KA MANTA LAMBAR RAJISTARKA (APPLICATION ID) TA CDCFIB? Ga Yadda Za Ka Dawo Da Ita Cikin Sauƙi
Yayin da hukumar CDCFIB ke shirin fitar da sunayen waɗanda suka yi nasara (Shortlist), masu nema da dama suna fuskantar matsalar manta lambar rajistarsu, wato Application ID. Wannan lamba tana da matuƙar muhimmanci domin ita za ka yi amfani da ita wajen duba sunanka ko buga takardar shaidar jarabawa.
Idan kana ɗaya daga cikin waɗanda suka manta tasu lambar, kada ka damu. Ga matakan da za ka bi daki-daki domin dawo da ita:
Matakan Dawo da Application ID:
Shiga Shafin Yanar Gizo na CDCFIB:
Ziyarci dandalin rajista na hukumar ta hanyar latsa wannan adireshin: https://recruitment.cdcfib.gov.ng/
Nemo Wurin Dawo da Lamba:
A jikin shafin, nemo inda aka rubuta "Forget Application Number? Retrieve it Here" (Ka manta lambar neman aiki? Dawo da ita a nan) sannan ka danna.
Shigar da Lambar NIN:
Sanya lambar shaidar ɗan ƙasarka (NIN) guda sha ɗaya (11) a filin da aka tanada.
Shigar da Lambar Waya:
Sanya lambar wayar da ka yi amfani da ita lokacin da kake cike aikin.
Shigar da Sunan Uba (Surname):
Rubuta sunanka na gida ko sunan mahaifi (Surname/Last Name) yadda yake a jikin takardunka.
Tantance Lambar Tsaro (Security Code):
Za ka ga wasu lambobi ko haruffa a jikin hoton tsaro (Security Verification Code), ka tabbatar ka rubuta su yadda kake ganinsu.
Tantancewa (Validate):
Bayan ka cike dukkan bayanan, danna maballin "Validate" domin na'urar ta tabbatar da bayanan naka.
Dawo da Lambar (Retrieve):
Daga ƙarshe, danna maballin "Retrieve". Nan take lambar taka ta Application ID za ta bayyana a jikin fuskar wayarka ko kwamfuta.
Shawara ta Musamman:
Da zaran lambar taka ta bayyana, tabbatar ka yi Screenshot ko ka rubuta ta a wuri mai kyau domin kada ka sake mantawa da ita.
Kada ka manta ka tura wannan bayani (Share) ga 'yan uwa da abokan arziki waɗanda suke fuskantar irin wannan matsalar.
Domin samun sabbin rahotannin guraben aiki da dukkan matakan CDCFIB kowace rana, ku ci gaba da bibiyar shafinmu na Haskenews.com.ng.
0 Response to "KA MANTA LAMBAR RAJISTARKA (APPLICATION ID) TA CDCFIB? Ga Yadda Za Ka Dawo Da Ita Cikin Sauƙi"
Post a Comment