-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Gidauniyar CATAI Ta Bude Shafin Daukar Ma'aikata Masu ND/NCE, HND, Da Digiri Domin Aiki A Arewa (2026)

Gidauniyar CATAI Ta Bude Shafin Daukar Ma'aikata Masu ND/NCE, HND, Da Digiri Domin Aiki A Arewa (2026)

Gidauniyar CATAI Ta Bude Shafin Daukar Ma'aikata Masu ND/NCE, HND, Da Digiri Domin Aiki A Arewa (2026)



Hukumar Centre for Advocacy, Transparency, and Accountability Initiative (CATAI), wadda take daya daga cikin manyan kungiyoyin matasa masu fafutukar jinkai da ci gaban al'umma a Arewa maso Gabashin Najeriya, ta sanar da bude shafin daukar sabbin ma'aikata domin gudanar da ayyukanta na shekarar 2026.

Wannan dama ce ga kwararrun matasa maza da mata masu kishin taimakawa al'umma a fannoni daban-daban kamar ilimi, lafiya, da kare hakkin bil'adama.

Wadanda Za Su Iya Nema:
Ana neman mutanen da ke da wadannan matakan karatu:

  • Masters (MSc)

  • Bachelors Degree (BSc)

  • HND

  • ND / NCE

Guraben Ayyukan Da Aka Bude:
Akwai guraben aiki da dama da za a iya nema, ciki har da:

  • GBV Officer / GBV Assistant

  • Legal Officer (Jami’in Shari’a)

  • GBV Caseworker / Child Protection Caseworker

  • MHPSS Assistant / CFS Facilitators

  • CFM Assistant

  • Psycho-Social Support (PSS) Workers

  • Grant and Partnership Officer

  • Protection Monitoring Assistants (Musamman a Kaga da Ngala)

Abubuwan Da Ake Bukata:

  1. Kasancewa da kwarewa a fannin aikin da kake nema (shekara 1 zuwa 8).

  2. Dole ka kasance kana zaune a Najeriya (an lissafa jihohi da dama a cikin fom din).

  3. Iya hulda da mutane cikin girmamawa da sanin ka’idojin kare hakkin kananan yara da matasa.

Yadda Za A Cike (Method of Application):
Idan kana da sha’awar wannan aiki kuma ka cika sharuddan da ake bukata, zaka iya cike fom din neman aikin kai tsaye ta wannan mahadar (link) dake kasa:

👉 Danna Nan Domin Cikewa: https://docs.google.com/forms/d/1wXji58f81Un0-s0qUXfmeF_uy3tmNlO57t1rZ9Gh8sk/viewform

Muhimmi:
Tabbatar ka hada takardar shaidar gogewarka (CV) da kuma takardar neman aiki (Cover Letter) a matsayin takarda guda daya ta PDF kafin ka fara cikewa, domin za a bukaci ka dora su (upload).

Kada ku bari wannan damar ta wuce ku. Ku hanzarta cike naku yanzu sannan ku raba wannan labari ga wasu domin su ma su amfana.


0 Response to "Gidauniyar CATAI Ta Bude Shafin Daukar Ma'aikata Masu ND/NCE, HND, Da Digiri Domin Aiki A Arewa (2026)"

Post a Comment