KADA KA YARDA WANNAN DAMAR TA WUCE KA: Gwamnatin Tarayya Ta Hanyar Bankin Aikin Gona (BOA) Ta Buɗe Rajistar Shirin Noma na Kasa (NAMP) Domin Tallafawa Matasa da Mata da Taraktoci da Kayan Aikin Noma
KADA KA YARDA WANNAN DAMAR TA WUCE KA: Gwamnatin Tarayya Ta Hanyar Bankin Aikin Gona (BOA) Ta Buɗe Rajistar Shirin Noma na Kasa (NAMP) Domin Tallafawa Matasa da Mata da Taraktoci da Kayan Aikin Noma
KADAKU YI WASA DA WANNAN DAMAR! SANARWA MAI MUHIMMANCI AKAN SHIRIN NOMA NA KASA (NAMP)
Kasancewar Dan Najeriya: Dole ne ku kasance ɗan Najeriya ko kuma kamfani mai rijista a Najeriya da ke aiki a fannin noma.Filin Noma: Dole ne ku mallaki ko ku samu damar amfani da filin noma mai faɗi (mafi ƙarancin hekta 350 idan mutum ne, ko hekta 500 idan kamfani ne, a cikin kewayen kilomita 50).Ƙwarewar Gudanarwa: Dole ne ku nuna kuna da ikon sarrafa kayan aikin noma.Tsarin Kasuwanci: Ku mallaki ingantaccen tsarin kasuwanci (business plan) da ke nuna yadda za ku bayar da sabis, farashi, da kuma yadda kuke tsammanin samun kuɗi.Ikon Kuɗi: Ku nuna kuna da isasshen kuɗi ko kuma ikon bayar da gudunmawar kuɗi don hayar kayan aikin.Kudirin Biya: Ku jajirce wajen biyan bashin da aka ƙayyade a ƙarƙashin tsarin Bankin Noma.Yarda da Kula da Na'urori: Ku yarda a sanya na'urar bin diddigi (digital tracking) don lura da aikin taraktocin.Rijistar Kasuwanci: Idan kamfani ne, dole ne ya kasance mai rijista a Najeriya (CAC certificate ko rijistar haɗin gwiwa).TIN: Ku mallaki Tax Identification Number (TIN).Tabbacin Kuɗi: Ku samar da bank statement ko wani tabbacin ikon biyan kuɗi.Horarwa: Ku yarda da shiga horo ga ma'aikatan taraktocin da masu karɓar kuɗi.
Taraktoci masu ƙarfi guda 2,000. Da sauran kayan aikin gona guda 9,000. Wadannan za a ba wa waɗanda suka cancanta domin tallafa musu su zama ƙwararrun manoma da 'yan kasuwa.
Ziyarci gidan yanar gizo na Bankin Aikin Gona a: 👉https://boanig.com/namp-application or boanig.com/namp Cika duk bayanan da ake buƙata cikin tsari da kyau. Tabbatar kun saka sahihan lambobin waya da adireshin imel.
0 Response to "KADA KA YARDA WANNAN DAMAR TA WUCE KA: Gwamnatin Tarayya Ta Hanyar Bankin Aikin Gona (BOA) Ta Buɗe Rajistar Shirin Noma na Kasa (NAMP) Domin Tallafawa Matasa da Mata da Taraktoci da Kayan Aikin Noma"
Post a Comment