Akwai Albashi Mai Tsoka: Ga masu takardar shaidar kammala Sakandare (SSCE), Diploma, NCE, HND, BSc, BEd, BA, MSc, da Ph.D. An bude shafin daukar ma'aikata a Hukumar Green Concern for Development (GREENCODE)
Hukumar Green Concern for Development (GREENCODE) kungiya ce ta kasa da ke gudanar da ayyukan agaji da raya kasa a Najeriya, wacce take da gogewar sama da shekaru 10. Mun yi aiki tare da kungiyoyi na kasa da kasa (INGOs) da na cikin gida (NGOs) da dama wajen aiwatar da ayyukan da suka shafi al'umma kai tsaye.
Manufarmu ita ce mu ga al'ummomin karkara a Najeriya sun zama masu sanin ya kamata game da muhalli, inda aka kawar da talauci, kuma ake tabbatar da mutunta haƙƙoƙin dan adam. Muna aiki tare da talakawa, waɗanda aka ware, da kuma gwamnati don inganta kare muhalli da haƙƙin ɗan adam a cikin al'ummomin Najeriya, da nufin rage talauci ta hanyar ilimi, yada bayanai, bincike, horo, da ayyukan agaji na kai tsaye.
Muƙaman da ake Nema:
Ranar Buɗe Karɓar Takardun Neman Aiki: 8 ga Agusta, 2025
Ranar Rufe Karɓar Takardun Neman Aiki: 12 ga Agusta, 2025
Yadda Ake Neman Aikin:
Masu sha'awa kuma waɗanda suka cancanta su bi waɗannan matakai guda biyu:
Mataki na 1: Su cika fam ta wannan adireshin intanet:
https://docs.google.com/forms/d/e/1FAIpQLSeM8GcZ6GjycEbEZU2aXH21tMpTfsIStm3EY0H-ohNdqftgTg/viewform?usp=header
Mataki na 2: Su sauke (download) fom din cancanta na GREENCODE (GREENCODE competency form) daga nan:
https://docs.google.com/document/d/1Qlpw5iwqFJoV5gn3Pkd793-0GR7742to/edit?tab=t.0
Bayan an cika shi, sai a tura shi ta imel zuwa: hr@greencodeng.org kuma a sanya kwafi (copy) zuwa: greencodedata@gmail.com.
0 Response to "Akwai Albashi Mai Tsoka: Ga masu takardar shaidar kammala Sakandare (SSCE), Diploma, NCE, HND, BSc, BEd, BA, MSc, da Ph.D. An bude shafin daukar ma'aikata a Hukumar Green Concern for Development (GREENCODE)"
Post a Comment