dai ace na zama munafukin mata, amma kin burgeni, ke kuma da dai da kk kira shege, duniya ta san ni ne uban shi, sannan, tsinanne da kk kira min da ba zakiga tsinewa a 'ya'yana ba inshaa Allah ina mai musu addu'a ko keme abin qi Allah zai karen su, sai dai kiga tsinewar a kan kan ki dan ba yau na fara jin kin kira min Da da wannann sunan ba, ke yanzu ba abin kunya bane ace yar haka ta fara shiga tsakanin ku? To ina qara gargadin ki ki kiyayi randa bana gida ki taba wannann baiwar Allah ina tausaya maki" ya qarasa maganar cikin dariya ya fita qofar gida, duk abinnan da ake Mama bata ce uppan ba aikin ta take kawai, Goggo baki ya haye sama, abinka da farar mace fatar tai jawur, daki ta shiga ta dau waya ta danna Number n su Suwaiba, dannawa tai tayi ana turanci, gashi yau harda Malam din akai fadan ba mai duba mata yaji me ake fada, kama kan ta tai da taji yana ciwo ta hau kuka, zama tai gefen tamfatsetsen gadon ta da ta sake mai matuqar kyau da girma, kukan ta tasha ta miqe ta kwanta, yau ita Bilki ke bigewa baki da luddai??? Oh duniya, da kudin ka da komai ba za a ji tsoron ka ba yanda taga ana yi wa masu kudi, to kwarjini ne bata da shi ko me, miqewa tai taje gaban madubi, ta kalli kanta daga sama har qasa, ga atampa nan mai tsada sarqar gwal.da zobuna, komai ya ji, dubawa tai taga ashe fa har yanzu ko umara bata taba zuwa ba balle Hajji? Murmushi tai tace " Gaskiya mana, to ai ko kashin ku ya bude dan kuwa dole ne wannan shekarar a sake farali da  ni naga ta raini" komawa tai ta kwanta, bacci ya dauke ta, cike da mafarkai kala2 na ban tsoro, ta dade tana irin mafarkan nan, 'Ya'yan ta na cikin matsala, amma sai ta dangan ta shinda sharrin maqiya, in suka dawo za su je neman taimako.

Yau ce ranar da Juwairah ta wate domin gyaran jikin ta, Yah Jabeer din ta na gida, in da ba zata iya kaiwa ba shi yake taimaka bata ya mata, misali yanzu ba dika take iya wanke bayan ta ba, to ga wannan abin gyaran jikin da zatai yana buqatar taimako, da farko na ga ta hada lemon zaqi a wani kwano qarami, ta zuba sugar cokali daya, da zuma cokali daya, sai ta saka lemon tsami daya, ta juya su sai da sugar n ya narke sannan ta dakko soson ta, ta miqa mai daga shi sai gajeren wando( yammaza zasui aikiπŸ˜‚) gani nai zai tsoma soson a wannan hadin kan ya tsoma da sauri ta riqe hannun shi" Yah pls i want some ya ban sha'awa" tana turo baki, gaba cike da shagwaba" ke fa kk ce kin ware kwanon nan na gyaran jiki ne ko abu za a debo kin dinga kyankyami kenan shine yai zaki sha abun ciki?" Cike da mamaki," ni dai zan sha , plsssss" miqa mata yai a spoon din, aiko ido alumshe ta shanye kusan sai da ta shanye rabi yace " tsaya za mui abunnan ko na dawo ta gaba na qarasa baki ki shanye?" Kada kai tai alamar Aa su ci gaba da gyaran jikin, sai sude bakin take, fara wanke mata fuskar ta yai, da wuyan ta da  bayan ta , da wannan hadin da soson, zuwa hammatar ta, sai ya dawo ta gaba ya wanke mata tsakanin cinyoyin ta zuwa cinyoyin ta, guiwar ta a haka saida ya hade kaf jikin ta, bayan sun gama ne tai mai godiya, tare da furta mai kalmar da ta zama masu al'ada wato" I love u" maimaita mata shima yai ya daga ta, " wai wai wai Babyna gaba daya kinyi nauyi yanzu, da gyar fa na dago ki" turo baki tai kamar zatai kuka, dama yasani tsokana ce, dariya ya fara yana kame bakin shi, tura hannun shi tai daga kafadat ta zata fara tafiya, " Mai ciki ihmmm ganinan tafe, me ciki, wallahi bani son sunan nan" juyo watai ta biyo shi suka fara zagaye bangaren su tana kukan shagwaba, " inna kama ka a yau a gidannan ka fara tsallen kwado,da kaji ka shiga hannu na" tana ta huci ita a dole an tsokane ta, dariya yake harda riqe ciki dayaga ta gaji ta nemi waje ta zauna, zuwa yai kamar yana son yai tsallen kwado a gaban ta," Haba Babyn Yaya, kiyi hakuri, in dai nine i promise i will never do dat again ever, ya fada yana watsa hannu alamun yayi nadama yana karya wuya" na hakura amma ka jawa kan ka kai zaka kaini toilet a hannun ka ka dawo da ni, dama na kula tinda cikin nan yai girma sai dai ka tallebe ni ta gefe baka daukata, bazan lamunta ba ehe" " an gama ranki ya dade da imani" murmushi sukai a tare suka furta" I love u" wucewa yai ya je ya hada ruwa mai dan sauqin zafi ba wani mai yawa ba yaje ya dauke ta kan su fita tace ina zuwa zan dau wayata, a hakan ya kaita daki ta miqa hannu ta dau wayar, " Kashhhh ashe ma Nafee bata da waya, bari inna fito na leqa na karbo dankalin in ta gama hada min din" kai ta yai ya dauraye mata wannan danqon, sai ga jikin ta yana wani laushi da haske, kamar wata matat masu kudi, fatar taji hutu, sun fito kenan yana dauke da ita ya bada baya ya shihe daki Nafee tai sallama, dakata wa tai, sai da aka bata izini sannan ta shiga,baje ta tadda Juwaira a kujera, " me ciki, πŸ™Š Ooupsy ! Ga dankalin na mai da shi yai laushin kamar yanda kk ce na saka lalle dakwai amma ba dikan na juye ba bayan na kada kamar dai yanda kk ce gishiri da kuma manjan, sai kin ci dariya Innarmu cewa take wani abun dadin ne, wai Nafee, irin abun rannan zaku mana mai kwai?" πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚dariya suka saka harda jabeer, sai da sukai mai isar su sannan ya bata rai" ya ishe ku Innata ce fa" dariya suka qara tintsirewa harda shi din," Feena taso ayi wannan dake, kuma kiyi a hankali karki ji ma mata ta ciwo" " masu mata" ta fusta a hankali" me kk ce?" " niiiii me na isa cewa, ba abinda na ce ko nake shirin fada" dariya suka ba Juwairah tai ta yi kuwa, daga naya suka samu wannan hadin sukai ta murza mata a jiki kamar dilka, kafin kace me juwairah ta yi kamar wata amarya, suna cikin yi Nafee ta miqe ta dakko ayaba daya, da kwai, sai zuma da markadadden dankalin hausan da markade yai laushi, hade su tai har ayabar sukai laushi sosai ta koka ta saman kan ta tana tsagawa tana shafawa a can qasan kanta, shi kuma yana mata dilka, bayan ta kusa gama wan ne Juwairah tace" Amma dai Nafee baki saka albasa a hadin yau ba ko? Dan naji ba wari" " eh ban saka ba na san ba zaki so ba mayb ya saka ki amai"" kaiiii amma ko na gode yar uwa"( wannan hadin na dankalin turawa da lalle da kwai d manja kadan da gishiri ko baqar mace ce take yi tana haske , tana fitar da kalar ta mai kyau, ga laushin jiki, shi kuma hadin dan kalin hausa ana yin zallah na albasa madadin dankalin ko dan kali madadin albasa, kowanne yana fidda gashi sosai kuma ya hana shi karyewa, yai laushi da santsi, sai dai na albasa na da wari, dan haka in uwargida ta gama ana son ta samu abun wanke kai mai qamshi sosai ta wanke kuma in an saka ana son ai massaging scalf din sosai ya shiga ko ina) ba su suka gama ba sai wajen azahar, tayi bacci kan su gama, tashi yai yana miqa" wai gayu da dadi da wuya" " hhhhh Yah to ai kai zaka mora gwanda ka taba yau kaji ya take ji da da take yi ita daya" " waya fada maki da din ban taya ta wasu qana nan abubuwan? Ban dai taba irin wannan bane, ashe haka take shan wuya duk dan ta burgeni baiwar Allah" ya fada yana shafa gefen fuskar ta, bude idon ta tai" what ar u two talking about" nan da nan ta tsargu da qibar da tai suke, aiki hde fuska tai, Nafee da ta gane dariya ce taso kwace mata, amma tace bari nasan me zan" Ni dai daya fafa cewa nai ba ruwana in kk ji, dan haka ba ruwana yanzun ma zance na tafi innar mu na kirana, Yah ka fada mata" kama baki yai yana mamakin sharrin da yarinyar ke sn hada mai, kan yai yunqurin wani abu yaji ta janyo hannun shi gaba daya ya zube agefen kujerar, hawaye ta fara ta dora kanta a qafar shi" shikenan dan nai qiba sai a dinga tsokana ta, ai ba muni nai ba", tana yi tana shan majina, rasa me zai yai dan yasan sharri kam Nafee ta hada mai shi bai da hanyar fita, kamo ta yai ya hau massaging kafadun ta" kiyi hakuri princess, dama gani nai cikin yai girma sosai shinr nace ko yan biyu zaki haifa?" " cikin zumudi tace "Allah yasa yayana" " Ameen to tashi muje mui wanka an kusa kiran sallah" miqewa tai, a ranshi yace " wai that went well, Nafee Allah na son ki da ta burkicen yau sai kin wahala kema" wanka sukai ya gyara mata kan ta ya saka mata riga doguwa har qasa mai budadden qugu, ba qaranin kyau tai ba, kallon ta yake kamar kar ya daina, ita ko murmushi take , bayan sunyi sallah ne Innar mu ta aika masu da abinci suka ci, tin da ya saka mata ruwa ta sha ta bingire a zaunen ta hau bacci, daga ta yai ya kwantar shima ya kwanta, suka sha baccin su, Yah Jabeer kam ya dade kan ya samu wannann bacci, dan komai na shi nemaj kwace mai yai, ga rijiya da ruwa amma guga ta hana, ga princess din shi a kusa baccin me ciki ya hana shi more gayun da ta sha domin shi.ni ko nace sai kun tashi asha bacci laaaafiyaaa.......

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ     'YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ  


          BY HAERMEEBRAERH
QAWAYEN ARZIQI

Widad Ummu Hafeezah

My Roumie πŸ’–

Sis Ramlat

Baba larens

Aunty Ummu

Buzu nawaπŸ˜‚

Aseeya Ahmad Bunzu

Aisha Ali Garkuwar mu

Zahrah muhammad

Maryam( Mero tsokana😝) Maryam Alkali( Autan Hajiya) 

Fateema( Mum Sultan)

Aisha Bizzy

Zeenour Mustapha

Hussaina Cute one( kwailaπŸ˜‚)

And so many more of my good and loving freinds, that i can't write ur names, kuna da yawa, kun san kan ku na san ku, ina son ku sosai, Allah ya barmu tare da alkairi mai yawa, ya kare mu daga dikkan sharrin zaman tare. Haermeen Haermma love u XoXoπŸ’–.Page 19:


Da asuba yau Salma ta tashi da matsanancin ciwon kai da mara, in da Talle hankalin shi ya tashi ba kadan ba, kar 'Yar mutane ta mutu a hannun shi, shi dai Allah ya gani ba wani son ta yake ba dama, kuma shi ba zai yarda ya kashe 'yan kudaden dayake tarawa ba in sun rabu ya baro wata sabuwa ya dirza ba, tabbbb yaushe ma zai yarda ya taba bayan neman auren ma ya kankama, kuma yanzu haka dama wa'adi ya debar mata," kawai bari Alhj ya fita nan dai da Kano na auna ta gida, nace sai nazo ba shikenan ba" yana maganar zucin nan ne ya ji Alhjn na kiran shi, da gudu ya fita, " To ga wannan a kula da gida, ni zan tafi , wannan karon xan dan kwana biyu gaskiya wataqila bam dawo ba, dan amaryata kasan na fada maka ta samu qaruwar diya mace, so ina ganin zan dan jima kadan fiye da yanda aka saba, a kula da gida, kar na dawo na ji shigen labaran dana saba ji, ba zamu kwashe da kyau ba Talle" gyada kai yake kamar qadangare, Allah Allah kawai yake ya tafi ya kai Salma tasha ya dawo, kar ta mutu a hannun shi, " Allah ya kiyaye Oga ba zaka taba samun wani labari mara dadi ba" daga kafada Alhj yai alamar" ruwan ka" yana fita bayan ya rufe gate din ne ya koma dakin da gudu, samu yai ta dan samu dama ba kamar yanda ya barta ba, ta fito daga toilet da alama amai tai," ke hada kayan ki yau zaki ganin gida" cikin kaduwa da murna a gefe kuma kunya da tashin hankalin da wanne ido zata kalli su Juwairah da Mama Bilki? Uwa uba Goggon ta, tace mata waye mijin ta, driver? Ko gate man? Zubewa tai a katifa," Nikam Sweet na fasa ba yanzu ba ka bari na murmure, sannan mu dan samu kudi, ko a haka zan tafi ai sai a zage ka"  "a zage ki dai yo ni meye nawa in zaki miqe ki miqe ki kwashi dan abinda zaki iya dan kin ga ni daga yanzu ma barin gidanan zn ko kin dawo ba ganina zaki ba nima na bar aiki anan daga yau, dan na kwashi rabona wajen Alhj, qauye zan koma, na ji da iyalina, kuma ba yanda zaki ki san qauyen mu nan ma tinda ko sunan baki sani ba, ba kuma ki san hanyar bama, so in kin tafi ki manta mai suna Talle, ko Alhj Mansur da kk taba aura, ki manta kin sanni, sai dai in kin tashi tuna ni ki min godiya a ranki na sama maki hanyar zuwa ABUJA, harda qauyen ta ma, dan haka ga wannan" takarda da kudi dubu goma cass ya miqa mata, a zaunen ta daskare, bata gaskata me ake fada mata ba sai da taji tsawar shi yana maimaita mata da kuma bata umarnin tana bata mai lokaci zai fita ya gudu shi,( qarya yake mata ba inda zai gudu kawai sanin bata ko san sunan inda suke ba shi ya sa shi fadin haka, baya son ta yi tinanin dawowa ma) miqewa tai da taimakon shi, take ciwon kan ta ya dawo sabo, wani jiri ke diban ta, haka ta gama komai, ko nace ya gama hada mata komai, yana bata a hannu tana riqewa, idon ta a tsaye, hawaye na zuba, haka ya gama ya sata gaba ya kulle qofar ya dau wata jaka dan tsabar ya raina mata wayo ta zaci tare zasu bar gidan, mota suka dauka ya saka ta suka bar gidan kifa kanya tai a cinyar ta tai ta kuka sun isa ta tasha a bakin tashar ya sauke ta yai gaba ko waiwaye bai ba, a haka ta samu ta isa bata ko magana, in da taji ana kiran Kano nan ta isa ta shiga wata mota sauran mutum biyu, tana shiga wata arniya ta shiga itama, sunayen su aka basu su rubuta, amma ita tai shiru, kudi suka buqata ta miqa masu ko da ya qirgi kudin shi ya miqa mata sauran ta nade a hannun ta, tafiya sukai ta awanni haka ta zauna idon ta ya bushe qayau, har suka iso kano, adaidaita sahu ta dauka ya kaita har gida ta miqa mai kudi ya bata canji, har tai gaba ya bita ya miqa mata a hannun ta, yai gaba, yana " Allah ya kyauta" shiga tai ba ko sallama, Goggo Sarai tana zaune hakimar ana kada qafa akan kujera, tana hango Salma sai da ta kusa tintsirawa, da gudun ta zani na warwarewa tana gyarawa ta taro ta" Lafiya ? Me nake gani haka? Ina mijin naki? Daga wace qasar kuka dawo haka? Fashi akai muku? " duk wannan tambayoyin ne jere a bakin ta tana qoqarin shiga da ita daki, har Mama Bilki zata fita, Abba ya riqe ta, yace bassu, ni na je , yanzj da kinje kin ja magana,cewa za tai gulma ta kai ki" " To Abban su Allah ya jiyar da mu alkairi" " Ameen" fita yai ya isa dakin, zaune Salma take, idon ta na kallon waje daya kawai, ko qiftawa bata yi, kukan kuma ya tsaya, tambayar duniya taqi magana, Goggo banda kuka ba abinda take, " Subhanallahi, me ke faruwa ne, kin saka yarinya a gaba kina ta kuka haka? Ke Salma ki mana bayani, me aka miki, ina mijin naki kuma? Daga ina kk haka?" A sannan ne Salma ta saki wani kuka mai cin rai, ta dakko takardar ta miqawa Abban nata, dan yanzu haushin Goggo take sosai, duk ita ce bata basu tarbiyya mai kyau ba, uban su na son basu ta musu hudubar shedan,ta hana su saurara, wannan wace irin rayuwa ce haka, Salati sukaji ya sake ya aje takardar ya zauna" Malam me ya faru? Ku sanar dani ko hankalina ya kwanta" " mijin nata na can garin ABUJAN NE YA SAKE TA SAKI UKU" dora hannu a ka tai ta kurma ihu, ta hau jibgar Salma tana" Shegiyar yarinya me kk mai ya sakon ke, kk kama asara haka, mutumin da kuka fita qasar waje? Kuke shaqatawar ku cikin jin dadin rayuwa, ki zalunce ni ki zalunci kanki, ki sa ya sako ki, da dukkan alamu ma ciki ne da ke, amma ba zaki bar dan ki ya taso cikin jin dadi ba" kalmar ciki ne ya razana Salma kenan, tasan Talle ya mata illa, dan ko giyar wake ta sha, a yanda ta san waye Talle ba ma zatai gigin ta haihu ba ta kai dan ta qayen su, ai kamar yanda yace sun rabu ta manta da shi hakan za tai,ture hannun Goggo tai a jikin ta ta je gaban Abban ta ta durqusa," Abba na ka yafe min, ka ji tausayi na ba dan halayyata mummuna da nai a baya ba, ka duba girman Allah da soyayyae da da iyayen shi, ka yafen, ka tausaya ma abinda ke cikina in ya tabbata ina dauke da cikin kenan, karkai fushi da mu, ka bamu wajen zama a gidannan karka kori abinda zan samu, zan wahala ta hanyar halal na kula da abinda Allah zai ban, amma kar ka ce za a sake daga zancen uban dannan na gama shafin shi, sabon shafi nake son budewa" kuka ne yaci qarfin ta sosai, wanda yasan ya Abban su hawayen tausayawa diyar tashi, yarinya fara mai kyau duk 'ya'yan shi Juwairah ce kawai ta fisu komai, amma Salma na bayan ta, dubi yanda ta koma, ga qananan shekaru, har yau bata rufe ashirin din ba, daga ta yai tsaye ya rungume ta,aiko kamar jira take,dama she needs a shulder to cry on, ta rasa, for so long, ga strong and loving arms nan sun huging din ta, ya bazata ji gwarin guiwar fidda komai ba, kuka Abba ya barta tai har saida ta daina da kanta, yasan ta fidda koma meke cin ta a rai, zaunar da ita yai, yace ina zuwa, Mama Bilki ya kira bayan ya fada mata abinda ya faru, shigowa tai taje kusa da Salma, Salma na ganin ta taje da sauri ta rungume ta, tana neman gafarar ta, Mama Bilki yafe mata tai, ta zaunar da ita, " fada mana me ya faru" a cewar Mama Bilki, da gudu Goggo Sarai ta iso gaban Salma" yi shirun ki wannan sirrin mu ne karki magana a gaban maqiya" wani kallo dukkan su suka watsa mata, kowa da irin nashi, Salma magana ta fara, ta sanar da su komai da ya faru tin daga tafiyar ta har dawowar ta yau din, kuka sosai Abba keyi duk jarumtar shi, ya tausayawa diyar tashi,Mama Bilki ma haka, Goggo Sarai ga tausayi ga kunya itan ma kukan take, Salma ce ta juya ta kalle ta" Yanzu Goggo a wanne hali su Adda Suwaiba suke? Baki sani ba, kawai suna aiko maki da kudi kina ajewa, Goggo baki san ina ne Abuja ba, da tin tasowar mu kk kimsa mana son ta, yanda kk saka mana son abun duniya da hutu, da haka kk sa mana son ku kadai da muku biyayya da anyi yaran kirki,amma baki wannnan ba ba a kaiga dasa mana tsoron Allah da son Allah da ma Annabin rahama biyayya akan saqon da ya zo mana da shi ba, Goggo kin ci amanar kiwon da Allah ya baki, Abba na qoqari akan mu kina rusawa, ni yanzu ba zan zauna anan dakin ba, Mama Bilki ina riqon arziqin komawa wajen ki na zauna, dan tabbas nima ina zargin ciki garen yanzu watana kusan hudu bana ganin al'ada ga yawan ciwon kai da mara, sai zazzabi danake yawan yi, ki koyan dukkan irin tarbiyyar data kamata nima inna haifi nawa na basu,ba irin wannan tarbiyyat mara kyau da ma'ana ba" Goggo Sarai ce ta kwade mata baki," dan uban ki to ki dauki haihuwar ki da nai ma kice ita ce tai maki mana? Ku tashi ku fice man a daki gaba dayan ku bana buqatar kowa, yaran da suka san daraja ta da qimata za su zo su kula dani, dama ke tinda akai auren me kk tsinanan, baki tsaya kin nemi kamar na yan uwan ki ba , me kk samo banda wahala? Sai ku tattara ku je can, jikoki kuma yarannan biyu ba zan rasa su da ciki ba yanzu haka, dan ba zaman banza na aika su ba" miqewa sukai Mama na mata addu'ar shiriya a ranta, dakin ta ta kai Salma, abinci ta dakko ta bata, kamar mayya haka ta hau shi da ci tana hawaye, tana gama ci ta sha ruwa sai bacci, Mama Bilki ce ta gyara ta, tana tsananin tausayin ta, Abba sai godiya yake mata da sanya albarka.Su kuwa yan Abuja ana can ana shanawa, hanakali kwance, suna zaune ana kasafin sassan jikin su.........

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ

               BY HAERMEEBRAERH


My Saerwwaermaerh 

Ke ta daban ce Haermeen Hamma na son ki, 


Billy shantali (Billisiou)

Hassana D

Ummul

And dikkan Surukaina na Tabital fullaku, har da surukar zamaniπŸ™„πŸ˜™duk ina gaida ku ba adadi, ur love is daban in my qalbiπŸ˜‚ ANA MUGUN TARE.ME LOVE U XOXO❤Page 20:


Alhj Kallah, Alhj Salihu, Oga Zaks, su ka dai na iya ganewa a qaton table din da yake kewaye da manyan Alhjzawa, wanda a qalla zasu kai ashirin , gaba dayan su da shigar tasu ta red and white, with a little black on it, kowa muzurai yake, irin nima wani shegen ne😎, Oga Zaks ne yai gyaran murya, ya ci gaba da magana" A a Salihu, wannan qorafin naku bai karbu ba, kun san qa'idar qungiya, an baku dama, ku kadai na bawa damar da ban ba kowa ba, saboda koba komai ana qaruwa da ku sosai, amma wannan karon, u guys disappointed me so much, that u have to pay for what u did, dan haka , nake baku imarni ba shawara ba, u go back and bring ur wives here, dole ne a yanki abinda ake buqata daga wajen su, ba dan komai ba kuwa sai dan cika sharuddan Dodo, dan haka na baku nan da kwana uku, kuje ku gama sallama da su ku kawo su" miqewa yai cikin izza yai hanyar waje, guards din shi na biye, Alhj Salihu ne ya kife kan shin a table, dan a qashin gaskiya ya fara son Suwaiba duk da wautar ta da gabuntar ta,Alhj Kalla na kula da shi, taba shi yai akan su tafi, miqewa yai da kyar, suka fice , ana ta yan gulmace2 , ko ina ba a raba mutane da gulmaπŸ™„bayan sin isa gidan Saudat ne, suka shiga inda suke tattauna matsala irin haka, suka zauna, Alhj Kalla ne ya fara magana, dan ya kula in bai ba Alhj Salihu ba zai ce uppan ba, " Salihu ni ban ga abin daga hankali a maganar nan ba fa, duk da ni kaina a yanzu haka na fara son yarinyar can,koba komai duk matan da muke hulda da su yaran nan na kula suna da na su sirrin daban a jikin su, ga yarin ta ga kyau, amma kasan bijirewa Oga Zaks na nufin qarewar arziqin mu, nikk dana talauce gwanda na aikata abinda yake so, mu kaisu kawai, nono ne kawai za a yanke, to meye? Naga dai ana ciwon cancer ma a yanke masu nan kuma su rayu" " bazaka gane ba abokina, in ba wajen a ina mutum zai na hutawa? Kai ni fa bari kaji ba zan iya bane kawai, duk sokoncin yarinyar nan ina son ta, dan in tare kk da ita ta bara maka wani haukan sai kaji kamar kaita zane ta shegiya, amma tayi akwai zuma, banjin zan iya rabuwa da ita, yanzu ni dai shawarata shinr suje gida kawai su ga gida na kwana daya ko biyu su dawo muga ya za ai, tinda kaga bai kamata har in ma mutuwa za sui tsohon su bai gan su ba, dan ta uwar su ita tajiyo bamda case da ita ni" " haka ne kayi gaskiya, to bari na fada masu kawai gobe su shirya zasu gida ko ya kace, dan da kaina zan hada mata kayan ta, amma ka tashi ka tafi gaskiya dan saina dana sosai kan ta tafi, bamu san ya abubuwam zasu kaya ba" dariya sukai suka tafa, " shegen sama nima ba ri na hanzarta" aiko hakan akai washe gari da asussuba suka dau hanya kowa da drivern ta dan wadata, ga wata mota nan shaqe da kayan arziqi na bin su, haka suka iso gida cike da doki da murna, suna shiga gidan, Salma suka hango kanta akan cinyar Mama Bilki tana mata kitso, a kwance, kamar wata jaririyar ta, " Kan ubancan, me nake gani haka ni Suwaiba? Yaushe gidan ya koma haka? Da jin muryar ta Salma ta miqe da gudun ta tai kansu, tana ihun murna," Goggo fito ga su Adda sun zo, Mama kinga su Adda sun zo, ina Abba? Abba fito ka ga ikon Allah su Addana ne a gidan yau" suma basawa sukai aka ci gaba da murna amma cikin ransu akwai tambayoyi sosai, dakin suka shige tana ta kwasar bacci, tashin ta sukai, ta miqe tana mittsika ido, aiki tana wartsakewa ta gansu, sai kukan dadi ya kamata, ta ko hau kukan murna suma sunayi, Abba ne ya lallashe su, nan fa aka hau gaishe gaishe" Ayyyuririri, kai shiyasa nake son Allah, akwai shi da biyan buqatar bawa, dubi yarana , san kowa baqin cikin marashi, ga kudi ga kyau, ga hutu, naji dadin zuwan ku yarannan, ya mazajen naku?" Cikin murmushi da dagun kai an gama kumbura masu kan suke amsawa" suna lfy suna gaida ku, ga abubuwan kayan abinci nan da kudade da suka aiko a baku ke da Abba" cikin murna kamar zata kifa ta dafe kudin dika har na Abban nasu, shi ko ko wajen bai kalla ba, ya masu godiya, Mama Bilki ce ta shigo dauke da ruwan Pure water a plate ta doro masu sanyi ta kawo masu, ajewa tai ta zauna a gaisa" wai ni shin gaisuwar nan dole ce ne, a bar yara su huta, kuma in banda abin talaka, duba fa wa zai sha wannan ruwan, dan Allah kije an yafe Allah ya bada lada" Goggo Sarai ke maganar nan, cikin shewa suka hada baki" Hahaiiiiii Casssss sai Goggo, ashe ana nan ana ci gaba da gashi, Allah sassaka to" dariya tai cikin isa tana wani daga hanci, Mama Bilki ce ta tashi ta ja hannun Ammar da ke son shigowa sukai gaba, Salma ma tashi tai rai bace ta fita" wai Goggo me ke faruwa ne me nake gan?  Salma da waccan matar?" Abba ne ya basu labarin komai, nan da nan suka hau kokawa yar uwar su wahalar da ta sha, sannan ya qara masu da hukuncin da ta yanke, anan ne ransu ya baci sosai, suka kwala mata kira, bayan ta shigo ne suka balbale ta da fada kowa da abinda yake fada, sai da ta tabbatar sum gama ta miqe tai waje ba ta tanka ma kowa ba a cikin su, da bala'i Suwaiba zata bita ta daka Goggo ta hana ta, "aini yanzu na cire ta a Yarana nima, taje can ta qarata, ina da ku kun ishen rayuwa, kuma yanda kukai jan nan da alamar kuma kuna dauke da ciki, dan haka jika ne nake matuqar kwadayi yanzu a duniya fiye da komai, taje tai ta fama, ita ta sani, naku sun ishen zaman duniya dai ba na qiyama ba" kallo suka bi junan su da shi, take Saudat ta fada jikin Goggo tana kuka, Suwaiba ma idon ta ya cika da kwalla sosai, "Adda Suwaiba akwai abinda na si fada maki tin da na qi dan nasan halin ki tona mu zaki su kuma su kashe" cimin zaro ido Goggo tace" Suwa..... suwaye zasu kashen ku?" 😨" mazajen mu Goggo yan qungiyar shan jini ne,na gano hakan da jimawa, yanzu haka bamu da mahaifa da ni da Adda" wani mari taji guda biyu a fuskar ta, daya na suwaiba daya na Goggo" dan ubanki sharri kuma zaki masu, mutanen da suke kasuwanci a qasashe ko ta ina, arziqi ya wadata ya bunqasa shine zaki ce haka, so kk ki dawo kema ki xauna ki jamin asara, na haifi ya kamar ki da zan samu dukiya ki dankwafe kanki? To ki bude kunnen ki kiji, ko ya ake. Ciki gobe zaku koma va zan lamunci asara ba" cikin kuka ta rarrafa wajen Abban su," Abba ka yarda da ni, wallahi gaskiya na fada, yan shan jini ne, naji da kunne na" " na yara dake yata, dan baki taba fadan hakan ba kuma da dikkan alamu akwai gaskiya a zancen ki, wannan kudin nasu yayi yawa" " Abba ya zaka yarda da wannan maqaryaciyar ? Qayra ne fa kawai dan sun taba dukan mu sau biyu, shine fa ta qullaci abun take son ta gudu, to in ke bazaki koma ba ni xan kma dakina" " yauwa yar albarka, ai nasan in kowa zai juyan baya ke kin haifu" tashi akai inda kowa zuciya ba dadi, Saudat ta kafe bazata koma ba, inda Suwaiba tace ita zata koma, Salma kuma suna jiyo komai,hankalin ta ya tashi amma tasan bata da say a wannan kamarin,Mama Bilkince ta shawarce ta akan ta musu addua kawai, hakan akai kuwa ta kwantar da hankalin ta suka hau yankan farce bayan sun gama kitson.


" Bbyna wai ni yaushe zaki gaida Mama ne kafin a zo ya zamana bazaki iya fita unguwa ba kuma, tinda ita tana abunnan na mutan da taqi zuwa dakin ki har yau" " hmmmm kaidai bari abunnan na min zafi ace wai uwa ba zata je dakin yar ta ta gani ba? Ba komai, xan je ko gobe ne naji dazu Nafee tace su Adda sun zo, kuma Salma ta dade a gida" " Eh haka ne, rand naje gaida su ma na ganta ai, Allah ya kaimu goben..........❤

Na gode maku da nuna kulawar ku akaina masoyan YAN ABUJA naji dadi sosai da yanda novel dinnan ya samu karbuwa a zuqatan jama'a masu tarin yawan da ban san iyakar su ba, ina roqon ku da ku qoqarta ku sa na samu ladan abinnan, ta hanyar aiki da abinda kuka karanta na amfani , in da kukaji nai kuskure ku yafen ku nemamin gafarar Allah, wanda yaji dadin novel dina kuma ya mafana da abinda ke ciki ya min adduar samun biyan buqatuna na alkairi. Tanx Love u all❤

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    ' YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ

    

       BY HAERMEEBRAERH


Dan Allah masu tambayar novel daga farko ina qara baku hakuri da cewar, na kusa kammalawa inshaa Allah, so ina ganin it will be better and easy for me inna kammala nai document sai mai so ya same shi. Na gode. Love u xoxo❤


Page 21:To day is a busy day for Juwairah,amma dik da haka ta kafe yau take son ta je gida dan su gaida da yan uwanta dika, da farko Jabeer yaso hana ta ta bari sai jibi tace sam zata iya ba wani gajiyar da zatai, haka ya hakura, tana idar da sallar asuba azkar din ta dik a hanyar kitchen take yin shi, fitowa tai dan yi ma Jabeer  abinda zai samu ya tafi da shi Abuja wajen interwie da aka kira su na wani aiki da ya nema a NNPC, dubawa tai taga basu da wasu kayan abinci sosai as usual, ragowar Flour da ba zata wuce gwangwani hudu ba ta dakko da dan kifin da ta siyo a jiyan, na dari, da kayan miya albasa ta yanka mai ganye sosai ta daka attaruhun ta hada da dan kifin nan, ta soya sama2, nan take ta hada flour tai meatpie cikin mintina qalilan( da ace akwai wadatar a cikin meatpie dinnan zata iya amfani da nama ko kifin ya fi wannan da veges masu yawa a ciki in ta hada sai ta soya sama2 dika amma a yanzu tinda Juwairiyyar mu na da dabara sai ta cika albasa dan ya tada kifin) bayan ta kammala me ta dakko kamun su tai mai koko, ta hada mai shi ta kai mashi, daki kafin ta gama shima yana ta shirin tafiyar, jakar shi da komai ta hada mai dama, komawa tai ta samu zobon ta da ta dafa da yamma jiya ya sha kayan qamshi ta tace ta hada mai shi, ba qaramin dadi yai ba, ta samo wata yar robar ta cika mai da ita ta daure yanda ba zai zuba ba, ta debar mashi meatpie ta rage ma surukan su da zasu zo anjima wajen neman auren Nafeesa, sannan ta koma daki, qarasa tayashi hada komai tai, dai dai da brush din shi bata manta da saka mai a jaka ba, bayan ya gama cin abincin ne ya gama komai ya janyo ta jikin shi" My princess ba abinda zan ce maki sai dai nai maki fatan shiga aljanna, tin da ance sai miji ya yarje wa matar shi shiga aljanna zata shiga My Juwairiyyah na yarje maki shiga madaukakiyar aljanna da izinin Allah, ke macen kwarai ce, macen nunawa kowa ba tare dana kunyata ba, Allah ya sauke ki lfy, ya shiryar min dake , Allah ya qara miki imani, kinga ga wannan ba yawa kwama biyu zan kamar yanda na sanar dake, ki ta tayani addua inna samu aikin nan xamu samu hutu sosai, zan jiyar da ke dadin da baki taba zato mace zata iya samu wajen mijin ta ba, Juwaireren Mama ina son ki" ba abinda take zabgawa in ba murmushi ba, amma yana cewa Juwaireren mama ta turo baki tana buga qafa," Ni dai Yah Jabeer bana so, taso ka tafi kar ka makara, Allah ya karen kai mijina kaje lfy ka dawo lfy, Allah ya bada sa'a a abinda aka tafi nema, inshaa Allahu kai me nasara ne akan komai na alkairi da ka sa a gaba, dan haka  don't feel nervours, u will do just fine, u can do it, saboda kai din na daban ne a cikin mazaje,karka manta da karanta lahaula wala quwwata....... da hasbunallahu wa ni'imal wakeel, Allah will be at ur aid, he will guid and protect u, ina son ka Jabeerun Baba" ta fada tare da miqewa da sauri tana dariya bin ta yai ya cafko ta ya hade ta da gini, " maimaita me kk ce" turo baki tai tace " yo ni me nace, dan dai kawai an ga yau mijina zai tafiya sai kuma a ce za a min yar qure a ci zalina, dan irin wannan kallon da kk min ji nake kamar na dawwama da kai a haka a tsaye ba tare da duniyar ta juya ba" ta fada cikin qasa da muryar ta, wani irin farin ciki ke ziyartar zuqatan su, a cikin ran su kowa na yaba kyau irin na dan uwan shi, bakin shi ya kai saman nata, ya shiga sarrafa lips din su, cikin salon da dikkan su zuciyoyin su sai da ta narke, biye mai tai sosai suke jin dadin hakan, aka kace musu da sallama, Nafeesa ce tai sallama ta taho dan Juwairah tace ta zo sui komai da wuri zata gida yau, janye jikin shi yai a kasalance, ya riqe hannun ta ita kuma ta kwantar da kanta a jikin shi, fita sukai tare idon ta taf hawaye, yau je ranar farko da zai tafiya tin auren su,kuma har zai kwana biyu baya nan, saurin maida kwallar tai kar ya gani hankalin shi ya tashi, amma ta makara" Haba my Queen, ki kwantar da hankalin ki mana, inshaa Allah jibi da yamma kina maqale a qirjina,daga wannan tafiyar ko ina ban sake zuwa na barki qafa ta qafar ki kinji" ai kamar ya zuga ta ta bare baki irin na yaran nan ta fara kuka, rungume ta yai tai kukan sosai sannan tai shiru ta sake mai addua, ya suka fita har Nafee suka raka shi, Innar mu ke tsokanar ta" to kukan rabuwa da maso yi aka shaaaaa Hoh yan zamani, to dakko mayafi ki bishi" da gudu Juwairah ta tafi tana dariya, suma dariyar suke, sai da taje baqin qofar shiga wajen su ta juya, dan tsuke bakin shi taga yayi alamar kiss, ta waro ido ta kalli su Baba Balarabe dake gefe zasu raka shi qofar gida, rufe baki tai da hannun ta ta fada wajen nasu tana dariya, " Allah sarki mijina,kaje lfy ka dawo lfy cikin sa'a da nasara, tare da kariyar Allah" Nafee ce tace " Ameen masoyan asali" murmushi sukai suka shiga kitchen, lokacin takwas da rabi tayi, masarar da aka barza suka dakko nan da nan suka je suka tsinko zogalen da Juwairah ce ta shuka da hannun ta, da alayyahu, sai albasar su mai lawashi, gyarawa sukai suka dake gyada, da kayan qamshi attaruhu da maggi gishiri suka saka yanda zai isa yai dadi suka saka suka dora a wuta, nan da. Nan sai ga dambun masara mai dadi ya hadu, mai s Juwairah ta soya dayaji albasa, hadawa sukai a flask wannan zobon juye ragowar tai a wani babban jug nata sannan ta dakko meatpie dinnan ta aje Nafeesa ta ji dadi sosai tana taima yar uwar ta kuma matar yayan nata godiya har saida ta ba Juwairah haushi, godiyar tai yawa, ajewa sukai a gefe Juwairah ta sa Nafee debo wani alayyahun da albasar mai ganye, ta sa ta gyara, ta daka kayan miya wanna karon harda timatir, jelop rice mai dadi tayi wadda ta yayyanka dan naman d suka tafasa tin jiya, saboda bai da yawa yasa Juwairah tace bari su yanka qanana sai a soya sama2 su saka a abincin, har da dan carrot din su, nan da nan sai ga girkin da su suke ganin anyi a talauce ce amma wani gidan masu akwai din ma matat gidan ba zata zage tai hakan ba, wanka ta tafi tayi ta sa Nafee taya ta gyara gidan, dan bata son fita ta bar gida da datti in ta dawo ranta baya dadi, ganin dattin, sannan kuma ga gajiya, ( wasu matan taqamar fita za tai unguwa sai ta bar gidan kamar bola ta tsallake,na farko in kk dawo zaki iya baqin kunya gida kaca2, ko kuma ki dawo a gajiye,ga shi maybe miji ya kusa dawowa, shima ya dawo yaga yanda ya fita haka ya tarar wataqila harda qarin dattin ma, amma in kk gyara gidan ki fes in da haki kikai girki, da kij dawo wanka zaki fada ki fito tsaf dake,maybe sai bacci ma tinda baki da aiki, mata mu kulaπŸ‘‚πŸ») bayan ta fito ne abincin ta da zata ci yanzu ta dauka taci ta aje na daren da ta diba ta rufe kitchen din bayan ta wanke plate din data ci abinci,kmawa tai ta shirya ta fito, bangaren Innar mu taje ta mata sallama ta dau hanyar gida cike da zumudi da doki.Sallama tai a cikin gidan, inda ta isko ana ta daru, ita Saudat tace bazata koma ba, Suwaiba ta shirya tsaf da shirin tafiya, Goggo ta sa su a gaba da magiyar ta daure ta koma, ba zai qara dukan ta ba, Abba ya kafe shima bazata koma ba tinda bata so, Mama Bilki ce tace" Ayya Goggo tinda ta ce bazata koma ba a barta mana in aka kwan biyu kin taushe ta sai a maida ta dakin ta" Hhhh lallai yau daya kin yu magana mai ma'ana,Allah ya kaimu ta huce a maida ta" " Kaji Maman nan ina ruwan ki da sa mana baki? To bazan koma ba din har abada, sai dai ya biyo ni da takarda ta, ke kuma Allah ya bada saa zaki ce na fada maki" juyawa tai tai daki, Juwairah qarasawa tai cikin sake sallama,ta dan duqa ta gaida Suwaiba da ke qoqarin qota ta ta wuce, " Malama bani waje driver na na jirana" hannu ta saka a jaka ta dakko kudi mai dan yawa ta watsa mata" ga shi nan dama na san gaisuwar kenan, shine ya sa ki zuwa da wuri kar mu tafi ba a baki rabon ki ba" ta fada tare da ficewa a gidan, cikin qunci da haushi,tare da fushi irin na masi ciki in an tabo su ta jawo hannun yayar ta ta, kamar yanda ta wurga mata kudin a jiki itama wurga mata tai a fuska" ashe har yanzu baku canja hali ba? Ban zo dan wannan stupid money din naku ba, nazo dan na ga yan uwana dana dade ban gani ba da iyaye na, na zo domin zumunci, dan haka u keep ur filthy money with u it will help u some day" tai shigewar ta ciki ta bar kowa baki sake, tabe baki Suwaiba tai daga baya ta dake kudin ta ta shiga mota tana daga ma Abban ta da Goggo hannu, suka juya birnin tarayya ABUJA.

Komawa ciki sukai in da Abba yai bangaren Mama ya isko Juwairah da Salma, Salma tana ba Juwairah hakuri akan komai da ya faru a baya, tana ganin Abbam nata ta miqe da kyar yana ta zauna amma saida ta isa gare shi, hannu ya buda yau huging din ta" Abbana nai kewar ka ba adadi" " Juwaireren Mama nima haka da jibi muke saka rana zani ni da Salma mu gan ki" turo baki tai alamar shagwaba " Abbaaaa" dariya sukai dika," Oh mai hali baya fasa halin shi" inji Mama, dariya sukai dikan su, nan da nan Salma da  Juwairah suka qara shaquwa, hira suka shiga yi Salma ta ba ta labarin abinda ya dawo da ita gida, Juwairah akwai tausayi da saurin kuka dama,tausayin yar uwarta ne ya cika ta tai ta kuka kamar wadda aka daka, sai da ta gama ta rungume ta tace"kar ki damu yar uwa, da kin haihu zaki samu miji na gari inshaa Allah mai kudin dai da kk so da yardar Allah" " Aa Juwaireren Mama banni da talakan ma zan zauna" " Kaiii Salma harda ke" " Aa nima yau tabawa nai ai, ai baki taba jin na fada ba ko? To qara'i nai na da da ban tsokane ki ba" " to ke kadai na yarda ki ce man Juwaireren Mama, ke ma iya na sati daya kacal" ta fada cike da nuna ita din yar farin maman ta ce, dariya sukai harda iyayen su dika, anan Ammar ya tashi, da sauri Juwairah ta isa ta dakko shi, sai kallon ta yake, wasa take mai taji yana qoqarin magana, " Mamma" shine abin da ya furta, dadi ne ya kamata " laaaa mama yana magana dama?" " Aa ya dai iya barna wannan" dariya sukai. Haka Juwairah ta gama yinin ta cijin jin dadi,tare sukai girki da Salma, in da suka amu rashin mutuncin Saudat kala2, ba wanda ya kula ta,haka ta qarata,ta gaji ta koma daki.
SUWAIBA MUTAN ABUJAπŸ˜‚ taisa a buja a gajiye kamr ita tai tuqin, tana isa wanka ta fada gidan ba kowa sai masu aiki da ke bangaren su, bayan ta gama ne ta kwanta" Wawuya, yaushe zan bar wannan daula ta wuce ni, ana ki dawo kina wani ke gida yafi gidan miji, ai ni da barin Abuja dai da ziyarar ganin dangi" a haka bacci ya dauke ta, cikin baccin taji wani zafi kadan, ko bude ido bata sake iyawa ba..........

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ   ' YAN ABUJA.  πŸ’…πŸΌ


              BY HAERMEEBRAERH

Sweet Ummul (Khairee) qanwata ina mai yiwa Hamman ki fatan kasancewa cikin rahamar Allah, Allah ya yalwata mai qabarin shi da ni'ima da salama, Allah ya tashe shi cikin bayin shi muminai salihai. Dukkan victims na BOKO HARAM ina mai miqa ta'aziyya ta a wajen su, da musulmi baki daya, tabbas jiya komai ya dawo mana sabo, kamar jiyan akayi, My Sawwama Allah ya jiqan Abban ku ya mishi rahama da mu baki daya.ALLAH KA JIQAN DIKKAN MUSULMI WANDA SUKA RIGAMU DAMU IN TAMU TAZO.😭


Page 22:

Yau a gidan Talle an tashi da jimami, Jummala na ta fama kwara amai, ba ko qaqqautawa, Huwaila na kwance kamar ruwa, gashi ta dashe tai wani fari fauuuu kamar MeroπŸ˜‚ gaba daya wanda ya san ta da ya ganta yanzu ba zai gane ta ba sai an mai bayani, sai zubda yawu take a jikin gini," wato ku qananan 'yan iska ko, uban wa kuka bude wa qafa har gaba dayan ku ku biyu ace ciki ne da ku, yau in mahaifin ku yaji ya zanyi da raina, wannan abun kunyar ina zan kai shi a garin nan?" Marka ke magana tana share kwalla, shirun da sukai mata ya bata mata rai matuqa, sun ma mai da ta yar iska kenan ko, miqewa tai bayan Jummala ta koma daki in da Hawaila take, ta dakko mabirgin ta zankadede tai dakin ta rufe qofa, ji kake tim tim, tana jibgar su, ita Huwaila ba kwarin guduwa sai baki, nan take ta ko fara magana" Allah marka ki kyale mu ai iskanci ba kan mu farau ba, kuma naga iyayen yaran na gida ne, su bangis ne, kakan su na gidannan shima yana zuwa lalubar ki duk daren duniya baku ko gajiya ko daga wa juna qafa, mu ki daina dukan mu, dan naki bai fito ba namu ya fito bazaki kashe mu a banza ba, kk qara dukan mu sai na fada ma Baban mu in ya dawo kuna kebewa keda yayan shi" qam taji an qame mata bakin nata, rufe bakin ta Huwaila Marka tai bam tana waige2, tana kallon qofa, ko wani yaji? Jitai an banko qofar da mugun qarfi, wani tsoro ne ya kama ta ba ta san sanda wata muguwar tusa ta kwace mata ba, zama tai kusa da yaran suna ta toshe hanci dan azabar wari, Talle ne idon shi ya kada yai jawur akan na da, in aka ce xai iya kisa a wannan halin ba za.a musa ba, damqo wuyan Marka yai kamar zai kashe ta, ya jawo ta tsakar gida yaran su na biye, qananan na kuka manyan da suka ji kuma suka gane me ake suna mamakin abun, har qofar yayan nashi ya je ya wurga mai ita a jikin shi, daidai ya fito da tabarma a hannun shi zashi zaman qofar gida na safe da suke yi, janye jikin shi yai yana wani ja baya " Subhanallah,meye haka zaka raban matar ka a jikina, bayan kasan ba muharrama ta bace" wani gigitaccen mari Talle ya hankada mai, zai magana ya qara make shi ya tintsira, ya kasa magana ma, zaman yan bori yai a wajen ya hau kuka, kuka yake suma kuka suke, gaba daya sun kasa daina shiru, wani haushi ne ya kama Talle kukan uban me suke, kuka ai shi ya kama, miqewa yai a haukace ya bisu da duka, duk wanda ya samu ya maka, har yayan nashi, bakin shi dai kam kamar wanda aka rufe, tattare wa nai nace bari nai Abuja in sun gama dake2n na dawo naji ya masu ciki?


Allurar bacci yai mata ya tsaya akanta yana qarewa qirjin ta kallo, qiji a cike a tsaye, amma haka za a je a yanke su, ya roqe su tinda yana son ta a mata yanda ba zata mutu ba, a mata kamar za ai operation ne yanda daga baya zata ji sauqi, su ci gaba da rayuwar su, hawayen tausayin ta ne ya zubo mai for d first time in his life yaji tausayin wani da zasui aiki akan shi,hawa gadon yai ya rungumo ta ya dora kan shi a qirjin ta, wasa ya shiga yi da su, kamar zai cinye, da kyar ya hakura, ya dauke ta yai mota da ita, ya fara daukan dajin su Oga Zaks. Hankalin Alhj Kalla a tashe yake ganin rashin dawowar Saudat, ya zai yi yau? Ta ina zai fara samo wadda za sui aikin akan ta, tinda ita ta gudu taqi dawowa? Anya ma zai iya kyale ta haka? In yace zai mata wani abu.asirin su ne zai tonu, duk da yana da tabbacin ba yanda za ai dasu, dan manyan qasar sun daure masu g.... a haka dai yai ta tinani sai da Alhj Salihu ya mai waya yace shifa ya dau hanya, tambayar shi yai matar shi ta dawo ne shi? Ya tabbatar mashi da dawowar ta, miqewa yai ya ce" duk wanda yaci ladan kuturu dole ya mai aski" waya ya zaro ya kira Yar Gwal, tana wani rawar kai da jiki yau da sa'a ta tashi ta san a bata samu ba zata samu dubu dari biyar, to me ta manta? Da hanzari ta tashi ta hau shirye2n fita, qawayen ta ne suka fara tambayar ta ina zuwa da safennan, bayan qa'idar su fitar dare ne? Sanar da su tai inda zata, shewa suka dauka wasu kuma suka.tabe baki, a haka ta gama shiri.ta fita, a qofar gidan ta same shi ya hadu cikin manyan kaya mai irin nasu na zuwa gidan Oga Zaks, shigewa tai ta fara mai karuwanci da shafe2, biye mata yai dan yana buqatar hakan kan su isa, a motar suka samu nutsuwa,yace "ya kamata yau na kaiki wajen shaqatawa na musamman mui satia can ba mai takura mana ko ya neme mu" wani juyi tai da mazaunan ta a kan cinyar shi ta sakko ta zauna a gefenshi amma rabin jikin ta na nashi, tana sauke nunfashi, cike da kissa, murmushi kawai take, dan Alhjn akwai kai mutum duniyar sama, gaba daya jikin ta a mace yake, haka suka dau hanyar dajin Oga Zaks, suna isa motoci ne ba iyaka, bayan su  isa je taga mata kala2,maza duk shigar su daya, mata kamar guda bakwai, wasu da gani na aure ne, wasu irin ta ne, haka ta ga suna wata irin gaisuwa, sannan suka shige ciki gaba daya kamar su ake jira, harda wadan da basu zo da matan su ba ma, wani qaton waje taga sun nufa , kan su isa taga dukkan Alhzawan nan  da suka zo da mata, sun dakko wani red yadi sun nuna masu suna kalla har ita sai suka zube a qasa, ita dama Suwaiba oganniya ta dade a sume, daukar su sukai suka aje a wani gadaje da aka tanadar masu, Oga zaks ne da sauran mutanen wajen kowa ya cire kayan shi, haka suka tsaya ba kaya a jikin su, aka dakko wuqa, kowa ya kama wadda ya kawo, Alhj Salihu ne ya zo gaban Suwaiba, zuciyar shi a cunkushe, ji yake kamar ya bijire ma Dodon nasu,amma tinawa da azabar da zai shiga in yau bai wannan abun ba, kawai ya saka ma nonon Suwaiba wuqa, haka suka yanke masj Nono dukkan su suka tari jinin a wasu qorai qanana da suka rine da jini, kuka Alhj Salihu ya fashe d shi da yaja hankulan mutanen wajen, kowa daya kalle shi, ga uban ciki a gaba, ga baqi da yai yana maiqon zufa, sai dariya ta kama su, suka dinga dariya, saida Oga Zaks ya daka masu tsawa suka nutsu" Me yasa ka kuka Salihu?" Oga Zaks ne yai wannan tambayar," ina son matata Oga a san ya za ai a mata aiki a shafe wajen kar ta mutu , ka taimaka min Oga.kumin alfarmar nan oga" dariya sosai Oga Zaks yai sannan yace" karka damu i will keep my word ai , ni nace maka zamu san ya zamui matar ka baxat mutu ba, ita waccan guduwa tai ne?" Ya maida tambayar kan Kalla, " Eh Oga, da suka tafi ganin gida qin dawo wa tai ita" " ba damuwa yanzu dauke ta kui dakin duba marasa lfy da ita" da gudu Salihu ya dauke ta sukai can ya shimfide Doctors biyu ne suka hau kula da ita ya koma wajen tsafin nasu, jinin suka sha akai ta bayarwa wannan ya sha ya ba wannan, a haka suka gama suka rage dan kadan suka zuba a wani waje da naga sun qawata da ado suka zuba wa jinin nan danan ya tsotse kuwa,haka aka kammala komai sauran matan aka tattare su suka kai su wani daki baqi, ita ko Suwaiba da aka kammala bashi matat shi sukai ya saka kayan shi ya kaita mota, hanya suka dauka yana kuka hankalin shi tashe, Kalla na biye da shi a motar shi hankalin shi kwance, horn yai ta mai yanda suka saba in zasu rabu amma bai mayat mai ba, kada kai yai yaga ba ma amfanin komawa gida kawai bari ya tafi club, karkata motar shi yai ya tafi, sun isa gida ya dakko ta ya shiga daki da ita, kan gado ya aje ta, ya zuba mata ido yanda ta dashe tai fari alamar ba jini sosai a jikin ta, kwanta wa yai kusa da ita, ya rungume ta, a haka yai bacci, ba shi ya farka ba sai sha daya na safiya wanda ta sanadin motsin Suwaiba ne ya sa shi tashi, tash tai zata miqe taji wani sharp pain a qirjin ta , komawa tai ta kwanta cikin zubda kwallah, ji take kamar an yake naman wajen dan azaba, ni ko nace ba kama bane Suwai matar manyaπŸ˜‚

Baki ta bude tace.....

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA    πŸ’…πŸΌ

     Ina qara bada hakuri dai dan Allah masu son Novel din nan ta PC ba zai yu nai ta sending from d begining ba, i am so sorry, kui man hakuri zuwa dan kwanaki kadan zan kammala dika na mayar Document, inshaa Allahu, Na gode sosai,Love u from qarqashin heartπŸ˜ƒ, u guys ar awsome ❤

Page 23: 
Gobe ne ranar da Jabeer zai dawo, waya suke da Juwaireren shi, gaba daya ta shagwabe ta susuta mai lissafi, ji yake kamar ya dawo a daren, ko da fuskar ta ne ya kalla, ya san zai ji nishadi,  kwantar mai da hankali tai akan gobe suna tare, kar ya damu, tina mai tai akan yai addu'ar bacci kafin ya kwanta, sukai adduar tare suka kashe waya, bayan cika juna da "I love u", da sukai bacci ne a bangaren Juwairiyya da Jabeer  mara dadi, don tin da ya tafi hakan ne , baccin baya masu dadi ba junan su a kusa, a haka bacci barawo ya dauke ta bayan juye2 da ta sha, da sassafe ba yan tayi sallah, tayi abubuwan da suka zama na al'adar ta da safe kamar yanda kuka san Juwaireren Mama, tashi tai yau ranat gyaran lambun ta ne, taso ta bar shi tai gyaran gida tai ma Yah Jabeer din ta girke2, amma ta saka diguwar riga gajera, mai hannun vest, ta dau kayan gyara lambun ta taje, ta tattaba abubuwan da suke da buqatar gyaran, Juwairah akwai saurin aiki akwai kuma biyan buqata( ba a son mace ta kama aiki daya taita fama da an xo aga ba wani abun kirki da ta qulla bayan kuma ita a qasan ranta aikin nan take bil haqqi, gani take tana ta faman aiki amma an kushe ta, to yar uwa kin kama aiki daya kina ta yi kuma wataqila ba ma wanda ya fi zama dole ba, kin bata lokacin ki ya tafi baki qulla komai mai amfani ba, kinga in kina da miji mai mita akan komai dole zai magana, dan haka ana son mace mai zafin nama, mai saurin aiki, kuma tai aikin da kyau) tama gamawa ta wanke qafa da hannu ta shiga daki, ta hau gyaran ko ina, ta canja bedshit, ta dakko wancan ta fito da shi ta gyara palon ta, ta canja mazaunin kujerun ta, sallamar Nafee ne ya sa ta dan tsagaita da aikin ta, shigowa tai" haba matar Yayah ai sai ki kirani, da wannan tsohon cikin kk aiki irin haka, wata bakwai fa, kun shiga na takwas, ki ja mana aiki, habaa gaskiya banji dadi ba" ta fada tana turo dan bakin ta wai ita ba a kyauta mata ba, murmushi Juwairah tai ta kama kafadun ta" kar ki yi fushi da ni 'Yar qanwata, taho ki taya ni, na dauka kina taya Innarmu aiki ne, shiyasa ban kira ki ba, tayata aiki ai yafi nawa" murmushi sukai tare suka ci gaba da aikin, bayan sun gama canja fasalin wajen ne, suka debo ruwa da tsumma nan ma suka goge ko ina, kitchen ta tafi ta barma Nafee ta qarasa nan din,taje ta mai na shi kyaran sosai kamar Jabeer din zai leqa in ya fara shigowa, bayan ta kammala da nan ne ta wuce toilet, Nafee ce ta bita ta amshe wankin toilet din , bayan sun gama ne aka fara gyara tsakar gidan, in da yake anyi siminti, nan wanke wa Juwairah tai qasan kuma suka share" wai nikam me zaki dafa mai ne naga baki fara batun girki ba" His favorite u know, da kudin da ya ban jiya nai aike kasuwa an siyo man kwai, nama dankalin turawa, da cabage sai carrot da green beans kindan bak da su a lambu, sai flour ina da mai, an siyon yan kayan qamshi da maggi, dan wake zan mishi, kin san shi a duniya na kula yana son abunnan" " wai sosai ma kuwa, bakigan shi bane yana satar danwake a tukunyar Innar mu da dai kin sha dariya, Innar mu in ta kama shi sadaf2 take tafiya ta damqe hannun shi da ludayin tsamar danwaken, yai ta ihu ta qi saki" dariya sukai tayi sosai tinawa da wannan kabarin, miqewa sukai suka fara gyara dankalin, suka yanka veges harda na lambun nata, ta debi dan alayyahu kadan, da albasa mai ganye, suka gama yankawa sai ta soya dankalin nan ta dakko dafaffen naman ta da suka yanka qanana ta soya sama2 ta aje gefe, sannan ta rage man suyar ta dakko jajjagaggen kayan miyar ta, da ba timatir sosai guda biyu kawai tasa ba manya ba suma sosai, ta saka da tafarnuwa da kayan qamshi ta soya ta saka maggi da dan gishiri, sannan ta dakko wannan veges din ta zuba akai bayan ya fara soyuwa, ta juya suka tirara, sai ta juye akan wannan dankalin da daman, ta juya su, suka hade, dakko dafaffen kwanta tai shima bayan ta bare ta hada da shi ba tare da ta yanka ba, ta juya su tare,flask din ta ta dakko ta zuba wannan hadin ta rufe ta rage masu nasu,  dakko flour tai naga ta dakko wani gari" Matar yayah wannan garin meye?" " to tambaya an fara ne, garin wake ne na markada da yar dawa kadan, sai alabo, na niqo su shine zan hada da flour din yafi dadi sosai" " Auuuuhooooo, to ai sai ana yi ana tambaya ko kinga laifina?" " Aa aa matambayi baya bata ai" murmushi sukai ta debo kuka, mai dan yawa yanda zai santsi, ta dakko ruwan kanwar ta, ta zuba ta hada da wani ruwan dan bata son ta cika kanwa da yawa, ta kwaba yai laushi kwabin, ba tauri sosai ba ruwa, haka ta kwaba ruwan na tafara ta fara jefawa qanana, dan yafi dad, bayan ta gama ta tsame a ruwa mai kyau ta hada mai nashi a flask, ta miqe ta barma Nafee ta qarasa ita timatir daya ta dakko nunanne, ta fada mai sugar a tsakiya bayan ta yanka, ta hau goge fuskar ta da shi, sai da ga baya kuma ta dau rabin ta saka xuma ta goge fuskar shima, nan da nan wani duhun murhu da rana ya bace fuska ta dau kyalli da kyau, bayan ta gama kuma ta dakko lallen ta, ta saka mai man kwakwa kadan ta kwaba shi, ta hau murge jikin ta duk inda hannun ta ya kai musamman fuskar ta, kafin kace me Juwairere tai kamar ba ita ba," tab lallai Yayah na shan dadi aradu, yau fa ba ranar gyaran jikin ki bane, bama ki dade da yi ba amma ji yanda kk koma kamar wata tauraruwa" " Nafee kenan, ai ita mace ana son in mijin ta yai tafiya ko na kwana daya ne ya dawo yaga ta canja kawai ko ta ina, balle wannan da kk gane we ar talking about Yah Jabeer, My love, everything" dariya sukai, Nafee nata tsokanar ta ta gama ta shiga wanka, shigar da yake matuqar so tayi ta dakko kayan ta fara sakawa, doguwar rigar material ne aka mata irin na masi ciki, an daure sama kamar bra akai mata sai hannun ya zamana a wuya aka daure shi, cikin nan ya sha mai da gyara, sai kyalli yake gwanin sha'awa, sai dogon wando da akai mai fadi sosai ta zura, ta dakko kayan gyaran gashin ta, ta tsaga daga gefe, ta kwantar da shi, ta daure in a ponytail style, qamshi kam ranar kamar an barin turare, fuskar ta daga powder sai lipstick, ta gyara girar ta, ta saka kwalli,( kwalli na da matuqar tasiri ga mace, macen da ta saka kwalli ta iya kallo ta yi a rayuwa, in baki iya ba koyi ki fara)dogon hijab ta saka, tai sallar magrib ta zauna, tai azkar din ta, ta fara karanta qur'ani, ana kiran sallar isha'i ta tashi ta fara, Sallama yai ya shigo, yana ganin tana salla ya aje kayan shi yai alwala shima ya tafi masjid, tana idarwa qara gyara jikin ta tai duk da ba abin da yai, ta qara turare, ta gama, dauke kayan da ya shigo da su tai, na ajewa a kitchen ta kai ta fito da kayan nashi,masu datti ta fitar wamda bai amfani da su ba ta mayar wajen kayan su, sai wata leda da bata taba ba ta aje a gefe,daga alamu tsaraba ne, ruwan wanka ta je ta hada mai mai dumi, ta dawo kenan zata zauna taji shi, bayan qofa taje ta maqale tana ta dariya qasa2, shigowa yai yana ta dube2 bai ganta ba, sai da ya kama qugu sannan yace" Juwaireren Mama ko ki fito ko na zauna a qasa naita kukan rashin ganin ki, in an shigo nace baki son gani na ne" kan ya rufe baki yaji ta mai wata iriyar runguma ta baya wadda tasa shi fidda sautin da bai san ta ya akai yayi shi ba,( rungume mutum ta baya akwai yanayin da mace ko miji zasui ya zama ba wata runguma da ta fita dadi, ana yin ta ne ta hanyar zuro hannu a hankali ka zagaye mutum sai ka ja shi baya cikin shauqi ka manna shi da jikin ka) juyawa yai gaba daya ya daga ta sama, suna ta dariya, kisses kam kun san ranar an yi bari da ruwan su, zaunar da ita yai a cinyar shi, yana shafa cikin ta, yana ma cikin surutu kamar wanda yake hira damutum babba, dariya kawai take yi ita kam, " sannu da zuwa hasken cikin gidana, tin da ja tafi kaga daya gidannan duhu  ya mamaye shi, yau haske da ya bayyana daban ne, na gode Allah da ya ban kai a matsayin miji, Yah Jabeer ba zan iya rayuwa ba kai ba, i missed u so very much" ta qarasa tare da qanqame shi tana hawaye, dagota yai yana jin wani sabon qaunar ta na ratsa shi, dan yasan she meant every word, " Hushhh Husshhhh my princess, ki daina kuka, Yah Jabeer na Juwaireren Mama ne ita kadai, bana fatan na wayi gari baki kusa dani, u ar my happiness, i cant do without u, u ar everything that i ever wanted in my life, so don't be scared of loosing me, nine ya kamata naji wannan tsoron, amma ba zan damu ba dan nasan zuciyar ki, da ruhin ki , da gangar jikin ki nawa ne" wata runguma ta qara mashi da ta saka shi jin dadi sosai, daga shi tai ta ja hannun shi zuwa wanka ta taya shi yai wankan yai brush suka fito ta shirya shi bayan sun gama ne  kan shimfidar da suke cin abinci ta jawo hannun shi ta zaunar da shi, shikk binta kawai yake kamar raqumi da akala, dan waken ta fara zubawa a gefe, wanda har wani kyalli yake dan santsi sannan ta zuba mai wannann hadin da tai na dankali, zobon da ta dafa da abarba, da cittta kaninfari, kai da kayan qamshi dai da suka dace dika, ta saka harda cocumber, ta sa sugar, ci yake yana lumshe ido kawai, yana wani gurnanin magana amma ba a ganewa me yake fada, daukan zobon da aka saka a randar sanyi yai dan basu da fridge yai ya kurba, saurin bude idon shi yai sannaj ya mayar ya kulle, " Yah menene, yayi daci ne jo wani bu?" Ta fada tana zaro ido waje dan a tinanin ta ko bai mai bane, " matso kiji me yai" yana dan yatsina fuska, ita kuma sai ta danji zuciyar ta ba dadi, saboda gani take ta bata xobon garin iyayin mai hade2, dan ba ta san dama ana saka cocumber ba qirqira tai, matsawa tai kanta a qasa, " sai kin rufe ido zaki iya shan wannan abun, matso sosai na baki da kaina kiji ya yai" matsawa ta sake yi, ta rufe idon, jitai ya kama lips din ta yana masu wani salon da ya sa ta magana a qasan maqoshi, saida ya dade kan ya sake ta, ta kasa bude ido, dan wasu taurari ke mata yawo a kai" bude idon mana Princess, ni ba mai kudi bane bare na maki kyautar wannan kayan dadin da kk ban yau, amma na san i will make u feel something special, with every part of me" daukr ta yai sukai daki, zan bisu aka bugon qofa,nace ba sai an karya ma Hammana hanci na ba, zan tafi malamaiπŸ™„πŸ˜™πŸ˜™πŸ˜™πŸ˜™

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    ' YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ    

       BY HAERMEEBRAERHPage 24:" Adda Saudat dan Allah ki ban dubu daya mana ina son in dan ja jari ne ko ba yawa, xaman haka baya min dadi,ke ma kuma ya kamata kafin kudin hannun ki su qare ki kama wata sana'ar saboda kin saba yanzu da kudi, randa kk da buqatar su kk rasa ba qaramin damuwa zaki shiga ba" tinani Saudat take mai zurfi, can ta nisa tace" gaskiya kin ce wani abu kema, zan baki dubu biyar ki ja jarin, ni kuma zan fara kasuwanci ta waya da naga qawaye na da nai a whatsapp da facebook sunayi, ana samu in ka riqe amanar mutane, sai kaga ka samu riba mai yawa kana daga zaune" " yauwa Adda, sannan ina son nuna maki kinga Mama Bilki mace ce mai kirki, tana matuqar son mu, sai dai tabbas tana kishi da Goggo, wanda wannan dole ne a zaman kishiyoyi dama,mu sai mu kau da kai akan wannan, tinda iyayen mu ne, ba ruwan mu da hurumin su ta wannan bangaren, ya zama wajibi mu masu biyayya dikkan su, su a matsayin iyayen mu, itq a matsayin matar Abban mu" shiru Saudat tai domin maganar qanwar ta ta yau tana shigar ta, amma akwai nau'i na girman kai, da kishi a zuciyar ta, " hmmmm zan duba na gani" ta miqe ta dakko mata kudin ta bata, akan idon Goggo kuwa, " habaaaa Salma ai innice ke yanda na canja uwa, yan uwan ma canja su zan, auhoooo ba zaki iya canja yan uwa ba saboda kin same su su masu arziqi ne ko? Zaki roqa za a baki ko" " ni fa Gogga ba haka bane, ya kamata ki bude idon ki ki gane inda gaskiya ta dosa, ki daina rufe idon ki akan abinda bai kamata ba" " rufen baki sallamammiya kawai, an yi asiri da tuggu kala2 an rabani dake, to kije nima na huta da dawainiya, da dan wani da zanyi" juyawa tai tabar wajen Salma kuwa cikin qunan rai da baqin cikin halayya ta uwar ta ra shige dakin Mama Bilki, wadda taji komai, fadawa kan cinyar ta tai tana kukan takaicin hali irin na uwar tasu, shafa kanta kawai Mama Bilki take, bata furta mata komai ba," Mama ni fa ba kwadayi ne ya sa na tambayi Adda Saudat kudi ba, na tambaye ta ne naga ko tirare bani da shi, ga shi yanzu sai da Alimun ko lemon tsami nake amfani a madadin tirare, ba dan komai ba sai babu da take neman ta min yawa,amma in ina sana'a kudin zasu taimakan wajen kula da abinda ke cikina, shine Goggo take fadan maganganu marasa dadi akaina" " hakuri zaki Salma uwa ba abin wasa bane, dole mui mata biyayya in ba inda za a sabawa Allah bane, dan haka ki hakuri tin da kin samu jarin yanzu me zaki na yi na siyarwa?" " Mama Bilki ni da ina son na fara saida Meatpie ne, naga kina da injin yin taliya, kuma na kula kayan flour ana cinikin su, in ba su ba ban san me zan iya yin sana'a akai ba" " hakan ma shawara ce mai kyau, Allah ya sanya albarka" " Ameen mamana" kwantar da kanta ta sake yi a jikin ta ita kuma tana shafa gashin ta.

Yau kusan sati daya da kwana uku kenan Suwaiba na kwance tana jinya, Alhj Salihu dayaga zata farka ya danna mata allurar bacci ta koma, ko ya shaqa mata wata powder ta koma baccin, a haka tai wadannan kwanakin, zai mata wanka, zai canja mata kaya,sannan ya saka mata drip dan tana samun abinci ta jikin shi, ya zama babban likita kawai a cikin gifan shi, a haka sai da ya kula wajen ya warke tas sannan ya kyale ta da allurai na bacci da yake mata, yau ne ranar data bude idon ta tana kallo. Wajen kamar sabon waje aka kaita, a hankali ta bude idon gaba daya, akan na Alhaj Salihu ta bude su, kanta ne taji ya mata nauyi,kwantar da kan ta sake yi a pillow, jikin ta a mace ta bude baki tai magana da kyar" Me ya samen Sweet? Me yasa nake jin zafi sama2 a qirjina kamar naji ciwo?" " Shiiiiiiii karkina nagana sosai, hatsari muka samu a gidan, yan fashi  ne suka suka shigo, kina bacci suka yanke maki Nono, ni kuma dana dawo na ganki kin suma shine nake ta kula da ke" a firgice ta miqe daga kwanciyar," an cire man nono?" Ta fada tare da zaro ido waje wanda suka cika da kwalla mai dumi, " na shiga uku ni Suwaiba,ya zan rayu ba mahaifa ba nono, gaba me zan rasa kenan, Alhj na fa san kai ne sanadin rasa nono na Saudat ta fadan ban ji ba ban yarda ba, saboda ina son ka, ko da ina son kudin ka, ya zan rayu yanzu ba nono ba mahaifa" rushewa tai da wani kuka mai ban tausayi, cikin tausaya mata Alhj ya fara magana" ki yi hakuri Baby yau zan........ ka tse shi tai cike da bala'i" don't baby me again, i hate u, i hate u, i hate u" ta qarasa tana kuka mai ban tausayi, matsawa yai ya kamo ta ta zame," Don't touch me u monster, if u touch me again i swear i will cut ur balls too" cike da fushin da bai san tana da shi ba, wani shakkar ta yaji ta shige shi, miqewa tai cike da jiri, zata fita, " ina zaki kuma" " gidan mu zani, na gama auren ka, na gama aure a ABUJA daga yau daga rana mai kamar ta yau" " lallai ma Suwaiba, abinda baki sanj ba shine, ba inda zaki qara fita ko nam da can ne, kina tare da ni, dan yanzu ba zan iya rayuwa ba ke ba" ka mutu to, dan ba abinda zai hana ni barin gidannan, ko kana so ko baka so, in ka barni na tafi lafiya,ba hukumar da zan hadaka da ita, amma in ka hanani ba abinda zai hana ni hadaka da hukuma" wani murmushin rainin hankali ya mata ya ce" baki san wani abu ba, qungiyata babbar qungiya ce, manyan gwamnati da yan kasuwa ba wanda bab a ciki, ba yanda za ai ki hadani da hukuma kuma a samu hukunta ni din, mata dubin ki mun masu wannan aikin balle ke, dan haka hakuri zaki kawai mu qarasa rayuwa dake, in kin tafi wa zai na baki abun dadin danake baki?wa zaina debe maki kewa?wa zai zauna dake ba nono? Hakura zaki kawai mu zauna a haka" yana fada yana dhafa mata wuya, gaba daya ta qame ta dauke kantadaga ganin shi hawaye kawai take, ga wani tsoron shi a qasan zuciyar ta da take ji, yau ya zatai,kuka ne ya kwace mata sosai take yin kukan, key din motar shi ya dauka ya fice, anan ta durqushe tana kuka mai ban tausayi.
Talle kam ya saka marka a tsaka mai wuya ita da yayan shi, dan baya son maganar ta fita waje, gonar shi ta daji mai shegen nisa ya ke sasu zuwa gyaran ta, duba da cewar damuna ta kusa, kullum can suke tafiya ba abinci ba ruwa, amma shi zai je a machine din shi, da abincin shi da ruwan shi, saboda ya dinga ganin me suke masa, kar a masa ba daidai ba, su kuma su Baban gida gonar shi ta can wani qauyen dake kusa da su ya tura su, saboda ya yi yarjejeniya da su akan hakan, in ba haka ba ya kaisu birni ga hukuma, Kan kuce me Marka ta fita hayyacin ta, 'yan duwaiwakan nan duk sun zube, tai qashin wuya da jiki, yan gari sai gulma suke amma sunnrasa dalilin Talle nayin hakan, da dama sai suka alaqanta hakan da tsantsar rashin mutuncin shi, su Huwaila kuwa kullum sai sun yi surfen abinda za ai tuwo da shi sun dake da hannun su sun mayar gari, sannan sui tuwon, ga aikin qannen su da ya dora masu, wahaka kamar zata kashe su,ga qaramin ciki. Jummala ce ta fito daga dakin tana riqe da cikin ta, tana ta murqususu, " ke meye hakan zaki zo kina ma mutane kuka, kin gama aikin da na saka ki?"cikin kuka da tashin hankalin da take ji a jikin ta ne hasa ta budi baki zatai magana amma ta kasa, saboda wani abu da taji ya taho da gudu zai fita ta qasan ta, jini ne ya tsinke mata, nann d nan ta suma dan wuya, a gigice marka tai kanta,shi kanshi uban gayyar ya tsorata, daukar ta yai a hannu ya kai kan machin din shi, marka ma ta hau ta riqe ta, asinitin qauyen suka kaita, nan da nan aka tabbatar masu da bari tai, saboda ta sha wani magani na zubda ciki, ga jini yaqi daina zuba a jikin ta, suna buqatar a sai mata jini a qara mata zasui iya qoqarin su su tsaida jinin, Talle ne ya kalli matat shi, " sai ki fito da kudade da kk ajewa ai mata magani ko" ya fada cikin hade fuska, " to bari na koma gida" a qafa ta dibi hanyan duk tayi sanyi, ba cika da izzar nan ta da, kafin ta isa gidan ne ma likitan ta fito, take sanar da shu Jummala dai babu ita, sakamakon shan maganin zubda ciki da tai, yai resulting zub da jini mai tarin yawa a jikin ta, kuma sun kasa tsaida jinin har Allah yai cikawar ta, dafe kai Talle yai, nan take nadamar rayuwar shi ta baibaye shi, kuka yake kamar qaramin yaro suka samu wani mai machine din ya taimaka masa ya nemo mai motar da zasu kai ta gida tasha yaje ya samo masa motar, Tallen ya biya shi kudin, a motar aka maida su gida, Marka na shirin fotowa ta koma asibiti taga an fito da gawar Jummala, zubewa tai a qasa ta hau kuka da bori.......

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA    πŸ’…πŸΌ     


Hey guys, thank you all for ur love and support, ur comments....... ur comments ar awsome😍 i love u all from my head over my heals ❤❤❤Page 25:

Zanetake tana ta saqe saqe, tun fitar shi da safe har yanzu bai dawo ba, yana can ana sa toka sa katsi da shi, da Oga Zaks, akan deal din da sukai wanda ko Alhj Kalla bai san da shi ba, a baya sai da Alhj Salihu ya aminta da cewae ba za a kashe Suwaiba ba, za a san ya za ai a yanke mata nono kawai a bashi ita su tafi, ba za a sata a dakin duhun da aka saka sauran ba, dodon ya qarasa shanye jinin su suka mutu, in return, Alhj Salihu zai kai ma Oga Zaks Suwaiba for 2weeks, ya hanga ya hango, a gaskiya wannan karon ba zai iya ba, dan haka ne yau yaje akan a canja wani abun amma banda kai mai ita, a kyale ta haka mana ta wahala, shi yana son matar shi yanzu, amma sam Oga Zaks yace bai san zance ba, nan da sati daya zai buqace ta, idan bai kawo ta ba duk abinda ya same shi shi ya sani, hankalin shi tashe ya dawo gidan, ya isko ta ta fada dogon tinani, qarasa wa yai ya zauna kusa da ita, a doguwar kujera, ya zame ya dora kan shi a cinyar ta, ya rufe idon shi, cikin kulawa da tsoro ta fara shafa kanshi" Alhjna me ya faru? Me ke damun ka haka?" Bai bata amsa ba sai ma hawaye da ta gani ta gefen idon shi, hawaye ne na nadamar shigar shi wannan qungiya da yai tim farko, dan yanzu soyayyar Suwaiba tai mai yawan da ya farka daga baccin son abin duniya da yake duk da ita har yau tana nan akan bakan ta na cin daula, " Baby ki kwantar da hankalin ki akwai maganar da zamui dake yanzu, wadda na san kin sani an sanar dake, amma kin rufe idon ki baki son yarda, tinda baki ga zahiri ba" tashi yai zaune ya riqe hannayen ta ya fuskance ta suna shaqar nunfashin junan su, kanta har juyawa yake, dan tana tsoron ya tabbatar mata da abinda Saudat ta fada, da kuma tabbatar da zargin ta na maida ita Nonoless and mahaifalessπŸ˜‚tinanin ta ya katse ne a daidai lokacin da kalmar" ni dan qungiyar shan jini ne, dan samun kudi" wani ihu ta kurma ta dafe qirjin ta da yake a shafe kamar na Cute one kwaila😝miqewa tai, amma jiri da duhun da take gani ya sa tana koma ta zauna , kallon shi take sosai ta tabbatar shine din? Taba fuskar shi tai, shi kuma ya dora hannun shi akan nata, saurin zamewa tai ta rushe da kuka sosai," me yasa kk sanar dani? Sun ce ka kaini yanzu a yanken qafa ne ko hannu? Ko kaina suke so a yanke yanzu kai kuma ba zaka iya kai ni ba? Me yasa ka zabi shan jinin mutane kai kudi? Ina da son kudi da son abun duniya, qmma ba zan iya kashe mutum domin samun si ba, son kudi da abin duniya tane ya sa Saudat tana sanar dani na rufe ido kwakwalqata ta toshe zuciya ta ta rufe naqi yarda, mene ne hukumcin da ka yanke yanzu akaina har kk sanar dani wannan mummunan maganar?" "Babe pls calm down" ' calm what? U ar asking me to calm down after ur horrible confession? How would i ever trust u again? How do u espect me to trust u again with my life?" Ta qarasa cikin kuka mai cin rai, a idon ta kuwa ba wanda take hangowa sai Goggo Sarai, tai dana sanin kasamcewar ta uwa a garesu yanzu, da ta basu tarbiyyar da ta dace da basi zama masu son abun duniya ba, da basu zama idon su ya rife da son  kudi ba duk hint din da ake bata akan su yan shan jini ne amma ta runtse ido, tsabar son abun duniya, now she is in a very big trouble that she kow that she cant escape it, " Oh this life, ya zanyi yanzu ka fadan me ke faruwa yanzu to har kaji zaka fadan kai waye" hawaye ya share da sannan yace" Ogan mu ne da mukai deal da shi akan in ba a kashe ki ba zan kai masa ke, for 2weeks shine yake da buqatar ki ko ya dau fansa akaina, farkon zuwan ku ma sai da muka kai mai ku for 2weeks, ya dandana ku ya san akwai Ni'ima a tattare da ku mara misaltuwa, shine ya kwadaitu da na kai me ke akan alfarmar rashin kashe ki da ba ai ba aka yanke nonon ki dika" wani ihu Suwaiba ta sake ta hau kan Alhj ya na duka ko ta ina, qarshe da taga ko gezau bai ba sai ta kife  tana ta rusar kuka" kaico na ni Suwaiba, kaico na, na shiga uku,yau ina zan saka kaina, ga abinda son abin duniya ya kaini, duniyar ta juyan baya, bata riqe ni a masoyiya ba, yanzu ni aka kaiwa dan shan jini for 2weeks" kuka ta sake mai tsima zuciyar mai sauraron ta, qanqame ta Alhj yayi yana shafa bayan ta, da sigar lallashi , fizgewa tai tace" to ina jin ka? Kana nufin kai mai ni za kai shiya sa kk sanar da ni wannan karon ko me?" " ko daya, da ina son kai ki ai ba zaki sani ba zan kai ki, da da muke diban jinin ku dik wata sani kukai?" Zaro ido tai kamar su fado qasa dan firgita da tsoron shi, baya ta fara ja ta durqusa a guiwowin ta" dan son ka da annabin rahama kai min rai, kar ka qarasani, yanzu ni da mamaciya bamu da maraba, banda mahaifa, banda nono, jini na duk wata ake kwasa kamar a teku, an kaiwa wani qato ni ya gama sassaqata kamar tirmi, yanzu kana shirin maida ni sai ta Allah kuma" matsawa yai zai riqe ta ta ko falla da mugun gudu tai daki, kan ya isa ta fara qoqarin rufe qofar,yai saurin saka qafa ya tokare, ihu ta zunduma tana bashi hakurin yai mata rai ta tuba, ya maida ma Abban ta ita, dan yanzu ta tsani Goggo Sarai, ya taimaka kar ya tsotse mata sauran jinin nata, tura wa yai da qarfi ya janyo ta" ki nutsu dalla malama kar ki taran mutane ni, in da zan kai ki sauran duk sani kikai ba sai yanzu dana sanar dake ba? Na fada maki ne saboda ina son na maida ki gidan ku da kaina, in yaso duk abinda zai min ya min, na sadaukar da rayuwa ta domin taki ta tsira, Suwaiba this is how much i love u, i can give my life for urs" ya qarasa a hankali wanda ya sa jikin ta sanyi, qanqame shi tai tana kuka sosai," i don't want to lose u, i love u too, ban san sanda na fara son ka ba nima, a da kam tabbas kudin ka nake so, amma yanzu kai nake so, bana son abinda zai raba mu" sai ga Alhj Salihu na kuka kamar yaro, SO ba ruwan shi da girman ka ko qanqantar ka in ya shige ka yana saka aikata abinda ba hurumin ka bane aikatawa, haka sukai ta kuka ba mai lallashin wani, ba su ankara ba sai kiran sallan farko sukai na asuba, dan dama bai dawo da wuri ba sai 2am, miqewa tai jiki ba kwari for the first time, in her life da tai alwala dan wani abu na damun ta take son ta roqi Allah akai, shima dayaga haka alwalar ya yo, ya kabbara salla ta na bayan shi sukai nafila,suka hau addu'a akan Allah ya yafe masu, ya gafarta masu zunuban su, ya kubutar da su daga wannan al'amari da suka tsinci kansu a ciki, bayan sun idar da addu'ar ne suka yi subh prayer, suka tashi suka hau gado, bacci mai nauyi ne ya dauke Alhj amma ita inaaaa yaushe taga na barci, lallabawa tai ta bude wajen da take aje kudaden da yake bata, ta diba, ta dakko akwatin ta ta loda kayan ta a ciki, ta fita ta dau makullin mota babbar ciki a motocin shi, hawa tai ta nufi gate mai gadi ya bude mata, ta fice a dari, hanyar kano ta dauka, ko gajiya batai ba, haka ta iso gida a firgice, Alhj bai farka ba sai azahar, miqa hannu yai ya tabo Suwaiba yaji wayam, bai kawo komai ba, ya zaci ta shiga toilet ne, komar da kan shi yai ya lumshe ido,tinani yake ya kamata ya hada mata kaya ta tafi gida in yaso duk yanda sukai da Oga Zaks daga baya ya dawo da matar shi, miqewa yai zai shiga toilet din in ma wanka take suyi tare, yaga wayam, fita yai palo nan ma bata nan, leqa kitchen da sauran dakunan yai yaji shiru kuma bata nan, a hargitse ya fita waje wajen gate man yai," kai Audi ina Hajiya?" " Alhj ta fita da kaya da motar ka babbar" shafa kai yao daga gaba zuwa baya, komawa ciki yai, hankalin shi yana tsakanij tashi da kwanciya, na farko bata kware a tuqi ba bai fi sati biyu akai ana koya mata ba, gashi tana cikin tsoro, kar wani abu ya same ta, sannan can wani gefen yana jin haushin yanda ta iya gudun shi, duk da son daya nuna mata, kuma shima yaga soyayyar shi a tare da ita, miqewa yai ya dakko wayar shi ya hau kiran ta, tana ta ringing bata daga ba, hakura yai, ya je yai wanka yai sallah ya fita.Qarfe biyar ta isa gida na yamma, hankali tashe ta fada gidan, tana kuka, da sauri Salma da Saudat dake tsakar gidan suna murza meatpie din da Salma ke sana'ar shi yanzu, tashi sukai suna zare ido ganin ta shigo da uban gudu ne ya sa suma suka so kwasa da gudu amma suka tsaya, da daya ta diba a guje nasan sai dayar ma ta bita, tsayawa sukai suga me ya koro ta, fadawa tai jikin Salma tana kuka, " na shiga uku Salma, Saudat kinyi gaskiya, Alhj da kanshi yai confessing halayyar shi na shan jinin mutane, duba ku gani yanda aka maida ni" daga masu rigar tai qirjin ta ba komai, daidai nan Goggo Sarai ta fito sakamakon jin abinda Suwaiba ke fada............

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    ' YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ

        BY HAERMEEBRAERH

Masoya na da masoyan wannan Novel na 'YAN ABUJA, ina roqarwa wannan yaya tawa addu'a daga bakunan ku masu albarka, akan Allah ya biya mata dikka buqatun ta na alkairi, (Yah Ilham) Ina roqon Allah daya saka maki da alkairi ya biya maki buqatun ki na alkairi, Allah ya raya mana Naana, kin sani farin ciki jiya Allah kema ya faranta maki, na gode sosai Allah ya qara mana zumunci.❤Page 26: 

Nishi kawai take ita daya, gaba daya a gajiye take, ta gama shaving hammatar ta, tana son tai shaving HQ, duk ta gaji, tai zufa, shigowar shi ne yasa ta daga kai tana kallon shi, dariya ce ta zo mai amma ya san halin ta da yayi da ta fashe, " Yah Jabeer i need some help here please" ta fada with a shaky voice, da ji ta kusa fashewar kamar yanda yace," Au ai na zaci u don't need any help, tinda ai ko da dai da ba cikin ni nake yi, ke kuma ki taimaka min nima, shine kawai daga fita gaida Innar mu gajen hakuri yasa kk fara" haba ai kamar jira take ta bara baki sai hawaye," to ba na gaji da jiran ka bane, shine dan na ce ka taya ni kk son fadam magana ko, ba komai a barmin abuna zan yi da kaina" shi yanzu mamaki ne ke damun shi, kwata2 yarinyar ta canja, abu ba abu ba sai ta hau fada, ko ta hau fushi akai, yanzu dai me ye abun jin haushi anan? Murmushi yai na Allah dai ya raba ku lfy, na san meye matsalar ki, ni ne sanadi dole na lallaba ki," Husshhh Husshhh my princess, bari kuka, Yayan ki is here to help,can i have d shaving stick?" Share hawayen tai ta miqa mai, komawa tai ta kwanta ya gama mata, miqa mai hannu tai ta tashi ta nufi waje, ruwannan nan da ta ke hadawa na tsarki shi ta dauka wannan karon harda kaninfari da ganyen magarya, dan tana son wanke wajen sosai, wankewa ta je tai ta gama ta fito, still fuskar ta ba walwala, " Haba Juwaireren Mama Juwaireren Yah Jabeer, me kuma ya faru, me kk so gaba daya bana jin dadin rasa murmushin nan naki mai kwantar min da hankali, da ki hana ni murmushin ki gwanda ki hana ni ruwa inna dawo daga kasuwa a gajiye" bata san sanda murmushi ya kwace mata ba, dan tasan yanda yake matuqar son ruwan sanyi in ya dawo daga kasuwa, qarasawa inda yake tai, ta zauna a jikin shi tana kukan shagwaba, tana zamewa a jikin shi, gaba daya ta susuta shi, " Babe, ni agwaluma nake son sha" cike da kasala yake kallon ta" kin tabbata ita kk so yanzu?"ya fada yana kashe mata ido daya, yana shafa cikin ta, saurin kauda kai tai dan ta fuskanci effect din da take da shi a wajen shi musamman in tana shagwaba a jikin shi tana murza ko ina na jikin ta a nashi, tashi tai tana son gudu, dan she is not ready for him, saurin riqeta yai yace "tin dazu nake daurewa, yanzu ke da kan ki kin san ke kk jawo dan haka muje na duba bbyna sai inna gama naje na siyo maki agwaluma ya kk ce?" Biga qafa ta fara cike da shagwaba sannan tana qara narkewa a jikin shi, " Ni dai Honey ban da lfy" "muje na baki.magani to" " ni dai Aa" kan tai wani yunquri tini ya dauke ta sun yi bedroom din su. Jan qofar yau ma yai nace da qarfi, ka daina min irin wannan in ba haka ba na fara maku leqe, ai ni bance zan biyo ku ba damaπŸ™„πŸ˜™( yan uwana mata ina son fadakar damu akan murmushi, macen da ta cika mace ta san wacece ita, murmushin ta kawai ya wadatar da ita wajen bawa mijin ta farin ciki, komai bacin ran da mijin ta ke ciki, murmushin ta zai iya calming din shi daga dikkan damuwar shi, murmushin ta zai zama abun da mijin ta zai iya tinawa a ko ina yake ya jishi cikin nishadi yaji shima yana murmushin ba tare da ya sani ba, abu na biyu shine, da damar mata ba su iya shagwaba ba, shagwaba kala2 ce, amma wadda ta fi tasiri, ko da namiji na cikin fushi ki kwantar mai da hankali, ko da namiji bai da buqatar ki , ko bai da sha'awar ki yaji nan da nan ba wani abu da yake so a jikin shi ko kusa da shi sai ke, ba komai bane face shagwaba irin wadda yara suke yi dinnan suna hawa jikin mutum suna murza shi ko ina na jikin ki ya zama yana manne dana oga kina murza jikin ki da nashi kina zamewa, yanzu zakiji sauyin yanayiπŸ™Š)
Faduwar da sukaji anyi a bayan su ne yaja hankulan su sika juya gaba dayan su, Goggo Sarai suka gani zube a qasa, idonta bude hawaye ya wanke fuskar ta, ta sa hannu ta toshe bakin ta, da sauri Mama Bilki ta isa, dan ta kula gaba daya yaran nata kallo suka bita da shi, ba wacce ta motsa, daga ta tai, ta kaita kan kujerar dake daf da bakin qofar ta zaunar da ita, ruwa ta debo mata ta miqa mata a cup, kasa shan ruwan tai tana ta kallon Suwaiba da ta hade girar sama da qasa, tai hanyat dakin Mama Bilki, kuka ne ya kwacewa Goggo da taga yaran ta duk sun bar wajen sun yi dakin kishiyar ta da ta dasa musu tsanar ta a ransu, yau itace abin son su, wani gululun baqin ciki ta hadiya, ta kalli Mama Bilki da ita daya ce a kanta ta kauda kai taci gaba da zubda hawaye, Abban su ne yai sallama ya shigo, dakin Mama yake can ya nufa, kukan da yaji ana yi a dakin je ya ja hankalin shi ya qarasa da sauri, " Suwaiba ke nake gani? Meke faruwa ne, naga kuna kuka, ku sanar dani damuwar ku yarana, duk da banda arziqin da zan maku maganij ta, Allah ya horen bakin yi maku addu'a akan komai" Suwaiba ce ta je gareshi da gudun ta ta rungume shi, shima eungume ta yai kuka take mai ban tausayi, bai dago ta ba, sai da tai kukan ta ya ishe ta, sannan ta zame ta zauna a qasan qafar shi" fadamin diyata, fadan damuwar ku naji" " Abba.... Abba ka yafe min, Abba ka yi hakuri akan qin jin maganar ka da nai abaya, Abba nadama ta samen alokaci qurarre" " Aaa Suwaiba karki ce haka, lokaci bai qure maki ba yata" " Abba duba ka gani" daga mai rigat ta tai ta nuna mai qirjin ta da gefen cikin ta, anan ta juya wajen Saudat tace" Saudat nuna mai cikin ki kema" nuna mai tai itama tana kuka," me ke faruwa haka" Abban ya fada cikin tashin hankali ganin da yai Suwaiba ta zama Nonoless, " Abba mazajen da muka aura ta dalilin mugun son kudin mu, da influence na Goggo, Abba yan qungiyat shan jini ne su" ta qarashe cikin qunar rai da dacin da take ji a wuyan ta, a zabure Abban su yace " me kk ce? Shan jini fa Suwaiba, innalillahi wa inna ilaihirrajiun, Ya Allah, wannan wace irin rayuwa ce haka? Ya salam" zama yai ya dafe kan shi," to sanar dani me ya sami qirjin ki da kuma gefen cikin ki gaba dayan ku ke da yar uwar ki?" Kwashe komai tai ta fada mai, cikin kidima da tashin hankali ya miqe ranshi ya gama baci da jin abinda ya samu yaran shi, duk ta dalilin matar shi da ta kasa taimaka mai wajen ba yaran shi tarbiyya, ficewa yai a dakin ya nufi dakin Goggo," hankalin ki ya kwanta, Saratu hankalin ku ya kwanta nace, an mai damin Yara marasa haihuwa, ba zan taba ganin jikokina ba ta bangaren su, ke baki saki jiki kin haifa min yaran ba,ga shi kin ja sanadin son kudi da abin duniyan ki ya sa jikokin nawa ma zasu zama ragaggu, ban manta wa ke da kan ki ki kai kutunkutun ki ka tsaida haihuwa, wai yaran sun ishe ki, wace irin mace ce ke? Ki duba kiga Suwaiba an yanke mata nono gaba daya, banda jinin yaran nan da ake diba duk wata, tsahon wata takwas, ina zaki kai alhakin su?" A wannan lokacin Abba kuka yake, Goggo kuka , yaran kuka, Mama Bilki hawayen tausayin yanda rayuwar gidan na su cikin qanqanin lokaci ta koma take, wannan rayuwa ! Goggo ta kasa cewa komai, bakin ta rawa kawai yake, sai zatai magana sai ta ji bazata iya cewa komai ba, Suwaiba ce ta katse su da cewar" Abba ina neman izinin ka barni nai mana daki a ta can wajen, dan ba zan iya ci gaba da zama da Goggo a daki daya ba" murmushin takaici Abban su yai yace" kinji ? Kinji da kunnen ki, Yar ki ba zata iya zama dake ba? Kar ki damu Suwaiba, wannan kudin bai kamata ki amfani da su ba, kamata yai a bada sadakar su, ina da qasa, da ciment, dan dama ina da aniyat yin daki dan ku, koda kun zo ganin gida, dan haka da kaina zan yi" juyawa yai ya fita, kamar abun wasa Abban su ya fata hada qasa da komai, nan da nan Suwaiba da yan uwanta suka hadu suna taimakawa mahaifin su wajen yin ginin, harda mai ciki, Ammar ne ya tako dugui2, ya isa wajen su ya debo qasar a hannun shi ya miqawa Abban su, dariya sukai gaba dayan su, a haka Ammar ya zama shi ne ke saka su nishadi har yamma ta gabato Mama Bilki ko tana can tana masu girki har ta kammala, Goggo ba wanda ya kula da yin ta, ko kukan ta, sun maida hankali akan son yin dakin da zasu nesanta kan su da ita, ginin ya masu nisa sosai, a haka suka bar wa gobe sukai wanka, suka zauna bangaren Mama Bilki, suka zauna gaba dayan su, a babban faranti ta zuba masu, kowa ya saka hannu har Abban su suka fara ci, Mama Bilki ce ta miqe Abba ya kalle ta" Ina zaki kuma Sarauniya ta?" " Abban su zanje na kira Yaya ne, mu ci abincin dika" cikin zare hannayen su dika, tare da turo baki alamar basu yarda ba suke kallon ta" kin samu amsar ki a wajen su dan haka zauna mu ci bincin mu" komawq tai ta zauna, suka gama ci suka wanke hannaye suka sha ruwa, wanke kwanon Saudat tai ta aje ta dawo suka zauna suna ta hira, suna wasa da Ammar" Mama Ammar ya girma yai wayo sosai" " aiko dai kinga dik sa'annin shi ya fisu girma da wayo" " lallai kam" " Suwaiba, Saudat, Salma" daga kai sukai suka kalle ta jin yanda ta ambaci sunan su alamar ba wsa, amsawa sukai gaba dayan su suka zuba mata ido" ina son na baku shawara  a matsayina na uwa, sannan ina son ku duba abinda zan fada maku da da kyau, ku qoqarta amfani da shi, kun ga da farko dai uwa ba kamar ta a rayuwar duniya, Allah ya ce abi shi sannan abi iyaye, Annabin rahama ya jaddada bin uwa sau uku kan uba, dan haka ni ina son ku yafe ma mahaifiyar ku abinda tai maku, tabbas bata kasance uwa ta gari ba, mai ba yaranta tarbiyyar da musulunci ya tanadar, amma ta baku so, ta nuna maku qauna, na uwa da yaranta, in kun kula ita a tinanin ta tayi abinda ya dace daku ne, amma koma dai menene ina son ku sani, wanda bai yafe ma wani ba, shima ya ji tsoron kar Allah ya qi yafe mai nashi laifukan, dan haka nake mai baku hakuri a madadin ta, ku taimaka ku yafe mata, kar kuja wani ciwon ya kama ta dan Allah na roqe ku" cikin kuka suka matsa kusa da ita suka rungume ta, Suwaiba ce tai magana a cikim su" Mama Bilki ke alkhairi ce a rayuwar mu, ki yafe mana abubuwan da mukai maki a baya, tabbas mun cutar da ke sa kalaman mu, da ayyukan mu, bamu zama yara masu biyayya ba, ki hakuri ki yafe mana" " indai nice na yafe maku baku ce man komai game da Yaya ba?" Salma ce ta amsa masu dan Suwaiba da Saudat har yanzu akwai daci da wata irin qiyayya da suke ji game da mahaifiyar tasu, amma sun sani dole su yafe mata, sui hakuri da abinda ta musu" mun yafe mata Mama Bilki Allah ya yafe mana" " to ya kamata kuje ku sanar da ita kar ta kwana cikin damuwa" Suwaiba ce tai saurin miqewa" ni dai Mama ba zan iya zuwa yau ba, dan  Allah kar ki tirsasa ni yin abinda ban jin zan iya yin shi a yanzu" ta qarasa cikin kuka,"Bilkisu Allah ya miki albarka, amma ki bar su haka, zuqatan su cike yake da abinda ta musu, daga baya a hankali komai zai warware masu"  " to Allah ya kaimu, Allah kuma yansanyaya zuqatan ku ku yafe mata gaba daya" amsawa sukai dika da " Ameen"  hankalin Goggo kam ya kai qololuwa wajen tashi, Wanj duhu take gani ya rufe mata ido......

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ   'YAN ABUJA  πŸ’…πŸΌ

        BY HERMEEBRAERH


Page 27:

Kuka kawai talle yake ya kasa tsaida hawayen shi, wannan rayuwar ba wanda ya ja ma su ita face shi, mugayen halayen shi ne da yi ma yaran mutane sakin wulaqanci, da zinace2n shi ne ya kai su ga haka, gashi tsabar lalacewa Yayan shi ke neman matar shi ta sunna, Yaran yayan shi na neman na shi yaran, kaiii jama'a wannan wace irin musiba ce ta sauko mana a wannan zamani, Marka kam irin kukan qabilun nan take, tai girgiza tai girgiza tai kukan sai kuma tai dif ta cigaba da gyada kai, abun ya shigeta sosai ba kadan ba, jummala ta mutu sakamakon yunqurin zubda ciki, ga Hawaila tana kallo a gaban ta da ciki dan kuyat a gaba, itama ga nata farkan a gefe, wace irin rayuwa suka jefa kansu a ciki? Maqota ba mai zama wai da sunan makoki, ko sun shigo yada magana ne yake kawo su, wasu daga ciki zakuji suna cewa" Tohhhh abinda ya faru kenan hmmmm Allah dai ya jiqan ta amma zunubu kam an kwasa" ire2n kalaman mutane kenan ana yi ana kyabe baki, wasu kuma bayan sunyi gaisuwar sai sun dora da" ikon Allah kamar ciki nake gani a jikin Huwaila, ni dai bani da labarin auren ta, sannan mun san ba a shan ciki a ruwa, hmmmm Allah ya kyauta,gidan Talle kenan, gidan uwa ba kwaba ya ba hantara" kowa da abinda yake furtawa, baqin ciki kamar ya kashe Haule, wai yanzu nan ne gidan ubanta, gidan da ba tarbiyya ba kwaba, yanzu itama tambarin ya shafeta, ai kuwa da an gama arba'in guduwa zatai qauyen da taji wata qawar Marka da tazo kwanaki ta fada da sunan wata mata a matsayin mahaifiya gareta, mai suna Husai, qauyen yana nan kusa da su, in ta zauna a gidannan ko mashinshini rasawa za tai, in ko ta koma can ko sunqi karbar ta ba zata dawo nan ba, kwalla ta share ta ja hanci, tana kallon su cike da tsana, da tsanar halayen su, tashi tai daha wajen kwata2 tai shigewar ta daki,addu'a take taima 'Yar uwar ta a ranta na Allah ya yafe mata, Yayan Talle kuwa zaman daki ya kama shi, bai da damar fita waje dan abin kunyar da suka aikata, by now kowa ya san meke faruwa a gidan Talle, ba kowa a qofar gidan yan karbar gaisuwa ko yan gaisuwan, sai su Baban gida da Badamasin, Talle kallon su yake kamar ya shaqe su, amma yasan a iskancin da sukai shi yayi ninkin nasu sau ba adadi, nade tabarmar da yake kai yai ya shigo, fakam2 ya tsaya kan Huwaila, kwalama su Baban gida kira yai, suma shigowa sukai da tabarmin su a hannu, kai a qasa kamar munafukai," a cikin ku waye me cikin Huwaila?" Badamasi  ne ya nuna Bangis, shi kuma ya qara duqar da kai qasa," Yanzu yarannan wai har kunyi girman dirkama wata ciki? Ko dake maganar wai kun yi girma ma bata taso ba tinda ga misali kun bayar, kun yi sanadin mutuwar daya, ga daya nan da tambarin abin kunyar da zai bi zuri'ar mu har abada, dan haka sai ka bari ta haihu a maku aure kun renu dan shegen cikin gidan da kuka samar tare," cikin tsananin qunan rai yake maganar, ita dai Marka bata cewa umm bare Aa, tai dif sai hawayen nadamar rayuwar su ke fita mata, a cikin zuciyar ta tana ayyana wannan lamari ba laifin kowa bane face nashi, daya tsaya ya tsare mata sha'awar ta da buqatun ta da batai zina da auren ta ba,( dik d wannan ba hujja bace ga matan da suke ganin dan mijin su baya sauke haqqin shi akan su bari su bazama neman mazan waje, ko su fara aikata wani abun da ya kauce hanya, su sani Allah zai masu hukunci daidai da abinda suka aikata ne shima mijin Allah zai mai hukuncin abinda ya aikata, so ni a ganina ba dabara banw hakan, wadda ke da matsala haka maganij ta ya kamata su zauna suyi in ya gagara su tattauna da mijim to ta nemi waliyyan su su shiga lamarin haka islam ya tsara,bai halatta ta fada halaka ba da sunan rashin kulawar miji mu kiyaye)miqewa marka tai zata shiga dakin ta, ya dakatar da ita, " Marka ina neman yafiyar ki akan dikkan abubuwan da suka faru tabbas laifi nane, da na tsaya na zama namijin kirki da duk haka bata faru ba, ki yafe min mu dawo mu gyara rayuwar mu,"kauda kan ta tai saboda kukan da yake neman cin qarfin ta ga wani haushin shi da take ji na jefa su wahala da yai, Yayan shi ne ya fito daga dan qaramin dakin shi ya zube akan guiwowin shi" Talle qanina ka yafeni na biye wa son zuciya, da rudin shedan na aikata mummunan abun da ko mutuwa mukai sai yabi zuri'ar mu, ka taimaka ba dan ni ba domin Allah da zumunci ka yafen" kuka ya kifa hannayen shi a fuskar yana yi, Talle daga shi yai kawai ya dan daki kafadar shi dan shima kukan yake ji, kauda kai yai zai shige daki yaji maganar yayan nashi," a gaskiya sai mun gyata rayuwar gidannan namu kan komai ya tafi daidai, na farko yanayin yanda iyalin ka take yawo a tsakar gidannan ya jawo min matsananciyar sha'awar kasancewa da ita, dan zakaga tana yawo ba isasshen kayan da ya rufe dikkan jikin ta, tana tafe tana juya dikkan jikin ta, sannan ga maganganun ta danake jiyo wa yawancin su na batsa ne, wajen kallon ta da maganar ta bata kiyayewa, wadannan abubuwan sun ja ra'ayina matuqa, dan haka in muna son mu samu kwanciyar hankali da kiyaye war zinace2 a tsakanin mu sai mun kiyaye, sakewa yarannan da mukai shima ya jawo wannan bala'i da muka shiga har yai sanadin mutumar Jummai, ( sakacin iyayen yanzu da kusan nace kowanne gida hakan na faruwa,sai ace cousen din tane ai, kaji tana yayana ne, ko yana qanwata ce, amma da sun samu sarari su biyun su zai zauna ya lalube ta tsaf ya miqe, ita kuma tai dif da bakin ta,  da wuya kaga cousens din da a wannan zamanin suke gida daya ko suke yawan ziyartae juna wata barna ba ta gilmawa, wanj sa'in gaba ga iyayen zakuga suna kallon yanda Yarinya ke mannewa namijin amma sai su dau hakan a wayewa, kuga tana wasan banza da namiji sai ace ai yayan ta ne ba komai,sai barna ta faru a zo ana dana sani wasu ma ba a sanin barna ta faru sai sun aurar da yaran, za a duba yarinya bata kai budurcin ta gidan miji ba cousen ya dauke a cikin gida, maybe ma a dakin uwar ta, can u imagen, wannan wace irin rayuwar zinace2 muka shiga? Mu yawaita nemawa kan mu tsari akan zina yan uwa Allah ya kare mu) Talle ne ya amshe maganar da gaskata yayan nashi, kuna ya basu tabbacin dawowar shi qauye da zama, don ya gama xaman birni kenan, murna kam Marka ta yi ta da jin wannan zance, amma ba ta ce komai ba har yanzu, a haka suka watse kowa ya kama inda zai yi cike da alhinin mutuwar Jummala.


Su suwaiba sun kammala ginin dakin su tsaf, sai dai ba flasta, ba fenti, sai ledar daki da suka fara shimfida qaton buhu a qasa sannan suka saka ta, katifa biyu suka saka, babba da qarama daya, sai kayan sunda suka kwaso suka zuba ciki, daki yayi ba laifi, amma ba wani wadata da yalwa sai godiya kawai, kullum dare Suwaiba sai tai kukan rashin mijin ta da kuma yanda ta koma, yanzj wa zai aure ta? Yaushe Salihu zai aiko mata da takardar sakin ta? Ko yazo ma ta ganshi? Haka za tai ta saqe saqe har bacci barawo ya dauke ta. Goggo ta kamu da mummunan hawan jini, sakamakon sanya tinani da damuwa da tai, sannan yanda ta saba Yaran ta na manne da ita yanzu tsakanin su gaisuwa, in suka gaida ta sai dai tajiyo hayaniyar su da Mama Bilki tana koya masu abubuwan da ya dace, suna kuma wasa da Ammar kamar ciki daya suka fito, abun ba qaramin daga mata hankali yake ba, asibiti kam taje shi a kwanakin nan yafi sau nawa, dan sai kawai tana zaune taji wani jiri da duhu ya mamaye ta, sai suma, haka za su kaita a bata magani  sui qoqarinnda zasui ta farfado si sallame ta Abba ya maido ta gida, takan ce a ranta " Oh ni Sarai naga duniya,  Yarana danake taqama da su a idon duniya su suka juyan baya yanzu, Allah gani gare ka" yau Goggo ta tashi da matsanancin ciwon kai, in da ta dinga kiran Suwaiba ta na zaune tana jin ta tai shiru, Mama Bilki ce ta leqo ranta bace tace" Suwaiba kina son shiga aljanna kuwa? Mahaifiyar ki na kira kina ji ki shiru? Wallahi ki kiyayi Allah, ki kiyayi fushin uwa suwaiba, meyasa kk da ruqo ne, shi wancan mijin naki mai qaton ciki ba dan dan kyaun da yake da shi ba meye abin so a wajen shi, duk da wahalar da suka jefa ku kina nan kina faman son shi, kina begen shi, sai uwa wadda ta haife ki, itace baki san ki yafe wa ba ko? To na qara jin haka tana kiran ki kina ji ki zauna kiga ya zamu qare a gidannan da ke, shashasha kawai,kin miqe ko saina kwado maki wannan murfin kwanon?" A hanzarce ta miqe tana kallon hannun Mama Bilki mai kwanon, shigewa dakin Goggon tai tana zumbura baki" Gani" shine abinda tace ta ja ta tsaya, " Suwaiba nice fa Goggon ki, abar son ki, Suwaiba ba dan Adam din daya wuce kuskure, nayi kuskure, na yi nadama ku yafe ni ke da yan uwan ki, na san ban zama uwa ta gari ba,ko wannan ciwon da nake fama da shi ya ishen ciwon kai ba qaqqautawa, na rasa ya zan kuma duk.sanadin juyan baya da kukai ne, a tinani na a da rayuwa mai kyau nake baku, dan Allah suwaiba ku yafe wa Goggon ku kunji?" Kuka Suwaiba take sosai, harda majina, kusa da goggon ta taje ta zauna ta dora kanta kan cinyar goggon ita kuma ta hau shafawa, ba wanda ya qara cewa komai, nan take Goggo sarai taji kamar ana zare mata ciwon kanta, damuwar ta na raguwa.Da saurin shi ya shigo gidan bakin shi washe kamar gonar audiga, qoqarin shi bai wuce yaje ga mahaifan shi ba da matat shi, shiga bangaren Innar mu yai yaga wayam an karo qofar ba kowa, bangaren su yai cike da doki da zumudi, durqushe ya ganta gaban ta robar da ta hada zuma da zamzam ne da taiwa fatiha qafa bakwai take sha tinda cikin ta yai wata takwas dan samun sauqin haihuwa, ta shan ye ya kai rabin robar, zufa ke karyo mata ko ta ina, sai addua take tana qarawa," Allahu Allahu Allahu rabbi la ushrika bihi shai'an wa huwassami'ul aleem" shine abinda take fada taja maimaitawa, da sauri ya isa gare ta, ruwa ya fashe mata tana wani nishi na son ta sillubo koma meye a tattare da ita, sauri yai ya juya ta daga durquson sabida kar ta haihu a haka ta samu mummunan tsaga a gabanta, zaunar da ita yai ta gaba ya koma bayan ta yana qoqarin taimaka mata, dan yanda ya ganta, da yanda suke karantawa shi da uta a wani littafi na EVERY WOMAN ya san haihuwa ta zo, ba yanda zai ya fita da ita asibiti haka, suna haka sukaji sallamar Innar mu ta zo da kwadon zogale zata ba Juwairah, ai ko tana ganin haka itama ta duqa ta hau taimaka masu, nan take ta fara qoqarin nishi mai qarfi...........

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ   ' YAN ABUJA  πŸ’…πŸΌ
          BY HAERMEEBRAERH

NA RIQE KU DAN ALLAH KU DAN QARA MIN HAKURI KADAN NAN DA KWANA BIYAR INSHAA ALLAH ZAN KAMMALA 'YAN ABUJA ZAN MAYAR DOCUMENT YANDA DUK MAI SO ZAI SAMU. NA GODE SOSAI DA SOYYAR NOVEL DINA DA KUKE NUNAWA. ME LOVE U ALL❤

Page 28:
Kukan jaririyar da suka ji ne ya tabbatar masu da cewar Juwairah ta sauka, lfy, Yah Jabeer na gani ya na kissing wiyan Juwairah da tai zufa iyaka, shafo gefen fuskar shi tai tana murmushi, Innarmu ce ta dau Babyn tai gefe da ita tana " Oh yarannan ba ko kunya, ji yanda kai jage2 da hawaye harda majinar kuka dan abin kunya, ita mai haihuwar ma tai jarumta ko kuka ba tai ba  sai kai" cikin dakewa da alamun boye halin da ya shiga ya fara magana" a gaskiya Innar mu ba abinda zan ce dake sai ubangiji ya miki rahama, ya saki a aljanna madaukakiya, ke kuma Juwairah Allah ya maki albarka, ya biya maki dukkan buqatun ki, ni Jabeer yau na qara alqawarin riqe amanar ki har qarshen rayuwata" kallon Innar mu yai ya sake cewa" Innar mu da ace mazaje suna shiga dakin haihuwa da matan su da an rage kashe2n aure da wulaqanta mata, da maza sun daraja mata fiye da qima, Innar mu duba fa kiga irin wahalar da yarinyar nan ta sha" ya qarasa maganar cikin tsananin tausayawa da girmama matat tashi, jikin Innarmu duk yai sanyi itama, dan tabbas ta san iyaye mata sunyi matuqar qoqari na samar da mu dika, sai dai mui ta masu addu'a da qoqarin yi masu biyayya," Jabeeru duk abinda ka fada gaskiya ne, yanzu kaga yarinyar nan tana ta bushe wa, tashi ka dora mana ruwan zafi, ka zo ka saka ganyen magaryar nan a ruwan su tafasa tare saboda ya fidda dattin jikin yarinyar sosai, Jabeeru kazo ka dauki 'yar ma mana ka riqe mata kamar wani zai dauke ta" dariya yai yana sosa qeya ya gyarama Juwairah zama sosai yanda zata ji dadi sannan ya isa gare su, kallon yarinyar yake with so much love , ga wani irin kyau da Allah ya mata na musamman, wannan kyaun daga ina ta samo shi,juyawa yai ya samo amsar shi wajen juwairah, murmushi ya mata sannan yace" tabbas na samu amsata danake nema a zuciya ta , kyaun yarinyar nan duk naki ne Honey" " meye wata Hamee ni ta shi ka dora ruwan ka dawo ko kuma ka gyara ruqon ta naje na kwaso na bangare na dana zuba dazu, riqe ta na dawo" yara mai ita tai ta sa kai ta fice tana " yara ido ya bushe ba kunya, zamani duk ya canja iko sai lillahi" zuwa tai ta zuba ganyen magaryar a ruwan ya ci gaba da tafasa sannan ta kwaso bayan ta tace da rariya ta taho,yarinyar ta karba ta fara wanke wa, mamaki ne ya ishe ta ganin Jabeer na gyara Juwairah, " kai ni fa sai na bar maku wajen ku, wannan rashin kunya har ina, wa ya koya maka yanda ake ma mai jego ni Hansai" cikin dariyar da suke mata yace" Innar mu na koya ne a wani littafin anti-natal din ta littafai ne da suka qunshi yanda ake renon ciki da haihuwa da kuma yaran kansu, da irin taimakon da uba zai ba uwa in ta haihu, ina fatan kin fahimta, baya daga cikin kyautatawa namiji ya bar mace tai ta wahala ita daya bayan tate suka samar da abinda aka haifa ko za a haifa din, yana daga cikin karamci da kyautatawa tare da soyayya namiji ya shiga dumu2 ai komai da shi, hakan na qara ma ma'aurata fahimtar juna da so da tausayi, sai kiga aure ya dade ba fafa ba yaji bare kai qarar miji gida" innar mu gyada kai kawai take , a zuciyar ta tana ayyana gaskiyar dan nata, amma to be honest ita kunya suke bata, shiru tai kawai bata ce komai ba, Jabeer ne ya kammala gyara wajen ya tallabe Juwairah suka fita tsakar gida, kujera ya bata ta zauna ya fita wajen Innar mu ya debo ruwan zafi, ya shigo da shi cikin babban bokiti, ya raba biyu, daya a babbar roba daya na wanka, kai mata yai ya koma daki ya dakko ruwan kal fari, ya zuba kamar murfi uku a ruwan da zata zauna din, ya je ya fara tayata wankan," Yah Jabeer pls i can do it my self, Innar mu na nan fa, she may not say a word amma na san ba zata so ganin hakan ba," " ke ba abinda zata gani kar mu bata lokaci, mqza na gama maki kan ta gama da Babyn mu," a haka ya kashe ta da zance ya mata wanka ta zauna a ruwan taji dadi sosai, ya qaro wani, ya saka ta a ciki, ya qara ruwan kal din a ciki( ma'ul kal na wato ruwan kal yana wanke datti shima sosai, ya fidda qarni da warin HQ sannan yana matse mace, ya gyara ta, sai dai ba a so in ba kamar yanzu da aka haihu ba a cika amfani da shi shi da bagaruwa, baya2 ake son amfani da su, dan kar su yi illa ma wajen, kuma ana son in ana amfani da su a yawaita cin fruits da veges da kuma shan zuma mai kyau da zamzam, dan su zama sun saukar da ni'ima a HQ yanda ba zata bushe ba) bayan sun gama ne ya fito kenan Nafee ta dawo daga makaranta, shigowa tai da gudun ta, sakamakoj kukan bby da ta jiyo, ai suna ido biyu da Juwairah ta kwasa da gudu ta isa wajen ta ta rungume tana murna, " sannu matar Yayah Allah ya qara maki lfy ya raya mana abinda muka samu" " Ameen Nafee sannu da dawowa" " to malama sake ta haka taji da kanta" sakin ta tai amma bakin ya qi rufuwa kamar gonar audiga, gani tai ya dakko zanin haihuwar ya aje mahaifar a cikin leda zai wanke zanin, maza tai ta karbe, "Yah Jabeer barmun na wanke ni ban komai ba ai" " A'a sis basshi yanzu kk dawo skul bana son ki wahal da kanki, kayan jini ne ke kuma baki son su dan haka zanyi, beside ni ya kamata nayi, tinda ina kusa, ta yi me wuyar da ta haifo man the queen of beauties, shiga ki ga inda ake kyau barakallah" ai ko tini ya kwadaita mata gani yarinyat da gudu tai dakin, tana isa ta zube gwaraf gaban Innar mu, ta gyara yarinyar ta sha kwalli, tai matuqar kyau, idon ta bude fes kamar haihuwar sati, cikin zumudi ta amshe ta, tana mata addu'a Juwairah ce ta shigo da sallama daki tai ta na tasbihi ga Allah tana matuqar godiya daya sauke ta lfy, Mama Bilki ta sha addu'a yau a bakin Juwairah, ta gefen idon ta ta hango tsantsar kyau irin na yarinyar, " ikon Allah ke nan yanzu da wanne ido zani gida na kalli Mama da Abba, wai ni ce yau na haihu" shafa cikin ta tai da yai mata babba kamar bata haihu ba ga nankarwa da taji yayi, murmushi tai ta qara gode Allah, nan da nan ta hau shiri, man kade ta dauka ta shafe cikin da shi sosai ta murqe shi, dama ya sha gashi wajen Yah Jabeer, don jinin ya samu fita, bayan ta gama murje cikin ne ta kwalama Nafee kira dan ta zo ta daure mata cikin, zuwa tai ko ta tamke mata shi, tsam, ya koma kamar ba ta haihu ba, kayan ta ta saka atamfa riga da zani ya mata kyau sosai, kalar atamfar akwai pink da red a jiki, geshe jikin ta tai da turarika masu dadi ta fito, lokacin Jabeer ya gama komai yai wanka shima ya shigo, sannu tai masa da adduar Allah ya saka mai da alkairi, yai murmushi yace" is my duty love, so ki daina damun kan ki," murmushi tai mai da tasan yana biyan komai a wajen Yayan nata, kada kai yai alamar zamu hadu ne, kina tsokana ta ko, daki yaje ya shorya ya fito ya same su dika a zaune, gyaran murya yai ya kalli Abban su ya gaida shi, dan yana shiryawa ya shigo, yai ma harinya addua, Nafee na ta masu tsiya shi da Innar mu, miqa mai ita Abban su yai shima ya mata addua, sannan ya fadi sunan da za a ana kiran ta da shi, wato Hafsat sunan Innar mu kenan, Innar mu har kukan dadi tai, sannan yace ma Juwairah "sai ku nema mata sunan ku na yan gayu da na san dole sai kun saka mata," Nafee ce ta kalli Juwairah tace" matar yaya sai ki bamu suna" Juwairah tinani tai sannan tace" Na saka mata Abrar( mao tsoron Allah)" " Oh ni Hansai yanzu ina ni ina iya fadan Abras" dariya suka kwashe har Abba, Abban ne yace" haba Innar su, yanzu Abrah dinne zai gagare ki?" Haba me zasui in ba dariya ba dan shima ya kwafsa, gyaran murya Jabeer yai ya fara magana cikin tsantsar farin ciki da annashuwa tare da son sanar da su abin farin cikin  da ya same su yace" Abba Innar mu Juwaireren Mama and my little sis Nafeesa, ina mai farin cikin sanar damu ci gaban da ya same mu, a yau kuma a dazu dana dawo na zo da labari me dadi na samun aikin da nai, a NNPC na can Abuja in da suka ban gida dake kusa da gidan man da zan aiki, a unguwar Jabi, harda mota, sin dauken a matsayin Manager na wajen gaba daya, sanan kuma bangaren kasuwanci na yau na biya ta kasuwa, Saifullahi dana kan bari ya min jiran wajen in bana nan ya dakkon kudade masu tarin yawa, da kuma wasu jakunkunan da na saro ba su iso ba daga malaysia , to a yau suka iso, har wasu yan kasuwan sun sara, shine ya ban kudin da suka kai dubu dari biyu da talatin cif a hannuna, nan take na bashi talatin din nayo gida da sauran" juye2 ya farayi yaga ina ya wurga ledar da yazo da ita, dubawa yai ya hango ta can hanyar shigowa inda ya yar ya iso wajen matat shi mai naquda, kasa kudin yai kashi biyu, sannan ya qara kasa kashi daya biyu, miqawa Abban shi yai kashi daya, sai kuma ya dauki dubu goma ya ba Nafeesa sauran dubu arba'in ya bawa Innar mu, yace gashi su sa mai albarka," lallai wannan yarinya ta zama mabudin alkairi a gidannan, muna ma Allah godiya, nayi murna da farin ciki sosai najin wannan abun alkairi daya same mu, Allah ya taya ka ruqo da gaskiya da amana, Allah ya qaro maka arziqi mai yawa mai albarka," amsawa sukai gaba daya da " Ameen" Innar mu kukan dadi take tin da aka fara maganar, dan bata taba tunanin riqe kudi rabin wannan bama dan tasan ba ta dasu bata kowa ba ajiya, yau gata da su kuma nata, ai sai murna, ta kasa magana sai kukan dadi take na daukakar da Allah yai wa danta a lokaci daya" Innar mu ki bar kuka addu'a da albarkae ki Yah Jabeer ya roqa" Juwairah ce ta fadi haka a lokacin da ta ke kurbar shayin da Nafee ta hada mata mai kauri da dumi, share hawayen ta tai tace" Jabeeru ba abinda zance sai dai nace Allah ya qara maka albarka ninkin ba ninkin akan wadda ya maka, ina alfahari da kai a matsayin ka na dana, Allah ya karen kai daga sharrin maqiya" amsawa sukai dikka, Nafeema ba a barta a baya ba wajen taya murna da godiya balle mai jego kuma, kiran sallah je ya karade wajen tare da duhun da ya bayyana hakan ya nuna masu cewar magrib ta yi, miqewa sukai bayan sun gabatar da addua, sukai alwala mazan suka tafi sallah matan sukai a gida, bayan ya dawo ne ya dakko kaza a akurkin su, ya yanka biyu, ya kaiwa Innar mu, Nafeesa ce tace ni zanyi dan nasan yanda take son ta, dauka tai ta koma bangaren Juwairah ta dakko ridin da suka daka tare , sa madarar shanun dake aje a randar sanyi, dakko kayan qamshin da suka niqo harda minannas a ciki ta gyara kayan miya ta zuba wannan kayayyakin amma banda madarar, sai da farfesun ya dahu sosai sannan ta zuva madarar shanun, tana tafasa daya biyu ta sauke ta kaima Juwairah guda dayar dan dama dayar can ta batwa Innar mu ta dafa wa kowa a gidan a ci wannan ta mai jego ce, godiya ta mata Jabeer na shigowa ya zauna zai saka hannu, Nafee ta riqe" A'a Yah ga tamu can wajen Innar mu wannan nata ne, ita fa ta haihu ba kai ba, sannan na zuba mata maganin basir a wannan ka jira tamu" dariya yai sosai har yana kama ciki," yarinya zaki bayani ne kice kawai Nafeesa na hada maki kayan da zaki warke da wuri ki dawo na dora daga inda na tsaya ne kawai, banqi ba in an hanani ci saboda ita ta haihu tai wahala ya kamata taci tai qat amma batub ace wani basir in haka ne ai na fita bair nifa namiji ne" dariya sukai dika. Wajen jaririyar yaje ya dauke ta yana kallon ta yana mata wasa, wanj farinciki yake ji, nan take ya hau mata hotuna, yana gamawa ya danna kiran Abban su Suwaiba, lokacin duk suna tare har Goggo Sarai, duk da ba wani sake mata kowa yai ba amma sun rage gudun ta, sallama yai ya sanar da shi haihuwar, cike da murna kowa ke amsar wayar suna gaisawa, amma Juwairah sam taqi karbar wayar wai kunya take ji, dariya suke ta maya Suwaiba tace sai gobe zasu zo, dik da mamakin dake zuwatan Jabeer Juwairah Da Nafee bai hana su suma sakewa da ita aita hirarn ba, bayan sun gana ne Juwairah ta dauki pilon da aka kawo mata dan ta zauna ta jefawa Jabeer, tana.buga qafa cike da shagwaba" ni baka fadan zaka kira su ba kawai sai dai naji kana waya, kuma wai Abbana ka fadawa na haihu, wayyo ni Allah da wanne idon zan kalle su?" " da idon da kk kallen a daki ki ka kuren su kina lumshe su a daka lokacin inaa....." bata san sanda ta miqe da sauri ta damqe bakin shi ba, tana kallon inda Nafeesa take cike da kunya , duka ta kai mai mai zafi a qirji,ya ko yi qara, Nafeesa ce ta fita tana ta dariya" Yah Jabeer Allah mun bata" ta tashi daga jikin shi zata tashi, saurin kamo ta yai tana tirjewa" A'a faaaa ba zan iya da shagwabar nan ba bayan kin san ke ba lafiya gare ki ba, ki hakuri dan Allah ba zan sake ba kinji" kama kunnen shi yai alamun ban hakuri,murguda baki yai ta tashi ta shige daki ta dau jaririyat dake kuka ta fiddo nono zata bata, ga shi ya qura mata ido qurrrr, tura mai tai gaba "ni wannan kallon ya ishen, tinda ka gama naka turn din this is hers pls let her enjoy ita" ta qarasa tana murguda dan bakin ta, sakama bbyn nono tai a baki taji wata azabar zafi na tsotso, janyewa zatai amma jabeer ya hana ta ta hanyat kai bakin shi nata, rasa wanne zata dauka tai, zafin bada Nonon ko kuma kiss din da take karba???? 


Makaranta ku zaba mata daya...... lolsπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚

[11/26, 12:35 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ   'YAN ABUJA.  πŸ’…πŸΌ


     BY HAERMEEBRAERH

Page 29:


Alhj kallane ya kalli Alhj salihu yace, " kai nifa ba qungiyar da zan bari, haba me akai da maza inji karuwa, har yanzu fa da quriciyar mu, ko hamsin bamu rufa ba, akwai sauran rayuwa gaba na tuba" " hmmmm Kalla knan kai abokina ne mun taso tare dakai, iyayen mu da yan uwan mu mun bada su ta wannan harka, kana ganin zunubin bai isa haka ba? Tin da ba yanda za ai mu dawo da su? Ka duba fa in bamu tuba ba yanzu kowanne lokaci mutuwa na iya zuwa, ita bata sallama bare qwanqwasa qofa in......" " malam dakata, yqu in da abin da kazo kenan, i am very sorry to disappoint you, cos i am not ganna buy this shit, akan me ina tsaka da jin dadin rayuwa ta kace na koma rayuwar talauci, bayan kasan sharadin fita daga qunyiya mai da duk abinda ka mallaka ne daidai da allura ba a yarda ka aje ba, me na tanada wanda ba daga qungiya bane? Haka sidda madalaqan kasa na koma almajirin qarfi da yaji, kan kuma ka fita karka manta sai an yi asiran rufe maka tinanin ka na gidan Oga zaks da qungiya gaba daya wanda a kallah zai kai nan da sati uku, kai ka san dan mun riga da an bamu daukaka a qungiya ne yasa akai mana wannann alfarmar da qananan yan qungiya ne kashe ka za ai ko tinanin nan kai, ni dai ina nan kai kuma Allah ya taimaka ka fita lfy, amma ka sani sisina ba zan taimaka maka da shi ba in ka talauce, abotar mu na nan har yauma ta nade" baza babbar rigar shi yai.ya fice ya bar Alhj Salihu da tinani, wata zuciyar na kwadaita mai ci gaba da rayuwar hutu, daya ban garen na nuna mai illar hakan, in ya ci gaba da zama dan qungiya yakai soyayyar Suwaiba inaa? Kaiii daya rasa abar son shi gwara ya hakura da qungiyar nan Allah zai kawo mai wata hanyar, miqewa yai, yana miqewa wayar shi ta hau ringing, dubawa yai yaga kiran Alhj Kallah, tsaki yai kamar ba zai dauka ba, dan abin da ya mai dazu ya sosai ran shi sosai, amma sai yandaga yaji ko ya canja ra'yi ne zasu fita tare, yana dagawa yaji wata muryar daban da bai san ta waye ba" waye kai ina mai wayar?" " ranka ya dade mai wayar Allah ya mai cikawa yanzunnan ya samu hatsari wanda gaba daya kan shi ya fashe, sannann qafar shi ta dama ta karye" " innalillahi wa inna ilaihirra ji'un" kalmar da yake maimaitawa kenan, ya kashe wayar ya zauna, qarar message ne yashi, cikin tashin hanakali ya duba sai yaga address din inda Kalla yai hatsari aka turo mai, kamqr wanda aka ma allura haka ya miqe yana fadin" Allah na tuba ka yafeni, Allah ka gafarta min ni Salihu  daga yau nai alqawarin tuba daga zunubaina na daina harkar nan ko zan rasa raina ne" kuka hake matuqa haka ya kai ga motar shi ya tada yai inda aka kwatanta masa, wayar shi ce ta qara ringing " Oga Zaks" shine abinda ya gani, tsaki yai ya daga" Salihu kaji abinda wani ta fadan? Kana ina yanzu haka, da gaske ne Kalla ya mutu?" " nima ban sani ba sai na isa wajen na gani, ka oashe na kusa isa ga mutane can dai an taru.a wajen sosai" kashe wayar yai ya qarasa, yanda ya ga abokin nashi take ya yanke jiki ya fadi, wasu je a gefe suka taimaka mai da ruwa ya farfado, yai wajen shi a guje yana kuka, riqe shi mutanen wajen sukai suna bashi hakuri, umarni ya basu akan su taimaka mai su daga gawar akai masallaci mafi kusa a mai wanka a binne, kawai dan basu da kowa, haka ko akai , waya ya zaro ya sanar da Oga zaks, jikin Oga zaks yai sanyi amma dake zuciyar ta dake ko kuka bai ba, sai dai ma kawai ya mai taaziyya ne kawai yace in an kai shi yaje yana son ganin shi, kashe wayat shi yai yace" ba dole ma na fita ba, ai ko ba komai Kalla yai wa qungiya hidima, ya cancanci azo kan gawar shi a mai addua amma wai in an kai shi na je, ko baka ce ba zaka ganni kuwa" share hawayen shi yai shima yabi bayan yan tsiratun mutanen da suka gama rife Kalla a makwancin shi na gaskiya,mota ya fada yai gidan shi, tattaro duk wata dukiya tashi yai, yaje ya dakko ATM cards din shi, da makullan motar shi, da takaddun filaye da gidajen shi kamfani da komai ya zuba a motar, ya sa kai, bai zame ko ina ba sai qofar gidan Oga Zaks, yana isa a ka ya tsaya ma Oga Zaks , " ya haka Salihu, zaka zo ka tsayan akai kamar wani sanda" " miqa mai komai yao da suke a wani akwati, ya ce" Oga ina son barin qungiya ba dan komai ba sai dan ina son na koma tsaftatacciyar rayuwa, abinda ya faru da Kalla ya qaran son barin qungiya" take ya kwarorowa Oga Zaks duk abinda ya faru da Kalla da shi kafin hatsarin da yai, nqn danan jikin Oga Zaks ya dau rawa, qaton cikin nan kamar ana buga ganga haka yake qara, maganganun sun shige shi sosai, " To salihu ba za ai haka ba ka fita kai daya, yau kuma a yanzu zan tara mutanen mu, na sanar da su, wanda yaga zai fita ya biyo mu dan nima fita zan, wanda yaga zai zauna ga waje, amma zan so yanda ni ne na assasa wannan qungiya na rusa ta, dan ko na tafi zunubin xai bini" wani dadi ne ya lillibe Salihu dan bai zaci hakan ba, ya zaci zai sha wahala kafin ya amince mai, waya yasa ya kira mutanen su,kusan awa biyu sika dauka kan kowa ya hallara, ganin fuskar Salihu da ta sha kuka ya badu mamaki, nan take ko Oga Zaks ya fara zayyana masu komai, cikin qanqanin lokaci wasu da dama suka aje makaman yaqin su, wasu kuwa suna ganin ai su akwai sauran lokacin tuba,tsawar da Oga Zaks ya daka masu ce ta dawo dasu daga cece kucen da suke ta yi" na yake hukunci wannan qungiya rushe ta zan, wanda ya sake kafata shi ya sani, amma ni kam na gama , dan haka daga gobe zan rushe ta, tsakanina da dodo ko kashe ni yai na kubuta da ikon Allah, fatana Allah ya gafarta min, ya ba wa wadan da na zalinta ikon yafe man a filin qiyama" sai ga Oga Zaks na kukan nadama, basu rufe baki ba suka ji gidan na wani irin qara, mai firgitarwa, haba mana xo kuga gudu, kowa na gudun ceton rai, Salihu ne ya ke qoqarin taimaka wa Oga zaks su gudu, amma ya dakatar da shi" Salihu kai ta kan ka kawai, ni nasan tawa ta qare, da wannan uban tumbin nawa kk tsammanin samun gudu a gareni? Ka dube ni fa ka gani nayi ka bakwai, ka barni kawai, abin da na aikata zan girba, i am willing to give my life for urs, coz i started  everything, i think it has to end with me, just go, run for ur lyf, and pls don't forget to pray for me, ask Allah to have mercy on me" tura Salihu yai da qatfi a daidai lokacin da wani qaton baqin zaki ya fito daga wani baqin daki, yayo kansu, Salihu diba yai da gudu ya bar wajen, Oga Zaks salati kawai yake, ya cika wando da fitsari shataf, tsoro da tashin hankali ya ganshi qarara, tinawa yai ashe haka wadanda suke ba dodon suke ji kan su mutu, take yaji qirjin shi na wani mugun bugu, cafka zakin nan ya kaiwa wuyan shi ya hau cinye shi, Oga Zaks kam an tafu inda Kalla ya tafi, Salihu kuwa gudu yake kamar me , mota ya gani da makulli jiki me ita wataqila tsabar tsorata ne ya hana shi ci gaba da tada ta, dan harda takalmi qafa daya a ciki, da alamar danshi a sit din, maybe fitsarin shima ya sakeπŸ€” take Salihu ya tada motar ya debi hanyanyat kano.

Sin gama gyara gidan tsaf, sun ma iyayen nasu girki, wanka sukai, suka gyara jikin su, jikin Suwaiba duk ba kwari haka take jin faduwar gaba, Saudat kam ita in banda sharar dakin su ba abinda ta tsinana, komai kusan Salma da Suwaiba ne sukai, gaban ta sai tsananta bugawa yake, amma sai tai ta maimaita addu'o'i a bakin ta, haka itama Suwaiba, bayan sun shirya ne suka dauki hanyat gidan Juwairah me jego, sun isa daidai Jabeer ya fito riqe da towel din da yake gasa mata jiki musamman cikin ta da bayan ta da shi, kallo suka bi shi da shi , saka makon ganin Juwairah ta fito tana" Ni dai gaskiya a canja min me yin wanka, kai gaba daya kamar ba wankan ne ke kai ka.......... " maganar ta maqale dan ganin yayun nata na shigowa, niyyar ta ta koma bandakin dan juyawa tai tare da damqe bakin ta, zata shige, Saudat ce ta ruqo ta da sauri tana dariya," Me Yah Jabeer din ke maki? In kina son a canja maki mai wanka sai na dinga maki, amma ni sai ruwan ya tafasa sau uku sannan zan amfani da shi" zaro ido tai waje tace" A'a Adda Saudat a barmin Yah Jabeer din mu lallaba a hakan" dariya suka kwashe da shi, Jabeer yace" kuji yarinyar nan fa,  wai zata lallaba a haka sai kace wani mugunyar nake mata" Nafee ce ta amshe da" Hmmmm Yah ai shiru kawai da wannan maganar amma ko dazu naji qarar ta" hararar ta yai yace " Suwaiba ku shiga ciki mana kuka tsaya a waje" shiga sukai har me jegon, Nafee ce ta miqe sakamakon kiran ta da Innar mu ke yi, zuwa tai ta bata wani kwanika biyuo ta kawo wa juwairah, amsa tai tai ta tafi bangaren juwairah, sallama tai ta shiga suna ta hira kowa na yava kyaun jaririyar da sunan ta" wannan suna na yan gayu anya kowa zai iya fada" cewar Salma, dariya Nafee tai da ta qarasa aje kwanon gaban Juwairah dake shafa man kade a cikin ta," ai jiya sai kun sha dariya dan daga Innar mu har Abban mu basu itmya fada ba" " ai ko wannan suna zan so jin shi a bakin Goggo" cewar suwaiba, dariya suka bushe da ita dikkan si sun san a kwai case dib fadan Abrar a bakin Goggo sarai, Juwairah ce ta gama shiryawa Suwaiba ta daure mata cikin ta, sannan Jabeer ya shigo dauke da plate da Spoon da cup sai tea spoon, gaishe shi sukai dika ya amsa tare da yi masa barkar qaruwar da aka samu, godiya yai ya isa gun kwanukan ya bude, farfesu ne na naman qaramar dabba, yasha kayan qamshi irin na jiya harda ridi, gefe kuma kabewa ce innar mu ta dafe ta tai laushi ta dame ta tai kamar kunu, sannan ta zuba maya madarar shanu mai matuqar yawa sai zuma, zuba mata yai a cup din ya zuba mata naman a plate, " oya maza taso ki ci ki shanye, dan bana son kina zama da yunwa" turo baki tai gaba, " ni fa na qoshi, dazu da asussuba na qarasa naman jiya saboda yunwar dana tashi da ita, yarinyat nan ci gare ta kamar Innar ta Salma" dariya suka dauka da dikkan su" ai ko baki isa qoshi ba da dan ragowar naman nan, in baki matso kin fara ci ba zan maki dura gaban su, dan dora ki cinya zan na maki irin na kwanaki" zaro ido tai waje sai gata a qasa ta saka pilo ta hade qafafun ta waje daya ta miqe su( haka ake so mai haihuwa tana zama, kai ko ba haihuwa ba a son zaman nan na ware qafa, kabewa da madarar shanu da xuma duk wadda ta hada ta zata bada labari bazan ce komai baπŸ™Š) kaiwa baki tai ta fara  ci dadin da ya ziyatce ta bata san sanda ta cinye ba ta shanye kabewar dika, " just like a gud gurl" kissing din gefen fuskar ta yai ya dauke kwanukan zai fitar Salma tai saurin karba, " haba yayah muna nan ai sai ka bar mana aikin in mun tafi ka ci gaba" muemushi yai ya sakar mata yace" ni bari naje.na shirya zan wuce Abuja yau zuwa qarasa shirye2n komawar mu bayan suna" anan ya sanar da su komai game da aikin da ya samu, murna suka taya shi , da fatan alkairi, fita yai yai wanka, ya dawo zai shirya Juwairah ce ta tashi taje, yna shiryawa suna.hira tana hada mai kaya a jaka, duk da hana tan da yau.sai da ta hada masa, bayan ya gama ne ya dauki Abrar ya mata addu'a yau kissing din ta ya hade bbyn da maman ya rungume, daidai ya sake ta yai gaba ne ya dawo" Af nayi mantuwa" " me ka manta honey?" Matsawa yai kusa da ita ya janyo ta jikin shi yana mata kallo qasa2," No no no u can't do this now pls, Adda Suwai ba is here, Adda saudat is here, and Salma too, pls kai hakuri har ka dawo, kasan lips dina ja suke kuma zasu gane, ni dai dan Allah ka daina bani kunya," ta fada tana yar kwalla dan ya kyale ta, lake mata hanci yai yana" mun kusa komawa gidna mu mu uku, mu yi abinda muke so" dariya tai na samun nasara, ta mai addua ta rako shi suna zuwa palo tai fuska ta zauna kamar ba tare suke ba, kunya ce da ita kamar me, dariya suka mata Salma tace " kinji da shi ciwon ajali a dan yatsa, mu zaki layancewa," dukan wasa ta kai mata tace" Adda Suwaiba kin ganta ko" dariya sukai" ya kamata ki rage shagwaba yanzu kin haihu," cewar Nafee, murguda mata baki tai ta kauda kai.
Ahj Salihu ya iso kano da kyar ya gane gidan su suwaiba....


.

[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA    πŸ’…πŸΌ


          BY HAERMEEBRAERH

Page 30:

Alhj Salihu ya iso gidan su Suwaiba da wajen bayan la'asar kadan, dai dai su kuma suna dawowa daga gidan Juwairah, daga nesa ta bayan da ya juya Suwaiba ta gane shi, ya rasa dan aike, kuma yana matuqar jin nauyi, kunya, da tsoron wacce karba za a mai, shin dalilin kafa kai da yai a jikin motar, wasu siraran hawayen nadamar rayuwar shi ke bin kuncin shi, ga rashin abokin shi da yai, kuma kusan a gaban shi zakin nan ya kaiwa Oga Zaks cafka a wuya, what if shima ya biyo shi? Ga Suwaiba da iyayen ta da 'yan uwan ta, maybe this is a bad idea for him to risk there life for his mistake, he was trying to walk away, when he hered her voice, calling out his name in a passionate way" Baby? kai ne?  Kai ne da gaske nake gani? What are u doing here?" Qarasawa tai da gudu ta fada qirjin shi tana kukan missing din shi da tai, shima rungume ta yai kamar wani zai kwace mai ita, gyaran murya Salma tai masu," Adda a waje kuke fa, kn san halin mutane, ba za ai tunanin mijin ki bane, za a fara qananan maganganu" janyewa sukai daga yanda suke taja hannun shi zuwa cikin gidan su ta tsaida shi a soro, Saudat kam ta qame qam a wajen, dan zuciyar ta bugawa kawai take, ina nata mijin? Ya akai suka rabu yau? Bayan ta san ba sa rabuwa? Wannan tambayoyin Salihu ne kawai zai amsa mata su bayan ya samu nutsuwa, dan ta kula shima ba a nitse yake ba, Salma da tai gaba ne ta dawo baya ta ja hannun yayar tata sukai ciki, ta kula da cewar Saudat na cikin damuwa tin safe yanzu kuma data ga Salihu shi daya ba nata mijin abun ya qaru mata, ko ba komai tana son mijin ta kawai halayen shi ne yasa ta gudowa taqi komawa, what could possibly happen to him? Sun riga sunyi Sallah gidan Juwairah dan haka bayan sun shiga sanar da Abban su sukai Salihu yazo ga kuma a yanayin da suka gan shi, a da Abban was furious, amma da Mama Bilki ta taishe shi, akan ya tafi cikin nutsuwa ya bude ma Salihu zuciyar shi yaji me ke tafe dashi, in yazo da rainin hankali gidan su yazo, ta bashi goyon baya ya mao duk abin da yaso, kada kai yai cikin qunan rai ya fita amma sai ya danne bacin ran nashi, kamar yanda matar tashi ta bashi shawara, Sallama ya mai ya miqa mai hannu amma Salihu ya noqe, ya durqusa qasa yana mai kuka mai ban tausayi," Abba ni mai laifi ne ba a wajen ku ba har a wajen Allah, babban mai zunubi ne,na taso ban san menene ilimin addini ba, duniya kawai na saka a gaba, bani da ilimin addini daya ratsa zuciya ta da zai hana ni aikata dukkan abubuwan dana aikata, dan son ka da Allah da Annabin shi ka yafen abinda nai wa Suwaiba, ka yafewa abokina diban jinin Saudat da yai domin ya mutu, a dazu kan na iso nan, ta hanyar hatsarin mota" wani qarar kwanuka da qarar Saudat ne ya dawo da su daga maganar da suke, faduwa tai a wajen a sume, da gudu Abban su yai kanta, ya daga ta yai ciki da ita, ruwa suka yayyafa mata, a hankali take bude idon ta, ya sauka kan Salihu da ya shigo ba izini, kuka ta saka ta kai mai naushi a baki, " mugaye azzalimai, kashe shi kuka ko? Dan na san yanda Kalla ke sona zai biyo bayana ko bajima ko ba dade, shine kuka kashe shi?" " Saudat you have to calm down, u get it all wrong, ni da kk gani ni na shawarce shi akan mu fita daga qungiya dan son da muke maku, da kuma tsoron Allah daya shigeni, amma Kalla ya qi, ya mun bayanin shi akwai sauran lokacin tuba, na mai wa'azi da in mutuwa ta riske mu kan tuban fa, yace akwai lokaci, yana fita yai hatsari mummuna, kan shi ya fashe qafarshi ta......." " Stop it ! Stop it !" Saudat ce cikin tsawa take hana shi qarasawa, tare da fashewa da kuka mai ban tausayi, a nan dai ya qarasa labarta masu komai daya faru har a wajen Oga Zaks, Goggo dake gefe da ta fito cikin bala'i taji komai, sai jikin ta yai sanyi, ta koma kwallar tausayin yaran ta, ba laifin kowa bane illa laifin ta, ba su taba sanin Saudat na son mijin ta haka ba, kawai ta gudar wa mutuwa ne sai yau, daga ta Mama Bilki ta sa Abba yai ya kaita dakin su, ya kwantar da ita, kuka kawai take, Mama Bilki ce ta shiga bayan Abban su ya fito" Saudat ki hakuri , na san rashin masoyi akwai zafi, amma soyayyar da zaki nuna wa kalla a matsayin shi na mijin ki shine addua, tinda bai sake ki ba kk qi komawa, dan haka daga yau zaki fara takaba, har tsawon wata 4 (hudu) da kwana 10 ( goma) dan haka har abada mijin ki na buqatar adduar ki, baya buqatar kukan ki, kinji" ta qarasa tare da shafa kanta, cikin sakewar jiki ta dora kan ta a kan cinyar Mama Bilki hawaye masu zafi na fitowa saga idon ta, nan take ta hau kwarorowa mijin nata addu'a, mama Bilki na amsawa, haka har ta samu sauqin zuciyar ta itama, Salma na maqale tana tina nata mijin tana hawaye, ga tausayin Addar nata da ya dame ta. Bayan yayi alwala yai salla ne ya kuma ci abinci Abba ya ce suje gidan Yayan shi,( gidan su Juwairere) tafiya can sukai, a motar da ya zo da ita, sukai wa Yaya Balarabe bayanin komai, ya gamsu sannan ya amince da mijin Suwaiba zai zauna a shagon gidan har Allah yasa su Jabeer su koma Abuja sai su su zauna a bangaren su, Abba godiya yai wa yayan nashi, ya koma gida, in da Yaya Balarabe yace, zai fara koya mai ilimi na addini dan ya na da qarancin shi, godiya yai sosai, Nafee Abban su Jabeer ya kira ta gyara shagon, aka shimfida mai yaloluwar katifar da wankakken zanin gado da pilo, sai yar sallaya, da buta, da ruwa mai kyau a bokiti rufaffe, Abban su yace in yana buqatar zagawa zai iya shigowa cikin gidan, godiya yai ta musu kamar zai kwanta, zuciyar shi cike da tausayin rayuwar da zai koma, sannan qasan ta kuma cike da murnar ganar da shi gaskiya da Allah yayi.Yau kwana tara kenan da haihuwar Juwairah, anyi suna, suna ya qayatar, dan Jabeer ya yi qoqari sosai, ga akwati nan biyu da yai ma mai jego da jaririya, daya babba daya qarami, gobe suke son komawa Abuja, dan wajen aikin na buqatar Jabeer, sun gama kwasar duk wani abu da zasu dauka, sauran kayan zata barwa Addan nata da mijin ta, a haka taje gida taiwa Saudat ta'aziyya ta kuma yi wa iyayen ta sallama, ta sha kuka kamar wadda za ai wa auren dole, da kyae suka lallashe ta, sai da taga Jabeer ran shi ya baci da kukan ta sannan ta hakura, sun dawo gida bayan Isha'i Nafee idon ta ya kumbura saboda kukan rabuwa da bestyn ta kuma yar uwar ta, sannan matar yayan ta da ke son ta,Innar mu ma ba a barta baya ba wajen matse kwalla,tana qara bawa Juwairah hakurin zaman da sukai a baya, Baba Balarabe ma jikin shi sai da yai sanyin rabuwa da Juwairah, dan yarinya ce mai shiga rai matuqa, da kyawawan halayen ta, da kuma iya zama da mutane, a haka aka kwana gidan kowa da abinda ke ran shi.

Washegari da sassafe, Jabeer da Juwairah dauke da Abrar suka fito suka shiga sabuwar motar Jabeer zasu tafi, Nafee ta riqe hannun Juwairah tana matsar kwalla, Jabeer ne yace" My little sis ki yi hakuri,kwana nawa ne zamu qara dawowa, ran da fa Saudat zata fita takaba ranar za, a fara bikin ki ko kin manta, dan haka ki kwantar da hankalin ki, sannan wataqila ma Salma ta haihu kafin nan zamu zo, kinji Sweery," hawayen ta ta share, tai masu adduar tafiya lfy su da samun sa'a da nasara,Innar mu sa Baba Balarabe ma haka, sai mijim Adda Suwaiba dake gefe shima yana masu fatan alkairi, motar ya tayar sukai gaba, cike da kewar juna, Salihu gaba daya ya canja, fatar shi tai duhu, tumbin nan ya sauka,sai kyaun shi ya fito, ashe yana da kyau yaci kudin haram ya gina tumbi tulele ga kumatu kamar nawa( lols just kidding nawa mai kyau neπŸ™„πŸ˜Ž)πŸ˜‚ tausayin shi ne ya kama Baba Balarabe ganin yanda ya koma a qasan ran shi kuma yana ayyana ko zasu fara zuwa kasuwa tare ne wanjen gwanjon su da shi ne? Bayan su Innar mu sun shiga gida ne ya same shi ya mai wannan tayin, cikin jin dadi ya amsa da zai yi ko meye in dai halal ne ba damuwa, qasa yai da murya da kan shi" to Baba ai ban da jari kuma" " kar ka ji komai, akwai jari a wajena ,ko da dubu biyar zaka iya farawa mu gani" godiya yai ta zubawa kamar me, Baba Balarabe da yaga ba zata qare ba dariya yai ya shige cikin gidan ya bar shi anan,.
Suwaiba ta tare da mijin ta,kuma kasuwanci ba laifi wataran a samu ya siyar da kayan dika, ribar dubu biyu ko ukuma, wataran kuma su ragu, a haka shi da ya fara da capital na five thousand yanzu ya kai seven thousand, ai an samu, kuma a ciki yake qoqarin ci da su.
Salma da Huwaila kusan ta tare suka haihu, Salma ta haifi Yaran ta biyu masu matuqar kama, da kyau, ita kuma Huwaila ta haifi namiji, mai kama da Bangis sak, kwana tara ne a tsakanin su,yaran Salma sun girmi na suwaiba, an yi suna in da akai suna ba komai a dukka gidajen sai to gwanda na Salma ma, dan anci an sha,mutane ne dai ba su zo ba sosai, ita ko Huwaila , komqi qayau sikai sunan nasu, ga habaici da suke sha wajen yan gulmar da ke zuwar masu barka da kuma wanda suka zo sunan, yaron Salma na mijin An sama mai Muhammad, macen Fateema,a hakan suke kiran su, sai yaron Huwaila da aka sama suna, Umar, rayuwa tai ta juyawa wadannan bayin Allah da dadi ba dadi duk haka ake ta fama, wanda kusan ko ina ne dama yanzu a wannan lokacin haka ake ta fama, in da gidan Baba Balarabe ya bunqasa da arziqi dan Salihu ya shiga gwanjo da sa'a sosai, yanzu har dila biyu yake budewa, Juwairere kam arziqi ba a magana sai godiya, gidan su mai kyau daki biyu da dinning, sai babban palo, mai dauke da manyan kujeru da kayan kallo, yarinyar ta sai wayo take.
Shirye2n bikin Nafeesa ne ya kama gadan gadan, in da Saudat kuma sauran kwana uku kenan ta fita takaba, a yau din ne su Juwairah da Jabeer tare da diyar su Abrar za su zo, Jabeer ba qaramin qoqari yai ba a yan watanni biyun, dan ita Juwairah bama ta sani ba tinani take in sun je ina zasu sauka, bangaren su yanzu Adda Suwaiba ne a ciki, bata da masaniyat daki daya da bandaki da palo madaidaicin da Jabeer ya masu a filin dake gefen gidan su wanda yake kamar kango je a da, sai yar tsakar gidan qarama sosai ba wani fili sosai, ba laifi a irin gidajen cikin gari a kano wannan yayi kyau, sai wajen azahar suka iso, wajen Innar mu ta shiga, Nafee da gudu ta je ta rungume ta suka hau murna, bayan sun natsu ne ta miqe aka hau gyara amarya da ita.....*Juwaireren mama na gayyatar dukkan fans din novel din 'YAN ABUJA zuwa wajen bikin Nafeesa, Allah ya bada ikon zuwa ameenπŸ˜‚*

[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA    πŸ’…πŸΌ
       BY HAERMEEBRAERH

Page 31: A yanzu hankalin Talle ba qaramin tashi yai akan ya nemo Salma ya bata hakuri akan abinda ya mata, dan yasan tinda ya sake ta, ga ciki tabbas tana nan qullace da abinda ya aikata mata, kuma baya fatan ma.yace zai maida ta, saboda ba zai iya riqe ta ba yanda ya kamata, ba irin rayuwae sa salma ke.mafarki ba kenan, " Ya Allah ka bata ikon yafe min a duk sanda na bayyana a gaban ta ina mai neman yafiyar, ko bam samu zuwa ba na mutu.Allah ka wakilci ce ni a zuciyar Salma ta yafe min" " Haba Talle, sai yaushe zaka daina zubda hawaye ne? Na baka shawara mu kama akuya daya mu siyar, ka samu na mta dana guzuri, kaje wajen yarinyar nan ka nemi yafiyar ta, amma ka kafe kace a'a to taya kudin zasu samu? In aka siyar nima ba sai na samu na kafa wani jarin ba? Ko dari dari biyu muke samu a rana a matsayin riba ai zamu toshe wata gabar, balle nasan zamu samu yafi haka, ga tashin hankalin batan Haule, duk da ina kyautata zaton gajiya tai da halayen mu ta gudu wajen mahaifiyar ta, amma abun na matuqar damuna" " ta zancen Haule kwantar da hankalin ki, ta na wajen mahaifiyar ta, da kyar suka amshe ta, amma yanzu baki ga gatan da take sha ba, abokina da yamin hanyat auren babar ta ta ne ya ke sanar sani hakan, yana mun godiyar kyautawa da nai na barta tazo taga mahaifiyar ta" " Allah sarki, a gaskiya mun tafka babban kuskure a rayuwar mu Allah ya bamu ikon gyarawa, me zai hana ka samu a islamiyyat malam Sallau kaga ana karatu kyauta, awa biyu zamu bayar a a kwana uku kawai, dan akwai jahilci mai tarin yawa a rayuwar mu, kai kuma ka na zuwa ta bayan isha'i kai da Yaya" " gaskiya kin kawi shawara dan abubuwan da muka tafka da da ilimi a tattare damu musamman na addini da bamui ba, Allah ya yafe mana" " Ameen" " ina yarinyar nan Hawaila? Ki taran su har Baban gidan zuwa anjima za ai maganar auren ta, gobe juma'a, suna da daki, a bangaren su, da katifa dan haka ban ga dalilin ta ci gaba da zama a gaban mu ba ko me kk ce, kin ga a hankali muka samu sai mu mata kayan daki kamar kowa" " wannan shawarar tayi, tin da ga yaron su nan Umar Allah ya bayar gwanda ai auren gobe komai ya wuce,Allah ya sanya mana albarka dikkan mu, ya yafe mana" " Ameen, na gode maki da kk canja halaye daga munana zuwa kyawawa, yanzu kyaun ki ya fito matata, nima ina fatan kin ji dadin canjawa ta?"ya fada yana mai matsawa kusa da ita, ita kuma tana wani sissine kai, wai kunyaπŸ˜‚" naji dadi mana Talle sosai, nan gaba ma swatyn nima zan dinga kiran ka irin yanda kk cewa Salame" dariya ya kwashe da ita ta gane inda ta dosa ( Sweety) shine abinda take son cewa.


Da yamma za a tafi dinner kowa ya sha gaye hae ya gaji, ba a cika wa Nafee irin kwalliyar nan ta yanzu ba,ta dai sha powder da kyaran jikin da ya fito da kyaun ta, ( aikin Juwaireren mama kenan) ba qaramin kyau tai ba, sun so kwarai a aske mata gira ai shaping din ta amma Juwaireren mama ta hana, domin hakan haramun ne, tinda akwai abinda ake yi a danyi dabara kamar an yi shaping din, to gwanda ayu hakan, aiko nan take Adda Suwai nonoless aka dauk ma Nafee kwalliya, ta yi matuqar kyau, haka Saudat sa Salma maman yan biyu, Yaran su ma sun sha gayu, ga qamshi dake tashi a jikin su mai ni'ima kowa son daukan su yake, Shamsiyya, Innarmu, Goggo Sarai Mama Bilki da sauran dangi sun sha kwalliya suma, amma ance ba za a je sa iyaye ba, nan fa Goggo Sarai za a fidda halin "ni dai gaskiya ko su Bilki ba zasu ba ni a tafi dani, dan nasan irin wajejen nan akwai kwalama" wani kallo Suwaiba ta mata, " Haba Goggo har zuwa yaushe zaki daina wannan halayen ne?" Sinne kai tai tace" Yannan wasa dama nake ina ni ina zuwa wajen matasa" kuma a qasan rai dai ana son zuwaπŸ˜‚fita tai daga dakin tai wajen masu soyawa amarya kaji da za a tafi kaita garin Kebbi, dan hanya akwai nisa, ba tsaywa siyan abu a hanya zasui ba, kuma a cikin garar ta Jabeer yace a saka harda kajin, can ta nufa tace" wannan biki nanarziqi ne in ban ci a wajen ninner din ba na ci anan"( dinner). Kada kai Salma tai da taji me take fada, mai hali baya sake hali sai dai ya lafa,in dai abun ya shige shi. 

A wajen dinner wajen ya qayatu angon Nafee ba dai kyau ba shima, sai dai Nafee ta fishi kyau da dan haske, tin da suka isa yaran  Salma na wajen Suwaiba nonoless, Salma sai ta fito kamar budurwa ba mai jego ba, kyaun Saudat kuwa itama ba a magana, anan abokan ango da suke zaune kusa da shi suka qura masu ido kamar zasu sace su gudu, ana tsaka da rawa da shagalin biki ne suka taso, da dukkan alamu gidan su daya, dan kamannin da suke da shi, Sallama sukai, su kuma sika amsa, Juwairere da Adda Suwaiba tashi sukai,suna masu murmushi, su kuma suka zauna a wajen da suka.tashi din, Saudat jikin ta har rawa yake tana son barin wajen, dan a zuciyar ta nan take ta tino da Kalla, dayan e yace" Haba sarauniyat kyawawan duniya ina zaki, bayan ga sarkin ki ya iso domin ya dauke ki ya kai ki masarautar masoya?" Murmushi tayi, she us so nervous, ji take kamar ta zura da gudu, Oh duniya yau Saudat ke jin nauyin mazaπŸ€”πŸ˜Ÿkomawa tai ta zauna, tana ta wasa da hanun ta, dayan ne yace ma Salma," Angel,  da farko ni suna na Salmanu,kuma aboki ga ango, wannan yaya na ne, farouq, tin da kuka zauna anan muka sa idon mu ana ku mukaji ba zamu iya barin ku tafi ba tare da mun isar da manufar mu ba, dan da dikkan alamu ku yan uwan amarya ne ko," cikin nuna kulawa Salma ta kalle shi dan itama sai taji ya mata," Eh mu yayun ta ne, amma bayin Allah ba ku sammu ba baku san ya muke ko rayuwae mu take ba kawa sai ku fara isar da manufar ku, to da farko dai ku duba kuga wadan can yaran na hannun yayata"duban su suka kai wajen suka ga kyawawan yaran, sannan suka dawo da kallon su suka fada mata sun gani, ci gaba tai da magana dan bata son abinda zai karya masu zuciya gaba dayan su gwanda ai maganar gaskiya,dan ta kula dikkan au samari ne basu taba aure ba," to yam biyun nawa ne ni na haife su, amma aure na ya mutu, ita kuma wannan yayar tawa, mijin ta Allah yai mai rasuwa ne,a yau ta fita takaba," cikin mamaki da tausaya wa suke kallon su,dan duk yanda akai mijin daya saki Salma na da tabin hankali ko shafar aljanu, hauka ne kawai zai sa kana da mace kamar wannan ka sake ta, nan take sukai wa Saudat ta'aziyya sannan farouq yace" a gaskiya ni har yanzu ina ciki kaifa dan uwa? Dan ba zan taba barin wannan tsaleliyar ta wuce ni ba zan a sara mai yawa, domin da dikkan alamu akwai tarbiyya awajen ku" a sannan Saudat tai magana" yanzu dai kui hakuri zuwa a gama biki da komai sai kuje gida ku samu mahaifin mu akan komai, dan as for me kam wanda na san haka yar uwata ma, sai abinda mahaifin mu ya zaba mana" godiya sukai sosai kuma suka qara tabbatar da taebiyyar su, karbar No wayar su sukai, sukai sallama suka tafi, Adda Suwaiba ce ta dawo ita da Juwairah, suna zama Salma ta labarta masu komai, suna cikin addu'ar neman zabin Allah ne Muhammad din Salma ya hau kuka, kuka yake sosai har Salma ta rude kamar za tai kukan itama,miqo masu hannu suka ga anyi"hey little buddy come here" Salmanu ne ya karbe shi  kamar  yaron da aka bawa chocolate nan da nan yai shiru, jijjiga shi yai ya tafi wajen yayan su suna ta hira da sauran abokai, wannan ya karbe shi wannan ya karbe shi, a haka daga baya Salmanu ya karbe shi, har yai bacci a kafadar shi,cike da so Salma da yan uwan ta ke kallon shi,an gama komai za a tafi gida ne ya iso, ya miqa mata shi, godiya tai ta mai, yace" ya kk man godiya ne dan uba ya kula da yar shi ai ba wani abu bane" murmushin jin dadi tai idon ta cike da kwalla ta gyada kai tai gaba, bayan sun fita ne suka fuskanci basu da abin hawa zuwa sukai kowa da motar shi, ya zo ya faka, Yaha Jabeer ya iso dan daukar matar shi da su ne ya samu labarin komai wajen Juwairah, murmushi yai yai fatan alkairi yace mata shige to mu mu tafi dan kinga sun isa gare su nasan kuma gida zasu kai su, nima a gajiye nake, wanka nake so mai dumi,ko na murmure" murmushi tai tace "Hmmm Abu Abrar kenan na gane in da ka dosa, to yau kam a very big N-O to u saboda i am so exchausted" dariya yai yace "we shall see then, i know u can't resist my charm"yana wani kashe mata ido daya, kauda kai tai tana muemushi, dan tabbas ta bakin nashi ne, ya san abubuwan da yake ya kwace mata dikkan lissafan da take da shi....... *Nafee tace a fada maku tana godiya da zuwa biki, amma 'yan maermue group da suka je sukai ta dibar kaji suna boyewa, su raba da sauran wanda basu je ba, musamman Mum Sultan Bizzy Aisha, da Roumio, a canja hali malamaiπŸ™„*

[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA    πŸ’…πŸΌ          BY HAERMEEBRAERH*I dedicated this page to all my Kebbi state people,  i heart u guys, u are wonderful, and kind, wish to came back soon inshaa Allah, Missing you bahut bahut*❤❤❤❤Page 32:'Yan kai amarya basu tafi ba sai wajen qarfe 12 na rana, Innar mu ta sha kuka, Nafee mai son gida kamar me, ranar tun tana kukan sai da yakai ta gaji ajiyar zuciya kawai take lodawa, sai kace wacce za ai wa auren dole, kowa sai da ta bashi tausayi, Salma ba ta samu zuwa ba haka ma Suwaiba, Saudat ita aka wakilta a madadin su, sai Mama Bilki, wadda cancanta ce ta sa aka zabe ta a masu zuwan, tinda ita Goggo Sarai har yanzu bata da tinani masu kyau a kanta banda wauta tai mata yawa, sai girman shekaru da jiki kawai ta aje, tana jin zafin rashin tafiya da ba ai da ita ba amma haka ta jure, Juwairah ta so matuqa ta je amma Abrar ta sha gajiyar biki bata da lafiya dan haka Jabeer yace ba inda zata, tayi kuka kamar me, amma haka ta hakura ba yanda zatai, wasu mata suka dauka biyu daga bangaren su Abban Suwaiban wato Goggo Karima da Goggo mero, sai ta bangaren Innar mu, suma biyu, Innar Fateema, da Inna Aishe, sai wata aminiyar Innar mu wato Baba Maryam, ba su isa kebbi ba sai takwas na dare, gaba dayan su jikin ta qaura yai la'asar, tun Nafee na irin abun amaren nan a mota tini ta janye mayafin a fuska ta sake, tambaya ko tafi nawa tana ma, abokin angon dake tuqi, dan motar daga ita sai abokin angon dake tuqa su sai wani a gefe sannan ita da angon, mota uku sukai, janyo ta mijin ta yai jikin shi ta kwace a kunyace tin suna Gusau, da wahala tai wahala da kanta ta dora kanta jikin shi ta sha baccin ta, ko da ta farka ta zaci zataga sun kusa isa amma taji shiru, kai na taqaice maku sai da Nafee ta matse kwalla, tinanin ta daga Kebbi Nigeria ta qare,lokacin da suka isa ana ta kiraye2n sallar isha'i ne, suna zuwa gidan dake unguwar Alieru Quaters, a bangaren Three bed rooms a nan aka aje ta, fasalin nasu gidan daban ne dana sauran, ya tsaru iya tsarin zamani, kana kallo zaka san gidan masu hali ne, yan uwan ta kam sai san barka suke, da mata  addu'ar Allah ya zaunar, kwanan su biyu aka tashi juyowa da su, Saudat kuka tasa data tuno hanyar da suka kwaso, sai lallashin ta ake abokin angon daya tuqo su yana ta mata dariya" a gaskiya zan fada ma Umar farouq ya shirya matat shi raguwa ce" ai tana jin haka ta miqe ta goge hawayen ta tare da zabga mai harara" inji wa? Ni kar ka wani fada mai mu tafi" dariya aka saka dukka wajen banda Nafee da take rabe a gefen mijin ta tai kalar tausayi, ai ko suna sa kai ta fashe da nata kuka, bayan sun fita ne suma suna cike da tausayin ta angon ta ya dauke ta cak yai ciki da ita yana lallashi, su Saudat sun kama hanya sun baro nafi, wajen mijin ta mai matuqar so da kulawa, tare da tausayin matar shi, dake tashin qarfe bakwai da rabi sukai sun iso kano qarfe wajen uku na rana ne kowa sai da aka aje ta gidan su, drivern daya kawi su Mama Bilki ne ya tsaida Saudat, " ba daban Farouq ya rigani ba kuma yana matuqar son ki, tabbas dana kawo kaina nima, amma ba zan iya tafiya bam sanar dake sirrin dake raina ba, na kamu da son ki a kwanakin nan da mukai kusan wuni a tare daku, ina maki fatan alkairi, Allah ya baku zaman lafiya da zuria mumina saliha" taji dadin fahimtar shi da kuma yabawa da hankalin shi sosai dan haka ne ma yasa tace mai," na gode sosai da siyayyar ka  a gare ni, ina ma ka fatan alkairi, Allah ya baka wadda ta fini, tabbas abotar ku akwai amana kuna da halin manya," murmushi sukai sannan daga baya ya mata sallama ya ja ya tafi.

Kwana biyar tsakani, bayan waya da musayar  saqwanni dake tsakanin masoyan hudu, sai gashi wata lahadi da yamma, wasu dattijai suka zo gidan Abba Baballe, da nemawa Farouq da Salmanu auren su Saudat din, a wasu maka2n motocu suka zo, wanda yasa Abba jin tsoron kar a maimaita yar gidan jiya fa, amma saka makon bayani da suka samu shi da Baba Balarabe, da kuma shaidu sun tabbatar da cewar tabbas mutanen kirki ne, a nan take suka roqi arziqin a daura auren in ba damuwa, saboda ba a kusa suke ba, kowa da garin da yake aiki, shi Abban su Farouq mazaunin Abuja ne, sai qanin shi dake lagos, dayan kuma a kebbi yake, Abba Baballe sawa yai a kira wani kawun su daya rage masu da abokin shi babba, nan take aka daura auren su Saudat da Farouq, Salma da Salmanu, akan sadaki dubu hamsin hamsin, tare da alqawarin Salmanu zai riqe yaran Salma kamar nashi in sun masu izini, su Abban Suwaiba sun yarda amma sun qara da cewa in ba takura, suka jaddada masu, cewa shi Salmanu ba Salma kawai yake so ba, har da Yaran ta ya gani ya kamu da qaunar su dika, Abban Suwaiba yaji dadin hakan sosai, a haka taron ya tashi cikin farin ciki da yarjeje niyar sanda Amaren da angwayen suka shirya a tsakanin su ayi tarewa.
Bayan wannan daddadan labarin ya iske su Juwairah ne ta roqi Jabeer akan ya barta har tagama batun tarewar Yan uwan ta kan ta koma, ya amince amma shi da yamma zai koma Abuja sabida aiki, sun bari akan in ta kammala ta sanar da shi sai su koma tare, kudi ya bar mata mai yawa a hannun ta kan ya tafi, tin kan tafiyar kuma sai tai tajin ba dadi zai tafi ya barta, bata son abin da zai raba ta da mijin ta , musamman wannan bata san kwana nawa ba zai dauka, shima gaba daya bai som rabuwar tasu amma dole ya qarfafa mata guiwa , haka suka rabu kowa na kewar dan uwan shi. Ta dawo daga raka shi ne taji wayar ta na ringing dake kan fridge din ta, dauka tai taga Nafee ce, bayan sallama da gaisuwa ne tare da tambayar bayan rabuwa Nafee tace" matar yaya kunyi min mntuwa fa, kun manta tsimi na ba a sako da shi ba" " Subhanaka ya raheem, ai ko kinga har yanzu ba wanda ya kula, ba damuwa ai kinga yanda na hada maki wancan, ki hada wani wannan na ba su Adda Saudat, keee an daura auren su ma jiya, tarewa kuma ance ba yanzu ba sai sun shirya magana da mazajen su, iyayen sunce basu buqatar komai sai matan yaran su za a kai masu" cikin murna Nafee ke addu'a, bayan gama murnar ne tace" nifa matar Yaya na manta wasu abubuwan dan sake fadan mana pls" " kai Nafee ko angon ya kwashi romo har da basirar ki ne?" Dariya sukai Nafee tace cikin shauqin son mijin nata" matat yaya wato My love daya ne tamkar da ba iyaka acikin maza" " Oh ni Juwarah yarinya ta fitsare bari nayi na gama fada maki na kashe wayata, ina nan ina tausayin ki ashe ke kin gama.zama yar hannu ma abin ki, " dariya sukai tayi kafin Juwairah ta lissafa mata kayan hadawar da suka qunshi" kanin fari kadan zaki saka ba mai yawa ba saboda masu magungunan gargajiya sun tabbatar da shan shi da yawa na kawo ciwon hanta, dan haka ki saka kadan sai citta mai dan yawa, minannas, sai ki matse ruwan rake mai yawa, ba a qara wani ruwan fa da wannan ruwn raken iya adadin yawan dakk so da shi zaki amfani, sai ki samo zuma mai kyau sosai ki saka sai ki dake kayan qamshin nan ki saka a ciki, sai kin ga yai kauri kadan ma'ana bai irin ruwa tsululu ba, zumar ce zata saka yai kaurin, ki dinga sha da yamma,amma pls wajen nemo zumar ku tabbatar me kyau ce kin san yanzu an bata zuma, na ba su Adda saudat wannan nakin nima na dan sha" " na gode matar yaya sai an jima ki shan fan bbyna, ina gaida yaya" nima ina gaida angon ki" .
Wahse gari sallama taiwa Innar mu ta tafi gidan su ba zata dawo ba sai an gama tarewar yayun ta, ta kaiwa Yayun nata wannan tsumin, sannan tun da suka fada mata mazan su sunce ai nan da kwana biyar za a kaisu su tare, nan da nan ta hau taya su gyaran jiki kala2, sai ga su sun fito amare sak, itama sai da ta gyara dan a cewar ta itan ma amarya ce, tin da taje, take ma su kwadon zogalen daya sha timatir dahuwar ruwa2 haka take kwashewa, timatir mai yawan gaske take saka masu gulin yaji kayan qamshi,(wannan hadin ga masu son hips din su ya fito zasu na ci sosai har su samu biyan buqata ko su saka zogalen a danyen shi bayan sun wanke shi sai su mai hadin, sannan ana iya yin hadin da alayyahu ma) sannan ta samu kabewa tai ta hada masu da madara da zuma suna sha,( wannan kuma yana gyara masu skin din su ba kadan ba)lokaci ne na mangwaro ta dake da siyo masu mangwaro suna sha ba qaqqautawa( mangwaro na qarawa mace ni'ima sosai da dumin jiki)  ga tsarki da hadin ta na musamma da baya wuce ta, isu isu suke abin su, Goggo Sarai gaba daya jikin ta yai sanyai,bata taba nadamar rayuwa irin ta yan kwanakin nan, ganin cewa tabbas Allah shine mai yi ba mutum ba, duba da cewar gashi dai duk bala'in son kudin ta, ta kai yaran Abujar kuma sun wahala, babbar ma har da nakasa, finally gashi yanzu Allah ya basu ' YAN ABUJA na kwarai, hawayen da take qoqarin mayar wa ne wani ya gangaro," Yaya ki daina kuka, in yaran nan suka gani zaki daga masu hankali" " Hmmm Bilki dole abun ya damen, bam zamo uwa ta gari ba, na tsani rayuwa da turbar dana dora yarana akai a baya" " haka ne Yaya kinyi kuskure babba, amma yanzu ai ya wuce, ya zama tatihi,kuma in shaa Allah hutun da kk nema masu su ji shi," cikin gyada kai da yarda da maganar ta ta dauki kwanon abincin ta isa dakin su ta miqa masu ta fice..........

[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ     'YAN ABUJA    πŸ’…πŸΌ       BY HAERMEEBRAERH
Page 33: 


Washe gari angwaye zasu zo tafiya da amaren su, su Goggo Karima dai ana nan sune yan rakiya Abuja, yau shiga kasuwa, su kai har Juwairah,kudin da angwayen suka basu na siyan kayan lefen su da basu samu damar hada masu ba shi suka je suka hado, bayan sun gama ne sika fara siyan  kayayyakin da in sunje zasu buqata wajen gyaran jiki ko ni'imar su, wadan da suke ganin ba samu zasui da sauqi ba a can, musamman hadin kayan qamshin da Juwairah ta basu shawarar niqa mai yawa su tafi da shi, dan ko shan shi da madara da zuma, zasu buqata, a gefe daya Juwairah ta lodarwa mijin ta kayayyaki kamar dangin qanan kaya, vest, boxers, da turaruka, sai takalma, da huluna biyu, masi kyau sosai, mamaki ne ya kama su suka kasa jurewa sai da Saudat tace" ke kuma ya naga kina ta siyan kayan maza ne, baki saiwa kanki komai ba sai tirare da kayan bacci," " Adda Saudat Yah Jabeer na debarwa, ba dan komai ba sai dan yanda shima yake man dukkan hidima da qarfi da iyawar shi, na sani komai zan mai ba kamar ya shi ba ne, sannan wannan abun da na siya already yana da su, amma kyautata wa juna na qara soyayya, kyauta tsakanin miji da mata musamman irin wannan ta tiraren da miji ya fi so, tana da matuqar tasiri a zuciyar namiji, shiyasa naga ya dace tinda ya wadata ni da kudi shima na sai mashi" " lallai Juwairere ke kin ma fi Mama Bilki iya tattalin miji, na rasa waya koya maki, ko kayan baccin ki da tiraren ki is for his on benefit" dariya sukayi" Salma ai gaba kin ga in ya tashi bani zai ban wanda yafi wannan tinda yasan ko me zan duk inda aka je aka dawo zai amfana shima in one way or another" tafiya suke suna jinjina wayo irin na qanwar tasu, a sama sukaji muryar ta"Adda Saudat ku daina mamaki na, kowacce mace tana da kaifin hankali da basirar zaman gidan miji, bambancin mu shine wata tana shiga kwakwalwa da zuciyar ta tai tinani, ta mafana da baiwar ta wasu su amfana, wata kuma dunkufe kanta take, bata son yin dogon tinani sam, bama ta son tana zurfafa tinanin ta akan komai, da matsala ta same ta sai tace sai ta nemi shawarar qawa, wani lokacin ai sa'a ta samu shawar qwarai wani lokacin sabanin haka, amma in da zamuna bude zuqatan mu da maza su ji dadin zama damu, aure daya rage mutuwa, da hakuri da sanin ya kamata ya wanzu gidan auren mu, Adda muna a garin da ba mu da iyaye acan mu ne iyayen junan mu mu zamu taimaki kan mu, dole sai mun zama masu irin wannan tinanin gudun shiga matsala kan dayan mu ya kai mana agaji" wani kallon so da qaunar qanwar tasu ke yawo a zuqatan su, a haka suka samu abin hawa bayan an masu niqan kayan qamshin, gida suka nifa a gajiye, wajen bayan azahar, alwala sukai sukai sallah, sannan sukai wanka suka ci abinci, sai baccin gajiya.

Tin da sassafe angwaye suka jera mota uku Jabeer kuma ya dakko hanya shima amma bai iso ba Adda Suwaiba da Innarmu sun zo suma,  amare ana ta dan koke koken rabuwa da gida, Saudat kuwa tsoro ne fal cikin ta na komawa Abuja, ji take kamar ta fasa auren, amma ta dake, tana son tai wa mijin ta kyakkyawan zato,  Adda Suwaiba anyi anyi tai rakiya tace ita da Abuja ko a film ba ta so taga Alihu a can ba, haka aka hakura aka barta she will come around wataran zata je ne, Jabeer ne ya iso, inda nan kai tsaye gidan su Juwairah ya sauka, ta sauke shi da abinci da komai na motsa baki, Amare sun daga sun bari akan in sun je zasu nemi gidan su, tin da Jabeer bai huta ba, haka suka tafi Goggo Sarai na ta zabga masu addua da Abba sannan Mama Bilki, kwalla kawai Goggo Sarai ke sharewa , bata san wannaj karon me zai faru ba," Adduar fatan alkairi zaki bisu da ita, ki daina zurfafa tunani, ki masu kyakkyawan zato Yaya," " To Bilki Allah ya kao su lfy, Allah ya zaunar da su da alkairai marasa yankewa" amsawa dukkan si sukai da" Ameen" suka koma ciki, inda Jabeer na dauke da Abrar, Ammar na wajen Suwaiba tana ta mai wasa, dan ya damu sosai da rashin Adda Calman shi,  fitowa tai zata debo mai dambun naman da ya ragu a kitchen wanda akaiwa amare, giftawar ta Abrar ta gani ta ko sa kuka tana miqa hannu, komawa tai ta dauke ta, Yah Jabeer na mamakin soyayyar su, " haka suke , in dai Adda Suwaiba na kusa to pa ni na huta,sai mu yini ko Nono bata nema, sai dai tai ta bata kunun ta" " ikon Allah lallai akwai soyayya mai qarfi a tsakanin su", gama wa yai suka shirya komawa gidana su,inda suka tafi da Suwaiba itama, a motama Abrar na hannun ta, tayi bacci, sun isa gida Suwaiba da Innarmu suka tafi bangaren su , suma suka tafi nasu gidan, a hankali ta dorawa Juwairah Abrar a cinya amma juyawa tai ta qanqame ta, sai Jabeer ne yai dabara ya raba su, tafiya tai cike da qaunar yarinyar a ranta tana share hawayen baqin cikin rashin haihuwa, shafa marar ta tai daidai lokacin da ta shiga bangaren su, hawaye na fita mata masu dumi, Salihu ne dake gidan a zaune ya hangota ya tashi cikin hanzari ya isa gareta, rungume ta yai dan ya fahimci halin da take xiki, kuka ta saki mai ban tausayin mai sauraro" yanzu mine shikenan ba zan haihu ba, da ba zai taba samun mazauni a wannan marar ba? Ya zanyi da son yara dake addabar zuciyata?" Kuka shima yake sosai sai da sukai ma'ishi sukai shiru" kiyi hakuri ni na jawo maki wannan nakasar, ki gafarta min, nima ina cikin quncin rashin haihuwa,musamman inna kalli yanda Abrar ke son ki, take matuqar qaunar ki, sannan na san zaki haifamin yara kyawawa kamar ta, amma na mana mugunta, Allab wadaran rayuwata" rufe mai baki tai da sauri" pls don't say that again, Allah ya albarkaci rayuwar ka zaka ce, kabci gaba da gyara kurakuren ka na baya, ka duba ka ga ni fa yanda Allah ya maka albarka a kasuwancin nan, har fili ka siya, nan gaba kadan gida zamui mu koma, mu ci gaba da jin dadin rayuwar mu, to mene na daga hankali, Allah ke bada haihuwa ya ba wanda yaso,mu ba zamui kuka da Allah akan bai bamu ba,saboda mu da kan mu mukai wa kanmu mugunta dan haka hakuri zamu ci gaba da yi," Juwairah ce ta koma gidan ta da gudu tana kuka, garin Kayan qamshin da ta niqo wa Addan nata ta sake ya fadi a qasa, kuka take sosai har tana shessheka, wani irin tausayin su ne cike a zuciyar ta, Jabeer gaba daya ya rude" Babe me ya faru? Waya mutu, Ya Allah Sanar dani ko na sama maki kwanciyar hankali, ki sanar dani kome kk so na miki , kukan ki na daga hankalina" kwalla ce ta fito idon shi yai qoqarin mayarwa"  Sweet one ka taimke ni ka bawa su Adda Suwaiba Abrar" maganar ta doke shi, kuma yaga tsantsan rashin hankalin ta,kyautar mutum sukutum, ya zai iya wannann kyauta? Amma duba da yanda take kuka sosai, hankalin ta a tashe ne yasa ya kama ta ya zaunar, ya umarce ta da ta sanar da shi akan wane dalilin zai ba da yarinyar shi guda daya tilo, bayanin komai ta mai cikin kuka bata rage komai ba, shi kanshi sai da ya share hawayen, " Tabbas roqon ki ya amsu,nima Allah ne ya ban ita ai ba ni naba wa kaina ba,dan haka na basu ita halak malak, ko bayan raina Abrar Hafsat Ta su Suwaiba da Salihu ce"sai ya kashe murya just to cheer her up"kinga da mun koma sai na sake wani zubin a nan wajen, na sama mana Abban ki ko" yana shafa marar ta" kai anan ma yau ba sai mu fara ba, har Allah ya sa a dace, kinga daga gobe sai a koma kiran ki Maman Abba" dariya ta saka ta kai mai dukan wasa ya goce ta bishi ta haye cinyar shi tana qoqarin sai ta hargitsa mai sumar kanshi yana qocewa, a haka suka fada kujerar a kwance suka hau kissing juna kamar su cinye kansu, nace toooooo abun na manya ne Hamma yace babyna baki girma ba zo mu tafi kar su batan keπŸ˜‰πŸ˜‚Da wajen qarfe goma sun gama shirin tafiya sun hada akwatin kayan Abrar da komai Sallama suka je yi ma su Innar mu, Su suwaiba da Salihu suka shigo, cike da fara'a suka gaggaisa, Abrar na ganin Suwaiba ta ko hau qoqarin zuwa wajen ta, cikin shauqi da kewar yau zata rabu da Abrar din ta dauke ta ta rungume tana kissing din ta, ita kuma sai dariya take, irin na yara, wata kwalla Juwairah ta share ta son yar ta ta amma tabbas haka zata bawa Addan nata ita, miqa mata akwatin yarinyar tai tace" Addan daga yau kin zama Ummu Abrar, dan Yah Jabeer ya miki kyautar ta gaba dayan ta, kin cancanci zama uwa a gareta, dan haka ga tanan, dama ita ba wai ta damu da nono bane, kunun nan da kk bata shi yakamata ki ci gaba da bata, Allah ya raya maku ita da imani," ta ja baya Suwaiba da Salihu tare da Innar mu Baba Balarabe ne ya katse shirun" a gaskiya Juwairah ke alkairi ce ga rayuwar zuri'ar mu baki daya, tabbas Qanina da Bilkisu sunyi matuqar qoqari na baki tarbiyya managarciya, wannan shine dalilin da ya sa kk zama haka, Allah ya muku albarka, kai ma Jabeer naji dadin wannan kyauta da kai, duk da nasan ita zata saka ka, amma da baka aminta ba da hakan bai samu ba," godiya sukai innar mu tace" Suwaiba Allah ya taya ku riqo, ya sa ki qoqarta bata tarbiyya mai kyau, yanda zata tashi abar so ga kowa" Suwaiba da Salihu kuwa kukan farin ciki ya hana su magana sai gyada kai, wanda hawaye ke kwarara a idanun su, zuwa tai ta rungume qanwar tata, da durqisawa a gaban Jabeer, dago ta yai ya na buga bayan ta, yana kada mata kai, Salihu ne ya je ya miqa mai hannu daga baya ya rungume shi ya saki kukan murna" Na gode na gode baku kula da rayuwata ta baya ba kuka mana wannan kyauta Allah ya faranta maku, ya baku yara masu albarka kuma," Ameen kowa ya amsa sannan suka tafi, suna tafiya Juwairah ta saka kukan rabuwa da yar ta, hannun ta ya kama shima yana jin wannan kewar, amma ba yanda zasui, Allah ya basu ladan hakan, a haka har tai bacci.

[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ   


    


       BY HAERMEEBRAERH


Page 34:
Labarin kyautar Abrar zuwa ga Suwaiba ba inda bai shiga ba a dangin nasu baki daya, inda kowa yake farin cikin irin wannan kyautar da ba kowa ke iya ta ba, ( mutane in baka haihu ba sun iya maka tereren baka haihuwa ko kalmar juya ta shiha tsakanin ka da su, musamman dangin miji daga sanda aka ce basu da cikakken ilimi, jahilci ya musu yawa to daga ranar ka shiga uku in baka haihu ba, ba sa tinanin cewar ma ko laifin daga dan su me? Aa kawai ki haihu kamar ke zaki bawa kan ki haihuwar, sun manta cewar komai nufin Allah ne, Allah shike bawa duk wani wanda muka gani da da, shi bai isa qoqarin shi ya bashi ba, komai himmar shi a gado kuwa, ko sune Ayu qarewar making love ba zai haihu ba sai da izinin Allah, to me zai hana mu tane su zama irin Juwairah, da ka zo kana ma wanda bai da da gorin haihuwa, mai zai hana kai tinda ka samu Allah ya baka kai ma ka dauka ka bawa wanda kk tinanin juya ne bazai taba haihuwar ba? Ba zaka iya ba? To karka shiga hurumin Allah, matsalar nan ta fi faruwa a tsakanin mu mata, yayyab miji , qannen miji, da surukai, to ki sani ke yar uwata mace, ko wacce mace dangin miji ce wataran, in kikai a gidan ku kika je wani gidan wata ce zata shimfida maki nata ikon, wataqila ma wanda yafi naki, dan haka ki mai kyau kiga mai kyau, kikai sabanin hakakiga abinda ya fishi, ko daidai shi, in kina kyautata wa ana munana maki,ki hakuri jarabawa ce daga Allah zai maki magani zai kuma baki lada mai yawa, Allah ya sa mufi qarfin zuciyar mu) .
A sati biyun  da suka koma Juwairah ta shiga kitchen da yamma, a lokacin ta gama komai na girki, gyaran gida, wanka, da kuma tsaftace ko ina na jiki da muhallin ta tana jiran Haerbeebeen ta ne, miqa hannu tai ta dakko wata roba da ta cika ta da niqaqqen garin ridi, a hankali take jin jikin ta ba kwari tin kwana biyu da suka wuce, cup din da ke hannun ta ta matsar jikin robar domin diba, tana budewa taji qamshin kantun da take so na neman ya zama mata wari, amma ta daure a haka ta saka spoon ta diba, zuwa tai tukunyar da ta dafa madarar shanu, wadda Jabeer ke nemo mata a cikin wani qauye anan Abujan, ta dibi yanda zai ishe ta, zumar ta asalin mai kyau mara hadi ta diba ta saka, yanda take buqata, palo ta koma ta zauna, bayan tai bismillah ta riqe cup din da hannun ta na dama ta kai bakin ta ne, wani irin amai ya yunquro mata, da gudu ta miqe zatai hanyar dakin su taje toilet,karo taci da shi yana shigowa, wani yunquri da tai sai anjikin shi, jikin ta har rawa yake yi, dan azabar da take ji a jikin nata, aje jakar shi yai hankalin shi a tashe matuqa, ya kama ta tai ta kwarara amai, sai da ya zamana bata iya fitar da komai sai yunqurin azaba, sannu kam ta shata har bata iya amsawa,idon Jabeer sunyi jaa saboda tausayawa matar tashi,tabbas in hasashen shi gaskiya ne wannan karon da alama mai wahalarwa ne, dan ya kula kwana biyu kenan tana fama da wannan wahalhalun, ga zazzabi dake addabat ta, haka ya jata suka tafi toilet,kayan su ya cire masu,ya saka su a bathtube,ruwa ya cika masu suka dauraye jikin su sannan ya tsiyaye ya saka wani, wanka ya musu suka fito, bayan ya shirya ta ne ya kwantar da ita a agado yaje ya shirya shima,zuwa yai kusa da ita ya kwanta ta bayan ta" Honey kaje kaci abinci everything is ready at the dinning area" " I know,but i can't eat when u are like this, me ke maki ciwo, me kk so, dan daga ganin ki da kuma aman da kikai,bakici komai ba in ba wainar flour din da kikai mai manja ba da safe," turo baki tai daga baya ta kwabe shi irin na shagwababbun nan, shi kuma yana jin yanayin saukar nunfashin ta ya san na kuka ne, saurin juyar da ita yai, " What is wrong my love,pls tell me ur problem,or what you want, i will provide you with anything i have inshaa Allah"  kukan da take son yi ne na shagwaba ta fara, rungume ta yai yana kissing wuyan ta a hankali yana shafa bayan ta,sai da tai ya ishe ta tai shiru tana ajiyar zuciya, a hankali ta fara magana" Yah Jabeer banda lfy, kwana biyu jikina ciwo yake sosai, ga zazzabi da amai, abubuwan danake so sai naji vana son su," sai ta qara saka kuka, " Shhhhhhhh, yi shiru my bby, ki daina kuka, ko zaki gwajin ciki a gida ne, tinda muna da abin yi" jimmmmm tai kafin ta wuntsila daga gadon cikin doki da zumudi, binta yai a baya yana mata dariya, dan ya kula bata kawo hakan ba sam, sai yanzu, zuwa tai tai gwajin ta fito, layukan na farko ya fito radau na biyun ga shi nan dai, amma tabbas akwai shi, kwabe fuska tai tace" ni ban gane komai ba," " to ko asibiti zamu?" " ehhhh haka za ai ina zuwa" fita tai da hanzari taje ta sake kayan jikin ta zuwa doguwar riga da babban mayafin da zai rufe har mazaunan ta, bayan ta gama ne ta juyo taga shima shiryawar yake, a tare suka fita, sun isa wani makeken asibiti, a unguwar tasu ta Jabi, suna zuwa sukai mata gwaje2 inda suka dau wasu yan lokuta, likitan ya tabbatar masu da tana dauke da ciki ne na sati biyu, wata irin murna ce ta kama su, Jabeer ba ko kunya ya daga ta sama ya hau juyi da ita, ita ko sai dariya take, kissing din ta yai kadan sannan ya aje ta, godiya ya hau ma Doc da bakin shi ya qi rufuwa shima, yana mamakin irin soyayya ta wadannan mutane, bayanan yanda zasu kula da cikin ya musu, wanda sun riga sun sani,amma sai suka koma kamar ba su taba ma sanin ya ciki yake ba tsabar murna, bayan sun gama ne suka fito Jabeer na wanilallaba ta kamar kwai, " Babe me kk so ki ci kinga kar kina barin kan ku da abinda zaki haifa mana da yunwa" kada kai tai a hankali tace"ni ba komai kawai ina son wainar flour ne irin ta dazu," aiko ba wata wata ya saka ta a mota sukai gida, suna zuwa ya shiga kitchen, ya hau mata wainar, daukan, abinda ta kasa sha yai shi kuma bayan ya gama mata, tana ci yana sha,"lallai babyn nan, da qoqarin shi,da gaske so yake kar ana shan abubuwan da zasu qara mai kuzari" dariya suka saka dikkan su" ko kuma abubuwan da zasu qara ma Abban shi kuzari ba" qara fashewa da dariya sukai( hadin kantu da madara ko da nonon Raqumi hadine tested and trusted dake saukar da ni'ima sannan yai maganin wasu cututtukan jiki in baka da nonon Raqumi sai kai da madarar shanu).


Saudat ce na hango ita da angon ta suna ta zagaye gidan suna guje2 cikin tsantsar so da qauna tare da begen junan su, wani irin shaquwa ce ta musamman a tsakanin su,tare da tausayawa juna, dan suna cikin gudun ne santsin tiles ya kusa kwasa Saudat a qasa, amma da ikon Allah sai bata fadin ba, ta dai tsorata ne kawai, da hanzari ya isa gare ta,yana wani juya ta" Sweet one baki ji ciwo ba,ta ina kk bige??" Kamo fuskar shi tai gaba daya a hannun ta, ta matso lips din shi irin yanda mutum zai iyayi da hannu ko da bakin shi ya tsuke su sui tsini, haka ta mai itama, sannan ta kai nata bakin tai kissing din shi, sai da taga suna neman faduwa ta tsaya" me ma kk tambaya ta dazu?" Ta fada cikin qunshe dariya,da daga gira,cikin in-ina ya fara bata amsa" Ammmmm..... immmm.... damaaa... cewa... nai.... imm.... can u pls kiss me again" dariya suka saka sosai har tana riqe ciki,daga ta yai ta bayan ta cikin nata suka samu wajen zama a kujerun nasu, bayan ya kwantar da ita a kujerar ne ya kwanta ta bayan ta,ya rungumo ta ta ciki,suna ci gaba da dariya, a hankali sukai shiru yana mata wasa da gashin ta" Babe me yasa baka damuwa da batun rashin haihuwar da kasan ba zan yi ba, saboda rashin mahaifa, bayan kai baka taba aure ba, ar u planning to have another wife ne nan gaba?" " My dear ina so ki san cewa da auren da haihuwar duk nufin Allah ne, tayu a baki da mahaifan mu haihu, ta yu ba za mu haihun ba, to ina son ki sani, haihuwa is a blessing that everyone will love to have it, amma ni bana daga cikin wadan da suke ganin in mace bata haihuwa bata da amfani,to ina soyayyar da yake mata? Dama dan Yara kawai ya aure ta? Ita ce take ba kanta? Idan zan maki kishiya saboda baki haihuwa tabbas na zama daga cikin azzalumai, na kuma zama daga cikin masu butulci ga Allah, domin ya min kyauta countless, to me zai sa dan akan abu daya danaoe so ban samu ba na mai butulci? Ba zai yu ba, daga ranar da kk ji na qara aure Saudat ban qara shi dan baki haihuwa ba ne, sai dan itama ina son ta,kuma Allah ne ya halatta mana qara auren, dan haka ki kwantar da hankalin ki ni ba mai ra'ayin tara mata bane, bana.son hayaniya, bqn son takura, mata da yawa na saka ni damuwa dan bana son raba fada kullum," ya qarasa ta yanda tabbas yasan hankalin ta ya kwanta da maganganun shi, amma hawayen dadi sun kasa tsaya mata, tabbas Allah ya azurta ta da namijin gaske, Allah ya qara mai hakuri da juriya akan hakan ta ayyana a ranta, ci gaba da shafa wuyan ta zuwa bayan ta yai ita kuma tana wani miqewa tana juya jikin ta anashi, tini ta burgita shi,ni kuma na ja sayyarar qafata na waje a 100😟
"Ki taho da fidar yarannan, da tissue love" amsawa tai shi kuma ya zauna yana masu wasa, bayan ta iso ne ta zauna kusa da su," ni dai gaskiya ban yarda ba nima sai an min wajen zama a nan, dan wayo kullum ni a qasa ko gefe su a cinya"ta fada tana turo baki,dariya ce ta kama shi, sai ya dauki Muhammad ya dora a wuya, sannan ya dago ta ya saka a cinyar shi,murna ta saka tana mai kiss a kumatun shi, " Na gode na zaci ai ce min za ai nai hakuri yaran su zauna da ba zan yarda ba sai dai a maida su daki ni na hau" ta fada tana sauka, dariya yake sosai, dan Salma ba dai kishi ba, kishi take da yaran nan sosai , dan gani take gaba daya ya kwashe soyayyar ta ya basu, lokacin shi gaba daya nasu ne in yana gida, amma a qasan ranta ba qaramin dadi take ji ba, hankalin ta a kwance yake dan bata tsammaci hakan a wajen saurayi da bai san ya zai gama kula da kan shi ba bare wasu yaran har biyu,  kujerar basu abinci ya saka su,ya dorawa kowa a gaban shi, ya basu cokula a hannun su na dama,sa kyar suke riqewa saboda rashin iya hakan, amma yana tsaye in zasu karkace ya gyra masu, ta baya ta ziro hannun ta ta tsugunna itama ta kwantar da kanta a bayan shi ta furta"I love u" shima waiwayar da kan shi yai suka hada ido yace mata" i love u more" kiss ya mata a goshi ya juya ga yaran su( da na kowa ne, baka san wa zai more shi ba, dan haka bahaushe yace, da da dukiya ba a masu mugunta, in ka lalata wataqila kai zaka amfana a gaba,ka bata to da me zakai amfani, in ka gyara kuwa ka amfana, wani ma sai ya gama gyarawar ya zamana ba shi zai mora ba ya gyarawa al'umma ne, ladan shi na a wajen Allah, wani kuma sai ya bata ya mutu ya barwa al'umma annoba, yana qasa ana rubuta mai zunubin mummunan upbringing da ya ba wani,mu gyra duniyat mu lahirar mu ta amfane mi)
Talle ne ya shirya tsaf da yar jaka a hannun shi, wadda ta qunshi kayan yara mace da namiji dan bai san me Salma ta haifa ba, incase ko wace gender ta haifa za a samu na ta kayan, sallama suke da Marka inda qasan ranta kishi ne danqare, amma yanzu halin ta mai kyau data koya ya danne kishin, miqamai leda tai da ta daka kuka daddawa, sa kubewa, tace ya kai masu, godiya yai mata,Huwaila ce ta leqo da gyada soyayya itama dan sana'ar ta kenan yanzu, tq bashi tace ya gaida su ya nema masu gafar ta, amsa yai ya sa kai......

*To masu karatu Talle fa yai shiri, wa zai bishi ya fada mai bata gidan kar yai wahalar banza*πŸ˜‚

[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ   'YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ


            BY HAERMEEBRAERH
Page 35:
Talle ne ke ta kwada Sallamah a qofar gidan su Salma, da ga can Ammar ne ya fara leqowa, like a big bo he is, da tsamin bakin shi yake tambayar wa ake nema, yaro yana da kaifin hankali, shekara biyu da watanni amma akwai qoqari ga karatun qur'ani a bakin shi tar, na bokon iyakar shi A B C D, sai counting da Mama Biliki ke dan koya mai, komai akai yana sane da shi kuma yana ganewa, murmushi talle yai, aranshi yace wannan yaro da ya dan da Salame zata haifan ya kai shekarun shi ai sai nace dana ne suna kama, " Yaro ina malam," " faya nan" ( Baya nan), Talle ne yaga yaron ya kalli gaban.shi yana dariya ya fita da gudu yana " Abbana Oyoyo" shima wajen ya kalla sai yaga ashe Abbam su Salame ne ya dawo, saurin isa yai wajen shi, inda gaba daya Abbam ya sauya fuska, daga fara'a zuwa bacin rai, " me ya kawo ka?" Tambayar da ya wulla mai kenan" Abba dan Allah dan son Annabin rahama kai hakuri, ka yafeni, tabbas na kasance daga cikin jahilai, marasa sanin Allah a baya, sakamakon jahilcin da ya mamayi zuciyata, kuma naqi na nemi sanin Allah da dokokin shi, ina jin girman kai, da ganin na wuce wajen ai, hakan tasa na aikata munanan abubuwa a rayuwata, kala2 wadan da naga isharar su Abba, babbar isharar shine mutuwar 'ya ta, kama dan uwana yaya na da mata ta suna zina, daya 'yar tawa ga ta can da dan gaba da fatiha, ga abinda ke dagan hankali rabuwa da Salame d nai, ta tafi da cikina na rabunda ita rabuwa cikin rashin tausayi da imani, a yanzu nayi nadama, na koma islamiyya ni da iyalina dika, ka yafe min ba dan halaye na ba sai domin Allah" kalaman shi sun saka jikin Abba yai sanyi amma ya wuce cikin gida kamar bai ji shi ba, yana shiga Mama Bilki ta sauke shi da ruwa da abinci, ga kuma ruwan wanka ta kai mashi,tana goge masa zufa ne tare da jera mishi sannu da zuwa cikin rattausan lafazi, umartar ta yai ta kira yayar tata,miqewa tai ta tafi, ta kira Goggo Sarai da tai zurfin a cikin tinanin baya, yanzu da hankali ke qara shigar ta, ba qaramin kunyar Mama Bilki take ba, tasowa tai kamar wadda kwai ya fashe ma a cik, ta biyo ta, " Gamu Abban su" dagowa yai ya kalle su cikin sha'awar yanda suka koma a nitse ba hayaniya ko mummunan kishinnan, Ammar ne yaje wajen Goggo Sarai ya zauna a cinyar ta, shafa kanshi tai tana mai murmushi, Abba labar ta masu komai yai sannaj ya sanar da su Tallen na qofar gida ma yanzu, haquri ya ba Goggo Sarai da yaga ranta ya baci, yama juyawa yaga fuskar Mama Bilki ma a bace, domin shi mijin Salma shima ba qaramin azzalumi bane kwantar masi hankali tai da dadadan kalamai sannan suka hakura, aika Ammar yai yace yaje ya shigo da baqon nan, tafiya yai ya sanar da shi, Talle ya shigo qafa duk ta sage mai saboda tsaiwa, waje Abba ya matsa mai kan tabarma, tayin abincin ya mai Goggo Sarai ce ta qaro ruwan sha da wani abincin, ci sukai suka qoshi, sannan Abba ya kira su again, " da farko dai ina son sanar da kai dukkan mu nan iyayen Salma mun yafe maka, kuma muna saka ran itama ta yafe maka, tabbas ka cutar mana da yarinya, ka zalumce ta, amma duba da cewar muma masu zunubi ne a wajen Allah kuma mu roqe shi ya yafe mana, banga dalilin qin yafe maka da zamui ba, daga qarshe ina mai sanar maka yanzu haka Salma na Abuja gidan kudi gidan hutu ita da yaran ka dan biyu ta haifa, kuma ta samu miji saurayi ya dauki yaran kamar mallakin shi, ni ba zan sanar da kai ina Salma take ba a yanzu dan ta fara samun farin......." " ban katsi nunfashin ka ba Abba, amma tabbas nima ba zan so abinda zai hana ta farin ciki ba a daidai wannan lokacin, tabbas, na amince su ci gaba da rainon yara na, lokaci zuwa lokaci zan dinga zuwa nan din, ana gaisawa,ga address dina saboda wataran ko za a buqaci hakan," takardardaya rubuto tun a gida ya zaro ya miqa ma Abba, idon shi ya kada yai jawurr, tabbas har yanzu akwai son Salma a ran shi, wanda tin da ya dauka sha'awa ce kawai, miqawa Abba ledar Hannun shi yai ya mai sallama dan komai dare gida yai, ya ma yaran shi addua, an nuna mai hotunan su, inda Mama Bilki ta dakko mai wasu ajiyayyu tin na jarirantar su,har randa zasu tafi, hawaye kawai yake sharewa, duk yaran shi ba mai kyaun wadannan da ya koro, dan duk macen da ya aura in zata tafi sai ta dire mai da ko yar shi, ko in taje gida ta haihu zata dawo mai da shi, Haule ce kawai take itama kyakkyawa saboda uwar ta, yana tina ta sai zuciyar shi ta qara tsinkewa,ya kula yara uku ya bari yanzu, amma wannan na daga cikin horon da Allah zai masa ya raba shi da yaran da yafi qauna, tashi yai bayan ya sake masu sallama ya isar da saqon su Huwaila,godiya suma sukai masa, ya kama hanya sai qauyen su.*BAYAN SHEKARA BIYU*Salma ce ke zaune da jaririya a hannu da suke kira da suna Faiha, gefe Juwairah ce tana riqe da hannun yaron ta qaqqarfa mai kuma barna, Salim, Sai Suwaiba da ke ma Abrar kitso a lallausan gashin ta mai tsaho, gefe kuma a kwance a kujera Saudat ce ke latsa waya tana ta doka murmushi, Maganar Juwairah ce ta katse shirun nasu" In baka tsaya ba Salim zan kira Daddyn ka ya dauke ka ku tafi kona huta," da sauri yaron ya zauna a cinyr ta ya nutsu, dan a cewar shi Daddy is no fun to be with, amma Mummy, yana son zama da Mummyn shi ko da duka zatai mai in yai halin nashi na barna, ' Yan biyu ne sika shigo da gudu, suna haki" Mummy Daddyna yace wai ki bada Faiha, Salim da Abrar mu je park" kowa a cikin su daidai lokacin da kowa yace Daddyna sun kalli juna da harara,ba su fada a tsakanin su sai akan abu biyu, chocolate da kuma Daddyn su, sai kace kaya haka ake rabon shi a tsakanin su, wannan yace nashi ne wannan yace nashi ne, fatima ce tace" kaiii wannan Muhammad din sai son yi min kwace kk kullum for how long zaka gane cewa Mummy ce taka ni kuma Daddy nawa" " Fateema ke ce baki san komai ba hat yanzu" ya fada yana mata kallo wai shi harara, dan kwata2 bai kaita wayo ba, ga shi fadan ma bai iya ba" kai ni ku karbe ta sarakan rabon iyaye,kada Allah yasa ku zaben din ga Faiha in ta girma zata zaben ai" miqa masu ita tai suka karbe ta,dariya saudat tai sosai tace" Mummy ar u jelouse ?" Dariya dika suka dauka, Juwaira ta sauke Salim ya bisu,daidai an gamawa Abrar kiston ta, miqewa tai tace" Tanx Mum" tai kissing kuncin Suwaiba ta fita a guje, murmushi tai mai nuna alamun jin dadi ta bita da"ku dawo lfy kui adduar fita daga gida kan ku fita, kar a manta da yin addua in zaku dawo," daga nesa ta amsa mata da" inshaa Allah mum, i love u," " i love u too baby" nan ma Saudat ce dake ta Chatting da mijin ta ta sake dagawa tace" lovers kenan" nan ma dariya sukai, juwairah ce ke kallon ta da Yan uwan ta cikin farin ciki da nishadin da Allah ne kadai yasan iyakar shi," to ya kamata mu ma muje Shopping, akwai wasu abubuwan danake so mu siyo yau" ta fada tana kashe masu ido, Saudat ce ta diro da sauri ta dage hannaye sama tana murna" Yeeeeehhhhh shopping" " u always act like a kid Saudat," inji Salma, pilon kusa da ita ta wurga mata, " eh din anyi,my husband always treat me like one," ta qarasa tana murguda baki, dariya suka saka, Juwairah tace" yeh u ar always his baby" " and u ar more like baby to me than she is always my love" juyawa tai taga Jabeer ya shigo cikin qananan kaya, tare da mijin Saudat, tsallen murna Juwairah ta daka taje ta rungume shi,wanda dama yana fada hannun shi is open, rungume ta yai kamar su kadai ne a wajen,gyaran murya mijin Saudat yau yace,babban Yaya muje ki, tinda shi wancan Baban yaran ya debe su muma mu kai su shopping din kawai, kallin juna sukai matan, ba haka suka so ba, akwai dan abubuwan su na mata da suka so kwasa, amma ba damuwa sun taya su zaba ma, dakko hijaban su sukai,Juwairah har da Niqab Yah Jabeer yake sata sakawa, haka suka fita, gwanin sha'awa, waya sukai ma mijin Salma ya same su a Sahad dake can ABJ din, aiko Salma da tana jin ta out of place sai murn,sa riya sukai mata, a can suka hadu da yaran da mijin Salma siyayya sukai sosai kafin kowa ya nufi gidan shi, Suwaiba gidan Jabeer zata kwana kafin wase gari mijin ta yazo su tafi.Arziqi ya wadata a zuri'ar gidan Abba Baballiya, gidan kuma 'YAN ABUJA, albarkar Allah ta sauka masu, ko ta ina,inda a tsakanin Jabeer da yake dan su da surukan su, kowa qoqarin yi ma iyayen abun da zasuji dadi suke, an canja fasalin gidajen iyayen daga na qasa zuwa na cement, da kayan alatu kala2, ga shaguna da suka bude masu, na saida kayan masarufi suka saka amintattun yara suke kula da wajen, shiko Yah Jabeer kasuwancin shi yana nan da kamfanin jakunkuna na AF2 dake malaysia, abun ba a cewa. Komai sai godiyar Allah,makaranta mazajen dika ke tinanin maida iyalan nasu nan kusa su ci gaba da neman ilimi har sai sun ce ya ishe su, Suwaiba nonoless tin bata son saka bra din acuci maza irin ta Cutie har ta fara, mijin ta ya masu gini a unguwar Kabuga, qaton gida, yanzu harkar gwanjo ta bude sosai, Talle arziqi ba laifi, ana nan an zama manyan ustazai masu ma wasu wa'azi musamman da basu misali da rayuwar su, Saudat da mijin ta, sun fawwala ma Allah dukkan lamuran su, na rashin haihuwa, ba sa damuwa a ransu ko adan, tin ana zuga mijin ta yai aure har an gaji, domin soyayyar su suke sha, da shaquwa ga fahimtat juna dake tsakanin su.
Allah ya albarkaci rayuwar mu baki daya.*Masoya novel na 'YAN ABUJA ku dakace ni gobe domin jin wasu bayanai da sharhi da zan akan wannan novel da inshaa Allah nake saka ran zai amfanar kuma zakuji dadin shi da yardae Allah, ina roqon ku da kuma fatan duk abinda na fada daidai kuma kuka san abin koyi ne da ku qoqarta saka wa a ayyukan ku, sannan wanda nai kuskure ku yafe ni akai, ina jiran gyaran ku akai daga yau zuwa gobe inshaa Allah na gode. Me love u XoXo❤*

[11/26, 12:36 PM] Hermeebrah: πŸ’…πŸΌ    'YAN ABUJA   πŸ’…πŸΌ
        BY HAERMEEBRAERH*Assalamu alaikum Jama aree bandi raabe am, yidibee novel 'YAN ABUJA, mido yetta on masin,beyeddi on holli am haa dow defteream, mido yeela ko end jangi pat end habdai end naftira bemai koo na pat ba end habda ko sedda on, mido usa mido yetta on walama bana fulbe haa on woni fu ha duniya do miyetti, walama bana yare IBRA, end doo woondi inshaa Allah, mido yidimon*❤*Ina kuma riqon duk wanda Allah yasa ta fara bin wannan novel daga farko ko ta riski wannan page din koda bata bi daga farko ba ta daure ta karanta wataqila ta samu koda abu daya ne mai amfani a ciki*Page 36:
Zan yi sharhi ne akan wannan novel namu na yan abuja,  inna gama nawa wataqila ba zai yu na fidda komai ba ina son kuma makaranta ku fiddo man da naku hakan zai sa naji dadi maybe gaba na sake mana wani novel dinπŸ˜‰1-  da farko dai gaba daya a kuma dungule nai magana akan iyaye da tarbiyya ne, yanda iyaye in Allah ya basu yara ya zasu saka su akan hanya mai kyau wace tarbiyya zasu basu, me yaka mata su saka masu a zuqatan sh saboda gudun kar su tashi ba akan tarbiyya mai kyau ba.


2- sannan nai magana akan kwadayi, mahaifiyar su Suwai nonoless ta taso da su akan kwadaryi sa burin zuwa inda ba lallai ne arziqin su na can ba, unlike Juwairah da suka raina ta akan auren Yah Jabeer.3- Ana son mace ta zama mai tarbiyya mai kyau, wadda ko ina ta shiga za ai sha'awar ta da halayen ta in bata nan ai kewar ta, ki iya zama da kowa da kyakkyawar mu'amalat, ki kasance wadda ko minti daya miji yai baku tare zaiji damuwa da tashin hankali, da duk wanda kk tare da shi ma.


4- Ana son mace ta zama mai tattali mai dabara in ba wannan a gida ta san ya zata hada wancan ya bada outcome mai kyau mai dadi, yanda ba mai gane ma rashi ne ya jawo hakan, sannan ta zama tana qoqarin dasa kowacce hanyar da zata kawo masu sauqi a gidan ta, kamar yanda Juwairah tai lambu a cikin gidan ta.


5- Mace mai rufawa mijin ta asiri a kowanne lokaci abar so ce ga kowa, ba namiji ma kadai ba ga kowa.


6- Mace ki zamo mai tsari, ya zamana kina da lokutan yin abubuwa, in kina haka za a same ki mai tsafta, baki kwaba wannan da wancan, misali, kina girki wannan bangaren zaki iya ci gaba da gyaran daki, sannan ko ya za ai mace in zaki wanki ki fara gyara dakin ki da gidan ki sai ki zuba wankin ki tayi, akwai wasu dana kula ko nace da dama, taqamar zasui wanki sai kiga gidan kamar bola da kin magana ace wanki zan shiyasa, yana daga cikin tsari ki ware ranar da zaki na ma gidan ki gyaran tsaf misali muce a qarshen sati ko sati biyu ko wata daya ki fitar da komai daga mahallin shi ki share ki wanke ko ki goge, sannan yana daga tsari ki ware ranar zuwa kitso da qunshi, sannan ranar yin gyaran jiki irin dai na Juwairah, in Allah yasa gidan ki kina da halin yin lambu kin yi to ki ware mai lokacin duba shi, in baki da lambu a sameki dai da wata shuka da kk kula da ita ga lada ga huce takaici ga amfani,musamman ZOGALE.7- kar ki zama mai kwadayin abun hannun namiji, komai qanqantar shi komai yawan shi, in kk kasance mai kwadayi tabbas zaki wahala, wataqila ma a kwadayin qima da darajar ku ta zube son ki a hankali ya fita daga zuciyar shi, sannan qataqila in bakinda rabon zama da wani sassa na jikin ki ki rasa shi in d process of kwadayi, da roqo, kamar dai irin na Saudat mahaifaless.8- A rayuwa kullum Namiji shine jagora shine uba shine yaya ko da kuwa qani je yana zama shugaba, ko abokin shawara, dan haka in baka kasance mai tausayi da tallafawa mace ba ka aje sunan ka a namiji ka daura dankwali ka bi layin matan aita buga cinya da kai, ku duba rayuwar Yah Jabeer da Abban su Salma , Yah Jabeer ba abinda bai taya matat shi, har da gyaran jikin, shaving, gyaran gashi, wanka, wanki, wajen haihuwa ma tare sukai komai, da ace mazan mu na zuwa dakin haihuwa suga azabar da mata ke sha, wataqila da sun rage ma mata rashin mutuncin da suke masu, sun tabbatar matan suna ta mata, suna matuqar qoqari, suna jarumta, da tausayi da sadaukarwa ya shiga zuqatan maza, da sun tarairayi abinda aka haifa masu da kyau da mutunci. Ta wani bangaren kunga yanda Abban su Salma ya dabbaqa sunnar Rasulullah yake kiran matan shi da suna masu dadi, kamar Gimbiya Da kuma Sarauta, wannan sunna ne ko mai tsufan ku soyayyar ku karta gushe,SO baya tsufa sai dai masoyan su tsufa ju jeme, amma soyayyar su na nan.9- mace kar ta zama mai zazzafan kishi, zai lalata mata rayuwa da tarbiyyar yaran ta, zai sa miji duk son daya ke maki ya fara raguwa, sanan mutane ma masu hankali zasu fara tsanar ki, kuma daga baya kizo kina dana sani, lakin kar ki bari kishiya ta zama tana cin kashi akan ki,dan ko islam bai yarda ka zama mai sako2 yanda mutane zasu raina ka ba,kamar Mama Bilki, ta riqe zaman auren ta da amana ba mummunan kishi, tana da sanyin hali da hakuri,amma me bata yarda a taba yaran ta ba, ta tsaya masu, sannan kuma bata tsayawa ai hayaniya da ita in abu yai yawa action ta dauka, πŸ˜‚ amma ban ce mace ki zama sarkin fada ba fa in dai tabbas zaki dau halin Mama Bilki sak to ratuwar ki da kishiya zaki samu sassaucin zama.
10- Qofofin Allah a bude suke ga bayin shi da suka yarda akwai shi kuma shi mai rahama ne, to duk zunubin da suka aikata ko da shirka ne, har dai in basu mutu akai ba suka tuba to Allah zai yafe masu,kamar yanda misali ya tabbata akan Kallah ya ce akwai lokacin tuba a gaba amma me yana fita mota ta mai lalata, ta dauke shi a duniyar, ai kunga ba lokaci kenan, mutuwa tana jikin skin din ku, at anytime zata iya cika mana aiki da izinin Allah dabularnin mala'ikan mutuwar, take za a zare ran mu, sannan shi Salihu daya tuban ga shi kudin dai yaoe dasu a bayan na haram daya tuba ya gyara ya sha wuya na dan lokaci na sana'a wan da a da bai san ya zai ba, daga baya kuma yai kudi ta hanyar halal.11- Matan da basu taba haihuwa ba sui hakuri, Allah na sane da mu baki daya, ki zama kina wa kanki wannan adduar yar uwa" Ya Allah Ya rabbi ya khaliqu kulli shai'in Allah ina riqon ka, indan haihuwa alkairi ce a rayuwata da ta mijina da al'ummar musulmi da musulunci Allah ka bani, idan sabanin haka ne Allah ka samin hakuri da juriya tare da dangana, Allah kar ka bani, ka shiryar mana da sauran yaran musulmi su zama masu albarka" wallahi damuwar eashin haihuwa na maki alqawai in dai kinyi adduar nan da ikhlasi Allah ba zai barki haka ba sai ya maki zabij da kk nema.12- Ta bangaren maza kuma in matar ka bata haihu ba ba shi zai sa ka juya mata baya ba, dan mace bata bawa kanta haihuwa, wataqila matsalar daga wajen ka ne, to misali ace ma daga wajen ka ne mace zata iya hakuri ta zauna da kai a haka, ka duva ka gani ba ta da wani namijin bayan kai amma zata zauna da kai, kuma ba shi zai hana kai ta maya rashin mutunci ba, amma kuma in ita ce mai matsalae wataqila ka sake ta, in ka barta kuma ka ce aure zakai ba zaka zauna da juya ba ita daya, ka gani mata ko yaushe su ake tauyewa duk inda aka je aka zo, me zai hana mazaje ku dage ku dabbaga sunna, ku kuma qoqar ta ku tabbatar ma duniya ba addinin da yaiwa mace martaba da qima sama da ISLAM?


13 - ko wanne stuation dayan ma'aurata ya shiga dayan ya nuna mai i am by ur side no matter what, duk daci duk zaqi ba zan barka ba tare muke a ciki.


14- soyayyar yan uwantaka abu ne mai matuqar mahimmanci sai da hadin kai bawa ke zama sarki, sai d hadin kai mayaqa kan samu nasara, in kanku a hade yake zuriar ku zata zama abin tsoro da kwarjini ga kowa, za ai tsoron taba dayan ku, za a na ganin ku as ka tabo daya goma ta shafe ka wa zai so?
15- mace ana son ku zamo mai iya tarairayar miji, mai bashi haqqin shi na auratayya a koda yaushe, mai iya salo kala daban daban, ba tare da kauce hanya irin na matan yanzu da suka maida kallon turawa suna zina ya zama wai suna koyon style na auratayya wa'iyadhubillah, me ya kai ki ko me ya kai ka? Me suke da shi da mu bamu da shi, zuciya ce da kwakwalwa, muma muna da ita,a rana in kin so zakui style kala biyar ko fi, ku gamsar da juna,ba tare da kowa ya koya maki ba, to ku sani ni a nawa duk namijin da zai saka mana wani shirme mu kalla kafin sex ba namiji bane, rako su yazo in sun gama sabgar su ya bisu su koma, dan ba rashin zama na mijin da ya wuce ka kasa dagawa mace sha'awa sai kun ga wasu awaki na yi sannan ka samu ka take matar ka da ya fi wannan, ga illoli dake tattare da hakan, fushin Allah da tsinuwar shi akan ku dika, haihuwae yaran da ake cewa yanzu sun kashe iyayen su, sannan kuma ciwon makanta, sai mai wannan hali ya shirya masu in bai daina ba. Sannan illar kallon nan yanzu ta shine aka yawaita mata yan lessbians da maza gay dan musiba da qazanta Allah ya kare mu da zuriar mu.


16-  Sadaukarwa, ka sadaukar da farin cikin ka dan wani musulmi ko dan uwan ka ya samu farin ciki shima, ga lada ga qarin arziqi da zai same ka, zaka samu da yardar Allah Allah ya mayar maka abunnan da ka sadaukar har da fin shi ma, kamar yanda Juwairah ta sadaukar da Abrar ma Suwaiba nonoless.


17- kowacce mace dangin miji ce ki kula da yanda zaki tafi da dangin mijin ki kema naki dangin mijin su kula dake in kika qi yin da kyau zaki ga ba kyau kema.18- kula da tarbiyyar yara a tsakanin dangi, musamman cousens a wannan zamani, cousens sun ja an aurar da zawarwan yammata da yawa, ba tare da an sani ba, zaki ga suna wasan banza ba za a hana ba ace wai ai yayan ta ne, ba aure tsakanin su? Ke ko da aure yanda zamanin nan ya baci akwai limit na komai, ko kiga ya damu da ita da yawa,ko yaushe suna tare mamat2 ace ai suna matuqar shiri,kin tintibi dalilin shirin? Sannan kuma wajen bacci a bar yara sakaka ta nam wallahi cousens ke dada bata mana yara da qanne, dan haka mu kula dan kin tsaya akan yar ki baki laifin komai ba a duniya da lahira.18- ina ma mata nasiha da qamshi, da kwalliya,tsafta girki iya magana musamman da yawan mu bamu iya kalamai ba da magana komai yabawa muke, ki iya kwanciya, kirsa, kwarkwasa, iya saka qananan kaya,da daura zani, iya kallo,shagwaba, wayyo da mata sun san me ke cikin ta da wataqila har makarantar koyar da ita an fara bude masu, ki iya girki, macen da ta iya girki mai aji ce ki ba ta da aure, ba raini tsakanin ta da kowa, ki zama mai sassauqan halin da kowa zai so mu'amala dake. 
*ina riqon mu dab Allah ko daya mu qoqarta mu saka a aikin mu za a samu gyara da canji, wadda take da abinda na manta ban saka anan ba qofa a bude take da ta rubuto mana da sunan ta da komai dan mu qaru*

0 Response to "YAN ABUJA hausa novel"

Post a Comment