Gwamnatin Tarayya ta sanar da buɗe wata sabuwar dama ta tallafin kuɗi ga ‘yan kasuwa masu rajistar kasuwanci a Hukumar yi wa Kamfanoni Rajista (CAC). A ƙarƙashin wannan tsari, za a raba tallafi tsakanin naira miliyan ɗaya (N1,000,000) zuwa naira miliyan uku (N3,000,000) ga waɗanda suka cancanta. Yanzu haka shafin yanar gizon shirin yana tafiya yadda ya kamata.
An ware jimillar naira biliyan ɗaya ga waɗanda za su amfana da shirin. An tsara wannan tallafi ne domin ƙarfafa ƙanana da matsakaitan ‘yan kasuwa (MSMEs) a faɗin ƙasar, tare da inganta harkokin kasuwanci da samar da ayyukan yi.
A cewar bayanan da aka fitar, masu son cin gajiyar wannan damar dole ne su gabatar da wasu muhimman takardu, ciki har da takardar shaidar rajistar kasuwanci daga CAC da sauran takardun da suka shafi kasuwancinsu.
Haka kuma, ana buƙatar masu nema su gabatar da gajeren bidiyo na kusan mintuna biyu a harshen Turanci, inda za su bayyana yanayin kasuwancinsu, yadda yake gudana, da kuma dalilin da ya sa suka cancanci samun wannan tallafi.
Masu sha’awar shiga shirin na iya yin rajista ta yanar gizo ta wannan adireshin:
https://msmeclinics.gov.ng/award-apply/
Ana sa ran wannan shiri zai taimaka matuƙa wajen bunƙasa kasuwanci da tallafa wa ‘yan Najeriya masu ƙoƙarin dogaro da kai.
Allah ya ba da sa’a ga duk masu nema.
0 Response to "SABUWAR DAMAR TALLAFIN KUƊI GA 'YAN KASUWA DAGA GWAMNATIN TARAYYA"
Post a Comment