
Ma’aikatar Sadarwa, Kirkire-Kirkire da Tattalin Arzikin Dijital ta Buɗe Shafin Tallafi/ Horaswa ga Matasan Najeriya
Ma’aikatar Sadarwa, Kirkire-Kirkire da Tattalin Arzikin Dijital ta Buɗe Shafin Tallafi/ Horaswa ga Matasan Najeriya
Ana sanar da jama’a cewa Ma’aikatar Sadarwa, Kirkire-Kirkire da Tattalin Arzikin Dijital ta Tarayyar Najeriya tana gayyatar jama'a masu sha'awa don shiga cikin wannan dama mai muhimmanci da aka buɗe don ci gaban ƙasa ta hanyar fasaha da kirkire-kirkire.
An kafa wannan ma’aikata ne domin ƙarfafa tattalin arzikin Najeriya ta hanyar amfani da fasahar sadarwa da kirkire-kirkire. Ma’aikatar tana da manufar ƙarfafa amfani da fasaha da faɗaɗa damammaki a kowane fanni na rayuwa, samar da ayyukan yi, da kuma inganta shugabanci na gari.
Wannan dama ce ga matasa da sauran jama'a masu sha'awar shiga fagen fasaha da ci gaban dijital. Idan kana da buri da kwarewa a fannin ICT, kirkire-kirkire, ko kuma kana da sha'awar ci gaba a fannin tattalin arzikin zamani, to, wannan dama ce a gare ka.
Domin ƙarin bayani da yadda ake nema, ziyarci shafin yanar gizon
- www.fmcide.gov.ng Ko https://fmcide.gov.ng/about/
- Aiko da saƙon imel zuwa: info@fmcide.gov.ng
Yadda Zaku Cike
Ranar Rufewa - Application Deadline: 14th May 2025
Kar ka bari a ba ka labari! Ka kasance cikin masu gina sabuwar Najeriya ta dijital.
0 Response to "Ma’aikatar Sadarwa, Kirkire-Kirkire da Tattalin Arzikin Dijital ta Buɗe Shafin Tallafi/ Horaswa ga Matasan Najeriya"
Post a Comment