-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Auren Miji dan Kasauwa - Zaman Auren

Auren Miji dan Kasauwa - Zaman Auren

Auren Miji dan Kasauwa - Zaman Auren

 Shi dai miji dan kasuwa ana nifin mai saye da sayarwa. Miji dan kasuwa mutun ne wanda kullun Yana fita wurin sana'arshi Kuma kullun din yanada lokacin dawowarsa gida.

Miji dan kasuwa mutun ne wanda kudi na iya shigo shi kowane lokaci, saboda sana'arsa ta saye da sayarwa.

Macen da take aure da miji dan kasuwa, ya kamata ta san wasu abubuwa ta yanda zasu ji dadin zama.

Na farko, shi miji dan kasuwa y kamata mace tasan Kuma tasa aranta da samunshi ba kullun bane saboda yanayi na kasuwa.

Kada miji a tambayeshi wani abu yace Babu ki kama tunzuri ko fushi, malama abin ba haka yake ba , kiyi haquri saboda Babun ba kullun take ba, bakisan shi irin yanayinda yake ciki ba akan Bai samu ba, shima haquri yakeyi, amma kin tada hayaniya sai ki qara sa mijinki cikin Wani yanayi, inji hausawa sukace, Rana zafi, inwa quna, shi baiji dadin kasuwa ba, Kuma y zo gda baiji dadi ba.

Mijin yace yau ba kasuwa, ba'a samun Abu kaza, sai kice tau, Allah y sauwaqa yasa da rabo nan gaba.

 Abu na biyu mace tasan idan bata tausayin mijinta ga harkar nemansa, to ranarda ya samu bazata ganeba, zai ta barinta taci gaba da tunanin ai babun ne, kiyi haquri ki lallashhi mijinki, shi namiji dan lallashhi ne.

 Abu na uku, ya kamata mace ta riqe lokacin fitar mijinta da dawowarsa domin ta shirya ma hakan.

Ki shirya ma mijinki kafin ya fita yaci abinci, yyi wanka, idan Maison zuwa da abinci ne ki hada masa sannan ki bishi da addu'ar tsari, kariya da Kuma kasuwa mai albarka.

Sanna idan zai dawo ma a shirya mashi, a tarbeshi a bashi kula mai kyau bakin gwargwado.

 Sannan abu na qarshe, maza suji tsoron Allah, idan sun samu su kyautatawa matansu, idan babu su basu haquri.

Anyiwa en kasuwa shaidar maqo, wanda hakan ba dadi, ya kamata iyalinka so Mori samunka, bawai Kai kadai ke morarsa ba.

0 Response to "Auren Miji dan Kasauwa - Zaman Auren"

Post a Comment