-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

YADDA AKE ZAMA DA TALAKAN MIJI

YADDA AKE ZAMA DA TALAKAN MIJI

YADDA AKE ZAMA DA TALAKAN MIJI.

Da farko akwai abinda ya kamata mata su lura a Zamantakewar auratayya. Idan mijinki yana talaka Yanada kyau kiyi Kokarin saka masa farin ciki a kullun ta yadda wannan halin bazai bayyana gareshi ko shiyi tasiri a gareshi ba. Ta dalilin wannan kyakkyawar kulawa da kike bashi kullun shi zai sa ya manta duk wata damuwa dayake cikin ta Kuma hakan zai kara ma alakar aurenku karfi sosai.


Idan kinada miji talaka abunda yafi dacewa dake ki kula da kayansa Na sakawa irin yadda idan ya shiga Mutane baza a kyamace shiba hakan zai kara saka shi farin ciki a rayuwa. Idan ya kasance yana zuwa Aikin kwadago akasari masu zuwa aikin kwadago zaka ga suna bada kayan abincin gobe tun kafin Safiya ta waye Safiya na wayewa idan ya fita kwadago kiyi kokari idan ya dawo ya tarar da abinci a gida daga nan kin Samu kanshi. Haka Kuma idan mijin naki ya kasa yimiki wani Abin lalura kamar rashin saya miki wani abu sai kiyi hakuri ki Kuma kai zuciya nesa ki dauka cewa idan Yanada hali zai saya miki. Idan wata rana Allah yabashi arziki ke zai kokarin yaga kinji dadi kamin duk wani ya more ma Samun sa.


Haka Kuma idan Allah yabashi Wasu kudi a wajen neman sa da ya fita na wannan wunin in sunada zumullah zaki iya amsar wani Abu daga gareshi Domin ki fara naki irin naki kasuwanci Na cikin gida irin wanda mata ke yi masu karamin karfi kamar su kosai, wara, kunun zaki, dankali, gasa masara, dadai sauransu. Hakan zai kara Taimaka muku ta fannin cefane da sayen Wasu kayan lalurar gida kamar su: Alanyahu, magi, gishiri, sabulu, omo, mai gyada, mai ja na girki dadai sauransu. Wata rana magidanci zai iya tashi babu lafiya a jikinsa Kuma akasarin talakawa basu cika ajema Kansu abinci isasshe a gida ba kullun sai sun fita nema sannan su kawo aci. A shawarce idan mijinki yana baki kudi kada ki saka su acikin kasuwanci ki kadai, kiyi Kokarin tanadin wani Abinci kina ajiyewa ba tare da sanin wannan talakan mijin naki ba idan wata rana ya tashi ba lafiya zaki dauko wannan ajiyar Da kikayi ba tare da saninsa ba sai ki gyara shi ki Dora girki Kina gama girki sai ki zuba masa ki kai masa Acikin wannan halin na jinya da yake ciki baki San kalar jin dadin da zaiji ba tare da hamdalah da ajiyar zuciya tare da saka miki albarka. Wannan zaisa shikara kaunar ki yaji duk duniya baida mai iya rufa masa asiri kamar ki sannan zaki koya ma 'Yayan ki mata training(Horo) Na daban idan sun Samu Kansu Acikin gidan talaka irin Baban nasu zasu koyi wannan Halayyar irin taki a Matsayinki na mahaifiyar su. Shiyasa ake son uwa ta kasance mai halin kirki a Mu'amala ta auratayya Tsakaninta da Mijinta hakan nada Matukar tasiri zuwa ga yaranta.


Sannan Kuma bugu da kari zaka samu matar talaka bata cika samun sukuni Acikin dangi ba ko makwafta musamman idan akwai wani buki wanda zai gudana, zaka ga tana shiga damuwa kamin lokacin bukin yazo. A Matsayinki na matar talaka abinda yafi dacewa gareki shine kisaka hakuri gaba sannan sutura da kike da ita mai kyau kiyi kokari ki zama mai Adana ta kisamu Wasu kaya wadanda zakiyi Aikin gida dasu irin yadda ba sai kinyi amfani da wadancen masu kyau ba sai ki Adana su duk wani bukin aure ko suna sai ki wanke su tare da goge su ki saka kije bukin suna da abinki. Idan kika fake wannan zaki saukaka ma mijinki a Bangaren lalura ta yau da kullun Kuma zai kara miki kima daga gareshi hakan zaisa diyanki su koyi Tsafta da tanadi irin Wanda kika jima kinayi a gidansu.


Idan mace kina auren talakan miji idan Har yana Samun tausayawa daga gareki bazaiji dadin kulla wata alaka da wata ba koda ya Samu wata yalwa ta arziki daga baya bazai ji yanason kara aure ba kasancewar jin tsoron kada ya hadu da wacce batada hali irin naki.


A Matsayinki na mace mai auren talakan miji kada ki bari ki baiwa Mutane dama ta ci miki fuska ko su nuna bukatar su gareki tafi ta mijinki Muhimmanci. Da dama matan da mazajen su basuda hali zaka gansu a gidajen masu hali suna Aikin shara, wanke-wanke, wankin matan gida da guga wani lokacin ma hadda girki, to idan hakan ta faru kada kibari kibasu damar yimiki Wasu maganganu na nuna kasawar mijinki ko Kuma su nuna miki biyar umurninsu yafi kibi umurnin mijin naki hakan zai iya janyo mutuwar aurenki sannan baki San wane miji zaki tarar ba idan kin sake yin wani aure Kuma zaki bar 'Yayanki cikin wani hali kila ma tarbiyar su ta lalace kasancewar bakinan a gidan wannan mahaifin nasu. Idan Kuma kinada tunani kinsan cewa idan mace Na tare da diyanta Acikin gidan Mijinta rayuwar wadannan yaran nata sai tafi daraja.


Shi zaman hakuri da namiji talaka ga diya mace zai kara ma diyanta kima da daraja kasancewar duk Wanda zaiyi aure a kowane gida yana Duba da Halayyar uwar yarinya shiga ya take rayuwata a gidan Mijinta daga nan zaka gane cewa idan Har wannan itace uwar yarinyar da kake nema babu shakka itama wannan yarinyar zata biyo Halayyar mahaifiyar ta. Akwai abubuwan Da ke zama riba ga mace mai hakuri a gidan talakan miji kamar haka: karama kanta kima ga Mutane, nemawa diyanta daraja, bata amana da Karin yabon halayenta dadai sauran su.


Halayyar kirki ga mace mai auren talakan miji Yanada Matukar Muhimmanci zuwa gareta Domin koda Allah ya jarabeta da mutuwar Mijinta zata iya Samun wani Bawan Allah yazo nemanta Domin ya aureta sabida Yanada yakinin cewa ko ya aureta shima bazaiyi kasa a guiwa ba ta dalilin Halayyar da aka shede ta da ita ta kirki. Haka Kuma Wasu mazaje idan zasu nemi Karin aure suna haduwa da kalubale daga wajen iyayen su mata amma idan iyayen suka Samu tabbacin cewa wacce zaka aura tanada hakurin zaman aure to zasu Baka dama cikin sauki ba tare da ka wahala ba kayi aurenka cikin salama musamman ma idan matar da Dan nasu yake aure batada halaye masu kyau irin Na wannan matar mai hakurin zaman gidan miji wacce mijin nata ya rasu.


Daga karshe mace mai auren talakan miji idan ta saka hakurin zama Dashi a zuciya daya tana ribatar rayuwa mai kyau a duniya Kuma Har a lahirar ta zata zama Abin misali ko a gidan Mijinta, gidansu, makwafta Dadai sauransu

0 Response to "YADDA AKE ZAMA DA TALAKAN MIJI"

Post a Comment