-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Shirin TVET na Gwamnatin Tarayya: Tallafin ₦22,500 a Duk Wata - Abinda Zakuyi Idan Aka Rubuta Maku (‘Pending Approval’, ‘Approval Request’, ‘Approved’, ko ‘Rejected’) a Dashboard

Shirin TVET na Gwamnatin Tarayya: Tallafin ₦22,500 a Duk Wata - Abinda Zakuyi Idan Aka Rubuta Maku (‘Pending Approval’, ‘Approval Request’, ‘Approved’, ko ‘Rejected’) a Dashboard

Shirin TVET na Gwamnatin Tarayya: Tallafin ₦22,500 a Duk Wata - Abinda Zakuyi Idan Aka Rubuta Maku (‘Pending Approval’, ‘Approval Request’, ‘Approved’, ko ‘Rejected’) a Dashboard



Barka da zuwa HaskeNews.com.ng Muna son yin bayani dalla-dalla game da matsayin aikace-aikacenku na shirin TVET domin ku fahimci abin da kowane matsayi yake nufi da kuma abin da za ku yi tsammani a kowane mataki.

1. APPROVED:

Wannan shi ne matsayin da kowane mai neman shiga shirin TVET yake fata! Idan aikace-aikacenku ya nuna ‘APPROVED’, yana nufin an duba an kuma amince da aikace-aikacenku ɗari bisa ɗari. An saka ku a cikin jerin sunayen waɗanda za su ci gajiyar shirin TVET. Taya murna! Wannan yana nufin za ku shiga sahun waɗanda za a koya wa sana'a kuma za ku fara karɓar tallafin kuɗi na ₦22,500 a duk wata.

Abin da Zaku Yi:

  • Ku fara shiri domin horonku na TVET.

  • Aiwatar da koyo da samun sabbin fasahohi da za su taimaka wajen haɓaka kasuwancinku ko aikin ku.

2. PENDING APPROVAL:

Idan kuka ga ‘PENDING APPROVAL’ a dashboard ɗinku, yana nufin cewa a halin yanzu ana kan duba aikace-aikacenku. Ba a amince da ku ba tukuna a matsayin wanda za a ba wa horo, amma kuma ba a kore ku ba (ba a yi muku ‘rejected’ ba). Aikace-aikacenku yana cikin jiran yanke shawara daga hukumar shirin.

Abin da Zaku Yi:

  • Ku ci gaba da haƙuri kuma ku riƙa duba dashboard ɗinku lokaci-lokaci.

  • Idan an amince da ku, za ku samu matsayin ‘APPROVED’.

Shawara: Kar ku damu, idan da rabonku, za ku sami amincewa!

3. APPROVAL REQUEST:

Wannan matsayi na ‘APPROVAL REQUEST’ yana nuna cewa bayanan da ke kan dashboard ɗinku sun wuce matakin farko na tantancewa kuma an tura su zuwa mataki na gaba, inda za a ba da amincewar ƙarshe. Wannan yana nuna cewa hukumar shirin tana duba bayanan ku don tabbatar da komai yana daidai kafin su ba ku ‘approved’.

Abin da Zaku Yi:

  • Ku kasance da kyakkyawar fata kuma ku duba dashboard ɗinku lokaci-lokaci don ganin sabbin canje-canje.

  • Ku kasance cikin farin ciki, kashi 90% ko fiye na masu ‘Approval Request’ sun samu amincewa!

Shawara: Ku kasance cikin kwanciyar hankali, kuyi shirin zama cikin wadanda za su ci gajiyar shirin.

4. REJECTED:

Wannan shi ne matsayi mafi muni kuma yana nuna cewa ba a amince da ku ba a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda za su ci gajiyar shirin TVET, wato ba za ku sami tallafin ₦22,500 a duk wata ba. Abin takaici, aikace-aikacenku bai ci nasara ba a wannan karon.

Abin da Zaku Yi:

  • Kar ku yi ƙasa da gwiwa, akwai yiwuwar ku sake gwada aikace-aikacenku a cikin shiri na gaba.

  • Za ku iya duba matakan da aka ɗauka a cikin aikace-aikacenku don fahimtar inda aka samu matsala.

0 Response to "Shirin TVET na Gwamnatin Tarayya: Tallafin ₦22,500 a Duk Wata - Abinda Zakuyi Idan Aka Rubuta Maku (‘Pending Approval’, ‘Approval Request’, ‘Approved’, ko ‘Rejected’) a Dashboard"

Post a Comment