-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Federal Civil Service Commission Ta Fidda Sunayen Wadanda Aka Yi Shortlisting – Ga Abin Da Ya Kamata Ka Yi

Federal Civil Service Commission Ta Fidda Sunayen Wadanda Aka Yi Shortlisting – Ga Abin Da Ya Kamata Ka Yi

FCSC TA FIDDA SUNAYEN WADANDA AKA YI SHORTLISTING – GA ABIN DA YA KAMATA KA YI

Assalamu alaikum. Idan ka/kin yi applying na aiki a Federal Civil Service Commission (FCSC), yanzu hukumar ta fitar da jerin sunayen wadanda aka yi shortlisting.

Matakin Da Ya Kamata Ka Dauka:

  1. Ka shiga wannan shafin:
    👉🏽 https://recruitment.fedcivilservice.gov.ng/login

  2. Ka saka email da kalmar sirri (password) don shiga.

  3. Idan ka manta da password, sai ka latsa "Forgot Password?" domin mayar da shi.

  4. Bayan ka shiga cikin account ɗinka, za ka ga form. Ka cike shi da kyau.

Tambayoyin da ke cikin Form ɗin sun haɗa da:

  • Kana da wani nakasa? (Do you have any disability?)

  • Zaɓi wurin da kake so ka rubuta jarabawar CBT

  • Idan kana da wasu karin digiri (degrees), ka saka su

Wanda aka zaba zai ci gaba da matakin jarabawa (CBT). Ka tabbata ka duba ka kuma cike form ɗin cikin lokaci.

Allah Ya ba da sa'a. Amin.

0 Response to "Federal Civil Service Commission Ta Fidda Sunayen Wadanda Aka Yi Shortlisting – Ga Abin Da Ya Kamata Ka Yi"

Post a Comment