-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Sabbin Bayanai Kan Shirin NIYEEDEEP/YEIDEEP

Sabbin Bayanai Kan Shirin NIYEEDEEP/YEIDEEP

Sabbin Bayanai Kan Shirin NIYEEDEEP/YEIDEEP

Game da NIYEEDEEP ko YEIDEEP, da fatan za a cike a karkashin daya daga cikin sunayen.

Bayani akan shirin NIYEEDEEP / YEIDEEP

NIYEEDEEP da YEIDEEP abu daya ne. Sai dai sunan NIYEEDEEP ne aka fara amfani da shi, kafin daga baya a maida shi zuwa YEIDEEP. Tun da farko, wadanda suka cike a karkashin sunan NIYEEDEEP, bayan sun kammala cike-cike, an ba su lambar code kuma ana sa ran za su bude asusu a daya daga cikin wadannan bankuna masu zuwa:

FEDILITY

KYSTONE

LOTUS

Daga baya, bayan an canza sunan zuwa YEIDEEP, an kara wasu bankuna, inda adadinsu ya karu daga 3 zuwa 12. Akwai wadanda a baya sun bude asusu ta intanet amma ba su ga asusun ba nan take. Wannan ba matsala ba ce, za ku ga asusunku. Wasu daga cikinku kuma na sani sun riga sun gani yanzu. Har zuwa yanzu, akwai kusan mutum dubu dari tara da suka rage waɗanda har yanzu suke da damar cika wannan shirin kafin a rufe shi gaba daya.

Duk wanda ya cike a yanzu ko wanda aka cike masa, ya jira. In sha Allahu za a bude masa asusunsa kuma za a tura masa abin da ya shafa. Lambar wayar da ka yi rajista da ita tana da muhimmanci a wannan tsarin. Ka kula da asusunka sosai saboda ana iya nemanka domin ka ba da shi.

Jimillar mutum miliyan shida ne za su amfana daga wannan shiri, a cikin maza da matan da suka nemi cikawa. Kuma ana sa ran nan ba da jimawa ba, in sha Allahu, za su fara amfana. Yanzu haka, sama da mutum miliyan biyar da dubu dari ne zuwa yau da dare suka sami damar cikawa. Har yanzu ana karbar takardun neman cikawa, amma cikawa ba ta tafiya yadda ake so sai dai idan an sami sa'a musamman a cikin dare. Wanda bai cike ba, ya garzaya ya cike. Wanda ya riga ya cike, ya roki Allah Ya sa ya dace.

0 Response to "Sabbin Bayanai Kan Shirin NIYEEDEEP/YEIDEEP"

Post a Comment