-->

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL

FOLLOW HASKE NEWS WHATSAPP CHANNEL
To continue receiving our daily updates on news, jobs, and opportunities, please follow our new channel above, Thank you for your continued support Haskenews Media & Publishing Services
Ina Masu Takardar SSCE, Diploma, NCE, HND, BSc, BEd, BA, MSc da PhD Gidauniyar OHRI na Neman Ma’aikatan Sa-kai (Volunteers)

Ina Masu Takardar SSCE, Diploma, NCE, HND, BSc, BEd, BA, MSc da PhD Gidauniyar OHRI na Neman Ma’aikatan Sa-kai (Volunteers)

Ina Masu Takardar SSCE, Diploma, NCE, HND, BSc, BEd, BA, MSc da PhD Gidauniyar OHRI na Neman Ma’aikatan Sa-kai (Volunteers)

Gidauniyar One Health Resilience Initiative (OHRI), wata ƙungiya mai zaman kanta (NGO) da aka yi wa rajista a Najeriya, tana sanar da buɗe shafin ɗaukar rukunin farko na ma’aikatan sa-kai (Volunteers) domin cike guraben ayyuka daban-daban a cikin ƙungiyar.

Game da Gidauniyar OHRI:

OHRI tana aiki ne wajen inganta lafiyar mutane, dabbobi, da muhalli ta hanyar haɗa ayyukan kiwon lafiyar al’umma, yaƙi da sauyin yanayi, kare muhalli, da kuma ƙarfafa al’umma. Ƙungiyar tana gudanar da ayyukanta a jihohin Adamawa, Gombe, Jigawa, Kano, Taraba, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja (FCT).

Muhimmiyar Sanarwa:

Waɗannan guraben ayyuka ne na sa-kai (unpaid volunteer positions), kuma a halin yanzu ba a biya albashi. An tanade su ne domin mutanen da ke son samun gogewar aiki a fannin ci gaban al’umma. Masu aikin sa-kai za su amfana da:

  • Samun takardar shaida (Certificate)

  • Faɗaɗa sanayya da ƙwararru (Networking)

  • Samun fifiko wajen ayyukan da ake biyan albashi a nan gaba idan ƙungiyar ta samu ƙarin tallafi

Guraben Ayyukan da Ake Buƙata:

  • Programs & Technical Manager

  • Support Staff (Driver / Cleaner / Security)

  • Community-Based Organization (CBO) Representative

  • Community Champion / Volunteer

  • Field & Office Assistant

  • Safeguarding & Inclusion Focal Person (State)

  • State Finance & Admin Officer

  • State MEAL Officer

  • Project Officer (State Level)

  • State Coordinator

  • Security Focal Person

  • ICT Officer

  • Procurement & Logistics Officer

  • HR/Admin Officer

  • Operations Manager

  • Compliance Officer

  • Accountant

  • Finance Officer

  • Finance & Compliance Manager

  • Knowledge Management Officer

  • Research & Data Analyst

  • M&E Officer

  • MEAL Manager

  • Communication Officer

Yadda Za a Cike:

Masu sha’awar wannan dama kuma masu cancantar da ake buƙata za su iya cike takardun neman aikin ta hanyar latsa adireshin da ke ƙasa:

Hanyar Cikewa (Link):
https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSeWg69MuVvFfhhmQPHGQAcNDvGBeogCau7Axy0x3TbAGs5LKw/viewform

Wannan dama ce ta musamman ga matasa da masu neman gogewa a manyan ƙungiyoyin ci gaban al’umma. Domin samun sabbin rahotannin guraben aiki kowace rana, ku ci gaba da bibiyar shafinmu na Haskenews.com.ng.

0 Response to "Ina Masu Takardar SSCE, Diploma, NCE, HND, BSc, BEd, BA, MSc da PhD Gidauniyar OHRI na Neman Ma’aikatan Sa-kai (Volunteers)"

Post a Comment