Sharuɗɗan karbar bashi ba tare da riba ba (Non interest Loan) Na KASEDA - Hukumar Ci Gaban Kasuwanci ta Jihar Katsina
Sharuɗɗan karbar bashi ba tare da riba ba (Non interest Loan) Na KASEDA - Hukumar Ci Gaban Kasuwanci ta Jihar Katsina.
1. Dik wani mai karamar sana’a da masu manyan kasuwanci (MSMEs) suna iya nema.
2. Kasuwancin mutum ɗaya da aka yi wa rajista da CAC na iya nema, Mai Company na iya nema, banda ƙungiyar masu haɗin gwiwa ko makamantan su.
3. Mafi ƙarancin bashi (loan) shine ₦500,000 (Dubu dari biyar) kuma mafi girma shine ₦10,000,000 (Miliyan goma.
4. Akwai jinkirin biya na watanni 3 (moratorium) bayan mutum ya karba kudin da tsawon lokacin biya na watanni 36 (3 years).
5. Ba a buƙatar ka bada wani abu ko jingina (collateral) abinda ake buƙata kawai shine kasamu (ma’aikacin gwamnati daga mataki 8 ko sama da haka ko kasuwancin da aka yi wa rajista).
6. Wannan ba bashin ƙungiyar haɗin gwiwa bane daga gwamnati yake kai tsaye.
7. Idan mutum ya cika dika wani sharadi ana tura kuɗin kai tsaye zuwa asusun kasuwancin da ake anfani dashi.
8. Tsarin biyan kudin ana biya ne a kowane wata.
9. Biyan kuɗi zai fara bayan jinkirin biya na watanni 3 bayan mutum ya karba kudin
10. Dole ne wanda ya karba bashin ya biya a kowane wata ko kuma a yi amfani da GSI ta hanyar BVN ɗinsa don biya daga duk wani asusu da ke da alaƙa da BVN ɗinsa.
11. Kudin da aka samu yana karuwa idan ana biya a kan lokaci. Sanan mutum zaya iya sake nema kuma za a bashi fifiko na musamman da saurin yadda da nashi a nan gaba.
12. Da zarar ka biya cikin lokaci, za ka iya neman adadin da ya fi wanda aka ba ka da farko.
Thank you DG Dr Babangida Ruma
0 Response to "Sharuɗɗan karbar bashi ba tare da riba ba (Non interest Loan) Na KASEDA - Hukumar Ci Gaban Kasuwanci ta Jihar Katsina"
Post a Comment