Kamfanin Sydani Group ya sanar da bude guraben aiki ga kwararrun matasa maza da mata domin cike gurbin matsayin LGA Supervisor a karkashin aikin TRACK-Zero Project da ke gudana a Jihar Sokoto.
Wannan babban aiki ne da aka tsara shi domin inganta harkar rigakafi (immunization) da tabbatar da cewa dukkan yara sun samu kulawar da ta dace, musamman wadanda ba su taba samun rigakafi ba.
Bayanai Game Da Aikin:
Wurin Aiki: Jihar Sokoto.
Matsayi: LGA Supervisor (Mai kula da ayyuka a matakin karamar hukuma).
Wadanda Za Su Iya Nema: Masu Diploma, HND, ko Digiri (Degree).
Abubuwan Da Ake Bukata (Requirements):
Dole ne mai nema ya kasance yana da shaidar karatu ta Diploma, HND, ko Digiri a fannin da ya dace.
Yana da kwarewa a harkar gudanar da kididdiga (enumeration) ko ayyukan rigakafi.
Yana da basirar jagoranci da iya tsara rahoto (reporting skills).
Iya magana da harshen Hausa da Turanci (English) sosai.
Iya hulda da shugabannin al'umma da sauran masu ruwa da tsaki.
Ayyukan Da Za A Gudanar:
Kula da tafiyar da ayyukan shirin TRACK-Zero a matakin kananan hukumomi.
Jagoranci da horar da ma'aikatan wucin gadi (ad-hoc staff) da ke fita fage.
Tuntubar shugabannin al'umma domin wayar da kan mutane kan muhimmancin rigakafi.
Tattara bayanai da gabatar da rahotanni kan nasarorin da aka samu.
Yadda Za A Cike (How to Apply):
Idan kana da sha'awar wannan aiki kuma ka cika sharuddan da ake bukata, zaka iya amfani da wannan mahadar (link) da ke kasa domin cike fom din neman aikin:
Danna Nan Domin Cikewa: https://office.sydani.org/job_application/new?job_title=LGA%20supervisor%20-%20TRACK-Zero%20Project
Wannan babban zarafi ne ga wadanda ke da kishin inganta lafiyar al'umma a Jihar Sokoto. Ku hanzarta cike naku kafin lokaci ya kure.
0 Response to "GURABAN AIKI: Sydani Group Na Neman Masu Diploma, HND, Ko Degree Domin Aikin ‘LGA Supervisor’"
Post a Comment