Labari Mai Daɗi: An Buɗe Guraben Ayyuka a Kamfanin Fasahar Kiwon Lafiya na eHealth4everyone

An sake samun wata babbar dama ga masu neman aiki a Najeriya, musamman ma a fannin kiwon lafiya da fasahar zamani. Kamfanin eHealth4everyone ya sanar da buɗe shafinsa na ɗaukar sababbin ma'aikata a gurabe daban-daban.
eHealth4everyone wata babbar ƙungiya ce da ke aikin samar da fasahar kiwon lafiya ta zamani, wacce ta sadaukar da kanta don bunƙasa lafiyar al'umma a faɗin duniya. Sun yi imanin cewa idan aka inganta lafiya, to tabbas al'umma za ta sami ci gaba mai ɗorewa.
A bisa ga haka, eHealth4everyone sun sanar da buɗe shafin ɗaukar ma'aikata a sassa daban-daban domin bai wa masu cancanta dama su cike guraben aiki.
Guraben Ayyuka da ake Buƙata:
Ga jerin guraben ayyukan da ake da buƙata a halin yanzu:
Finance and Admin Intern (Masu Yi wa Kasa Hidima - NYSC)
IT Support Intern (Masu Yi wa Kasa Hidima - NYSC)
Business Development Executive
Public Health Engagement & Advocacy Officer
Executive Assistant
Database Management Assistant
Database Management Intern (Masu Yi wa Kasa Hidima - NYSC)
Software Quality Assurance & Testing Intern (Masu Yi wa Kasa Hidima - NYSC)
DevOps Intern (Masu Yi wa Kasa Hidima - NYSC)
Python Web (Django) Developer
Data Quality Assistant
Hanyar Neman Aiki (Method of Application):
Duk masu sha'awa kuma waɗanda suka cancanta, za su iya miƙa takardunsu ta hanyar shiga shafin intanet na eHealth4everyone a adireshin da ke ƙasa:
Adireshin Neman Aiki:
https://e4eapplication.paperform.co/?utm_source=MyJobMag
Ku danna wannan adireshin domin cike fom ɗin neman aiki kai tsaye.
Kada ku bari wannan babbar dama ta wuce ku. Muna muku fatan alheri
0 Response to "Labari Mai Daɗi: An Buɗe Guraben Ayyuka a Kamfanin Fasahar Kiwon Lafiya na eHealth4everyone"
Post a Comment