Sanarwa ga Masu Neman Tallafin NAMP: Sabon Portal Ya Fito, Ku Shiga Ku Kammala Aikace-aikacenku
Sanarwa ga Masu Neman Tallafin NAMP: Sabon Portal Ya Fito, Ku Shiga Ku Kammala Aikace-aikacenku
Masu neman tallafin National Agricultural Mechanization Program (NAMP) sun fara samun saƙo daga shirin wanda ke nuna cewa an matsar da duk bayanan aikace-aikacen su zuwa sabon portal na yanar gizo.
Wannan shiri na National Agricultural Mechanization Program ana gudanar da shi ne tare da haɗin gwiwar Bank of Agriculture da kuma Heifer International domin tallafawa manoma ta hanyar samar da kayan aikin noma na zamani da kuma ƙarfafa harkar noma a Najeriya.
A cikin saƙon da aka aikawa masu nema, an bayyana cewa an migrates (matsar) da duk bayanan aikace-aikacen da aka cika a baya zuwa sabon portal. Duk da haka, aikace-aikacen yana nan a matsayin Draft, wato har yanzu ba a tura shi domin a duba ba.
Abin da Masu Nema Za Su Yi
Masu neman tallafin suna buƙatar su shiga sabon portal domin su:
Duba bayanan aikace-aikacen su
Cika duk wani bayani da bai kammala ba
Sannan su submit aikace-aikacen domin a fara duba shi
Idan ba a submit aikace-aikacen ba, ba za a iya tantance shi ba.
Hanyar Shiga Portal
Masu nema za su iya shiga portal ɗin ta wannan adireshi:
http://namp.bankofagriculture.com/login
Bayan shiga portal, yana da matuƙar muhimmanci a canza password ɗin da aka ba ku nan da nan domin kare bayananku.
Muhimmin Shawara
Masu neman tallafin NAMP su tabbatar sun shiga portal ɗin da wuri domin su kammala aikace-aikacen su kafin lokacin rufe karɓar aikace-aikacen ya wuce.
Haskenews zai ci gaba da kawo muku sabbin bayanai game da tallafin noma, damarmaki ga manoma, da shirye-shiryen gwamnati da za su amfani al’umma.

0 Response to "Sanarwa ga Masu Neman Tallafin NAMP: Sabon Portal Ya Fito, Ku Shiga Ku Kammala Aikace-aikacenku"
Post a Comment