-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

2025 Kalaman Soyayya Masu Dadi

2025 Kalaman Soyayya Masu Dadi

2025 Kalaman Soyayya Masu Dadi 



Masoyiyata kin taka matakin da babu wacce mace da zata takala Domin ta cimmiki Acikin zuciya ta ke tamkar fadama ce Acikin zuciyata koda banyi amfani da ita wajen saka kayan lambu ba to Zan iya amfani da ita Domin in kwashe yan uwa da abokan arziki muje musha sanyi mai Ni'ima acikinta. Babu dare babu rana akan kalu balen da nake gani a wajen masoya masu son shiga soyayyar ki amma kin kasa basu dama su shiga cikin zuciyar ki. Wannan dalilin yasa suke bina da bakar yadiya domin su cimma mummunar manufa akaina. Masoyiyata nayi ta mujadala da duk wata cuta wacce zata iso gareki Domin ta hanaki samun sukuni hakan yasa na fara jayayya da mujadala da kowace cuta dake duniya domin lafiyar jikin ki ta tsayu akan ki. Na zama tamkar wani wawa, lusari, maras kan gado akan tasirin da soyayyar ki tayi Acikin birnin fadar zuciya ta. Kowace fadar sarki tanada nata fadawa amma ke fadar ki ni kadai ne nake so in kasance wazirinta, in kasance Dan galadiman ta, in kasance limamin fadar ta, in kasance Dan malikin ta, in kasance sarkin dogaranta, in kasance jakadanta, in kasance sarkin yakin ta, in kasance maji dadinta, in kasance Dan masaninta, in kasance Zarummai nata, in kasance talban ta, in kasance sarkin kofar ta, in kasance magajin masarautar ki, in kasance Dan madamin ta, in kasance garkuwanta, in kasance dallatu a fadarki, in kasance sarkin noman fadar ki haka Kuma in zama yarima a wannan babbar fadar taki kasancewar baniso kowa ya Kusanci wannan masarautar taki mai dinbin daraja da alkibla mai kyau tare da mutunta soyayayya da kauna Hadi da amana yake sarauniya ta mai haskaka kirjina ta sanyaya kalbin zuciya ta kece rayuwa ta Kuma ke ce bugun kirjina da saukar kirjina. Ban iya misalta miki soyayyar da nake miki a rayuwata Domin idan zanyi miki wannan misalin tamkar fitar rayuwa zai kasance agareni ban iya so ba Domin zaucewa nikai Kuma Har abin ya wuce misali wani lokacin idan na fita hira cikin abokaina sai sunyimin magana cikin tsawa sannan hankalina ya dawo gareni Kuma bazasu tambayeni dalilin yin hakan ba Domin sun Riga da sun kece Silar maidani haka sabida tsananin soyayya da kauna da nake miki. Kunnuwa na sun dakatar da jin kowane sauti na cikin duniya sai sautin kyakkyawar muryar ki mai zakin gaske Hadi da shauki na rayuwa. Ko rana ta fito Garin Allah ya Waye bazan iya tadda kaina in Fahimci halitta da duniya in gane minene ba kasancewar idanuwa ne kyakkyawar fuskar ki Kawai suke da muradin gani a koda yaushe. Kwakwalwa ta batada wani tunani Wanda take ko Kuma wani karatun da zata iya haddacewa face karatun da ta dauka daga gareki na soyayya da lobayya yake tauraruwar da ke haska duniya Domin duk wani mai soyayya da kauna zuwa ga masoyi ko masoyiya su more mata. Babu wani tazara guda dake motsi acikin birni da babbar jahar zuciya ta Domin soyayyar ki da kauna sun riga sun mamaye ta. Soyayyar ki acikin zuciya ta tamkar wata inuwace mai dauke da sanyi da lambu tare da yayan lambu masu dandano na zaki a zuciyata da kalbina. Babu wani yanayin sanyi ko zafi ko na ruwan damana da zai shigo a duniya in Fahimci lalle ga yanayin da muke ciki sabida son da nake yimiki da kaunar da nake miki sun mamaye duk wani tunani na da Wasu sassan jikina dake hade da kwakwalwa ta yayimin babbar illar da bazan iya gane kowane yanayi ake ciki ba. A gidanmu suna gayamin kowane lokaci na dare idan na kwanta sai inyi ta sambatu tare da dariya acikin kwanan da nakeyi ina ta kiran Kalmar sunanki ina murmushi ina dariya ina kaura kaina ga bangon dakinmu wannan ya samo asali ne domin tasirin da soyayyar ki tayi a gareni. Duk wani bangon dake jikina banga wanda baida kusurwar soyayyar ki acikinsa ba kasancewar gangar duk wata jikina da ruhina sun samu shedar soyayya da kaunar ki sun Riga sunyi cinkoso da turnuke duk wata kusurwa dake da amfani mai juyawa a kullun safe da dare. Babu wata halitta a duniya wacce bata Fahimci soyayya da kaunar dake tsakaninmu dake ba ke hatta da namun daji sun shaida cewa ni dake masoya juna muke Kuma na amana wadanda bazasu taba rabuwa tsakaninsu ba Har karshen rayuwar su wannan dalilin yasa duk wani kwaron daji ya ganni zaiyi Kokarin isowa ta wurina ba tare da ya cutar daniba Domin yasamu sirrin soyayya ta amana wadda yaga muna gudanarwa ni dake Domin yaje ya cimma sauran namun dawa ya koyar dasu Minene ake cema so da amana da kaunar juna a Tsakanin namiji da mace. Hankalin da kike Dashi da tunaninki tare da kulawar ki shiyasa kike da mutunci a idanun juma'a Domin suma susamu amincewar ki don Samun kwanciyar Hankali a soyayya da kauna.


Na wayi gari da zazzabin cutar rashinki a kusa dani Kuma naje shagon magani Domin a auna ni akace in wuce asibiti Domin wannan ba karamar matsala bace nan take na isa asibiti Domin Neman lafiya ta haka aka fara gwadani da injimin awon hawan jini likata ya gane ba wannan matsalar hawan jini bace, aka kwashe ni aka kaini wajen gwaje_gwaje saida aka fara yimin awon maleriya Ashe ba ita bace, aka kaini wajen awon shawara aka gano Kuma ba ita bace, akayimin awon ciwon suga Kuma ba wannan matsalar bace, aka yimin ciwon cuta mai karya garkuwar jiki Kuma ba'a gano komiba aka kaini aka yimin gwajin ciwon hanta haka Kuma ba'a daceba don ankasa gano minene matsalar daga baya likitan yayi hoto ya gano cewa lalle wannan ciwon Yanada bukatar ayi hoto, hakan na faruwa sai ya gano cewa duk wata kussuwa dake amfani ga zuciya ta Riga ta rufe nan take ya kira Mutanen da Nike Mu'amala dasu ya nemi ya San sunanki yana Samun sunanki Kawai ya iso a dakin jinya ta yana kiran sunanki nan take na tashi nayi watsi da zanen gado nayi hamdala ga Ubangiji mahalicci Domin ni na San na Samu lafiya ido rufe. Zanyi yekuwa tare da afkawa Acikin sansanin daji domin daukar sonki ta rikitamin lissafi tare da juya kwakwalwa ta banida wani tunani Wanda nake Dashi face tunaninki haka Kuma banida wata alkibla wadda na fuskanta daga yanzu Har karshen rayuwa ta face alkiblar ki yake masoyiyata abar kaunata wadda babu wata ya mace wadda take kusa dani a Yankin kirjin zuciya ta. Kowace diya mace ana iya tsayawa a bayyana halittar surar jikinta amma ke an kasa Samun mai iya bayyanawa Mutane surar cikin jikin ki kasancewar ke macece mai kyauwun da ba'a iya masaltashi Dana mutane, munyi ta binciken yadda za'ayi acikin nahiyar duniya asamu irinki Amma an kasa. An gano yadda za'ayi a magance matsalolin Nigeria an kasa gane minene matsalar dake damuna Kuma kowa ya kasa gane minene mafarin shigata damuwa. Ya ke masoyiyata alkawalin Mu dake ki rike Domin soyayyar ki da kauna itace ta hadamu Kuma zaiyi wuya a rabamu Domin sonki nake babu wai a wannan soyayyar. Za'a wayi gari kiga munyi aure idan da rabo mufe da kyaure, soyayya ita ta hadamu ko mutuwa bazata rabamu ba zamu rayuwa cikin inuwa daya Domin ita soyayyar Mu batada farashi. Kin zama farar mace mai farar zuciya kowa na ta nuna yanason farar mace ni Kuma babu yadda zanyi in sallamar da soyayyar ki sabida muhimamncin ki a wurina. Farar mace irinki sa'a ce Kuma Samun ki babbar riba ce. Lalle nayi fice acikin maza wadanda sukayi Saar rayuwa a doron duniya. Na shirya aika sakonnin so zuwa gareki Kuma alfarmar da nakeso daga gareki ki karbamin wannan sakon. A sonki na tunzura Kuma na gagara na yunkara dake nake hari, babu irinki a idona babu irinki a bayana da sonki nake kwana a zuciya. Sonki na zan nine na daya sonki nake bana gajiya, dani dake mun zama Abin misali a soyayya. Yadda kike sona ina sonki muradina ina fada miki naji soyayyar ki a kirjina ya masoyiyata. Amana soyayyar ki akwai dadi Domin abani ita yafi abani kudi yadda kike mini Nima zan miki kigane kinyi matsayi acikin zuciya ta. Ga sakon soyayya ki rike mini Domin ke kadaice zaki iya rike mini shi amana tare da karrama wannan sakon bisa ga amana. Ga zoben soyayya na zinari zan baki ki saka a wannan kyakkyawan hannunki Domin banison rabuwa dake yake farin cikin zuciya ta muradin duka ruhin rayuwata da matsayina. Duk abinda nake Dashi zan iya mallaka miki shi. Dagaske kaunarki nake, sai ambato naki nake ko baki nan zan shiga kewa dake nakeson mukasance. Da nayi kira zaki zo baki ma Jira na ke kike zuwa can ki tsaya. Tun lokacin da kina karama nine ke yimiki rakiya zuwa gida. Abinda zaisa inbarki a rayuwa babu shi a fadin duniya abinda kikamin a rayuwa baya misaltuwa ko ba gareniba ga kowa a fadin duniya. Duk wata danger ta wuta zan iya taka ta inyi tsaye Har sai ta zama gawayi ina samanta akan soyayyar da nake miki yake shibata kizo ki matso kusa dani Domin kici abincin so, tuwon so, shinkafar so, taliyar so, naman shanu na so, naman rago na so, naman kifi na so daga karshe kisha ruwan soyayya kije kiyi gyasa a wurin masoya Domin ki kara firgita su su dauki babban mataki na maida Hankali wajen nuna soyayya a tsakanin su. Na sakama zuciyata hijabin da babu wata diya mace wacce zata iya ganinta Domin ta yunkuro ta kawomin ziyara Har inji zan iya saka soyayyar wata a zuciyata bayan taki soyayya subhanallahi! Har naji na fada wani irin mugun kogon da ban iya fita acikinshi Domin na fadi Kalmar da bamu iya jurewa daga ni Har ke Domin tamkar daukar rayuwa take ga Dan Adam sabida babu yadda za'ayi inji zan iya hada soyayyar wata diya mace da ta

ki

0 Response to "2025 Kalaman Soyayya Masu Dadi"

Post a Comment