
Damar Aiki ga Matasan Najeriya: ZOA International ta Bude Shafin Daukar Sabbin Ma'ikata
Friday, May 9, 2025
1 Comment
Damar Aiki ga Matasan Najeriya: ZOA International ta Bude Shafin Daukar Sabbin Ma'ikata
Game da ZOA International
ZOA ƙungiya ce ta ƙasa da ƙasa wadda ke bayar da agaji da tallafi ga mutane masu rauni da suka tsinci kansu cikin rikice-rikice na tashin hankali ko bala’o’i irin su ambaliya, yaƙe-yaƙe, da fari. A yankuna masu ƙalubale, ma’aikatan ZOA suna tallafawa kai tsaye waɗanda rikici ko bala'i ya raba da muhallansu.
Ayyukan da ake buƙata
- Disaster Preparedness (DP) Specialist – Sokoto
- Disaster Preparedness (DP) Officer
- Disaster Preparedness (DP) Specialist – Borno
- MEAL Coordinator
- Disaster Preparedness (DP) Assistant
- MEAL Officer
- Logistics / IT Officer
- Finance Officer
- Accountability Officer – Borno
Yadda za a Aiwatar da Neman Aikin
Duk wanda ya cancanta kuma ke da sha’awa ya tura takardar CV dinsa zuwa: recruitment.nigeria@zoa.ngo yana saka sunan aikin da yake nema a matsayin taken imel (subject).
Lura:
- ZOA na aiki da manufar daidaito da rashin wariya wajen daukar ma’aikata.
- Mata, nakasassu (masu larura ta musamman), da masu asalinsu daban-daban ana karfafa musu gwiwa su nemi aikin.
- CV bai kamata ya wuce shafi 3 ba.
- A hada da sunayen mutane uku masu bada shaida daga wuraren da aka taba aiki a baya (shaidar kada ta wuce shekaru 5).
- Za a gudanar da bincike kan bayanan da aka bayar (background checks) da kuma tuntubar tsoffin masu aiki da ku (reference checks), musamman dangane da halayenku da riƙon amanarku, ciki har da batun rashin da’a (misconduct).
- Za a nemi tsoffin masu aiki da ku su cike takardar “Bayani kan Hali” (Statement of Conduct) dangane da batun rashin da’a (misconduct), kamar cin zarafi na jima’i, ko gallazawa.
Ku yi amfani da wannan damar domin zama cikin ƙungiyar da ke kawo sauyi ga rayuwar mutane. Kada ku jinkirta – ku nemi aikin yanzu!
We are grateful for your service
ReplyDelete