Yan Mata: Kada Ku Ji Kunyar Faɗin Soyayyarku ko Shawara Ga 'Yan Mata Kan Bayyana Soyayya
Kada ki ji kunyar gayawa saurayi kina son shi, 'yan mata. Wasu suna yawan cewa, kada ki kuskura ki gayawa saurayi kina son shi. To wannan ba shi da tushe.
Soyayya a zuciyar mace ai ba laifi ne. Idan kika ga namiji ya birge ki da ɗabi'unsa, da hankalinsa, ko halayyarsa, kuma kika ji kina son shi domin kina hango akwai alkhairai tare da shi, ba abin kunya ba ne. Ki fito ki gaya masa gaskiya. Amma ki tuna wannan, komai na iya faruwa idan kika bayyana ba tare da hankali ba.
Kafin ki bayyana masa, ki tabbatar kin fahimci hankalinsa. Ki duba mutuncinsa. Shin mutum ne mai tunani? Shin yana da girmama mata ko mutum ne mai wulaƙanci da girman kai? Shi idan kika bayyana masa, zai daraja kalaman ki, ko zai yi amfani da su wajen raina ki? Amma idan har kin tabbatar yana da kirki, mutum ne na gari kuma na ƙwarai, babu laifi ki furta kina son shi. Amma ki faɗi hakan da mutunci da ladabi saboda soyayya ta gaskiya ba ta da nauyi idan an ɗora ta a bisa hikima da dabara.
0 Response to "Yan Mata: Kada Ku Ji Kunyar Faɗin Soyayyarku ko Shawara Ga 'Yan Mata Kan Bayyana Soyayya"
Post a Comment