YANDA ZAKI ZAUNA DA KISHIYA
YANDA ZAKI ZAUNA DA KISHIYA
Kishiya ba wata abar tashin hankali bace ya danganta da yanda kika sama ranki.
Zaman yanada dadi idan kishiyar ba tada hayaniya, tasan kanta Kuma ta tsaya a matsayinta.
Kuma zaman zaiyi dadi idan har wanda yake mallakarku yana kwatanta adalci tsakaninku, idan akwai wannan toh zaman zai danyi ma'ana.
Kishiya ai abokiyar zama ce indai akwai fahimta, idan kinda kishiya mai fahimta Kuma mai qudutin kwarai a ranta abubuwa zasu rinqa zo muku da sauqi ta yanda bakwa tsammani.
A dauki misalin aikace aikace na gida, idan da kishiya zakiji sauqinsu, sannan ko fita ta kama akwai inda zaki bar yaranki cikin gidan mahaifinsu batareda kinje dasu Wani wajen ba, indai akwai zaman lafiya bama ki daga hankalinki ba akan yaranki na wurin abokiyar zamanki.
Akwai lokutanda wasu basa ma gane aii wannan ga yaranta wannan ga yaranta idan aka samu amintaccen zama.
Shi dai kishi Halal ne, Allah y halattaci ga bayinsa kowane jinsi. Amma kishi na hankali da sanin ya kamata, ba na hauka da tada tarzoma ba .
Kishiyarda bata da nifin alkhiri ba Allah a ranta wannan zama da ita akwai wahala, saboda a ko yaushe kana Jin tsoron ta inda zata bullo domin cutarda Kai.
Hakan iya zama d ita sai an Kai zuciyar mesa.
Na farko sai kin riqe Addu'a, domin addu'a makamin duk Wani mai imani ce.
Sannan Abu na biyu ki riqe gaskiua a duk lamurranki.
Abu na uku ki zama mai taka tsan tsan ga lamurran da ya shafeta.
Abu na hudu kiyi biyayya ga mijinki gwargwadon iko muddin shi baya cutarda ke .
Abu na qarshe ki riqe girman ki, ki kama mutuncinki da na yaranki.
Amma Jan kunne a nan komai haqurin ki a nawa tunani kada ki juri walaqanci a wurin kishiya, ki zama mai iya tsaya ma kanta.
Kishi ba hauka bane, kishiya ba aljana bace, mutunce kamaar kowa, aurenta akayi kamar yanda aka aureki, kisani wataqila gidanku ba mahaifiyarki kawai bace, ki tuna kina haihuwa Kuma watarana inda rabo zaki aurarda 'ya, idan aka kaita hannun kishiya ki tuna da abinda kama Wani kaima sai anyi maka. Itama 'yar wasu ce, yanda kike 'yar su ba tsintota aka yi ba.
Ki kwantarda hankalinki kiyi Ibada, ki samu lada Kuma ki rabauta a duniya da lahira.
0 Response to "YANDA ZAKI ZAUNA DA KISHIYA"
Post a Comment