NEYIF Ta Buɗe Gurbin Aikin Field Enumerator a Borno
NEYIF Ta Buɗe Gurbin Aikin Field Enumerator a Borno
North East Youth Initiative for Development (NEYIF) ta fitar da damar neman aikin Field Enumerator domin gudanar da ayyukan tattara bayanai da sa ido a ƙarƙashin shirin INSEIP.
MUHIMMAN BAYANAI
Kungiya: North East Youth Initiative for Development (NEYIF)
Matsayi: Field Enumerator
Wurin aikin field: Kaga LGA, Jihar Borno
Wurin reporting: Damaturu, Jihar Yobe
Nau'in aiki: Daily Work
Ranar rufe neman aiki: 2 Oktoba 2026
GAME DA AIKIN
Wadanda za a zaɓa za su taimaka wajen tattara bayanai da gudanar da ayyukan sa ido a cikin al'ummomin da aka ware.
Ana buƙatar masu neman aikin su kasance masu gaskiya, ƙwarewa, iya sadarwa da kuma kula da sahihancin bayanan da suke tattarawa.
WANDA ZAI IYA NEMA
Mai nema ya kasance yana da ɗaya daga cikin waɗannan takardun karatu:
National Diploma (ND)
Nigeria Certificate in Education (NCE)
Higher National Diploma (HND)
Bachelor's Degree
FANNONIN KARATU
Masu karatu a waɗannan fannoni ko makamantansu ana ƙarfafa su su nema:
Social Sciences
Development Studies
Statistics
Public Health
Agriculture
Community Development
Sauran fannoni masu alaƙa.
SHARUDDAN HARSHE
Iya Turanci yana da muhimmanci.
Iya Hausa ƙarin fa'ida ne.
Iya Kanuri ƙarin fa'ida ne.
WAJEN AIKI
Aikin field zai gudana ne a Kaga Local Government Area, Jihar Borno.
WURIN REPORTING
Masu aikin za su riƙa kai rahoto a Damaturu, Jihar Yobe.
YADDA ZA A NEMA
Masu sha'awar aikin da suka cika sharuddan su gabatar da application ɗinsu da kansu a ofishin NEYIF da ke:
NEYIF Office
Plot 165–167, VBTR/026/R
Don Eliebet Housing Estate Extension
Damaturu, Yobe State
MUHIMMIN BAYANI
Masu cika sharuddan ne kawai za a yi la'akari da su.
Masu nema su tabbatar sun cika mafi ƙarancin sharuddan karatu.
Dole ne mai nema ya kasance a shirye don gudanar da aikin tattara bayanai a wuraren da aka ware.
Sanin Hausa da/ko Kanuri na iya zama ƙarin fa'ida wajen mu'amala da al'ummomin da za a gudanar da aikin.
RANAR ƘARSHE
2 Oktoba 2026
Masu sha'awar aikin su hanzarta gabatar da application ɗinsu a ofishin NEYIF da ke Damaturu kafin ranar ƙarshe.
0 Response to "NEYIF Ta Buɗe Gurbin Aikin Field Enumerator a Borno"
Post a Comment