-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

BAKIN ALJANI

BAKIN ALJANI

BA'KIN ALJANI                  1⃣to5⃣

✍�✍�✍�NA✍�✍�✍�
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA💁👑
😍😍Mrs Nura Kuriga😍😍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Dedicated to my fans😘

Da sunan Allah mai rahma mai jin qai wanda ya sake bani dama na rubuta wannan sabon labarin. Tsira da amincin Allah su  tabbata ga annabi Muhammad ( s a w)

"Wani uban ihu take sake wa tana faman kokarin ta kwaci kanta daka rikon da aka mata. Maza har biyar ne suka riketa duk ma aikatan gidansu ne ciki harda masu uniform din sodoji, yayinda gefe kuma wata mata ce tana ta kuka duk ta rude, lokaci daya kuma tayi shiru. Ganin haka hajiyan ta matso kusa da ita tana fadin "khausar2 tasa hannu da niyan ta taba ta, lokaci daya ta saki ihu duk ta watsar da mazan da suka riketa. Ta dago ta shakema hajiyan wuya, idonta yayi jaa, Hajiya sai ihun naiman taimako take amma duk cikin mazan nan sun kasa zuwa domin yanda ta watsar dasu bada wasa ta musu ba. Hajiyan tace khausar ki sakeni nice fa mumy dinki ce." Wani dariya khausar din ta saki cikin wani murya Mara dadin ji, tace kinyi kuskure na sake aurama khausar wani auran, duk da alamomin da muke ta nuna miki amma kika 'ki, khausar tawa ce, tana gama fadin haka wani iska mai karfi ya gauraye gidan, alokacin khausar din ta fadi sumamma, gani haka yasa tace ma ma'aikatan gidan suyi sauri Su dauketa su kaita dakinta, aiko suka dauketa sai dakinta aka rufe kofan da key, Hajiya sai faman kuka takeyi tana fadin maiya sami khausar lokaci daya, muna fira amma duk ta birkice. A dai2 lokacin Dr ya shigo tare da sallamah, Hajiya tayi saurin tashi bayan sun gaisa ta shiga yi mashi bayanin abunda ya faru, nan da nan Dr din yace tana ina? "Hajiya tace muje tana dakinta kai tsaye Dakin suka nufa, sun sameta a zaune tana ta zubar da hawaye, Hajiya dai ita a tsorace take don ba karamin shaka dazu tasha ba, tana ganinsu ta tashi da sauri ta rungume hajiyan tana fadin mumy maiya faru dani jikina sai ciwo yake min. Hajiya ta kara sa kuka tace khausar ba komai bari Dr ya dubaki. Tace to nan Dr ya Shiga yimata tambayoyi tana bashi amsa, harya gama ya bats wasu Magani yace tasha sannan ta dinga cin abinci a kan kari. Suka fito shida Hajiya bayan sun fito ne, Hajiya tace mai yake damunta Dr yayi dan murnushi yace Hajiya ulcer ne yana sa mutum yaita sumbatu in yayi yawa. Na bata harda maganin da zai sata ta dinga cin abinci sosai, ita dai kan Hajiya ya kulle, taya za'a ce khausar nada ulcer yanda take cin abinci mai uban yawa abun tun yana bama Hajiya tsoro harya daina, Dr ne ya katse mata tunanin da fadin Hajiya sai anjima, tace to ngd, gida ta koma kai tsaye Dakin khausar din ta nufa, tana shiga taga duk ta barbaza gashin kanta, kofan Dakin ya rufe, wutan dakin da yake fari ya koma kalan purple wata murya mai ban tsoro ta fara magana, kinyi kuskure kin aurar da khausar gun Wanda sai yaban wahala kafin in samu nasaran raba su, saina nuna miki kinyi kuskure duk da alamomin da muke nuna miki akan kar ayi auran amma kika qi, Hajiya dake gefe a tsorace ganin hannun khausar tayi yayi tsawo ta janyo ta Dashi tana wani irin dariya, Hajiya tana fadin khausar mumy dinki ce, ki sakeni. Amma ina bata ma San tana yiba, idon Hajiya ya kad'a yayi jaa saboda azaban matsan da ta mata, lokaci daya ta jefar da hajiyan gefe, Hajiya tayi saurin tashi tana nishi dakyar ta nufi kofa da nufin ta fita, amma kafin ta karasa sai taga wajan ya koma katon rafi da wasu manyan dutsuna a ciki. Khausar ta saki wani dariya mai ban tsoro tace ina zaki, na fada miki kinyi kuskure sai munyi maganin ki, Hajiya tayi karfin halin cewa mai nayi muku? dan ta fahimci ba khausar din bace. Wani maciji ne ya sauka a bakinta ya sareta aiko jini ya fara fita. Ta fara kuka, khausar tace har zaki iya tambayan mu bayan kin San kuskuran da kikayi. Ta saki dariya saiga wasu manyan macizai suna nufota duk macizan suna dariya suna fito da harshe suna nufot{truncated by whatsapp}

Maryam Obam😘😘👹👹BA'KIN ALJANI👹👹

                  6⃣to5🔟

✍�✍�✍�NA✍�✍�✍�
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA💁👑
😍😍Mrs Nura Kuriga😍😍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Dedicated to my fans😘

"Ganin suna nufota yasa ta fadi 'kasa su mamma, ta farka ta ganta a dakinta duk jikinta na mata ciwo ga bakinta na mata wani azaban zafi, taga khausar kusa da ita tana kuka, da sauri Hajiya ta tashi tayi bayi taga bakinta yayi mugun kumbura, ta fito khausar ta bita da kallo sannan tace mumy maiya sameki na tashi na ganki a dakina a kwance a 'kasa ina ta tashinki kinki ki tashi saida na kira Dr yace min wai akwai abunda ya harbeki, shine ya miki allura, Hajiya da ta kura ma khausar ido, babu abunda takeyi sai hawaye, maike faruwa ne? Khausar ce ta katse mata tunani da fadin mumy maiya harbeki? Hajiya dake hawaye tace niba ban San ko miye bane khausar, nan dai khausar din tayi shiru, Hajiya ta aiyana a ranta tabbas ya kamata ta kira barrister salman  ya dawo domin yasan abunda ake ciki, jin khausar din tayi tana dariya mai karfi tare da wani murya mai kaman na kuturu ta fara magana,"Hajiya wannan Kadan kika gani khausar tawa ce, saina azabtar dake kaman yanda nima kika min. Hajiya dake kan gado bata San sanda ta sauko tayo kasa ba, duk ta fita hayyacinta, jin khausar din tayi tana cewa mumy maiya sameki? Hajiya ta fashe da kuka tana fadin khausar tashi kije dakinki dan Allah, wani uban dariya khausar din ta kuma saki mai ban tsoro, tace hajiya kina da iko da khausar amma bamu ba, haka zaki kasance cikin kunci kaman yanda kika samu, hajiya ta kudun dune waje daya kukan ma yanzu ta kasa yi saboda tsoro, idon khausar taga yana canzawa yana komawa green ta kuma tsorata, wata iska ta gani yazo yayi sama da ita, tun daka lokacin bata kuma Sanin inda kanta yake ba, tadai farka ta ganta a cikin wani daji an daureta ga khausar nan tana ta rawa da kuma karan kida da take ji, duk ta tsorata can taga wata mai kama da khausar itama tazo, wata ta kuma zuwa, masu kama da khausar suka cika wajan baza ma ka gane wacece aini yin khausar din ba, sai rawa sukeyi kaman macizai, ga kidin da akeyi ba dadin ji, hajiya tayi mugun fita hayyacinta ji tayi kaman ana zaneta da bulala ta fara ihu tana fadin duk addu'an daya fado bakinta, lokaci daya aka tsaya da dukan, wani hayaki ta gani taga khausar a ciki tasa wani kaya na alfarma akan wani Kujera, tana dariya mai karfi, ta fara magana cikin wani yare, lokaci daya saiga wasu hallita sun fara bayyana mai ban tsoro, dukan su suna da kaho a Kansu sannan fuskansu sak irin na tsuntsu jikinsu irin na mutane, suna sanye da wani bakin yadi a jikinsu, suka fara nufota duk addu'an daya fado mata yi takeyi saida suka zo daf da ita, suka tsaya jin wani kara tayi mai razanarwa tun daka lokacin bata san inda kanta yake ba, tadai farka taganta a kwance a gadon asibiti, ga kuma babban danta dake gefe sai Barrister salman dake kusa Dashi, ganin ta farka da sauri ashraf ya fita kiran Dr, bai jima da fita ba saiga suka dawo tare da Dr, hajiya hawaye ke zuba a idonta domin tana tausayin Yar tata, amma yanzu tunda barrister yazo da dan sauki, Dr ya mata sannu da jiki sannan ya mata tambayoyi, yace ta rage yawan tunani domin jininta ya hau sosai, hajiya tace a sallameta ta koma gida, aiko haka akayi aka bata takardan sallama, suka nufi gida, alokacin da suka Shiga falo khausar ta fito cikin wani riga da wando ya kamata sai kamshin turare takeyi, barrister salman da tun shigowarsu ya kura mata ido cike da kaunarta, tana waigowa tagansu da gudu ta nufi hajiya ta rungumeta tana fadin mumy yanzu asibitin nake shirin zuwa, hajiya da duk ta tsorata da lamarin khausar din, tace an sallameni, nan ta waiga ta kalli ashraf tace bros kayi saurin zuwa gskiya, yayi dariya yace ki saki mumy karki fadar da ita mana, tayi dan murmushi ta waiga sai a sannan ta lura da barrister salman suna hada ido taji wani nugun faduwan gaba, kanta ya fara yimata wani azababban ciwo, mumy ta lura duk saita kara tsorata, khausar ta saki mumy da gudu tayi dakinta, duka suka bita da kallo cikin mamaki, ita hajiya tasan komai tsoro abun ya kuma bata, ashraf yace mumy wai maike damun khausar ne? Hajiya tayi murmushi tace kuje Ku kimtsa sai kuci abinci muyi magana a tsanake, kowa ya wuce da abunda yake sa'kawa a ranshi, mussaman barrister salman da abun yafi damunsh{truncated by whatsapp}

Maryam obam😘👹👹BA'KIN ALJANI👹👹

            1⃣1⃣to1⃣5⃣

✍�✍�✍�NA✍�✍�✍�
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA💁👑
😍😍Mrs Nura Kuriga😍😍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Dedicated to my fans😘

Yaga kaman khausar batayi farin ciki da ganinshi ba, kodan ya aureta ne? Ya fada toilet yayi wanka ya shirya cikin wasu kananan kaya sai kamshin turare yake yi, ga glass din dake idonshi ya kara mai kyau." Ita kuma khausar alokacin da tashi ga dakinta wani irin yanayi ta shiga, tare da jin tsoran barrister salman, zama tayi a dakinta tasa key, don bata ma San fita balle ta hadu da salman ta rasa dalilin haka. Ashraf da barrister suna zaune suna cin abinci saiga hajiya nan tazo itama ta zauna, "barrister yace mata ya jikin? Tace da sauki alhmdlh, ya dan kalleta yace hajiya wannan ciwon na bakin kifa? Hajiya tayi dan shiru kaman bazata yi magana ba, can dai tace barrister akwai matsla ashraf dake cin abinci yace mumy wai maike faruwa ne? Dazu naji security suna wani magana akan khausar Dana karaso wajansu sai kuma suka canza maganan, nan hajiya ta fada musu abunda ke faruwa,bata boye musu komai ba, dukansu sun shiga cikin damuwa ba Wanda ya iya furta kalma koda dayane a cikinsu, can dai ashraf yace mumy kodai ba'kin aljanni ne ya aureta? Sai yasa duk mazan data aura suke mutuwa, mumy itama kanta ta shiga rudani," tace anya ashraf nidai na rasa gane miye matsalan," sai a sannan barrister ya iya magana yace hajiya kina ganin matsalan bada ka kwakwalwanta yake ba? Bata taba irin wannan abun ba sai jiya,inaga mu kaita asibiti a dubata," hajiya ta danyi shuru can tace shikenan hakan yayi, suka ci gaba da cin abincinsu. Jin khausar sukayi tana ihu, da sauri suka nufi dakin suka bude, suka tsaya suna kallonta da mamaki, domin ganinta sukayi tana bacci,bayan yanzu sunji ta tana ihu, Hajiya dai a tsorace take. Dukan su suka kalli juna, ashraf ya karasa wajan da take kwance yana taba ta, aka shake mai wuya, khausar din ta fara dariya kaman mai hauka,barrister ya matsa kusa da khausar din domin ya taimaki ashraf ya kasa kwacenshi saida ta gaji dan kanta ta sakeshi, ashraf sai maida numfashi yake, idonshi yayi ja don azaba, itako khausar din bacci ya dauketa, haka dukansu suka fito daka dakin ashraf dakyar yake tafiya, kowa da abunda yake sakawa a ranshi, barrister yace ma hajiya wannan wani irin ciwo ne haka? Kodai gskiyan ashraf ne da yace ba'kin aljani ne ya shigeta. Hajiya tace nima abunda nake ta tunani kenan, ashraf yace mumy akwai wani mai bada Magani na yan bori kanwar abokina ta taba samun irin wannan laluran shiya bata Magani ta warke. Hajiya tace to kakirashi, ya doka ma Abokin nashi kira, bugu daya ya dauka, bayan sun gaisa yamai bayanin dalilin kiran nashi, yace bari ya turo mai number mutumin, yayi godiya, ko minti daya ba'ayi ba ya turo mai no din, ya kira mutumin ya dauka suka gaisa, yayi mai bayani, mutumin yayi dariya yace ai wannan mai sauki ne gobe da safe zanzo, sukayi sallama akan sai yazo goben, rufe kofan khausar din akayi da key, kowa ya nufi dakinshi. Washe gari da safe kaman yanda akayi alkawari damai Magani yako zo, bayan yayi nocking security suka tambaya waye yace mai Magani ne, suka bude mai gate suka mai iso har cikin falon gidan, suka Tarar da hajiya da ashraf barrister ya fita akwai Wanda suke San ganinshi, hajiya suka mai sannu da zuwa, aka cika shi da kayan ciye2 bayan ya gama suka mai bayanin komai yayi dariya yace aiko wani irin aljanine muna maganinshi duk taurin kanshi, sudai Su hajiya shiru sukayi, yace a Kai shi dakin ta, bayan sun Shiga suka ganta a zaune tana hawaye, ya kalli hajiya da ashraf yace su fita Su rufe kofan ta waje, karsu bude har sai ya basu izini, suka amsa da toh suka fita, ya matsa kusa da khausar da niyan ya taba ta yana kalan rawan yan bori, tashako mai wuya tako ina zuga mai bulala akeyi yana ta zunduma ihu, hajiya da ashraf duk sun rud{truncated by whatsapp}

Maryam Obam😘👹👹BA'KIN ALJANI👹👹

         2⃣1⃣to12⃣5⃣

✍�✍�✍�NA✍�✍�✍�
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA💁👑
😍😍Mrs Nura Kuriga😍😍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Dedicated to my fans😘

Wannan kake kira so bayan ka cuceta ka rabata da masu sonta? Ka kashe Su gabaki daya har lahira ba zasu sake dawowa ba, duk son da suke mata basu kaini ba, a halin da ake ciki yanzu ma bani Kadai bane ke sonta a cikin mu jinni mun kai mu dari da takwas masu sonta, "yanzu zaku rabu da ita ko Yaya? Bazan iya rabuwa da khausar ba ina sonta. Kai duk da ka cutar da ita kana cewa ba zaka fita ba ka kashe mata masoyanta. Ba laifina bane na iyayenta ne na nuna musu alama da yawa yanda ba zasu aurar da itaba suka ki, suka mata aure, alaman mai kaka nuna musu? Sau da yawa nakan sakar mata jini in zatayi al'ada nakan sa mata tayi wata uku zuwa hudu tana yi, tasha gayama mamanta tun tana daukan abunda muhim manci harta daina, nakan yawan sa mata taji bata San shiga cikin mutane, sannan ina yawan sa mata saurin fishi,da naga duk da wannan abun anaso a mata aure duk da ta nuna bata so da farko harta yarda, Nima saina bari ranan da aka Daura auran angon yayi hatsari ya rasu, na biyun kuma suna fira da abokanshi shima ya rasu, na ukun saida ta tare ranan farko shima ya rasu, tun daka lokacin kowa yake tsoran auranta duk da kudin da suke Dashi bamai sha'awan auranta kwasam saiga dan uwan babanta ya fito Wanda ya dade yana sonta hajiya ta amince aka Daura auran lokacin bikin ya tafi London, Ranan da yayi waya zai dawo a ranan na fara bayyana don bazan bari ta tare ba domin mata tace, yanzu haka mu wajan Dari uku ne a jikinta nida yarana duk muna kula da ita. Malam yace to duk naji yanzu inaso ka fita ka barta. Bazan fita ba bazan iya ba. Mlm ya kuma watsa mata ruwan dazu ta saki ihu sai juyi takeyi gashi an daureta, yaci gaba da karatu."ta fara fadin ya Isa haka zan fita yanzu,mlm yace to fita, tayi hati shawa so uku ta fadi sai bacci, mlm ya kalli hajiya yace to alhmdlh yanzu inta farka shikenan babu wani Matsala sai a godewa Allah, sannan ga wa in nan maganin kar ayi wasa dasu ta dinga shafawa sannan wannan zaitun ne da habba ta dinga sha, hajiya sukayi godiya suka mai shatara na arziki, mlm Habu shima anyi mai alkairi sosai suka wuce, daka barrister har ashraf ba Wanda yabar dakin suna zaune suna jiran farka wanta, har aka kira magrib bata farka ba, sai wajan 9 ta tashi tare da salati, tana tashi taga barrister da ashraf da mumy tazo zata mike taji jikinta babu kwari, tana magana a hankula tace Yaya salman yanzu nayi mafarkin kazo Ashe da gaske ne kaida ya ashraf, sukayi murmushi tare da hamdala, ta kalli hajiya tace mumy jikina kaman ammun duka nake ji, duk ba kwari, hajiya tayi murmushi tace ta tashi taje tayi wanka, ta tashi ta fada bayi tayi wanka ta fito alokacin Su barrister sun fita hajiya ce kadai a dakin, hajiya ta mika mata maganin tace daka yau wannan shine man shafawanki ta amsa ta fara shafawa, tun daka lokacin sauki ya samu aka fara maganan tare wanta gidan mijinta, barrister ya kammala ginin shi Wanda dan zaman da yayi da khausar sun shaku da juna sosai, hajiya ganin haka tace Su tafi gidansu tunda ya gama komai Allah ya muku albarka, suka amsa da amin, suka koma gidansu a ranan khausar ta zama babban mace kuma cikakkiyar mace, barrister yayi farin cikin yanda ya sameta. Duk wannanlokacin khausar na amfani da maganin ta, barrister yana lura da ita baya wasa wajan yaga tayi amfani dashi.
WAYE BARRISTER SALMAN?
barrister salman fari ne yana da dan tsawo amma ba sosai ba gashi yana da dan jiki amma ba za'a kirashi mai'kiba yana da yawan ibada dan kanin Alhaji Isa ne Baban khausar iyayenshi sun rasu a wani gobara da sukayi tun daka lokacin rikon shi ya dawo wajan alhaji isa, ya dade yana San khausar ganin kaman bata ra'ayin shi yasa bai gaya mata ba dan tasha fada ita bata San auran zumunci domin in baiyi dadi ba yakan bata zumunci, ganin son da yake mata yayi yawa yasa yabar kasar yaje London karatu inda ya karanta low, Alhaji Isa mahaifin khausar su biyu ya Haifa daka ashraf sai khausar ya auri hajiya sakina auran zumunci ne sukayi yana da kudi sosai ya rasu tun khausar na shekara Goma sha biyar Wanda a yanzu tana shekara ishirin da biyu, khausar chocolate colour ce tana da manyan ido ga hancinta dan siriri bakinta dan karami tana da kyau sosai tun tana karama mutane ke fadan kyanta gashi hajiya tana gyarata sosai, inka ganta sai kaji kaman ka sace ta don kyau, khausar kwatata bata San maganan aure tun mahaifiyarta tana ganin wasa take,biyu daka mazan data aura cikin abokan ashraf ne, Wanda duk suka mutu ranan auran, na ukun ne abokin barrister salman.

👹👹BA'KIN ALJANI👹👹

       2⃣6⃣to3⃣0⃣

✍�✍�✍�NA✍�✍�✍�
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA💁👑
😍😍Mrs Nura Kuriga😍😍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Dedicated to my fans😘

Ganin duk Wanda ya aureta yana mutuwa yasa kowa yake gudun ta, itako hakan ya mata dadi dan basan auran take ba, wani rana ashraf yaje London wajan barrister yayi mishi zuwan ba zata, alokaci salman yana falo yana kallon hotan khausar yana fadin khausar sonki zai kasheni Allah ya jarabe ni da sonki, waiga wan da zaiyi yaga ashraf yayi sauri ya boye hotan tare da fadin ashraf "wht a surprise" ashraf yayi murmushi tare da dafashi yace barrister dama kana son khausar shine kaki fada kabar abun a cikin ka, Haba dan uwa, nan barrister ya fada mai irin son da yake mata, da kuma dalilin shi na boyewa nan ashraf yayi murna ya dauki waya ya Kira hajiya ya fada mata komai takoyi farin ciki dajin labarin, salman yace ayi komai inya dawo saita tare nan yasa aka fara yimai gini, khausar ba karamin hauka tayi ba najin zata auri salman, ganin babu fashi yasa ta hakura ita kanta tana mamaki irin halaryanta haka dai akayi aure suna waya da salman jefi2 ranan daya ma hajiya waya akan zai dawo alokacin suna zaune da khausar suna fira, hajiya ta fada mata salman zai dawo inya dawo zata tare, shine sanadin bayyanan jinni dinta.Bayan shekara biyu khausar ce rike da jakan barrister da dan karamin cikinta na wata uku, tana tayi mai shagwaba tana fadin yanzu har sati daya zakayi? Yace ai kaman yanzu ne babyna tayi rau2 da ido ya sumbace ta a kumatu suka fita tamai rakiya ya wuce ta nufi gida, gabanta sai fadi yake tana shiga wani bacci mai nauyi ya dauketa sai wajan magrib ta farka, tana tashi taga wani bakin mage idonta green ta fasa ihu ta fad{truncated by whatsapp}

Maryam obam😘👹👹BA'KIN ALJANI👹👹

       3⃣1⃣to3⃣5⃣

✍�✍�✍�NA✍�✍�✍�
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA💁👑
😍😍Mrs Nura Kuriga😍😍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Dedicated to my fans😘

Kasa sumamma tun daka lokacin bata san inda kanta yake ba, barrister tunda ya tafi yaji hankalinshi bai kwanta ba, gashi ya kirata bata dauka ba. Kuma baya San kiran hajiya kar hankalinta ya tashi, tunda ya kira masu gadi sunce bata fita ba, hankalinshi ya dan kwanta, yadai yanke shawaran gobe zai dawo gida. Washe gari tunda yayi sallah asuba ya kamo hanya sai faman gudu yake kaman zai tashi sama, sai wajan takwas da wani abu ya Kawo, yana zuwa yayi horn mai gadi ya wangale gate ya shige, mai gadin na gaida shi baima San yana yiba, kofar falon ya nufa yana murdawa yaji abude, ya shiga bai ganta falo ba, ya nufi dakinta bai ganta ba, ya nufi nashi dakin tun kafin ya karasa gabanshi keta fadi yana zuwa yaga jini a wajan murda kofan, yasa hannu ya bude kofan yayi baya da sauri, tare da kara goge idonshi ganin khausar yayi gaba daya hallintan ta ya canza idonta yayi ja ga hakoranta sun zazza'ko gashin kanta duk a barbaje, ya kasa d'aga kafanshi wani kasala yaji ya rufeshi lokaci daya. Ta d'ago da kanta suka ha'da ido, ta kwashe da dariya tana kasa2 dakai tayi tsalle ta diro a gabanshi yana tsaye ya kasa komai, ta fara magana cikin wani murya mai ban tsoro barrister kayi laifi mai girma wanda saina horar dakai, da duk wanda ya rabani da khausar, ka aureta kuka sa aka 'ko nani nida sauran yarana kuka rabani da ita, yanzu na dawo ba wanda ya Isa ya fitar dani kuma dukanku saina nuna muku kunyi kuskure, a nan ne barrister ya fara magana kai azzalumi ne baka da imani sai wutar Allah taci ka, duk ka wahalar da khausar baka da tausayi kuma saina fitar dakai daka jikinta yanzun nan, ya dauko wayanshi da nufin ya kira Hajiya aiko ta shake mai wuya tare da jefar dashi ya fara ganin wani dishi2 ya kuma kokarin tashi ta d'aga hannu saiga wani abu kaman mashi ya sauka a hannunta amma bai kai tsawan mashi ba, tace baka isa ka fitar dani ba kuma saina dau fansa a duk Wanda suka fitar dani wancan karan, barrister ya bude baki zaiyi magana kenan ta chaka mai mashin a kirji, komai nashi ya tsaya cak, ta fashe da wani dariya mai sauti, ta kuma d'aga hannu saiga wata kwalba ta sauko a hannunta ta saka barrister cikin kwalban, tayi dariya tare da fadin bamai iya fitar dakai, ta rikide ta koma kalan barrister taje ta samu ma'aikatan gidan tace duk subar aiki ta sallame su, suka ce ranka ya dade lfya kuwa? yace eh kawai bana bukatan aikin ne, suka ce toh jiki a sanyaye suka fara hada kaya, har saida taga sun bar gidan kafin ta koma ciki. Hajiya na kwance wajan shabiyun dare taji kaman ana nocking tace waye haka Kodai ashraf ne? Anya kuwa shida ya tafi Dubai jiya to waye? Tashi tayi ta nufi falo kai tsaye kofan falon ta bude ba tare da tambayan waye ba, tana bude wa taga idanuwan mutane a jikin bango, wani jiri taji yana dibanta ta fadi tayi kasa,ta farka ta ganta a kwance a waje tayi saurin tashi tare da tunanin maiya kawota waje harta kwanta ta kasa tuna komai haka ta bude kofan falon jiki a sanyaye ta shiga, jinta take kaman wacce tayi shekaru bata gidan ganin komai tayi ya canza mata dakinta ta nufa ta kwanta bacci ya dauketa bata tashi ba sai wajan goma na safe,tana ta tunani tayi sallah ma kuwa, da sauri ta tashi ta nufi bayi tayi alwala tayi sallah tare da neman Allah yayi mata gafara, ashraf yana can Dubai amma hankalinshi ya kasa kwanciya kwana biyu sai mugayen mafarki yake, yana yawan mafarkin gashi a wani daji an daureshi da wasu igiyoyi, da mafarkan shanu nabinshi, ya dage da addu'a sosai, ranan daya cika sati a Dubai ya dawo gida, tunda yazo yaga hajiya ta canza gaba daya, wani zubin in tayi abu kaman karaman yarinya, shidai hankalinshi ya kasu kashi biyu dayan ban garan yakira khausar bata dauka haka ma barrister shiru, yaje gidan ya ganshi da kwado alaman basa nan dayan bangaran kuma hajiya da duk komai nata ya canza gashi ta dameshi da ya kawo mata khausar ya rasa miye mafita duk ya shige duhu ya rasa maike faruwa........... Hmmmm masu karatu muje zuwa, waiya ashraf zaiyi da mumy data dameshi da son ganin khausar? Sannan barrister dake cikin kwalban da bamai iya budewa. Lolz ko zaku zo muje mu gwada budewa ko zamu iya taimaka wa😜😜

Maryam Obam😘👹👹BA'KIN ALJANI👹👹

       3⃣6⃣to4⃣0⃣

✍�✍�✍�NA✍�✍�✍�
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA💁👑
😍😍Mrs Nura Kuriga😍😍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Dedicated to my fans😘

Ashraf ne kwance kan Kujera a falo ya rasa maike mishi dadi sai tunani yake wai ina barrister da khausar sukaje? Kuma basa daukan waya. Mumy ce ta katse mai tunani da fadin ashraf wai ba zaka kawo min khausar ba? Inba zaka ba bari ni inje da kaina yayi sauri ya tashi yana fadin mumy naje gidansu a rufe kuma basa daukan waya, ta kalleshi tayi shiru can dai tace to duk Inda suka Shiga ka dubo mun su, ya bude baki zaiyi magana ta dakatar dashi da fadin kar kace komai kawai kayi abunda nace,"yace toh mumy, ya koma ya kwanta tace ka tashi mana kaje, ya tashi ya dauki key din motanshi ya fita, yana tunanin wannan sabon abun, na farko dai khausar ba yarinya bace kuma tana tare da mijinta, amma mumy duk ta damu, kai tsaye gidan su khausar din ya nufa amma kaman kullum a kulle da kwado, zama yayi a mota ya kasa ko motsi ba abunda yake sai tunani, toh wai ina sukaje? Kaman daka sama yaji sallama yayi sauri ya amsa, wani mutum ne bayan ya gaida ashraf din, yace dan saurayi Ina ganinka kwanan nan kana yawan zuwa wannan kofan gidan ka tsaya kuma kana daukan lokaci a wajan shin anya lfya kuwa? "Ashraf da yayi shiru yana sauraranshi yace wallahi kuwa, gidan yayana ne sannan matanshi kanwata ce, kulum sai mun kira wayansu yana ringing amma basa dauka wajan kwana talatin kenan ga gidan kulle da kwado, duk wajan da nasan zan sami mijin naje babu lbri. Mutumin yayi shiru can dai yace to anya lafiya kuwa? Ni kaga ga gidana can kusa da gidan barrister gidan yake,yaci gaba da fadin kuma ina yawan zama a waje don nayi ritaya, toh amma akwai wani abu dake ban mamaki wani zubin nakan ga gidan ba kwado inna zo zan tura yaki buduwa dan akwai Wanda yaban sa'ko inba mai gidan, haka zanyi ta zama ko masu gidan zasu fito tunda naga babu kwadon inna dan Shiga gida kalan in zaga kafin in fito sai inga an mayar da kwadon, toh wannan abun yana daure min kai. Nan dai ashraf yayi shiru ya rasa abun cewa, can dan dattijon mutumin yace to koh zaku balle kwadon ashraf yayi saurin kallonshi da murnushi a fuskanshi yace aiko wannan shawaran yayi, amma bari inje in dauko mumyna ayi komai a gabanta, mutumin yace hakan yayi, inka dawo saika min sallama in fito yace toh ya figi mota, kai tsaye gida ya nufa yana zuwa yayi parking ya fito tun kafin ya karasa falon yake jin ihun hajiya tana fadin khausar khausar khausar da sauri ya karasa yana bude kofan ta kura mai ido da alaman tambaya, shima haka ta ban garanshi don yayi zaton ko khausar dince tazo, ta kalleshi tace ina khausar din? Yayi shiru ya kasa cewa komai dan yanda ta daure fuska, ta daka mai tsawa bada kai nake ba? Ina khausar ka fadamin ta matso kusa dashi ta wanka mai mari tare da fadin kar kace min baka ganta ba, yace mumy kiyi hakuri insha Allah duk inda suke na tabbata suna lfya, yanzu nazo ne dama mu.... Kafin ya karasa sai ganinta yayi ta fadi duk ya rikice ya nufeta da sauri yana fadin mumy mumy plz wake up mumy lokaci daya ya dauketa yayi mota da ita asibiti ya kaita suna zuwa akai emergency da ita, an dauki lokaci kafin ta farfado tana tashi ta fara khausar cikin murya mai karfi ta cika asibitin da kiran khausar, ashraf babu abunda yake sai kuka kaman karamin yaro yana tambayan kanshi shin wannan wani Sabon al'amari ne ya samesu, mumy ta koma kaman mai hauka ganin haka aka mata gwajin kwakwalwanta amma babu matsala gashi an mata alluran bacci taki yi, kwananta uku a asibiti duk ta fita hayyacinta ganin haka doctor ya kira ashraf yace dole a kawo mata khausar indai ana son ceton rayuwanta domin indai ba'a kawo ta ba gskiya komai zai iya faruwa, ashraf yayi shiru can yace doctor wlh duk yanda baka zato na duba khausar Amman ban ganta ba, har gidan TV na bada cigiya amma shiru, doctor yace to yanzu inaga ashraf inaga zan Baku sallama in yaso zan dinga zuwa gida ina dubata, dan inaga kaman hakan zaifi, ashraf yace nima haka nayi tunani gwara mu koma gidan. A ranan suka koma gida. Yaci gaba da neman khausar da barrister amma shiru babu labarinsu yanzu wajan shekara daya kenan, hajiya bata ko magana ta daina ihun da takeyi kullum tana zaune shiru hawaye na zuba a idonta, ashraf duk ya rame yayi dan duhu, kullum cikin zarya yake shiru ga doctor yace mai hajiya yawan tunanin da takeyi ya taba zuciyanta idan ba'ayi wasa ba komai zai iya faruwa. Tashin hankali ba'a magana wajan ashraf, wasa wasa abu har yayi shekara biyu shiru in mutum yaga hajiya da wuya ya ganeta domin gaba daya ta fita hayyacinta. Ashraf ne zaune a falo yayi uban tagumi saiga family doctor dinsu ya shigo harya matso kusa dashi bai sani ba saida ya taba shi yayi firgit ya d'aga kai yana kallonshi yace doctor Kaine? Dr yayi murmushi yace nine ashraf bayan sun gaisa ya tambayeshi jikin hajiyan yace da sauki, dr yace ashraf kasan wani Abu kuwa? Ashraf yace a'ah dr saika fada, dr  yace a gskiya ciwan hajiya yana daure min kai kasan kwanaki nacema zuciyanta yawan tunanin da takeyi zai haifar mata da Matsala, amma yanzu komai nata normal ashraf sorry to say anya hajiya ba matsalan jinni bane dan yawanci irin abubuwan da takeyi haka wata Yar uwata tayi mukai ta Magani sai daka baya aka gane, ashraf yayi sauri ya tashi yace tabbas sai yanzu na tuna ya dauki waya ya kira malamin daya taba yima khausar rukiya bugu daya yayi ya dauka yamai bayanin halinda ake ciki sannan yace mai ya taimaka yazo yanzu mlm yayi dariya yace shikenan dan ya gane matsalan sukayi sallama akan gashi nan zuwa, ya kalli dr yace gskiya na gode wlh da banyi wannan tunani..... Kafin ya karasa dukansu suka tashi cikin tsoro...... Hmm muje zuw{truncated by whtsapp}

Maryam Obam😘👹👹BA'KIN ALJANI👹👹

       4⃣0⃣to4⃣5⃣

✍�✍�✍�NA✍�✍�✍�
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA💁👑
😍😍Mrs Nura Kuriga😍😍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Dedicated to my fans😘

"Khausar suka gani cikin wani irin hallita fuskanta a daure ta tsaya tana kallonsu, ta fara magana cikin wani murya kayi kuskure ashraf duk da kai ban taba kaba amma yanzu zan nuna ma kuskuranka ta fara matsowa kusa dasu doctor dai suman tsaye yayi don ya tsorata, ganin ta kusa zuwa gab dasu ashraf yayi sauri yayi baya tasa hannu ta janyo shi ta shake mai wuya idonshi ya 'kada yayi jah don azaba yana fadin khausar ki sakeni,tun yana magana har ya kasa, doctor ya hango moper yayi saurin zuwa ya dauka yazo ya bugama khausar ta waiga ta saki ashraf ta chafko doctor shima tayi wurgi dashi ya fadi kasa sumamme, ta kara nufan aahraf ya fara Jan jiki ta daga hannu saiga wani abu kaman wuka a hannunta ta nufeshi harta cinmai ta d'aga shi sama ta d'aga wukan zata soka mai a kirji yayi saurin fara karanta ayatul kursihu, lokaci daya tayi jifa dashi ta tsaya tana kallonshi ta rikid'e ta koma wani hallita mai ban tsoro ta nufeshi ta kara shako mai wuya a dai2 lokacin malam ya shigo, yana ganin haka yayi saurin Ciro abu a roba yako yi sa'a ya watsa mata nan da nan ta saki ashraf ta fadi kasa saiga ainiyin halintan ta yadawo, aahraf yayi sauri yayi baya yana nishi dakyar, Malam ya nufeta ya kara watsa mata ruwan ta saki wani ihu Wanda saida gidan ya girgiza, a dai2 lokacin hajiya ta fito ashraf yayi mamaki ita dako motsi bata yi amma gashi yanzu ta fito, tana ganin malam ta fara fara'a ta nufoshi tana zuwa wajan da yake ta shake shi tayi wurgi dashi a dai2 lokacin khausar ta tashi ta fara dariya saiga masu kama da khausar sun cika falon, hajiya ta kuma nufan shi tazo zata taba shi yako watsa mata wani ruwa tayi 'kasa saiga halintan da suka fito masu kama da khausar sun fara bacewa, saida ya rage mutum daya san nan ta fadi kasa itama nan da nan Malam ya kara Ciro wasu abubuwa cikin gora har guda uku ya war watsa musu suka fara ihu tare da fadin karka 'kona mu, amma Malam ko sauraransu baiyi ba yaci gaba da watsa musu, wani iska mai karfi ya gauraye wajan saiga kwalban da akasa barrister a ciki, ashraf dake gefe yana kallon ikon Allah ganin barrister a kwalba ya tsorata shi, Malam ya fara karatu yana watsa musu ruwan suna ihu, khausar ta fara fadin karma 'kona mu zamu fita, Malam yace mai yasa ka kuma dawowa jikinta bayan ka fita? Yace na dawo ne saboda tayi wasa da maganinta da farko mijinta yana matsa mata akan tayi amfani dasu har aiyuka suka mai yawa bai cika zama ba itako saita daina amfani dashi gashi inata neman hanyan da zan dawo, ban samu ba saboda duk da bata amfani dashi mijinta baya bari tana wasa da ibada sannan koda yaushe tana cikin tsarki amma daka baya saita daina, tasa wasa na fara kokarin in dawo sai naga kafin in dawo ya kamata in tura mijinta wani waje ta yanda shima zanyi amfani dashi yanda ko nashiga bazan fita ba, kuma inaso in dau fansa akan fitar dani da akayi wancan karan har aka 'kona ni da yarana bayan mijin ya tafi shine na shiga jikinta ranan, da yaje garin da yaje yana ta kiranta bata dauka ba duk ya rude ya kasa zama washe gari da asuba ya taso yana zuwa ya ganta a wani yanayi shine har nayi nasaran sashi a kwalba na rufe sannan itama hajiya na tura mata yarana jikinta amma ita nata sai nasa su sa mata kaman hauka yanda ba za'a gane wani abuba, sannan koda yaushe suna amfani da zuciyanta su sata tana son ganin khausar, duk ta matsa ma ashraf ya memo mata khausar koda yaushe yana ta zarya amma babu labari, ta haka nake ta daukan fansa, ina amfani da hajiya ina horar da ashraf domin yarana sun kasa shiga jikinshi tun abunda ya faru da khausar na farko baya wasa da tsayuwan dare kuma koda yaushe yana cikin tsark{truncated by whtsapp}

Maryam obam😘

👹👹BA'KIN ALJANI👹👹

       4⃣5⃣to5⃣0⃣

✍�✍�✍�NA✍�✍�✍�
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA💁👑
😍😍Mrs Nura Kuriga😍😍
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨
Dedicated to my fans😘

Ganin haka sai muka shiga jikin hajiya muke wahalar dashi, shima, tana Zuwa nan tayi shiru, Malam yace to yanzu ku kun kyauta kenan kun shiga jikin bayin Allah kuna wahalar dasu ba tare da sunyi muku komai ba, saboda mugunta kuna ta cutar dasu, yanzu zaku fita koya? Khausar tace baza mu iya fita ba mun shigo kenan. Malam yace haka kukace dan kunga ina lallaba Ku, shine kuke fadin haka, khausar ta tintsire da dariya tare da fadin komai za kayi ba inda zamu, hajiya itama ta fara magana gwara ka rabu damu tun kafin kaima muma illa ta fara kokarin tashi ganin haka Malam yayi saurin watsa mata ruwan goran dake hannunshi ta saki kara, ya fara karatu suna ta bashi hakuri tare da fadin kabar 'kona mu bai tsaya da karatun ba yaci gaba dukansu suka fara magana cikin wani yanayi suna bashi hakuri akan ya tsaya shidai bai tsaya ba suna cikin haka kwalban da akasa barrister ta bude sai gashi yana fita kaman ana zaro shi, Malam duk da haka bai tsaya ba suka fara fadin munyi alkawari bazamu sake dawowa ba ka kona mu sosai mun tuba, sai a sannan Malam yace Su fita kaman jira suke dukansu a tare sukayi hatti shawa sau uku, suka fadi kasa bacci ya daukesu harda barrister kaman minti ishirin suka farka tare da salati ashraf dake gefe yana hawaye cike da tausayinsu yayi sauri ya matso ya rungume hajiya yana kuka tare da fadin sannu mumy, haka yayi masu barrister da khausar, Malam ya watsama doctor ruwa ya farfado tare da fadin dan Allah karki kasheni, ganin su mumy suna kallonshi ya fara sosa kai dan yaga alaman komai yayi normal, nan Malam yayi masu hajiya bayanin abunda ya faru dasu hajiya har saida tayi kuka tare da yima Malam godiya, ya basu Magani sannan yayi musu sallama hajiya ta mishi sha tara na arziki, sannan doctor yaba barrister Magani na ciwan dake kirjin shi da allurori, hajiya tace yaje ya huta da taimakon ashraf yaje dakinshi nada kafin yayi aure khausar itama tabi bayansu, saida yayi wajan wata daya kafin ciwan ya warke ya dawo kaman bashi ba, wani shakuwa ne ya kara shiga tsakaninshi da khausar da kuma San juna sun koma gidansu khausar ta kara samun wani cikin murna wajan barrister ba'a magana sai tattalinta yakeyi.
" Bayan shekara biyar ashraf ne da matarshi mai suna Nafeesa da dansu Wanda baifi shekara biyu ba, gefe kuma khausar da barrister sai hajiya suna zaune suna ta fira Yaran khausar biyu yanzu da Jidda, sai Khalid, suna rayuwa cikin jin dadi da annashuwa nima dai anan zan tsaya.
ALHMDULILLAH

GODIYA YA TABBATA GA ALLAH ( S W A) DA YABANI IKON KAMMALA WANNAN DAN GAJERAN  LABARIN. TSIRA DA AMMINCIN ALLAH SU TABBATA WAJAN FIYYAN HALITTA ANNABI MUHAMMAD ( S A W)

INA FATAN WANNAN LITTAFIN YA NISHDAR DAKU DUK DA BAIYI TSAWO BA, AKODA YAUSHE FARIN CIKIN MASOYA NA SHINE NAWA.

LUV U OL MY FANS😘😘😘
MARYAM OBAM😘

0 Response to "BAKIN ALJANI"

Post a Comment