Sanarwar CDCFIB: An Fitar da Sunayen Waɗanda Za Su Rubuta Jarabawar CBT don Daukar Ma'aikata a Hukumomin Gidan Yari, Shige da Fice, Kashe Gobara da Civil Defence
An fitar da jerin sunayen waɗanda suka cancanci rubuta jarabawar kwamfuta (CBT) domin daukar sabbin ma'aikata a hukumomin tsaro a Najeriya. Hukumar Kula da Ayyukan Tsaron Farar Hula, Gidajen Gyaran Hali, Hukumar Kashe Gobara da Hukumar Shige da Fice (CDCFIB) ce ta fitar da sunayen.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren hukumar, Manjo Janar Abdulmalik Jubril (mai ritaya) ya fitar a Abuja ranar Laraba. Ya bayyana cewa hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Ƙasa, Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa, Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa da kuma Hukumar Tsaron Farar Hula (Civil Defence).
Sanarwar ta ce duk masu neman aikin su ziyarci shafin hukumar na intanet — https://recruitment.cdcfib.gov.ng — daga ranar Alhamis, 30 ga Oktoba, domin tantance sunayensu da kuma tabbatar da samun damar zuwa mataki na gaba.
Hukumar ta kuma gargadi masu neman aikin da su guji amfani da wasu shafukan bogi.
0 Response to "Sanarwar CDCFIB: An Fitar da Sunayen Waɗanda Za Su Rubuta Jarabawar CBT don Daukar Ma'aikata a Hukumomin Gidan Yari, Shige da Fice, Kashe Gobara da Civil Defence"
Post a Comment