-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Shin kana daya daga cikin waɗanda suka cike shirin tallafin Gwamnatin Tarayya na TVET Initiative?

Shin kana daya daga cikin waɗanda suka cike shirin tallafin Gwamnatin Tarayya na TVET Initiative?

Shin kana daya daga cikin waɗanda suka cike shirin tallafin Gwamnatin Tarayya na TVET Initiative?

Idan haka ne, to akwai labari mai daɗi! Yana da kyau ku gaggauta duba matsayinku a shirin. A safiyar yau ne aka samu canjin matsayi ga dubban waɗanda suka cike shirin daga "Pending Approval" zuwa "Pending".

Shin kai ma matsayinka ya canza?

Shin kana cikin waɗanda nasu matsayi ya canza daga "Pending Approval" zuwa "Pending" ko ma daga "Pending Approval" zuwa "Approval"? Mu haɗu a sashin sharhi domin tattaunawa da musayar bayanai kan wannan ci gaban.

Fahimtar Shirin TVET Initiative

Yana da kyau mu sani cewa shirin tallafin Gwamnatin Tarayya na TVET Initiative, wani tallafi ne na musamman don horon sana'o'i da kasuwanci. Shirin ya haɗa da tallafin kuɗi na Naira 22,500 a kowane wata. Tsawon lokacin tallafin ya dogara ne da matakin takardar shaidar karatun da kuka yi amfani da ita wajen cikawa:

  • Idan da takardar shaidar sakandare ce: Zaku samu tallafin na tsawon watanni shida (6).

  • Idan kuma da takardar shaidar mataki na gaba da sakandare (Higher Qualification) ce: Zaku samu tallafin na tsawon shekara guda (12 months).

  • Zaku iya duba matsiyinku anan: https://www.tvet.education.gov.ng/

Muna fatan Allah ya sa mu dace baki ɗaya!


0 Response to "Shin kana daya daga cikin waɗanda suka cike shirin tallafin Gwamnatin Tarayya na TVET Initiative?"

Post a Comment