ZIRS Ta Fara Shirye-shiryen Daukar Sabbin Ma’aikata 75 a Jihar Zamfara
ZIRS Ta Fara Shirye-shiryen Daukar Sabbin Ma’aikata 75 a Jihar Zamfara
Hukumar Tara Haraji ta Jihar Zamfara (Zamfara State Internal Revenue Service – ZIRS) ta sanar da shirye-shiryen daukar sabbin ma'aikata guda 75 domin yin aiki a sassa daban-daban na hukumar.
Wannan mataki na zuwa ne bayan amincewar Mai Girma Gwamnan Jihar Zamfara, Dr. Dauda Lawal, na daukar sabbin ma'aikata domin karfafa ayyukan hukumar da inganta ayyukan tara haraji a jihar.
Gwamnan ya kuma bayar da umarnin tabbatar da adalci da samar da dama iri daya ga dukkan masu neman aikin da suka cancanta a fadin jihar.
A cewar sanarwar hukumar, an shirya bude shafin neman aikin daga ranar 6 ga Disamba, 2025 zuwa 3 ga Janairu, 2026.
Tsarin daukar ma'aikatan zai kunshi karbar takardun neman aiki, tantance cancantar masu nema, tabbatar da ingancin takardun karatu, jarabawar kwamfuta (CBT), jarabawar rubutu da kuma tattaunawar baki (Oral Interview).
Hukumar ta bayyana cewa za a zabi mutane 75 bisa cancanta, ka'idojin da aka tsara da kuma dokokin aikin gwamnati.
Yaushe Za a Fara Daukar Ma'aikatan ZIRS?
Masu sha'awar neman aikin da kuma sauran al'umma za su ci gaba da bibiyar sanarwar hukumar domin samun sahihin bayani kan fara aikin daukar ma'aikatan da sauran matakan da za a dauka.
Hukumar ZIRS ta kuma jaddada muhimmancin adalci da bai wa dukkan masu cancanta damar shiga wannan aikin.
Sanarwa daga:
Management
Zamfara State Internal Revenue Service (ZIRS).
0 Response to "ZIRS Ta Fara Shirye-shiryen Daukar Sabbin Ma’aikata 75 a Jihar Zamfara"
Post a Comment