Mujallar labarai ta Haskenews ta samu korafe-korafe masu yawa daga gare ku dangane da matsalolin da kuke fuskanta wajen cike-ciken neman aikin da ake yi a halin yanzu na Hukumar CDCFIB ta shekarar 2025. Wannan aiki ya haɗa da Hukumar Tsaro ta Civil Defence, Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, Hukumar Shige da Fice ta Kasa, Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Kasa, da kuma Hukumar Kula da Ayyukan Civil Defence, Gyaran Hali, Kashe Gobara, da Shige da Fice.Dangane da kokarin warware wadannan matsaloli, mun yanke shawarar rubuta wannan bayani don samar muku da matakai da hanyoyin da za ku bi domin samun nasarar yin rijista. Ku biyo mu mataki-mataki kamar yadda aka jero a kasa.
Mataki na 1: Tabbatar cewa kana da kyakkyawar hanyar sadarwa ta intanet (good internet connection).
Mataki na 2: Sauko (download) da manhajar bincike ta Chrome ko Edge. Idan kuwa kana da su, sai ka buɗe ɗaya daga cikinsu.
Mataki na 3: Danna wannan adireshin https://recruitment.cdcfib.gov.ng/application ko kuma ka kwafeshi (copy) ka liƙa (paste) a cikin manhajar binciken da aka ambata a sama.
Mataki na 4: Zaɓi ɗaya daga cikin sassan hukumomin da ke ƙarƙashin Ma'aikatar Cikin Gida da aka jero:
Hukumar Tsaro da Civil Defence ta Kasa (Nigeria Security & Civil Defence Corps)
Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (Federal Fire Service)
Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (Nigeria Immigration Service)
Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Kasa (Nigerian Correctional Service)
Hukumar Kula da Ayyukan Civil Defence, Gyaran Hali, Kashe Gobara, da Shige da Fice (Civil Defence, Correctional, Fire, and Immigration Services Board)
Muhimmin Gargadi: Kada ka zaɓi sassa da yawa, saboda kwamitin ɗaukar ma'aikata ya ce hakan na iya jawo a soke takararka.
Mataki na 5: Muhimmin lura. Kowane sashe daga cikin waɗannan da aka lissafa a sama yana da muƙamai daban-daban. Ka zaɓi muƙamin da kake so wanda kuma ya dace da takardun shaidar karatunka.
Mataki na 6: Shigar da bayanan tantancewa. Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) da lambar wayarka za su zama ID na musamman na neman aikinka.
Mataki na 7: Rubuta lambobin tabbatar da tsaro (security verification) kamar yadda aka umarta sannan ka danna 'Validate'. Jira na ɗan lokaci don ya tabbatar, sannan ka danna 'Next'.
Mataki na 8: Loda hoton fasfo ɗinka kuma ka tabbatar girmansa bai wuce 200kb ba. Bayan haka, ka shigar ko ka rubuta waɗannan bayanai. Galibi za ka ga an riga an rubuta su, don haka ka duba abin da ya rage kawai ka cike:
Bayanai na Kanka (Personal Information)
Bayanai na Hanyar Tuntuɓa (Contact Information)
Ƙarin Bayanai (Additional Information)
Bayanai na Loda Takardu (Upload Information)
Mataki na 9: Game da sashin 'Upload Information' (Loda Bayanai), anan ne kusan dukkan matsaloli da kurakurai suke faruwa wajen loda takardar shaidar shekaru (Age Identification) da takardar shaidar ƴan asalin jiha/ƙaramar hukuma (State of Origin/LGA Identification). Tabbatar cewa girman kowace takarda, walau ta PDF ko hoto, bai wuce 200kb ba.
Lura: A hukumance an rubuta 500kb, amma baya tafiya. Zaka iya rage girman takardunka ko hotunanka ta hanyar danna wannan adireshin: https://www.ilovepdf.com/compress_pdf
Mataki na 10: Shigar da tarihin karatunka, wanda ya haɗa da sunan makaranta, takardar shaidar da aka samu, fannin karatu, shekara, da sauran bayanai dangane da irin muƙamin da ka nema. Ga masu neman aiki da HND, Digiri, da PGD, dole ne ku shigar da lambar NYSC ɗinku. A ƙarshe, ka tabbatar matsayin cike-ciken (application status) ya nuna an TURA (SUBMITTED).
Muna godiya da kasancewarku tare da mu. Muna muku fatan alheri.
0 Response to "CDCFIB 2025 - An Samu Mafita: Hanyoyin Cike Aikin CDCFIB (Civil Defence, Immigration, da Sauransu) Ba Tare da Tangarɗa Ba"
Post a Comment